Sashe 71
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A bakin Anty Zulaihatu nake jin cewa wai Saifullah da Muhammad Taufik sun zo sun taya Yaya Alhassan murna har ma da kawo gudumawa a Anty Sawwama da ta kasance uwar amarya kuma uwar ango. Ranar da za a kai ni tare muka wuni da Anty Zulaihatu da kuma Amira ranar mun sha kuka sosai har sai idanuna suka kumbura har ya kai jallin da ba na iya buɗe su. Gidan a cike yake da mutane maƙota, ƴan uwa da kuma abokan azurki. Dangin mahaifin su Yaya Alhassan ba su nuna mini tsana ko ƙyama ba sai ma ja na a jiki da suke yi da yi wa iyayen addu'ar samun rahamar Ubangiji.
Ban gaskata cewar da gaske an ɗaura mini aure ba sai da aka fito ni aka saka ni a cikin mota domin kai ni ɗakin miji, tun da motar ta soma tafiya ƙirjina yake dakan lugudai taka birkin da aka yi ya yi daidai da lokacin da hawaye suka zubo daga idanuna sai dai mayafin aka rufe mini fuskana da shi ya hana mutane fahimtar kuka nake yi, haka aka fito da ni daga cikin motar aka shigar da ni cikin gidan. Bayan wata dattijuwar mata ta yi mini umarnin na shiga da ƙafar dama tare da addu'ar Allah ya sa na shiga ke nan sai dai a fito da gawa ba.
Anty Zulaihatu ne ta kai ni har cikin ɗakin miji ta kuma jira har aka yi rakiyar ango ta damƙa amanata a hannun Yaya Alhassan tare da yi nasihar idan ya cutar da ni ko ya wulaƙata ni, to ba ni ya wulaƙanta ba kansa ya tozarta. Haka suka tafi suka bar ni ni ɗaya ƙwal don na kai ga roƙon Amira ta kwana murzawa idanunta toka ta yi, da na matsa mata sai ce wa da ni ta yi to ita kuma na ta mijin ta yi ya ya da shi? Haka ina ji ina gani duk aka watsa aka bar ni ni ɗaya tamkar mayya.
Ina zaune a cikin ɗakin ina kuka na ji an buɗe ƙofa an shigo ƙamshin turaren da na ji ya bugi hancina shi ya tabbatar mini da wanzuwar Yaya Alhassan kusa da inda nake, kafin na ji ya kai hannu ya yaye mayafin da yake kaina ya sanya hannunsa ya tallafo haɓana yana kallon fuskana da ta kumbura ta yi tsimtim tamkar kwaɓin fanken da ya ji yis.
"Kukan nan ya isa haka Amatullah. Ki tausayawa kanki haka mana tun yaushe kike wannan kukan. Ya kamata kin san cewa kuka fa ba ya magani".
Shuru na yi ban amsa masa ba don ina da yaƙinin ko na buɗe bakina sautina ba zai fita ba.
"Amatullah". Na É—aga kai na kalle shi da hakan ya ba shi tabbacin cewa ina sauraronsa.
"Aurena da ke ya ƙara tabbatar min da cewar duk abin da kasance rabonka ne to fa ba ya taɓa wuce ka, na kuma ƙara tabbatar da sahihancin wannan karin maganan ta Malam Bahaushe da yake cewa zakaran da Allah ya nufa da cara to fa ko ana muzurai ana shaho sai ya yi. Allah ya ƙaddara cewa ke ce matar da zan aura a duniya ga shi kuma hakan a tabbata a lokacin da dukkanmu ba mu yi tsammani ba balle zato. Ina so ki cire komai a cikin ranki ki manta da duk wasu abubuwan da suka faru a baya domin yanzu sabon shafi ne ya buɗe a cikin rayuwarki. Na yi miki alƙawarin zame miki mijin marainiya wanda zai share miki hawayenki a duk sa'ilin da zuba kwanrayo. Zan kasance mai yi miki hidima har zuwa ƙarshen rayuwata, zan hidimta miki da karfina, lokacin da kuma aljihuna. Na yi ɗamarar sauya rayuwarki daga duhu zuwa bayyanannen hasken da zai haskaka miki hanya".
Take na ji kalamansa sun samar mini da nutsuwa a sashin ruhina, na É—au lokacin kafin na yi magana cikin dushashewan amo.
"Ina fatan na kasace mace ta gari kuma saliha a gare ka kamar yadda Annabinmu ya ƙira mace ta gari da mafi ƙololuwan jin daɗin duniya ga raywuar ko wani ɗa na miji, ina addu'ar Allah ya ba ni ikon yi maka biyayya akan komai matuƙar komai ɗin bai hauce wa hanyar Allah da koyarwan manzonsa ba".
Cike da jin daɗin kalamaina yake amsa wa da Amin, ya dafa kaina ya yi mini addu'a kamar yanda yake a addinance kana muka je muka yi alwala muka gabatar da salla raka'a biyu mu ka yi godiya ga Allah da ya nuna mana wannan ranar a cikin rayuwarmu, sannan muka roƙe shi albarkar da yake cikin auren da kuma zuri'a ɗayyaba. Sai da ya haɗa mini da magiya da lallashi kafin na iya cin kazar amarcin da ya shigo da ita, jikina gau ya ɗau zafi sa boda zazzaɓin da ya rufe ni ga shi dare ya yi balle ya je ya sayo mini magana, amma duk da hakan bai saduda ba ya ɗaga waya wai zai ƙira wani abokinsa mai chemist in bai rufe ba ya je ya karɓo mini magana.
Da ƙyar na hana sa fita ta hanyar muna masa cewa na ji sauƙi haka muka kwanta washe gari shi ya tashe ni sallan asubahi nan inda na yi sallan na kwanta baccin huce gajiyan da na kwasa ban tashi ba har sai da gari ya yi haske wannan ɗin ma shi ya tashi ni ya ce na je na wanka na zo na ci abinci sai na sha magani don har ya fita ya amso mini.
Kunya ya mamaye ni matuƙar don ni gabaɗaya ma na mance da cewar yanzu ni matar aure ce shi yasa na kwanta na sha baccina hankali kwance. Tashi na yi na wanka da ruwan zafin da ya sanya mini na zo muka ci abincin da ya girka kana na sha maganin bai fita har sai da dangi da ƴan uwa suka fara zuwa gidan nan ma sai da ya Amira da Anty Zulaihatu sun zo kana ya fita bayan ya shaida musu cewar ku kula da ni don ba na jin daɗi. Nan fa suka haɗe kai suka din ga yi mini tsiya zolaya kam babu irin wanda ba su yi mini ba.
Sai da suka yi sallan magrib suka tafi bayan sun yi mini nasiha mai ratsa jiki da kashe zuciya, shawarwari kuwa sun ba ni shi daidai gwargwado sun kuma É—aura ni akan hanyar da ta dace. Haka har na cika sati a cikin gidan aure Yaya Alhassan ne yake yi mana girkin safe duk yadda zan tashi da wuri don na yi aikina to fa sai ya riga ni, sai dai mu yi aikin tare, haka tun ina jin kunyarsa har na saki jikina mussamman da na ga yadda yake ta faÉ—i tashi wajen ganin ya kyautata mini ba dare ba rana, dole ni ma na yi azaman faranta masa na watsar da komai na rumgumi mijina da kuma laluman hanyar da zan bi in faranta masa rai.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya kwanciyar hankali da nutsuwa suka tabbata a gare ni, cikin ɗan ƙanƙanin lokaci na yi ƙiba na murmure fatana ta yi kyau har wani sheƙi nake yi kamar bayan kifi. Duk da ba nida haske amma fatata ta yi farau ta washe. Zuciya babu wani damuwa haka nan raina fari ƙal tamkar zaiba. Ranar da na cika sati huɗu muka yi baƙi Saifullah da Muhammad Taufik suka zo wani abun mamakin har da Sheik Dawood sun wuni suna tattaunawa da Yaya Alhassan, ni kam kunya ta hana ni sakat tun da na fito muka gaisa ban ƙara koda wullagawa ta cikin falon sai da za su tafi Yaya Alhassan ya zo ƙira ni. Tabbas ba na buƙatar sai an faɗa mini da kalmomin baki idanuna kawai sun nuna mini cewar Sheik ya sauya don mun sha ruwan addu'o'i da albarka daga gare sa, ya ɗauki Naira dubu asiri ya ba ni da za su tafi.
Haƙiƙa Yaya Alhassan ya cika mijin marainiyan da ya ambata kuma ya cika dukkanin alƙawarin da ya yi mini a darenmu na farko, ya inganta rayuwata matuƙa da kuɗin sadakina na shiga harkan kasuwanci atamfofi nake sayar wa da duk wasu nau'in kayan sawan mata, likkafa ta ci gaba don har lefe nake haɗawa mai rai da motsi na fita kunya. Kan ka ce kwabo rayuwa ta sauya jin daɗi ya zauna mana ni da mijina ba mu da wani burin da ya wuce faranta wa juna, na ƙara waye wa da samun ilmin zaman duniya da kuma mu'amala mutanen cikinta. Ranar ina zaune kwatsam sai ga Hajiya Muhibbat a cikin gidana tsabar farin ciki sai da na rasa inda zan tsoma ta mun sha hiran yaushe gamo da ita, tare da ba wa juna labarin bayan rabuwa nan take shaida mini cewar mijinta Saddam zai ƙara aure kuma Zinariya ce matar da zai aura, don ita da kanta ma ta shige masa gaba wajen neman auren, don ta fahimci suna don junansu kuma ba za su iya rabu wa, sannan Saifullah ma zai angwance da babbar jika a gun Sheik Dawood, na yi musu murna matuƙa da lokacin auren ya yi Yaya Alhassan da su Amir suka je su domin shaida ɗaurin auren. Sati ɗaya tsakani Amira ta haihu sai dai ɗiyar ba ta zo da raina ba.