← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 72

Sashe 57

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Don Allah Amira wannan zancen da gaske ki ke yi, kun yi aure da Mansur? To a ina kuke zaune kuma me yasa na gan ki cikin wannan yanayin?".

Sai da ta ja numfashi mai dogon zango kana ta ce"Amatullah za ki yi mamaki idan na shaida miki cewar yadda Mansur ya bayyana kansa a gare ni ba haka yake a zahiri ba, ya nuna min soyayya a zahiri alhalin a baɗili ba hakan ba ne a cikin ransa. Bayan barinki gida sau uku yana ƙoƙarin keta min haddina Allah ya na kuɓutar da ni, lokacin da iyayensa suka zo gidanmu aka sanya ranar aure sai ya mayar da ni tamkar matarsa ba ya shayi ko shakkan taɓa ko wani gaɓa a cikin jikina. Ya lalata min rayuwata yayin da hankalina ya gushe da tunanin tun da aure na zai yi hakan ba matsala ba ne, ban sa ni ba ashe wuƙa na ɗauka na burmawa cikina. Idanuna sun gama rufe burin auren mai kuɗi kuma ɗan soyayya kawai nake hangowa. Haka aka yi bikin ya yi da ya yi min ɓarin Naira kamar bai san zafin nemansu. Ya ɗanɗasa min gida na gani na faɗa komai na cikin gidan shi ya yi da ƙudinsa daga ni sai kayan jikina aka kai ni cikin gidan. Ban cika satikai biyu masu kyau a cikin gidan ba na fahimci na yi zaɓen tumun dare don na gani Mansur ƙwararren manemin mata, har daga wasu jihohin ake yi masa dillancinsu. A lokacin hankalina ya tashi matuƙa babu kalar bazaranar da ban yi masa ba amma ya murzawa idanunsa toka daga ƙarshe ma ya ba ni zaɓi ko in kwantar da hankalina na zauna na ci azurki na bar azurki a inda na same shi, ko kuma ya sauwaƙe min ungulu ta koma gidanta na tsamiya".

Ta tsagaita ta hanyar jan dogon numfashi ta fesar da shi daga bakinta kafin ta ɗaura daga inda ta yi birki"dole na ba da kai bori ya hau don ba zan iya rabuwa da shi, bayan soyayyan da nake yi masa hakan ina gudun dariyan da magauta za su yi mana ni da Umma idan aka ji cewar Mansur ya sake ni tun kafin na rufa wata guda a cikin gidansa. Haka na yi haƙuri na shanye dukkan baƙin ciki da takaicin Mansur a lokacin ko zanen lallen da aka yi min na bikin bai gama goge daga hannaye da ƙafafuna ba. Tun ina kuka da shiga damuwa har na saki raina na sa ba don har akan gadonmu na sunna yana waya da ƴan matansa, idan na ce zan tayar da hankali sai na ga ba ni ma da wani dalilin yin hakan tun da bai rage ni da komai ba. Bai hana ni ci ba balle sha haka nan sutura sai wanda na zaɓa zan saka a jikina. Ko da na sanar da Ummata sai ta ƙara ƙarfafa min gwiwa akan na zauna da mijina a cikin dukkan yanayin da na tsince shi, ta ƙara da cewar mazan wannan zamanin daman duk haka suke ko sun yi aure ba za iya rabuwa da ƴan matan da suke mu'amala da su, na yi matuƙar juriyan zaman da shi don a wasu lokutan har cikin ɗakina yake kawo mace sun yi duk abin da ransu yake so ba tare da na iya cewa da shi uffan ba har sai da ya kai jallin da na ji gabaɗaya auren ya fice min daga cikin raina. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya duk halin ƙuncin da zan shiga ba ya ɗaɗa Ummata da ƙasa in dai har zan kawo mata ƴan sulalla to baka lafiya ciki lafiya, shuru za ki ji tamkar Malam ya haɗiye shuruwa. Rana tsaka Mansur ya soma jinya tamkar ba zai yi rai ba ko da aka je asibiti aka tabbatar da cewar yana ɗauke da cuta mai karya garkuwan jiki, da aka gwada ni ma aka same ni da cutar a tattare da ni sai dai nawa bai yi ƙarfi tamkar na sa ba. Ina da yaƙinin cutar ba ta yi min illa kamar yadda tunani da halin ƙunci da kukan da na shiga ya yi min illa ba, lokaci guda na rame na fige na fita daga cikin hayyacina. Ko da na buƙaci ya sake don ba zan iya zama da shi ba Umma ta lashi taboki akan in har na kashe auren to babu ni babu ita kuma daga ranar na dai amsa sunan ɗiyar da ta haifa, haka na rumgumi haƙuri ya zama min abokin rayuwa, aka ce gani da wane ya isa wane tsoron Allah sai dai wanna karin maganar ba ta yi tasirin akan Mansur ba bayan faruwa waɗannan abubuwan aka kama shi da wata a wajen aikinsu yana lalata da ita, take aka rubuta takardan kora ya dawo gida ya zauna babu aikin fari balle na baƙi".

Daga haka ta fashe da wani gigitaccen kukan da na ji sautinsa yana ratsa wa har cikin ƙoƙon kaina, na kasa yin komai balle har na sama ƙarfin gwiwan lallashinta na haɗa mata da kalaman ban haƙuri. Haka ta yi ta gaji don kanta ta tsagaita tare da ɗorawa da faɗin"kin san an ce zara ba ya barin dami kuma yau da gobe mai ƙarar da sabulun wanzami, duk wani dukiyar da Mansur ya tara sai ya zo ƙarshe cikin ƙiftawan ido tamkar ki haɗa auguda ki cilla musu ashana. Nan fa rayuwa ta yi mana tsauri tun muna cin abinci sau uku a rana ko da kuwa babu daɗi muka dawo ci sau ɗaya ma yana neman gagaranmu. Dole ƙanwar naƙi Mansur ya ajiye duk wani girman kansa a gefe ganin yunwa yana neman halaka mu, ga shi tun lokacin da aka kore sa daga wajen aiki sa boda munin abin da ya aikata iyayensa suka yi fushi da shi suka janye masa dukkan tallafi. Yanzu da nake yi miki wannan maganar adaidaita Mansur yake ja don mu rufa wa kanmu asiri, ya yi nadama dana sanin abin da ya yi a baya ya kuma durƙusa a gabana amma duk da haka zuciyata ta ƙi amsar tubansa balle har ta yafe masa irin cutarwan da ya yi mata".

Har ta ƙare zancen na gaza motsa wa daga inda nake zaune, tamkar gunki na koma ba na iya yin komai illa kafe da ido da na yi yayin da hawaye suke kwaranya daga cikinsu. Cikin ƙarfin hali na furta kalmar"innalillahi wa inna ilahirin raji'un!". Ta tsuƙe majiyan kukan da ya zo mata kafin ta furta"ki na mamaki ko?". Na gyaɗa mata kaina da hakan ya ba ta damar ci gaba da cewa"to kar ki yi mamaki duk abubuwan da na faɗa miki babu kuskure ko kuma ƙage a cikinsa. Yanzu ma shi ya kawo ni har ƙofar gidan nan kuma shi zai zo ya mayar da ni, wallahi ban ji rasuwar Umma ba sa boda babu waya a hannuna da tun ranar na zo ni, sai yau da na zo Ummata take sanar da ni". Nauyin da ƙirjina ya yi mini ya hana mutane samun damar cewa da ita komai illa jinjina kaina da na ci gaba da yi ina amsa addu'ar neman rahama da take yi wa Umma a cikin zuciyata sa boda bakina ya gaza.

Muna nan zaune har aka yi ƙiran sallan zuhur muka fito muka yi alwala muka yi sallan tare da ita muka yi girkin rana muna aikin muna tattaunawa da jajanta lamarin da suka faru, bayan ni ma na kwashe duk irin rayuwar da na yi na sanar da ita ta jinjina lamarin ainun tare da tausayawa a gare ni. Sai da muka gama aikin girkin tsaf na zuba mana namu muka shiga cikin ɗakin, duk yadda ƴaƴan hanjina suke kukan yunwa na kasa kai ko da loma ɗaya na dafa dukan shinkafan cikin bakina illa juya cokalin da nake yi a cikin abincin na kallo ta na ga yadda take cin abincin hannu baka hannu ƙwarya, take na ji hawaye ya ciki mini kurmin idanuna wani irin tausayinsa ya mamaye mini rai da ruhina, tabbas rayuwa abar tsoro ce matuƙa kuma na yarda da wannan karin maganan da ake cewa duniya budurwan wawa ne.
"Ban taɓo zato rayuwa za ta zo mana a haka ba Amira. A duk sa'ilin da na rufe idanuna sai na din ga tuno irin rayuwar da muka yi baya sai na ji hawaye suna zuba daga idanuna ba tare da ni kaina na sani ba. Ki duba duk irin soyayyan da ku ka yi da Mansur da yadda yake ba ki kulawa yake kuma tarairayanki kamar ƙwai amma hakan bai hana sa wulaƙanta ki a cikin gidansa ba, hakan bai dakatar da shi daga neman wasu matan ba. Ki dube ni duk yadda nake ƙoƙarin kame kaina da killace mutumcina sai da na yi ciki ba tare da igiyoyin aure sun hau kaina ba, duk yadda nake martaba kaina sai da ƙaddara ta ja ni izuwa can inda ban san kowa ba, na yi zaman kaina a cikin gidan karuwai". Ban ƙarishe zancen ba sa boda kukan da ya kufce mini da ƙarfin gaske, ina yi Amira tana taya ni a haka Anty Sawwama ta zo ta iske mu ta din ga ba mu baki da kuma yi masa nasiha tare da ba musalai kala daban-daban.

Wunin ranar tare muka yi shi da Amira sai da muka yi sallan magrib Umar ya shigo ya shaida mana cewar wai ana magana da Amira a waje in ji mijinta. Kafin mu fito daga ɗakin har ya shigo ciki tare da Yaya Alhassan da ya dawo daga masallaci muka iske su a falo suna gaisawa da Anty Sawwama. Idanuna na tsayar ƙar akan fuskar Mansur tabbas kamanninsa bai sauya ki da da ɗan taƙi ba, amma ya lalace ya rame ya yi baƙi ƙirin da shi tamkar wanda ya yi taimama da garin gawayi.
Chapter 57 · 0% Book details