← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 72

Sashe 67

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Naira duhu uku ya zaro daga cikin aljihunsa ya ajiye mini a gabana tare da faɗin"ga wannan ki rage wani buƙatunki da shi, babu yawa ki yi maneji da shi".
Wani daɗi na ji ya cika mini rai da ruhina har sai da ya haddasa mini tsiyayar da ƙwalla zan yi magana ya dakatar da ni ta hanyar ɗaga nuni hannu alamar ba ya son jin komai daga gare ni.
"Ki yi abin da na ce miki kawai".

Na buɗe baki zan yi godiya ya kuma katse ni"ba na son wannan godiyan nakin da ba shi da iyaka. Duk abin da na yi miki ki sa a ranki cewar haka daman wani nauyi ne da ya rataya a kaina na sauƙe shi". Kaina kawai na jinjina masa kafin na furta"Allah ya saka da alkhairi ya ƙara buɗi da azurki mai amfani".

"Amin" ya Allah ya amsa da shi yayin da yake tashi ya miƙe tsaye haɗe da ƙara faɗin"babu wata matsalar ina fatan dai ko?".

"E babu komai Yaya Alhassan, tabbas a zamana da ku kun wadata ni da komai babu abin da na nema na rasa". Murmushi kawai ya yi ba tare da ya ce mini komai ba ya juya ya fita daga cikin ɗakin na raka shi da kallo har ya fice kafin na sauƙe ɓoyayyan ajiyan zuciya mai nauyin gaske. Na daɗe zaune a wajen kafin na tashi na je na nuna wa Anty Sawwama kuɗin ta yi ta sanya mana albarka tare da yi mana addu'ar Allah ya haɗa kawunanmu kana na fito na soma rage wasu ayyukan cikin gidan. Haka rayuwa ta ci gaba da gangarawa lokaci yana shuɗawa har aka dosa kwanaki biyar ba tare da Saifullah ya ƙira ni ba hakan nan du ƙiran duniyar nan da zan yi masa layinsa ba ya shiga, duk na bi na damu hankalina ya yi mummunan tashi da na zauna shuru to ba ni da aiki sai tunaninsa da tunanin halin da na jefa sa ba na sanin lokacin da hawaye yake zuba daga idona sai dai kawai na ji ɗumin su a bisa kuncina.
Duk wanda ya ganni ya san inda cikin matsanancin damuwa da ƙololuwan tashin hankali amma haka na yi ta ɓoye wa duk tambayar da za a yi miki cewa nake yi ba komai idan aka matsa mini ba sai na fashe da kuka ala dole suke haƙura su bar ni ba don sun sama abin da suke so ba.
Ranar da aka cika sati da faruwan lamarin a wata safiyar ranar lahadi ƙiran Saif ya shigo cikin wayata kafin na ɗauka ƙiran ya tsinke ina ƙoƙarin bin ƙiran ya ƙara ƙira a karo na biyu.

Jikina yana rawa na ɗaga ƙiran na soma amayar da tulin damuwar da yake kwance ƙasan raina.
"Lafiya kuwa kwana da yawa inna ƙira layinka ba ya shiga, sannan ba na ji daga gare ka ina fatan dai lafiya babu wani matsalar ko?".
Sai da ya numfasa kafin na ce da ni"ki na gida ne?".
"E". Na amsa da shi har zuwa lokacin jikina yana rawa tamkar mazari.
"Nan da awa É—aya mu na zuwa, ki sanar da mutanen gidan".

"Ku na zuwa kai da waye ke nan? Sannan lafiya zuwa haka bakatatan ba tsammani?". Na yi zancen jikina yana tsananta rawan da har sai da ya tilasta mini yin zaman ƴan bori dirshan a ƙasa ina sauraron amsar da ya dawo mini da ita muryarsa cike da rashin walwala.
"Idan mun zo za ki ga wanda za mu tare da shi, sannan za ki ji dalilin zuwan mu". Daga haka ya katse ƙiran ya bar ni da faman faɗin"hello! Hello". Har sai na fahimci ba ya kan layin kana na saduda.
"Innalillahi wa inna ilahirin raji'un!". Na furta ina dafe ƙirjina da yake buga wa fiye da kima a kimiyyance. Jikina a sanyaye na je ɗakin Anty Sawwama na sanar da ita zuwan su Saifullah, ita kan ta sai da ta tambaye ni ko lafiya na ce da ita ni ma ban sani ba. Haka na gudanar da aikin da ya kallafa a kaina cikin sanyin jiki da rashin kuzari.
Ina zaune a ɗaki na ji sallamarsu a tsakar gida na leƙo ta taga na ga tare suke da Yaya Alhassan da kuma Umar da suka yi musu jagoranci har zuwa cikin gidan suka shigo falo suka zauna, Anty Sawwama ta fito suka gaisa kana Umar ya zo ya ƙira ni na fito na gaishe su, ganinsa tare da Muhammad Taufik ya sanya jikin ƙara sanya tamkar kazar da aka gauraya a cikin ruwan gishiri, na je musu ruwan sha na ajiye a gabansu zan koma ciki Yaya Alhassan ya ce na dawo na zauna haka na yi na koma na zauna kaina a ƙasa ina sauraron yadda ƙirjina yake bugu tamkar zai faso allon ƙirjin ya fito waje ya taka rawan disko.

"To kamar yadda na riga na sanar da kai tun a waje wannan shi ne dalilin zuwanmu, don na ga ya dace ku san abin da yake faruwa. Sannan aminina Sultan ya buƙaci ya zo don ya gabatar da godiyansa a gare ku a madadin dukkan ahalinsu".
Saifullah ya yi zancen a dunƙule da ya sanya kan Anty Sawwama kullewa, take Saif ya warware musu duk yadda muka yi da shi akan wannan memory card ɗin akan kowa. Anty Sawwama ta cika da mamaki don a ta yi zaton hakan ba, Yaya Alhassan ma duk da Saif ya riga da ya sanar da shi zancen tun kafin su shigo ciki sai da ya cika da mamaki ainun.

A wannan karon Muhammad Taufik ne ya karɓe zancen cikin faɗin"tabbas sa'ilin da na saurari wannan sautin muryar ba zan iya fasalta tashin hankalin da na shiga ba, duk dauriya da juriya irin zuciyar na miji sai da na ji hawaye sun zubo daga idanuna na kasa fassara kaina da har sai da hankali na gushe daga gare ni. Saifullah shi ya kasance a tare da ni a cikin wannan yanayin mai tsauri ba zan taɓa mance wa da shi a cikin tarihin rayuwata, cikin hikima da fasaha muka tunkari Sheik da zancen kuma cikin ruwan sanyi ya amsa cewar duk abin da muka ji haka ne, kuma tun daga ranar da lamarin ya faru shi kansa ya yi nadama mai tsananin gaske, tun daga lokacin ya kasance cikin zulumi, fargaba da kuma jiran fitan sautin muryar a duniya sai dai kuma shuru lamarin da ya karya masa zuciya ke nan. Tsoronsa ɗaya kar asirinsa ya tuno a idon duniya kar kima da darajarsa ta gushe a idanun jama'an da suke yi masa kallon tamkar waliyi a gare su, haƙiƙa manyan mutanen da ya sani da tarin ƴan siyasan da yake mu'amala da su za su yi ɓatan dabo, don babu wanda zai so ya lalata tafiyar siyasansa sa boda ƙoƙarin kare masa martaban sunansa. Tabbas ya aikata laifin da ya yi ikirari sai dai yanzu ya yi nadama matuƙa don na hangi hakan a cikin idanunsa, Malam ya yi nadama matuƙa don har sai da ya yi ƙwalla kuma ya nema gafara a bisa samar da ni ta hanyar da ba ta dace ba, ya tara dukan iyayensa ya sanar da su abin da yake faru ya kuma roƙi yafiya da gafaransu. Tabbas ba mu san inda za mu sanya kanmu ba idan maganan nan ya watso a duniya, ba mu san wani hali Malam zai shiga ciki ba, na zo ne musamman na yi miki godiya a bisa madadin dukkan ahalin Sheikh Dawood akan killace wannan sirrin da kika yi kika kuma ɗamka sa a hannun da ya dace har ya iso gare shi a cikin sigar da ya dace".

Tun da ya soma maganar nake kuka marar sauti har ina ƙoƙarin shiɗewa, sai da Anty Sawwama ta riƙo hannuna tana murzawa a hankali cikin sigar lallashi da kwantar mini da hankali.
Muryarta a shaƙe sa boda kukan da ya gama galabaitar da ni na soma magana a hankali, sautina ba ya fita yadda ya kamata.

"Yaya Alhassan ka yi haƙuri na kasa bin umarninka, na kasa yi maka biyayya wallahi zuciyata ce take azalzala ta yayin da ni kuma na gaza jure wa har sai da na biye mata. Ban aikata hakan don na nuna maka ba ka isa da ni ba, ban aikata hakan don nuna maka cewa ba ka kai ka kafa mini umarni na bi ba. Yaya Alhassan na tuba na you nadama na gurfana a gabanka ina neman afuwa da yafiyarka".
Falon ya yi tsif babu abin da ake ki face sautin kukana.

Cikin taushin murya Yaya Alhassan ya soma cewa"Amatullah ba ki yi min komai hasalima kin yi tunanin da ni kaina ban yi shi, wallahi na ji daÉ—in abin da kika yi na kuma cika da alfaharin kasancewarki Æ´an uwa a gare ni. Kin yi wani babban lamarina da ya dace a yaba miki kuma a jinjina miki".
"Ƙwarai don tabbas kin zamo silar wanzar da haske a cikin rayuwata kin haska min hanyar da zan yi tafiya ba tare da ɗan jagora ba. Ba zan da wani baki zan yi miki godiya Amatullah". Muhammad Taukif ya yi zancen cikin sanyin murya harrufan har suna harɗe wa waje guda.

"Ba na buƙatar godiya don na yi hakan ne domin Allah ba don a gode mini ba". Na yi zancen cikin ƙarfin tare da tashi na koma cikin ɗaki ina shiga na zubo akan katifa ina ci gaba da kukan, na daɗe ina kukan har sai da na ji numfashina ya toshe. Lokacin Anty Sawwama ta shigo cikin ɗakin ta din ga lallashina da ba ni baƙi.

"Tashi ki je falo ki same su don ke suke jira". Ta yi zancen ta na goge mini hawayen da suka ɓata mini fuskana, kaina kawai na gyaɗa mata na tashi na fito kamar yadda ta umarce ni.
Kaina a ƙasa na fito falon bakina ɗauke da siririn sallama na ƙariso na zauna a ƙasa, shuru-shuru cikin mu babu wanda ya yi magana kafin can Muhammad Taufik ya yi kawar da shurun.
Chapter 67 · 0% Book details