← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 72

Sashe 29

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Uncle Saif ya ce babu kyau yawan suturu". Ya ba ni amsa ba tare da ya yarda mun haÉ—a ido da shi ba.
"Ba irin wannan maganar yake nufi ba. Yanzu dai ku zo mu je na yi muku wankan sai ku dawo ku yi wasan".

"A'a yanka mu za ta yi". Ayan ya yi zancen hawaye suna ciko masa idanunsa ga jikinsa da ya soma rawa sosai.
Cikin mamaki na ce"waye? Waye zai yanka ku kuma?". Duk su biyun suka sadda kawunansu ƙasa ba tare da sun ba ni amsa ba. Take na ji kifiyar tausayinsu ta ratsa zuciyata tare yin pieces da ita, jikina ya yi la'asar na rasa ta inda zan fara shawo kansu, sai da na ja dogon numfashi na fesar kafin na yi amfani da dabarar da ta faɗo mini a rai tamkar faɗuwar aradu.

"Ku zo mu je na yi muku wanka na shirya ku babu wanda zai ji". A tare duk su biyun suka ɗago kai suna kallona kamar za su miƙa wuya sai kuma Ayan ya jan hannun Aryan tana faɗin"ka zo mu tafi mu yi wasan mu". Daga haka ya janye shi suka koma inda suka wasan na bi su da kallo ina tunanin mafitar da ta dace.
[12/3, 7:18 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

___________________________________

Page 6️⃣0️⃣

Na yi ɗam jim ina ta tunanin ta yadda zan ɓullowa lamarin, can na ji wani dabara ta faɗo mini a cikin kaina tamkar faɗuwar aradu, na tashi na je inda suke wasan na zauna ina faɗin"ina ma zan yi wasan ku biyu ni kuma ni ɗaya". Duk suka ɗago ido suna kallona kafin can Aryan ya ce"kin iya ne?". Na gyaɗa masa kaina alamar e, ya miƙo mini motar guda ɗaya yayin da su ma suka dauki guda-guda, muka soma yin wasan ba mu yi nisa ba suka cinye ni lamarin da ya faranta musu rai da ruhi suka daka tsalle tare da ƙyalƙyalewa da dariya kamar za su shiɗe.

"Mun ci mun cinye ki Anti".

Na ɗaga ido na kalla Aryan da ya yi zancen na ce"ai gobe ma za mu ƙara gwadawa, yanzu dai tun da mun kama wasan ku zo mu je na yi muku wanka ku sauya wani kaya ku ji sanyi a jikinki". Kamar an yi ruwa an ɗauke lokaci guda fara'a da annurin fuskarsu ya ɗauke, duk su biyun suka yi shigo har sai da na kawar da shurun ta hanyar faɗin"idan ba kya so shi kenan bari na tashi na shiga ciki". Na yi zancen ina yunƙirin miƙe wa suka riƙo hannuna.
"Anti mu je ki yi mana wankan". Murmushi kawai na yi musu muka wuce ɗakin nasun, na cire musu kayan jikinsu na ɗaura musu towel muka shiga cikin banɗakin na yi musu wanka da ruwan ɗumin da na tara a cikin bokati. Na wanke musu sumansu da mayuka da sabule gyaran gashin, na ɗauko musu towel ɗin muka fito na ɗaura su akan gadon suna ta jijjiga kansu yayin da ruwan da yake cikin sumarsu yake watso wa a jikinsa, suna ta kyalƙyala dariya.

Na ke jikin wadrode ɗin kayansu na buɗe na ɗauko musu wata jamfa launin ruwan ƙasa. Ina juyawa Aryan ya ce"Anti ni kam ba zan kayan nan ba". Ina rufe bakinsa ya diro daga kan gadon ya zo ya zaro wani wandon jeans ya ce shi zai saka, yayin da Ayan shi kuma ya dage akan ba sai saka wannan wandon ba.
"To shi kenan Anti kowa ya saka kayan da yake so kawai ko?". Aryan ya yi magana ina tsayar da idanunsa a kaina, na durƙusa a gabansa kafin na furta"ai ba zai yiyu ku saka kaya daban-daban ba, tare aka haife ku tare aka raine ku tare ku ka girma komai tare ake yi muku. Kun ga Ummi ba za ta ji daɗi ba idan aka saka muku kaya daban-daban".

Ina rufe bakina Ayan ya ce"shi kenan Anti a saka wanda Aryan ɗin yake so kawai. Ni na haƙura ba na son Ummi ta ji ba daɗi". Sosai na ji yaron ya ƙara shige mini can ƙasan ƙalbina yaro ne mai matuƙar nutsuwa ga shi sam ba shi da hayaniya balle ƙiriniya irin na yara masu shekarunsa, a ɗan saman da na yi a cikin gidan nan a lura ya fi Aryan maƙon ɗan uwansa.
Take Ayan ma ya tadae rigima ya ce shi ma ya haƙura a saka kayan da Aryan ɗin yake so, haka suka din ga yi har sai da na kawo ƙarshen muhawarar ta hanyan ɗauko musu wani kayan.
Farin riga t-shirt na saka musu mai gajeren hannu gaban rigar an yi rubutu da jan kala, na saka musu wandon jeans da tsayinsa ya tsaya daidai gwiwansu.
Na gyara musu sumar kansu ya sha musu mai tare da taje musu shi, ya yi kyau tare da ƙara yin sheƙi gami da ƙyalle, sosai kayan ya amshi jikinsu da hakan ya taimaka wajen fito da ainihin sihirtaccen kyawunsu.

Na lura su ma kansu sun san cewar kayan ya yi musu kyau don gaban madubi suka tsaya suna kallon kansu suna dariya. Na zo na tsaya a bayansu Aryan ya yi wuf ya ce"Anti ni da shi waye ya fi wani kyau? Ai na fi shi kyau ko?".

"Ƙarya ne ai Uncle Saif ma ya ce ni ne wanda ya fi kama da shi". Ayan ya mayar masa da martani cikin gaggawa, duk suka juyo gare ni suna rige-rigen yin magana.
"Waye ya fi kama da Uncle Saif a cikinmu Anti?". Aryan ya koma jefo mini tambayar a karo na biyu, kafin na amsa masa Ayan ya amshe zancen cikin faÉ—in"ai ni Ummi ta ce da Abbinmu nake kama".

"To ni ai yanzu ban san Abbin nakun ba haka shi ma Uncle Saif É—in ban san shi sosai, ina dai ganin sa ne kawai. Kun ga kenan ba zan iya bambamce da waye suke kama ba a cikinsu".

Ina rufe bakina Aryan ya juya ya je ya É—auko mini wani hoton da yake ajiye akan dirowar dake gefen gadon baccinsu ya kawo mini.
"To kin ga wannan shi ne Abbin namun". Ya yi zancen yana miƙo mini hoton na karɓa tare da zuba idanu, hoton Hajiya ce zaune ta sha wani uban leshi launin hoda da ya amshi jikinta kuma ya hau da zubin jikinta, an yi mata kwalliya a fuskarta da ta zauna a fuskar ta yi ɗas da ita tamkar da shi aka halicce ta. Wuya da kunnenta har da hannayenta sun sha ado sarƙa, ɗan kunne da kuma awarwaro. Gefenta na hagu Ayan ne zaune yayin da gefenta na dama Aryan yake zaune. Wani mutum ne fari sol tsaye a bayansu ya ɗan ranƙwafo ya dafo kadaɗun Hajiya da hannunsa guda ɗaya yayin da ɗayan hannun ya ɗaura akan Aryan, dukkansu fuskokinsu washe da maɗaukakin annuri da ya gauraye da nishaɗi, sai dai na lura hoton kaman tsoho ne don a hoton su Aryan ba za su wuce shekaru ɗaya da wasu watanni da haihuwa ba.

Sai da na saka ido sosai na gano Aryan da Ayan sam ba sa kama da mahaifinsu, duk kamannin mahaifiyarsu Hajiya Muhibbat suka kwaso kwabo da kwabo babu abin da suka bar mata, sai dai hasken ubansu da suka ɗauko. Ban yi aune ba na ji an fizge hoton tamkar za haɗa da hannuna, babu shiri na ɗago kai don ganin wanda ya aikata hakan a gare ni, idanuna suka sauƙa akan fuskar Altine ta take tsaye tana ta cika ta batse wa.
Me ye kike yi a cikin É—akin nan sannan me ye wannan hoton yake yi a hannunki?".

Ba ta jira na ba ta amsa ba ta ci gaba da balbalin wutar ba'lain da take yi tamkar za ta yi aron baki.
"Watau kin ɗauko hoto kin sa a gaba ki na ta kallo, kin zuba wa mijin mata idanuna kamar mayya kin shagala da kallonsa har ma ba ki san sa'ilin da na shigo cikin ɗakin ba balle tsayuwar da na yi a kanki. Irin ku ne wanda ake ɗaukowa daga rana a shigo da ku cikin inuwa daga ƙarshe ku ku tura mutum cikin ranar, daman ni tun ranar farko da na gan ki nake kokonto a game da ke. Tukunnan ma me ye dalilin da ya kawo ki cikin ɗakin nan?".

Murmushi kawai na yi tare da miƙe wa tsaye, na kai duba na ga su Aryan da suke tsaye da na lura jikinsu gabaɗaya ya yi sanyi ƙalau har sun kasa motsawa daga inda suke.
Sai da na yi dogon tunanin kafin na ce"daman an iyakance mini inda zan shiga ne a cikin gidan ban sa ni ba?".

"Tambaya kike yi ko kuma neman sani?".

"Duk wanda kika ɗauka a ciki daidai ne ranki ya daɗe". Na yi zancen ina ɗage kafaɗana alamar babu abin da ya sha mini kai ko ya ɗaɗa ni da ƙasa.
Na sa kai zan fice daga cikin É—akin ta jawo gefen hijabina har sai da na yi tangal-tangal zan faÉ—i Allah ya kiyaye.
"Ke har kin isa ina miki magana za ki tashi ki tafi ki bar ni? Wace ce ke kuma da me ye kike taƙama, sannan wa ye ya tsaya miki a cikin gidan da har kike jin cewar za ki iya yin duk abin da kika ga dama?".
Chapter 29 · 0% Book details