← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 72

Sashe 34

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ta kawar da guntun hawayen da suke idanunta ta kai hannu ta amshi kofin shayin da nake miƙa mata, ta kai bakina ta yi kurɓa ɗaya ta ajiye a gefenta.
Cikina a sanyaye na furta"ban san me yake dsmunki a cikin zuciyarki don sanin sirrin dake taskace cikin tsokar zuciya haƙiƙa wannan sai mahaliccinta, amma don Allah ku yi ƙoƙarin ki cire komai daga cikin ranki in sha Allah watarana komai zai wuce har ma ya zama labari".
Sai da ta É—au lokaci ba ta tanka mini har na faÉ—a tunanin na tsallake iyakata ta hanyar faÉ—a cikin abin da bai shafe ni ba kuma bai kasance hurumina ba. Har na cire rai da samun amsa daga gare ta sai kuma can na ji ta ce"Amatullah".

"Na'am". Na amsa da shi cikin nutsuwa da kulawa.
"Kin taɓa yin soyayya? Kin taɓa son wani irin son da kike ji tamkar ba za iya yin rayuwa ba tare da shi ba? Kin taɓa tsintar kanki cikin ƙangin so mai dabaibayi? Kin taɓa ɗaukar so da ƙauna kacukam kika ɗaura akan wani ɗa na miji? Kin taɓa yin soyayya mai zurfi da sarƙarƙiya?".

Sai da na sauƙe numfashi mai nauyi kana na sama zarafin cewa"Ranki ya daɗe duk abubuwan da kika lissafa babu ko guda ɗaya da ya taɓa faruwa da ni. Hasalima ban taɓa yin soyayya ba a cikin rayuwata".

"In dai abin da kika faɗa haka ne tabbas ba za ki taɓa fahimtar duk abin da zan bayyana miki ba, Amatullah so wani mungun abu ne. Wallahi ko maƙiyina ba na masa fatan Allah ya jarabce shi da makauniyar soyayya".

"Don ban taɓa yin soyayya ba ai ba hakan ne zai sa na kasa fahimtar halin da kike ciki ba, sai dai na Hajiya ni na san ban kai na ji damuwarki ba amma in sha Allah na yi miki alƙawarin zan taya ki da addu'ar Allah ya kawo miki mafita da sauƙin halin da kika tsinci kanki a ciki". Ina dasa a zancen nawan na tashi na tattare kwanunkan da su Ayan suka gama cin abincin na kai kicin na wanke su, duk da ina jin yunwar kuma ina buƙatar na saka wani abu a cikin cikina, amma na kasa cin abincin sa boda yadda na ga Hajiya tana zubar da hawaye. Duk da ban san takamammen abin da yake damuwanta tare da yi mata ƙaiƙayi a cikin ranta ba, amma na tabbatar da cewar abin azimun.
A lokacin yarinyatata duk macen da na gani tana rayuwa a cikin babban gida, tana saka suturar da take so sannan ta hau manyan mota. Gani nake yi tamkar a duniya dai kam ba da ta wani matsala kuma sun gama dace wa a cikin duniya sai dai a yi fatan dace wa a gobe ƙiyama. Ashe kallon kitse nake yi wa dogo, sai yanzu da hankali ya ratsa jikina ma fahimci ko wani Bawa da irin na shi damuwar kuma mai ɗaki shi ya san inda yake yi masa yoyo.

"Idan tunanin za ki tsaya zauna kina yi ai da kin ui zamanki a can gida ba zai kin zo nan ba". Muryar Altine shi ya dawo da ni cikin duniyar zahiri daga karatun wasiƙan jakin da nake yi, ban ɗaga ido na kalle ta ba balle na ce da ita wani abu na tashi na je na rufe abincin na wanke hannuna na fita.
Har yanzu Hajiya tana nan zaune inda na bar ta ba gusa ba wnda a iya tsawon kwanakin da na yi a cikin gidan. Na lura ba ta cika sama a falon ƙasan ba rai da rai yana sama indai ba wani abun ba ne ya sauƙo da ita ƙasa shi ma tana gama wa take kowa wa sama.
Har na yi gaba zan wuce sai na ji ta ƙira sunan na dawo da baya na zo na durƙusa a gabanta kaina a ƙasa ina sauraron zancen da take yi cikin amo mai rauni.
"Amatullah ki ba ni shawara na rasa da yadda zan ɓutowa wannan lamarin gabaɗaya kaina ya kule. Tunanina ya tsaya a waje guda cak".

"Ranki ya daÉ—e ai ban san abin da yake damunki ba balle har na yi tunanin shawaran da ya dace na ba ki".

Ta ɗan yi jim ta ce"haƙiƙa Allah ya jarabce ni da tsananin son mijina. Hasalima ni na fara ganinsa na ce ina sonsa har kuma Allah ya ƙaddara za mu yi aure su haifa Ayan da Aryan. Su biyu iyayensu suka haifa daga shi sai ƙaninsa Saifullah da muke zaune tare da shi a cikin gidan, ba su da wani dangin kusa illa junansu hakan ya sanya suke matuƙar ƙaunar juna. Mun yi aure da Saddam amma sai bayan auren na fahimci ya aure ni kawai sa boda ya sama wacce za ta taya sa sanya ido akan ƙaninsa kasancewar sa ba mazauni ba, tun da muka yi aure da shi bai taɓa yin sati guda cur a cikin gidan nan ba. Ya yi wuta shi ne ya zo ya yi kwana biyar ya koma daga nan kuma sai ya sanda ya ƙara waiwayo mana. Soyayyar Saddam ta rufe min ido ta hanyar ba na iya ganin aibunsa kuma ba na ganin laifinsa akan komai duk da kuwa ni ma kaina na san yana cutar da ni".

"Hajiya ba kya tunanin cewa kuma yanayin aikinsa ne yake hana sa samun lokacin da zai zo gida? Kin ga fa ya wadata ku da komai na buƙatar rayuwa bai bar ku da yunwa ba, bai bar ku da ƙishi ba haka nan bai bar ku cikin tsumma ba komai na buƙatar rayuwa yana yi muku".
Ta saki wani sakakken murmushi kafin ta ce"ba za ki fahimta ba. Duk waɗannan abubuwan da kika lissafa ba su ne jin daɗin rayuwar duniya mussamman a cikin gidan aure. Aure ba na mutum ɗaya ba ne na mutane biyu da ake buƙatar ko wani ɓangare ya ba da na shi gudumawar, ban yi dogon karatun addini ba amma iya sanin da nake da shi na san cewa ƙissan rayuwar Sayyada Khadijatu da Ma'aiki sallallahu Alaihi Wasallama, ita ta fara ganinsa ta ce tana sonsa sa boda ta yarda da shi kuma ta yi na'am da kyawawan halaye da ɗabi'unsa. Shin ni na yi laifi don na yi koyi da macen da tarihi ya tabbatar da cewar ta hidimtawa addini da ƙarfinta kuma da dukiyarta? Mene ne lafina don na gan sa na ce ina son sa shin addini ya haramta hakan ne da na cancanci wannan azabtarwan?".

Na yi shuru ina tunanin ta inda zan fara kafin can na soma cewa"ki miƙa lamurranki zuwa ga Allah don shi kaɗai ne zai kawo miki mafita da sauƙin halin da kika tsinci kanki a ciki. Duk duniya babu wanda zai iya yaye miki damuwarki sama da wanda ya ɗaura miki. Ki yi sallan dare ki kai goshinki ƙasa ki yi Allah kuka ki sanar da shi damuwa da matsalolinki, ki roƙe sa cike da yaƙinin cewar zai amsa miki kuma ya yi miki zaɓi mafi zama alkhairi a gare ki. Ki yi azumi ki yi sadaka sannan ki yawaita karatun alƙur'ani don yana samar da nutsuwa a zuciyar da babu ita, ya haifar da kwanciyar hankali da salama a ciki ruhin da babu ita sannan ya na wanke ƙwaƙwalwa ya kuma daidata tunani".

Ta sauƙe wani gauron ajiyar zuciyarta da har sai da na ji sautinsa kafin ta ce"na gode in sha Allah zan yi duk yadda kika ce. Na gode sosai da wannan shawaran".

Ina ɗago kaina idanuna suka sauƙa akan Altine da take ƙarisowa inda muke ta murtuƙe fuskarta marar annurin nan tamau, da hakan ya ba ni cikakken tabbacin ta saurara duk abin da muke zanta da Hajiya.
"Hajiya sannu da hutawa, daman na zo mu yi wata magana". Ta yi zancen yayin da take zauna wa kusa da ƙafafun Hajiyar.

"Ina jinki".

"Ki ɗan ba mu waje ko". Murmushi kawai na yi na tashi na ba su waje na koma cikin ɗakin Altine na zauna, ganin zaman ba zai kai ni ko'ina ba. Hakan ya sanya ni ɗaukar alƙur'anin da na gani ajiye dirowa na fara karantawa.
Ban yi nisa ina yi ba Altine ta shigo ta amshe ƙur'anin daga hannuna ta rufe ta ajiye shi a gefe guda, ta zauna tana fuskantana tare da haɗe hannayenta wajen guda.

"Amatullah kike ko?".

"Ƙwarai ba ki yi kuskure Amatullah nake".

Ta gyaɗa kanta"ina so na yi miki gargaɗi na farko wanda shi za kasance shi ne na ƙarshe da zan yi miki wanda matuƙar ki na ƙaunar ci gaba da zama a cikin gidan nan dole ki yi bi abin da zan gindaya miki. Kin ga wannan shishshigewan da kike yi wa Hajiya da zummar samun wajen zama babu inda zai kai ki, sai dai ma ya sauƙe ki a tashar ƙasƙanci. Na ji har wani banzan shawara kike ba ta ke a dole kin cika kin batse, to daga yau na ja miki jan layi tsakaninki da Hajiya iyakan cin ki da ita gaisuwa ce daga nan kuma sai gobe".
Chapter 34 · 0% Book details