← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 72

Sashe 11

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Hajiya ga ta nan ai sai ki tambaye ta abin da yake faruwa ta yi miki bayani". Zuby ta ƙarƙare zancen tana yi mata nuni da inda nake tsaye har zuwa lokacin ban dawo daidai daga kiɗimar da na yi ba.
"Ke wace ce kike da suna?".

"Amatullah".

"To Amatullah lafiya kike zake ƙarfinki ki na kurma mana wannan ihun, gobara ce ta tashi ko kuma ƴan fashi ne suka yi mana da'iri ban sani ba?". Na girgiza mata kaina alamar a'a.
"To mene ne?". Ta yi zancen cikin tsare gida da turmuƙe fuska babu alamar wasa ko wargi a tattare da ita.
"Wani ne ya faÉ—o mini É—akina yanzu ma haka ya na ciki, ban san wane ne ba?".

"Wani kuma?". Ta jefa mini tambayar cikin mamakin ba ta jira amsar da zan ba ta ba ta juya ta shiga cikin ɗakin yayin da ragowar matan suka rufa mata baya, babu jima wa suka fito tare da mutumin da yake ta layi duk ya ɓata jikinsa da alama a matuƙar burge yake na fitar hankali.
Cikin maye ya ce"sorry sister mance É—akin cikas É—in tawa na yi na faÉ—a na ki". Ban ce da shi uffan ba har ya gama galantolinsa ya gama.

Zuby da tun farkon lamarin take tsaye a ƙofar ɗakinta ba ta gusa ba, ta dafe ƙirji tare da fiffito da idanu waje"na shige su ni Zubaida ɗiyar Sani mai kayan koli, wannan ai Habu ne saurayin Hafsy ƴar jama'are me ye ya kai shi cikin ɗakinki?".

Idanuna ya yi tsilli-tsilli kafin na furta"wallahil azim ban san shi ba, ko fuskanshi ma ban gani ba saboda babu haske a cikin É—akin". Ta galla mini hararar da ya tursasa mini yi wa bakina limzami babu shiri.
Hajiya Babba ta ce"yanzu ina ita Hafsyn take wannan abun ya faru?".
Zuby ta kada baki ta ce"Hajiya ta tafi club da wani sabon kamun da ta yi". Cikin zafin rai Hajiya ta ce"to kama shi ki san yadda za ki yi da shi, na kashe wannan case ɗin kowacce shegiya ta koma ɗakinta". Tana kama zancen ta juya gare ni"ke kuma ina so ki nutsu ki san inda kike". A dunƙule ta jefa mini zancen ba tare da ta warware mini ƙulin ba ta yi shigewarta cikin ɗakinta, na kasa jan ƙafana na bar wajen har sai da kowa ya watse ya bar ni a waje, masu shiga ɗakunansu da samarinsu suka shige masu shirin fita suka fita.

Sai da na ja dogon gashin na fesar kafin na nufi cikin ɗakina ina doso ɗakin na ji wani gungumemen wari ya doki hancina babu shiri na toshe hancina da tafukan hannayena. Ba n i da tocila balle na haska na ga abin da ya haddasa warin haka na ci gaba da tsayiwa a ƙofar ɗakin tun ina tsaye har na zauna, a nan ƙofar ɗakin na kwana.
Sanyin asuba da ya soma ratsa ni shi ya farkar da ni daga nauyayyen baccin da ya sace ni. Na farka na shiga na ɗauko buta na yi alawa a ƙofar ɗakin na shimfiɗa ɗan kwalina na yi salla, sai da na ɗan jira gari ya yi haske kana na koma cikin ɗakin.

Na tsaya cak tamkar gumki ganin yadda aka ɓata kan tabarman da amai ya yi kaca-kaca, ni na yi tamkar na ɗaura hannu a ka na dinga zunduma ihu ko zan ji sauƙin takaicin da ya cika mini zuciya. Ban san sa'ilin da hawaye suka fara gangarowa daga koramar idanuna ba sai jin ɗumin su na yi a bisa fatan fuskana. Ba ni da ajiyayyen ruwa ko kaɗan illa wanda na rage da na yi alwalar sallan asubahi.
Na fito na ga La'aniyatu ba su buɗe ƙofa ba, na rasa yadda zan yi. Ina waigawa na ga wani bokati na ɗauka na fita domin ɗeba ruwa, layin sharau don har zuwa wannan lokacin gari bai gama waye wa sosai ba. Ina tafiya ina kuka har na isa wajen ɗeban ruwan na ɗeba na ɗaura akaina na juyo zan tafi kenan na hango shi yana fitowa daga cikin masallaci.

Ban san dalili haka kawai na ji jikina ya É—auki rawa ya kafe ni da ido kamar yadda ni ma na É—aura idanuna akan sa, bai ce da ni komai ba ya zo ya wuce ni ma na É—auki hanyar komawa gidan. Tun daga zaure na ji ana kwararo ruwan ashariya, har na shigo cikin gidan ba a fasa ba ina shigowa aka nuno ni.

"Kin ga shegiyar da ta ɗaukar min bokati". Zuby ta yi zancen tana nufo inda na ke tsaye gadan-gadan, kafin na na yi aune ta tankaɓar da ruwan da yake kaina ya malale a jikina ya yi mini lijif.
"Yanzu ke don kuturun wulaƙanci ki rasa bokatin wacce za ki ɗauka a cikin gida nan sai bokatina?. To wallahil azim zan ja miki layi da kayana a cikin gidan nan". Tana dire zancen ta wafce bokitin ta yi shigewarta cikin ɗakin. Na dubi jikina da ya yi lajab na tuna irin dogon tafiyar da na yi kafin na je na ɗebo ruwan kawai sai na ji hawaye suna sauƙa daga idona, na koma ƙafan ɗakina na zauna na zabga uban tagumi.

A haka La'aniyatu ta fito ta iske ni ta nema jin ba'asin abin da yake faruwa na irge mata komai cikin kuka, ita ta taimaka mini da ruwa da wanke ƙazantar da Habu ya yi mini akan tabarmata, na fito da ita na shanya akam igiya na koma ciki na sha lemo da biskit daga cikin abin da Hajiya Muhibbat da ta ba ni. Sai da na jira tabarman ta bushe kayan jikina ma ya bushe na shigo da ita ciki na shinfiɗa, duk da ban da agogon da zan duba lokaci na fahimci lokaci ya ja don hasken rana ya game ko'ina, sai da a rufe ɗakin na ba da ajiyan ɗan makulin a La'aniyatu kafin na tafi.

Kamar ƙafafuna za su tsinke haka na ke ta zabga sauri har ƙafafuna suna sarƙewa, ina isa ƙofan gidan na ƙwanƙwasa mai gadin ya fito ya buɗe mini na durƙusa har ƙasa na gaishe shi kafin na shiga cikin gida.
Na yi sallama Altine ta fito ta watsa mini wani matsiyacin kallo, na rusuna na gaishe ta maimakon ta amsa sai ta jefo mini tambaya.

"Ke sai yanzu kika yi niyyan zuwa aikin? Wannan in ke za a tsaya jira sai kin zo ki girka ai kuwa watarana ba za a ci abinci a gidan ba".

A nutse na ce"ki yi haƙuri wani uzuri ne ya sani na makara. Amma in sha Allah ba zan sake maimaita irin hakan ba".
Ta gallo mini harara"Dalla can rufe min baki sai wani fiƙi-fiƙi kike yi da idanu kamar ta Allah. Sai ki jira don karin kumallo suke yi". Daga haka ta juya ta bar ni tsaye a wajen, haka na ci gaba da tsayiwa har sai da na gaji na zauna a bisa dakalin wajen. A ƙalla na fi mintuna talatin a zaune a wajen kafin Altine ta fito ta cikin izgili ta ce na shigo. Da rawan jiki na tashi na bi bayanta muka shiga, suna zaune a falo tare da tagwayenta da ba su wuce shekaru biyu da haihuwa ba a hashashena kenan, na durƙusa har ƙasa na gaishe ta ta amsa mini fuskarta babu yabo babu fallasa.

Kafin ta ce wani abu na soma da ban haƙuri"Hajiya ki yi haƙuri na makara wani uzuri ne ya riƙe ni, amma in Sha Allah hakan ba zai ƙara faruwa ba". Fuskanta ɗauke da maɗaukakin murmushi ta ce"kar ki damu ba komai, ai jiki da jini dole daman wataran a sama irin haka, yanzu mu je sai na zagaya da ke ki ga gidan ko?". Na gyaɗa mata kaina ina jin wani daɗi yana mamaye mini raina na fahimtan da ta yi mini, har na yi gaba zan ji ta a baya muka jiyo sautin da ya tilasta mata tsayawa.

"Anty wace ce wannan?". Ta waigo tana kallonsa yayin da su Aryan suka nufa wajensa.
"Ita ce sabuwar ƴar aikin da na yi maka bayani akan ta jiya". Yana ɗaura agogo a damtsen hannunsa ya ce"Anty a sallame ta, a nema wata kawai". Babu shiri na ɗago kai ina kallonsa ƙirjina yana tsananta bugu, jikina ya yi sanyi kamar kazar da aka jefa da ruwan gishiri.
[12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

________________________________________

Page 4️⃣8️⃣

Cike da maɗaukakin mamaki a bisa fuskan Anty Muhibbat ta ce"Saif me yasa wani abun ka ga ta yi?". Har yanzu idanunsa yana kan agogon da yake ɗaurawa a tsintsiyan hannunsa ya furta"Anty kawai yarinyar ba ta yi min ba ne, ki dubi yanayinta da kuma ƙarancin shekarunta ba na tunanin da za iya yin duk aiyukan da kika lissafa min jiya. Zai fi dace a sallame ta a nema wata kasai". Dukkanmu biyun muka yi sakeke muna kallonsa ni kam na gaza cewa komai saboda sanyin da jikina ya yi ƙalau tamkar jinjirar kazar da ruwa ya yi mata ɗan banzan duka.

"Saif ba wannan za ka duba ba, na lura tana cikin tsananin buƙatan wannan aikin ko don ta kula da rayuwarta a matsayinta na ƴa mace. Mata nawa ne masu irin shekarunta suke yawon ta zubar? Mata nawa ne masu irin shekarunta suke sayar da jikinsu don su sama abin da za su ɗauki nauyin kansu? Mata nawa ne masu irin shekarunta da suke iskanci don su sama abin da za su saka a baki salati? Mata nawa ne masu irin shekarunta suke faɗa harkan banza da na shaye-shaye?. Ga su nan wasu sun rasa hankalinsu, sun rasa tarbiyya da kamun kansu, sun rasa kyawun jikinsu wasu ma sun faɗa harkan barace-barace akan titi wasun su ma sun haukace. Duk waɗannan hanyoyin ba ta zaɓa ta bi ɗaya daga cikinsu ba ta zaɓa ta fito ta nema aiki don ta rufawa kanka asiri ta kuma ci halaliyarta. Saif irin waɗannan yaran su ya dace a ringa taimakawa".
Chapter 11 · 0% Book details