← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 72

Sashe 13

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Duk biyun sun yi kafin su kwanta wannan bacci da ka shigo ta tarar da su suna yi". Ya jinjina kansa yana miƙe wa tsaye"ki tada su ki yi musu wanka ki shirya su za mu fita tare". Yana dire zancen ya bi wata ƙofa ya bar cikin falon. Na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya ina duban Altine da take tayar da yaran ta riƙe hannunsu suka shige cikin ɗakinsu, na koma inda na taso na zauna gabaɗaya yunwa ta addabe ni, ina zaune a wajen ya fito ya sake shiga cikin wani farin sol ɗin yari haka nan ya bar kansa ba tare da ya saka hula ba amma da dukkan alamu ya gyara gashin don har wani ƙyali da sheƙi yake yi. Sai baza ƙamshi yake yi kamar wanda aka yi ɓari durom ɗin turare a jikinsa.
Ya nema waje ya zauna yana murza zoben da yake hannunsa ya ce"me ye sunanki?".

A nutse na furta"sunana Amatullah".
"A ina kike da zama sannan su waye iyayenki?".
"Mahaifina ya rasu mahaifiyata kuma ba na tare da ita yanzu, hasalima ni kaÉ—ai nake zaune a garin nan". Ya É—ago ido yana duba na"faÉ—aÉ—a min bayanin ban ga ne ba".

Na rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa kana na ce"ina zaman kaina ne bisa wasu dalili da suka tirsasa faruwan hakan".

"Mace mai zaman kanta, karuwa kenan ko kuma magajiya?". Da hanzari na É—ago ido ina kallonsa wanda shi É—in ma ni yake kallo a ci gaba da maganan.
"Idan na faÉ—a ba daidai ba sai ki gyara min".
Na girgiza kaina"haka ne yadda ka faɗa". Fitowar Aryan da Ayan shi ya hana sa furzo da zancen da ya yi niyya ya tashi tsaye ya je ya riƙo hannunsu suka fita, Altine sai washe baki take yi tana ɗaga musu da faɗin su kawo mata tsaraba. Ta wuce ta shige ciki ta bar ni a wajen, baƙin cikin kalaman da ya watsa mini ya sanya har sai da na zubar da hawaye, na ji duk son da nake ji wa wannan aikin da zumuɗin da na yi a lokacin da na yi katari da samun aikin duk ya fita daga raina. Tabbas ina son wannan aikin sai dai ba zan juri wulaƙanci wannan mutumin da kuma cin zarafin Altine a gare ni ba.
[12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

_____________________________________

Page 4️⃣9️⃣

Rawan da ƙafafuna suka soma yi shi ya tilasta mini zama dirshan irin na ƴan bori, ina jin ƙirjina yana bugawa da ƙarfi da ƙarfi. Ji na yi kamar na tashi na ruga da gudu na fice daga cikin gidan, tabbas na shiryawa dukkan ƙabuluaben da zai biyo bayan samun wannan aikin sai dai ban taɓa zaton zai zo mini a ranar farko ba.
Yunwan da ta ci gaba da ƙwaƙwulan ƴaƴan hancin cikina har ina jin mayar ana musayar kifiyoyi a cikin cikina.

Ba tare da na yi shawara da zuciyata ba na tashi da nufin tafiya don har cikin raina na ji cewar ba zan iya juran wannan cin mutuncin da tozarcin ba, ina fitowa harabar gidan na ga an wangale gate É—in mota tana shigowa, na tsaye a inda nake har ta daidaita parking ta fito ta iso inda nake.

"Ya na ganki a nan?".

"Ranki ya daÉ—e zan tafi ne na ga yamma ta na ta gabatowa".

"A'a wani yamma ne ta yi yanzun dududu ma ƙarfe nawa ne? Mu koma ciki". Daga haka ta yi gaba ba tare da ta tsaya sauraron jin abin da zan faɗa ba, ba ni da wani zaɓi da ya wuce na bi ta kamar yadda ta buƙata, don haka na bi ta a baya a har cikin falon gyalen kanta ta yaye yayin da take zama akan kujera tana mayar da numfashi.
"Ki zauna mana". Amon sautinta da ya sauƙa a masarrafar jina ya yi nasarar dawo da ni cikin hayyacina, na zauna a ƙasa a hankali na furta"sannu da dawowa ranki ya daɗe".
Cike da kulawa ta amsa mini da faÉ—in"yauwa Amatullah sannu ko? Ya na ji gidan shuru kaman Æ´aÆ´an ba sa nan".

Kafin na kai ga ba ta amsa na tsinkayo muryar Altine daga bayana tana faÉ—in"sun fita da Saifullah tun da ya dawo ya ce a shirya su za su fita".
"Ina suka je?".

"Bai sanar da ni inda za su ba, amma ina kyautata zaton idan suka saba zuwa suka je. Ki na son wani abu a kawo miki ne Hajiya?".
Ta ɗan lumshe idanunta kafin ta ce"ba na buƙatar komai, ku fara shirye-shiryen girkin dare tare da Amatullah, don zan yi baƙi da daren nan akwai abokan kasuwancina da za su zo mu tattaunawa. Ku shiga kicin ɗin ku duba duk akwai abun da babu ko ake buƙarin a ƙaro sai ki zo ki sanar da ni".
Daga haka ta tashi ta haura sama wanda nake kyautata zaton a nan É—akinta yake.

"To sai ki tashi mu je ko tun da dai kunnuwanki su ji abin da ta faÉ—a". Altine ta yi zancen cikin É—aure fuska tana barin cikin falon, na yi wuf na tashi na bi ta a baya muka nufin kicin É—in. Ta fara duddube-duddube can kuma sai na ga ta tsaya tare da dafe kanta ta juyo tana kallona.
"Sai ki je ki tambayo Hajiyar abin da za a dafa, in ta faɗa sai na duba na ga abin da ya dace a sayo ko wanda za a ƙaro".

"To".

Na amsa da shi a taƙaice ina ficewa daga cikin kicin ɗin, ɗakin Hajiyar na nufa na tsaya daga ƙofar ina yin sallama sai da na yi baki biyu a na ukun ta amsa ban shiga don a tunanina bai dace na shiga har cikin turakarta ba a matsayinta na matar aure, don na sha ji n ana cewa ɗakin mace sirrinta ne.
Ta fito jikinta É—aure da farin towel da ya tsaya daidai gwiwanta, na rusuna na gaishe ta ta amsa mini cikin wani irin yanayin da gaba É—aya na kasa gane kansa.

"Amatullah lafiya?".

Na ɗan duƙa kaɗan kafin na amsa mata cikin faɗin"daman Anty Altine ce ta ce na zo na tambaye ki abin da za a dafa". Ta ɗan shafo saman goshinta kafin ta ce"a yi fried rice, fine apple and coconut drink, sai a soya kaji a yi paper meat". Tana gama lissafa mini jerin gwanon abubuwan da za a yi ta koma cikin ɗakin tare da turo ƙafan ta rufe gaf, na ja ƙafana na koma cikin kicin na sanar da ita abin da ta faɗa, ba ta ce da ni komai ba ta ci gaba da abin da take yi.
Ta nuno mini wasu albasa ta ce na yanka su yayin da take ficewa daga cikin kicin ɗin, babu jimawa ta dawo muka ci gaba da aikin tare sai dai ba ta ce wa da ni uhm balle umm da zaran ta ba ni umarnin abin da zan yi ba ta ƙara cewa da ni komai. Aka kawo wasu kayan wanda duk dangin kayan marmari ne, ta ce na wanke su na yi kamar yadda ta faɗa aka zuba tuban da ayaba da inibi a cikin wani ƙayataccen kwanon gilashi, aka haɗa wanda za a markaɗa a yi lemon da za a yi. Muna gama aikin ana ƙiran sallan magrib har wani juwa ne yake ɗiba na tsabar yunwar da nake ji, idanuna suka yi ƙulu-ƙulu har wani dishi-dishi nake hangowa.

Muka haÉ—e komai muka jere shi akan dinnig table, ni na wanke kwanukan da muka yi amfani da su wajen gudanar da girki na tsaftace kicin É—in tsaf. Kana na je na yi alwala a inda na yi alwala na nema wani É—an wajen na shimfiÉ—a É—an kwalina na yi salla, don ba na so na je falo Hajiya ta fito ta ganni ko kuma na iske ta a ciki na hana ta rawan gaban hantsi.
Sai da na iddar da sallan na tashi na shiga ciki kamar yadda na yi tsammani kuwa na iske ta zaune a falon tana latsa wayarta da yake hannunta. Na durƙusa na gaishe ta ta amsa mini ba tare da ta ɗago kanta ta kalle ni ba.

"Ina Altine take ne?".

Bakin na ba ta amsa Altine ta iso wajen ita ma ta zube tana yi mata sannu da hutawa. Ba ta amsa ba ta É—ago kanta tana kallon mu gabaÉ—aya kana ta ce"Altine me yasa ba ki kai ta É—akinki ba, ina daga É—akina na hango ta ta taga na ga tana salla a cikin garden. Ki ja ta a jikinki don daga yau tare za ku na gudanar da dukkan ayyukan cikin gidan nan, sannan a É—akinki za ta dinga yin komai idan ta zo gidan nan".

"Ba matsala ranki ya daÉ—e yadda kika ce haka za a yi, ai faÉ—a na ki ne cika wa kuma nawa".
"An zuba wa Saif abincin shi ne, sannan kuma kun É—eba naku ne?".
Altine ta gyara zama kafin ta ce"na zuba masa komai, sannan mu ma na É—eba mana na mu".

Ta jinjina kanta"to ku je ku ci mana, na ga dare yana yi kuma Amatullah za ta koma gida".

"To ranki ya daɗe, tashi mu je ke kuma". Altine ta yi zancen tana kallona, ta tashi na bi ta a baya ɗakuna uku ne jere da juna a cikin falon wanda ɗaya na su Aryan ne, na tsakiyan kuma kamar a rufe yake ba a buɗe sa, na ƙarshen muka shiga wanda ya kasance nan ne ɗakin Altine ta ido ta nuna mini wajen zama tana faɗin"bari na je na ɗauko abincin".

Na yi zumbur na miƙa"Anty bari na je na ɗauko". Ta galla mini harara"ki je ina ɗin malama? Dalla koma ki zauna ba na son kinibibi da rawar kan banza da na wofi". Tana dasa aya ta juya ta fice daga cikin ɗakin tare da bankaɗo ƙofar ɗakin har sai da ya ba ta wani sauti, a sanyaye na zauna na tallafe kuncina, har ta je ta dawo ban gusa daga inda nake ba ta shigo da kula da flate a hannunta ta dosara mini a gabana.
Chapter 13 · 0% Book details