Sashe 30
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk da abin da ta yi mini ya yi mini matuƙar ciwo tare da tusa mini takaici amma ban nuna mata ba ko a fuska, maimakon hakan ma murmushi na sakar mata ina tsayar da idanuna ƙar a kanta.
"Ni ba kowa ba ce a cikin gidan nan face ƴar aiki kamar ki, wacce ta fito aiki domin rufa wa kanta asiri da kuma samun abin da za ta ɗauki nauyin buƙatun rayuwarta". Ina dire zancen na juya na yi ficewa ta ina jin wani gigitaccen tsawan da ta dokawa su Aryan yayin da nake fice wa daga cikin ɗakin ko kanzil ban juyo na ce da ita ba. Kai tsaye ɗakin Altine na nufa wanda kai tsaye zan iya ƙiran da ɗakinmu na shiga banɗaki na ɗauro alwala na zo na gabatar da sallan zuhur, na ɗaga hannayena sama ina jero kirari ga Ubangiji kana na shafa doguwar addu'ar da na yi wanda dukkaninta addu'ar neman rahama da gafara ne ga Abba. Wanda babu ranar da za ta fito ta faɗi ba tare da na yi tunanin sa ba ko kuma ya faɗo mini a cikin raina ba.
Hoton da na ɗauko a sashin Saif na tsince ɗaga gefen hijabina da na ƙulle na zura wa hoton idanuna yayin da wasu tambayoyi masu rikitarwa suke yi mini yawo a cikin kwanyata.
Tabbas akwai buƙatar na nemo wata iriyar alaƙa ce tsakanin Muhammad Taufik da kuma Sheikh Dawood ko kuma na ce baƙin Balarabe kamar yadda na laƙanci haka daga wajen Baba Mai gadi.
Numfashi mai nauyi na ja na fesar daga cikin baki sa boda tunawa da na yi da Amira, babu wanda yake saurin gane ina cikin damuwa ko da kuwa ban furta ba sama da ita, babu abin da ta ƙi jini a rayuwarta kamar ta ganni cikin ƙunci. Mun shaƙu da ita sosai ta yarda ba na shakkan sanar da ita dukkan sirrina domin ba ni da kaufi akan ta, ina jin ta tamkar ƴar uwar da muka rayu a mahaifa guda da ita kana muna fito duniya a tare kuma a lokacin ɗaya.
Na san ta yi nemana har ta gaji ta sadadu ta fawwalawa Allah komai, ko har yanzu suna tare da Mansur ko kuma Æ™addara ta raba su, wataÆ™ila izuwa wannan lokacin sun mallakin junansu sun cika burinsu na zama miji da mata oho? Æoyayyan ajiyan zuciya na sauÆ™e ina zame wa na kwanta sa boda sarawan da kaina yake yi mini tamkar ana buga mini guduma.
Ban yi nisa a cikin baccin ba na ji sauƙar ruwa mai sanyi a fuskana babu shiri na tashi sai dai duk da firgitan da na yi hakan bai hana ni kamo sunayen mahaliccina guda ɗari babu ɗaya ba cikin bakina.
Na cira kai ina duban Altine da take tsaye a kaina babu alamar ranƙwafawa tamkar wacce ta haɗiye taɓarya. Raina ya tuntsura yana tafasa tamkar talgen da yake bisa wuta yana ɓararraka.
"Kin fi kowa sanin cewar ai ba bacci ne ya kawo ki ba, da za ki zo ki yada baki ki na baccin asara wanda babu gaira babu dalili".
Tsam na miƙe akan ƙafafuna"na lura duk yadda na kai ga ƙoƙarin ganin na ba ki girmanki na kuma mutunta ki ba kya ganin hakan. To gwara na fito miki a mutum na fito miki a yadda kike so, Ina so ki sani ni fa baiwarki ba ne a cikin gidan nan hasalima matsayinmu ɗaya. Ki riƙe girmanki ni ma zan tabbatar da cewar na yi miki biyyaya a matsayinki da wacce kike gaba da ni amma idan kika zubar da mutuncinki babu abin da zai hana ni sanya ƙafa na take sa, ai daman idan malam bai ji kunyar hawa jaki ba to jaki ba zai ji kunyar jefar da shi ba".
Ina rufe bakina kawai na ga ta ɗaga hannu da nufin zabga mini mari na yi caraf na riƙe hannunta.
"Kar ki kuskura ki ƙara yin gangancin ɗaura hannunki a jikina da sunan mari. Don duk ranar da kika ƙara maimaita haka zan yi miki abin da tarihin rayuwarki ba zai taɓa cika idan babu shi". Ina dire zancen nawan na sakar mata hannunta na juya ɗauki hoton na ƙulle a gefen hijabina na fice daga cikin ɗakin, kai tsaye kicin na nufa na iske har ta fara aikin girkin abincin ranan, na nema waje tsaya tare da naɗe hannayena a ƙirjina ban taɓa komai ba har ta shigo cikin kicin ɗin tana ta faman harare-harare. Cikinmu babu wanda ya ce da wani ko kanzil. Haka nan ban motsa daga inda nake ba balle na yi wani aikin har ta gama girkin ta sauƙar ta ɗauko kula za ta zuba a ciki, ni ma na ɗauko plate na ajiye mata ta ɗago ido ta kalle ni kamar za ta yi magana sai kuma ta yi shuru.
Ganin ba ta da alamar zuba mini ina ganin ta gama zuba wa a kulan na ɗauki kudayin na zuba wa kaina na ɗauko na koma gefe, na soma ci. Ina ganin ta ta gefen idona sai banko mini harara take yi kamar idanunta za su faɗo ƙasa. Ina gama cin abincin na wanke plate ɗin na koma ɗaki na yi alwala na gabatar da sallan asr, ina zaune kan sallayan ta shigo ko sallama babu ni ma ban damu don ko ɗaga kai ban yi ba balle na gan ta.
Haka kawai na ji gabaɗaya zaman gidan ya fita akaina, don haka na tashi na fito falo ina fito wa na tarar da Hajiya tana sauƙo wa daga beni yayin da su Aryan suke biye da ita a baya.
Muka sakar wa juna murmushi ni da ita yayin da muka haɗa ido kafin na yi mata sannu da fito wa ta amsa mini cikin sakin fuska. Da hakan ya ba ni damar amayar da roƙona.
"Hajiya daman ina so na je gida ne idan babu damuwa".
"Za ki iya zuwa Amatullah ai na ga babu wani aikin ma da ya rage, mun yi waya da Saif ba za su dawo yanzu ba. Ni ma kuma yanzu zan fita shago ne akwai kayan da zamu haɗa su Aryan muka zan ajiye su a wajen Hajiyarmu. A taƙaice dai dawowarmu mu ma zai iya kai wa dare, mu je na sauƙe ki a hanya".
Cike da jin daɗi na ce"ina godiya Hajiya". Na riƙo hannun Ayan muka fita zuwa wajen motar muka shiga, ta ja motar muka fita a hanya ta sauƙe ni yayin da su kuma suka wuce.
Ban yi tafiya mai nisa ba na iso gida ina shigowa na hango Zinariya a ƙofan ɗakinta tana girki. Muka sakarwa juna murmushi kafin ta ce"kin dawo kenan? Ɗazu na leƙa ai ba kya nan?".
Na gyaɗa mata kaina yayin da nake zama akan dakalin ƙofar ɗakinta.
"Yau gidan shuru lafiya kuwa?".
"Kin san yamma ta yi ai yanzu kowacce ta shirya ta tafi waje kwastomanta". Na jinjina kaina ina girmama lamarin a cikin raina, haka ta yi ta ja na da hira har izuwa lokacin da wayarta da take cikin É—aki ta soma ruri.
"Taimaka ki ɗauko min wayata a cikin ɗaki. Kin fi kusa da ƙofar". Kaina kawai na gyaɗa mata yayin da nake tashi na shiga cikin ɗakin ina ɗaukar wayar ƙiran yana tsinkewa. Hoton fuskar wayar ya bayyana idanuna suka kai kansa. Take na ji ƙirjina ya harbawa tabbas indai ba ƙarya idanuna suke yi mini ba hoton Abbinsu Aryan ne tare da Zinariya a fuskar wayar kamar za su rumgume juna tsabar kusanci da jikinta ya yi da shi. Jikina ya ɗauki rawa ina ƙara ware idanuna don tabbatar da sahihancin abin da suke nuna mini.
[12/4, 7:36 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*
Â©ï¸ Maimuna Tijjani Iyam
______________________________________
Page 6ï¸âƒ£1ï¸âƒ£
Jikina gabaɗaya ya ɗauki rawa tamkar wacce aka jona wa wutar lantarki, na kasa yin komai illa idanuna da na ci gaba da ƙurawa hoton fuskar wayar.
"Ba ki sa ma wayar ba ne?". Tambayar da Zinariya ta jefo mini daga waje shi ya dawo da ni cikin hayyacina daga karatun wasiƙan jakin da na afka. A lokacin aka ƙara ƙiran wayar a karo na biyu na juya da nufin zan kai mata muka yi kiciɓus da ita a ƙofar ɗakin tana shigowa, na miƙa mata wayar yayin da ni kuma na fice waje. Na zauna akan kujerar da ta tashi tare da zabga tagumi tamkar wacce aka aikowa da saƙon mutuwar wani shaƙiƙinta.
Ina zaune a wajen har Zinariya ta gama wayar ta fito ta ja kujera ta zauna, na bi ta da kallo ganin yadda fara'arta ya ƙaro sam bakinta ya kasa rufuwa sai washe haƙwara take yi tamkar wacce aka yi wa wani gagarumin kyautar a zo a gani.
"Yau ina cikin alkhairi dumu-dumu, tun da na wayi gari na ke cin karo da alkhairi". Ta yi zancen cikin maÉ—aukakin farin cikin da ya bayyana har a cikin furucinta.
"Me ya faru haka? Na ga gabaɗaya fara'arki ta ƙaru".
"Alhajina ne ya ƙira ni yanzu muna gama wayar na ga alert miliyan guda a cikin asusun ajiyata".
Na bi ta da kallo kana na ce"miliyan guda? Wannan maƙudan kuɗaɗen na mene ne haka?".
Ta yi fari da idanunta kafin ta furta"kyauta ce kawai daga masoyi zuwa masoyiyarsa, ranar Alhamis zai aiko mota a ɗauke ni zuwa can garin Abuja ranar juma'a na ƙara kimtsa kaina na jira dawowarsa a yammacin ranar don ba ya ma ƙasa gabaɗaya. Ya yi mini alƙawarin tare da ni zai yi hutun ƙarshen mako kuma sa boda ni mussamman ya baro duk abin da yake yi ya zo shi".
"Irin wannan hidima haka amma dai babu É—awainiyyar iyali akansa ko?".