← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 72

Sashe 19

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da na cire rai da samun amsa daga gare sa, don har da ƙafafuna suka gaji na ji kamar na ɗaura hannuna a ka na yi ta kurma ihu tsabar takaicin da ya ƙunsa mini, na tsani na yi wa mutum magana ya yi banza da ni wannan abun ci mini rai yake yi sosai da sosai.
"Za ki iya tafiya kuma kar ki ƙara dawowa sashin nan don ba na buƙatarki a nan. Don haka ki san abin da za ki faɗa wa Anty". Yana gama zancen ya tashi ya ɗauki wayarsa da wasu makullan da suke kan teburin da yake gabansa ya zuba a cikin aljihunsa ya fita, ni ma tashi na yi na fita sanda na fito na gan shi har ya shiga motarsa Baba mai gadi ya buɗe masa gate zai fita na bi motar da kallo har sai da ya fice daidai lokacin da na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya.
[12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

_______________________________________

Page 5️⃣3️⃣

Ji na yi kamar na koma cikin sashin na binciko dalilin kasancewar hoton Muhammad Taufik a cikin ɗakinsa, gabaɗaya na rasa gane kaina balle fahimtar abin da yake yi mini daɗi. Na tsaya cak a wajen ina ta karatun wasiƙan jaki da saƙa da warwara cikin raina. Kamar daga sama na ji saurar dirin sauti a cikin kunnuwana da ya tursasa mini ɗago idona Ina duban Baba Mai gadi.

"Ƴar nan lafiya? Tun ɗazu na hango ki kin fito kin tsaya a nan kin yi shuru. Ko dai akwai wani damuwar ne?". Na saki taƙaitaccen murmushin da iya kansa kan leɓena bai kar har cikin zuci ba.
"Lafiya ƙalau Baba. Yanzu ma wajenka nake son na je in ba ka wani aikin ka soma koya mini ƙananun kalmomin yaren". Ya yalwata annurin fuskarsa kafin ya furta"ai kuwa ba na komai ina dai zaune ne kawai". Yana dasa aya a zancen ya juya na bi shi a baya har zuwa bakin gate ɗin ya zauna akan wani benci yayin da na zauna a kusa da shi.

"To yanzu ta ina za mu fara?". Na duƙar da kaina ƙasa"ai Baba tun daga gaisuwa za a fara koya mini har a gangaro a zo kan ƙidaya da wasu kalmomin da suka kasance na amfanin kullum-kullum". Ya yi dara kafin ya ce"to kamata ya yi ki nema takarda da biro ina faɗa miki ki na rubutawa, tun da kin yi karatun zamani ai ko?".
Na riƙe haɓa"na yi amma ban yi nisa ba". Kafin ya ce da ni wani abun Altine ta iso wajen kamar mai shirin zuwa filin yaƙi ta ja ta tsaya a gabanmu hannunta riƙe da wani baho ƙiran ghana must go ƙarami.

"Amma kin san akwai aiki a cikin gidan kika zo nan kika tare ko?".

Cike da mamaki na ɗaga ido ina kallonta da ta haɗe girarta na sama da na ƙasa. Ta murtuƙe fuska kamar magribar ɗinya. A hankali na ce"na wanke har kwanukan da aka ci abinci fa kafin Hajiya ta ce na je sashin can na gyara....". Tun kafin na gama ta tari numfashina"don kin wanke kwanuka kuma sai aka ce miki babu wani aikin ko? Ki tashi ki shiga ciki ki gyara ɗakin su Arya kafin na ce na kai saƙon nan na dawo, a fara shirin abincin rana".

"To ki dawo lafiya".

Na amsa da shi cikin sanyin murya ba ta amsa mini ba illa tsakin da ta tsirtar tamkar ta yi arba da ɗanyen kashi sakin yanzu-yanzu, ta ja bahon da ƙyar za ta bar wajen Baba mai gadi ya dakatar da ita ta hanyar faɗin"Hajiya Altine wannan kayan fa? Mene ne a ciki na ga ki na ja da ƙyar". Ta galla masa wani uban harara tamkar idanunta za su faɗo ƙasa"to ƴan sa ido masu zuwa lahira da cover shoe. Me ye naka a ciki? Ina ruwanka da ni balle kayan da zan fita da shi? Kowa ya tsaya a matsayinsa ka tsaya a matsayinka na mai gadi ni ma na tsaya a matsayina na ƴar aiki. Idan ba so kake yi mu ba wa hamata iska ba ni da kai".

Jijjiga kansa ya yi a taƙaice ya furta"Allah ya kyauta". Ta yi wuf ta amshe zancen tamkar jira take yi"Amin in da gaske kake yi". Daga haka ta ja bahon ta fita da shi duk mu biyun muka bi ta da kallo har ta fice na sauƙe sakakken ajiyar zuciya mai matuƙar sauti.
"Ɗiyata sai haƙuri fa zama da Altine ko na sakon ɗaya ne sai ka haɗa da haƙuri. Balle zaman awanni har ma ranaku da dama, kin gan ta nan tun farkon auren Hajiya aka kawo ta aiki a cikin gidan nan, Hajiya da mijinta har ma da ƙaninsa sun yarda da ita matuƙar yarda wanda har ya wuce kima sun yi imanin ba za ta a taɓa haɗa baki da ita a cutar da su ba balle ace ita da kanta ne za ta cutar da su. sai dai ba san cewa a cikin zaman da suke yi da ita cutar da su take yi su da ƴaƴansu ta ƙarƙashin ƙasa ba, ta yi musu illa sosai amma har yanzu ba su farga ba balle su gano fuska biyu gare ta". Tun da ya soma maganan na sake baki da hanci ina jin sa da kallo har ya kai aya kana na ja dogon numfashi na fesar kafin na zama lasisin faɗin"wani irin illa kenan Baba?".

"Iloli masu yawan gaske ma kuwa, kin ga Altinen nan da kike ji da gani ta ƙi jinin ta ga wata ko wani ya raɓe jikin Hajiya mussamman in ta lura zai karu da wani abu, ka mamaye komai na cikin gidan nan duk wata ƴar aikin da za ka kawo da sunan ta zama mataimakiya a gare ta sai ta yi yadda ta yi ta yi kwance-kwance ta ƙulla mata tuggun da ba za ta iya fitar da kanta ba. A ƙarshe da kanta za ta zaɓa barin aikin akan ta ci gaba da zama. Ki na ganin Altine hatsabibiyar mace ce, akan ta na ƙara yarda da cewar ko sheiɗan dole ya ji tsoron kaidin mace balle mu kuma bil adama. Ki yi hankali da ita".

"To wannan kayan da ta fita da shi ba ina za ta je da shi?". Ya saki taƙaitaccen murmushi kafin ya ce"a sannu a hankali idan Allah ya san zamanki a cikin gidan nan ya yi tsawon rai za ki fahimci inda take kai kayan". Ƙirjina ya buga da ƙarfin gaske cikin son ƙarin bayani na ce"ban gane idan zama na ya yi tsawon rai ba".

"Duk wata mai ƴar aikin da ake kawo wa cikin gidan nan a ta wuce adadin makonnin huɗu take fita. Don haka ke ma ki yi taka tsantsan ki kuma san irin zaman da za ki yi a cikin gidan nan, mussamman kasancewar ki yariya mai ƙaranci shekaru".

Jikin gabaɗaya ya yi sanyi ƙalau tamkar kazar da aka jefa da ruwan gishiri. Na gaza cewa komai duk da tarin tambayoyin da suka yi mini tsayiwar ƙayan kifi a maƙoƙarona da ƙyar haɗiye miyau ɗin da ya taru mini a cikin baki.

"Ƴarta ki kwantar da hankalinki ban sanar da ke hakan don na tayar miki da hankali, ko kuma don na kashe miki ƙwarin gwiwa ba. Ki ci gaba da aikinki sannan gefe guda ki dage da addu'a ki tabbatar da ba ki mu'amalance kowa da wani mummunan hali ba. Ki tashi ki shiga ciki kafin ta dawo ta same ki a nan ".

"To Baba na gode sosai Allah ya saka da alkhairi".

"Amin Allah ya yi albarka".
Ban iya amsa addu'ar cikin kalmomin baki ba sai a cikin zuciyana na amsa yayin da nake tashi daga wajen na nufi cikin gidan kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki.
Wayam na iske falon babu kowa sai su Arya da Ayan suna kallon TV na bi shi su da kallo. Ban san me yasa haka kawai a duk lokacin da na ga yaran nake jin suna matuƙar burge ni. Na daɗe ban ga yara ƙananu masu irin shekarun da suke da kwatankwacin irin nutsuwarsu ba haka kawai na tsinci kaina cikin sakin murmushi, sai da na ƙare musu kallon tsaf kana na wuce kicin na ɗauko tsintsiya da mopper na dawo na nufi ɗakin su Ayan.

Sai da na gyara musu gadon na sauya zanin gadon na saka wani na shara ɗakin na yi mopping kana na shiga banɗaki na wanke na feshe ko wani kusurwa da room freasher. Sai da na gama komai na fito jikina gabaɗaya babu gaɓar da ba ya yi mini ciwo. Ina ajiye tsintsiya da moppern na fito na wuce ɗakin Altine kamar kayan wanki na zube akan katifa ina mayar da numfashi kamar wacce ta yi aikin ɗaga ƙarfe, ko'ina a jikina ciwo yake yi mini har ba na ƙaunar motsawa, na lumshe idanuna a hankali ina jin wani mayataccen bacci yana fizgana ban san sa'ilin da na yi baccin ba sai jin sauƙan ruwan sanyi na yi a jikina.

Figigi na tashi ina jan wani dogon numfashi na fesar da shi yayin da nake tantance inda nake don gabaɗaya ɗakin ya juya mini na kasa gane komai tamkar wacce aka yi wa dashen sabon curin ƙwaƙwalwa a cikin kanta. Kafin igiyar firgicin ya gama saki na na tsinkayo muryar Altine raɗau a masarrafar jina.
"Kwanciyan me ye kike yi? Ai kwanciya bai kama ki tun da dai neman kuÉ—i kika fito yi. Ki tashi ki je ki share filin tsakar gidan nan tsaf".
Chapter 19 · 0% Book details