← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 72

Sashe 38

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jikina a sanyaye tamkar wacce aka zare wa laka daga cikin jikinta. Muryata can ƙasa na yi sallamar yayin da nake shiga cikin ɗakin Hajiya Babba sai da na yi baki huɗu ana biyar ɗin aka amsa mini tare da ba ni iznin shigowa, na shiga na zauna a ƙasa yayin da ita take bisa kujera tana latsa wayarta na gashe ta a amsa mini ba tare da ɗago kai ta kalle ni ba.
"Hajiya an ce kina nema na". Sai da ta salwantar da wasu mintuna kafin ta ce"e daman ƙiranki na yi na yi inda muka kwana da zancen nan nakin. Ya kamata zuwa yanzu mu san matsayar mu mu kuma san inda za mu ɗaura idan muka tashi".

Sai da na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya mai nauyi kafin na sama zarafin faɗin"Hajiya in sha Allah kwana kusan nan zan zo miki da magana mai ƙarfi. Ina ta yin iya ƙoƙarina ganin ban ba ki kunya ba...". Tun kafin na rufe bakina ta doka mini tsawan da sai da ta tursasa mini runtse idanuna.
"Ki rufe min baki ba dogon surutu na ƙira ki ki yi min ba, na ba ki nan da wata biyu idan kika gaza aiwatar da abin da furta. A iya wa'adin wannan lokacin kike da damar da za ki yi duk wani abin da za ki yi idan kika wuce hakan ko da da awa guda ne tabbas sai na wulaƙanta ki kuma na wulaƙanci fiye da zatonki. Sannan na haɗa miki kayanki ki bar min cikin gidana".

Cike da yarda da kaina na furta"in sha Allah ina sa ran kafin wannan lokacin ma na gama haɗa komai". Ta galla mini wani uban harara kana ta soma furzar da zancen da yake cikinta"ya rage na ki ki yi duk abin da kika ga ya fi dacewa da tsari da ginin rayuwarki. Ni dai na riga da na tsayar da magana a matsayina na mai gida kuma mai cikakken iko. Don ba zai yiyu na gina ɗakuna sa boda kasuwanci kuma ke ki zo ki tare a cikinsa ba tare da ki na tsinana komai ba". Cike da girmamawa na ce"in sha Allah". Ta ɗaga mini hannu alamar na tashi na ba ta waje haka na yi mata fatan tashi lafiya, jikina a matuƙar sanyaye na dawo cikin ɗakina kamar ruwa hakan na zube akan tabarmata ina mayar da numfashi tamkar wacce ta yi gudun ceton rai. Tunanai marasa kan gado da tushe suka soma ziyarta cikin kwamyanta da ta toshe wajen guda.

Ji na yi ba zan iya jiran safiya ta yi ba sa boda yadda nake tsananin son magana da Zinariya, wannan dalilin ya tilasta mini tashi daga inda nake kwance na fito da zummar zuwa ɗakin Zinariya sai dai na hango ƙofar an garƙame shi da kwaɗo, murmushi mai nauyi na ja na fesar daga bakina tunawa da na yi cewar ta sanar mini za ta fita ba za ta kwana a gida ba. Dole ƙanwar naƙi na koma cikin ɗakin na kwanta ina ta tunanin mafita da hanya mai ɓullewa a gare ni, a haka har wani bacci mai nauyin gaske ya yi nasarar ɗaukarta. Sanyin asubahin da ake busawa shi ya na ratsa cikin jikina shi ya yi nasarar farkar da ni daga nauyayyen baccin da ya kwashe na tashi da ƙyar na je na yi alwala na zo na gabatar da sallan, nan inda na yi sallan na zauna na zabga wani uban tagumi yayin da tunani kala daban-daban suke ziyartar cikin kwanyanta a lokaci guda.
Kyakykyawan ajiyar zuciya na sauƙe daidai lokacin da na ji an dafa kafaɗana na waigo a hanzarce don ganin wane ne, idanuna suka sauƙa akan fuskar Zinariya da yake ɗauke da maɗaukakin annuri fuskarta tamkar gonar auguda yayin da bakinta ya kai har kunne.

"Kin dawo ke nan?". A jefa mata tambayar yayin da take haye wa kan tabarman ta zauna tana fuskan ta na.
"Wai akan wannan abun kike kwana? Lalle ki na ƙoƙari kuma ki na rayuwar ƙunci. Wannan tabarman ai ba shi da maraba da kwanciyar ƙasa".
Taƙaitaccen murmushi na yi kafin na ce"yaushe kika dawo? Akwai matsala fa".

"Ƙarfe uku da wasu mintuna na shigo cikin gidan nan, na so na buga muku ƙofa ma sai kuma na fasa haka na yi kwanan farin ciki ina jin kamar garin Allah ba zai waye ba".
"Me ya faru haka na farin ciki?". Ta ajiye mini wasu takardu akan cinyata kafin ta ce"kin ga wannan takardun da kike gani takardun tanƙamemen gida ne na beni a can cikin birnin tarayya". Na waro idanuna cike da mamaki ina juya takardar.

"Ke kuwa waye ya ba ki wannan kyautar?".
Ta yi fari da idanunta wanda izuwa yanzu na fahimci kamar hakan É—abi'arta ne musamman a lokacin da take cikin farin ciki.
"Fitan da na yi daren jiya ne aka ba ni shi kyauta, ko kuma na ce miki aka mallaka mini shi halak malak, na tabbatar yau wasu za su yi kwanan baƙin ciki a cikin gidan nan kuma da yardan Allah wannan shekarar ni ce wacce za ta lashe gasar zakaran gwajin dafin da Hajiya Babba take shiryawa a duk ƙarshen shekara".

"Wacce gasa ke nan kike magana a kai?".

"Wata gasa ce da Hajiya take shiryawa duk ƙarshen shekara, a cire wacce ta fi samun kyaututtuka, mu'amala da manyan mutane da kuma samun alkhairai. Wacce ta ciri tuta ita ce gwarzuwan wannan shekarar".
Taɓe bakina na yi don wannan ba shi ba ne a gabana, wutar gabana ma kaɗai ta ishe ni ba sai na ƙara wa kaina wani nauyi da damuwar damuwa da waɗanda ba su san ina yi domin su ba.

"Jiya Hajiya ta ƙira ta yi buƙac ta ji yanda ake ciki, na roƙe ta ta ba ni lokacin inda a ƙarshe ta ba ni watanni uku rak. Idan har wa'adin wannan lokacin ya cika ba tare da na cika alwashin da na yi to sai duk abin da ya faru ni na jaza wa kaina. Tun da daman an ce duk abin da ya sama shamuwa ta zargi watan bakwai". Ta ɗan yi jim alamar zantukan nawan ita ma ya caja mata kanta. Na riƙo hannunta na sanya cikin nawa kafin na ci gaba da cewa"yanzu ya ya kike ga za a yi?".

"Gabaɗaya kaina ya kulle ban san abin da ya dace mu yi yanzu ba, amma ba ri na ƙira wanda na miki na sani a otel ɗin".

"Yauwa don Allah ƙira shi mu yi".

Ta É—aga wayarta ta lallatsa kafin ta kara a kunnenta.
"Mai gida kana wajen aiki ne?". Ban san wani amsa ya na ta ba na ji ta kuma ce wa"zan zo na same ke". Daga haka ta zare wayar daga kunnenta.
"Tashi ku je?".

"Ina za mu je?".

"A gabanki fa na yi waya yanzu, otel É—in za mu je mu same shi don ya fahimci mun É—auki abin da muhimmanci sosai".
Ta furzar da zazzafan iska daga bakina kana na ce"otel dai? Ki rufa mini asiri tun da uwata ta haife ni ban taɓa zuwa ko da cikin harabar otel ba kai ko wucewa ta gate din ban taɓa yi ba, balle har na shiga cikinsa".

"Ke dalla! Ki kwantat da hankali mene ne a cikin zuwa otel ɗin?. Ke dai kawai ki tashi mu je ai ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba".

Ta ƙare zancen tana riƙo hannuna maimakon na tashi sai na turje"kin san fa zan je wajen aiki". Ta galla mini wani uban harara tamkar idanunta za su faɗo ƙasa"idan ba za ki je ba ne ki fito fili ki faɗa min, ba sai kin tsaya ki na ta wani kewaye-kewaye ba Amatullah".

Na ɗan yi shuru na wasu mintuna kafin na furta"shi kenan mu je mu amma don Allah kar mu daɗe". Ba amsa mini ba ta yi gaba ina bin ta a baya har muka fice daga cikin ɗakin. Muka fito bakin hanya ta tara mana abin hawa muka hau, tun da muka soma tafiyar ƙirjina yake bugawa da ƙarfi da ƙarfi ban sama sauƙi ba har sai da na ji an taka birki hakan ya ba ni damar cira kaina ina ƙarewa inda muka zo kallo.
Sunan otel ɗin na karanta da aka rubuta da manyan baƙi, yana walƙiya da sauya kaloli daga shuɗi zuwa ruwan hoda.

"Sarauta hotel".

"Tabbas Saraute hotel ke nan fito mu je". Furucin Zinariya ke nan da ya yi nasarar dawo da ni cikin hayyacina daga karatun wasiƙan jakin da na afka, sai da na dogon numfashi na fesar kafin na sama damar saƙalo ƙafafuna waje daga cikin napep ɗin kafin na fito da ragowar sauran gangar jikina.
Na ƙare wa wajen kallo ganin yadda mutane suke ta hada-hada cikin kwanciyar hankali da nutsuwa, maza da mata a cunkushe a waje guda manyan motoci ne suke da shige da fice a waje tamkar ana wani gagarumin taro. Duniya-duniya inji kwaɗo da ya ji shi a cikin ruwan zafi, tabbas Ubangiji shi kaɗai ya bar wa kansa ilmin sanin abin da gobe za ta iya haifar wa. Yau wai ni ce a cikin otel inda duk nake ban ta ko fa mafarki zuwa ba sai ga shi yau ƙaddara ta jawo ni idan tunanin bai taɓa tunanin kawo ni ba.

Ganin yadda duk na rasa nutsuwata ya sanya Zinariya riƙo hannuna muka soma tafiya muka shiga ciki muka zauna a bisa wasu kujeru da aka tanada a wajen, ta ɗaga waya ta ƙira shi tare da sanar da shi cewar mun iso babu jima wa na hango wani mutum mai jiki ya nufo inda muke fari ne sol sannan yana da saje da kuma ƙasunba a bisa fuskarsa ya yi shigar ƙananan kaya ya sanya hular da ake wa laƙani da p-cap a kansa ya zo inda muke zaune ya zauna kusa da Zinariya, ya miƙa mata hannu suka tafa kafin ya ce"ina jinki don aiki nake yi na baro na zo na saurare abin da yake tafe da ke. Don kawai ke ɗin Zinariya ce". Da alama zantukansa sun yi tasiri a cikin zuciyarta da hakan ya sanya ta darawa sosai, har sai da sautin dariyar ya fita.
Chapter 38 · 0% Book details