Sashe 16
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na hijabina da ya karkace tare da ɗaura ɗan kwalina da ya faɗi, ragowar lemukan da Hajiya Muhibbat ta saya mini na ɗauko na sha na haɗa da biskit kafin na ɗauka makulli na fito na rufe ƙofan, ƙofar ɗakin su La'aniyatu a rufe ya ke don haka da makullin na tafi. A hankali nake tafiya kamar wacce take jin tausayin taka ƙasa, gabaɗaya ba na jin daɗin yanayin ƙarfi kawai nake yi nake ci gaba da tafiyan ina jan silifas ɗin da ya yi wa ƙafafuna yawa sosai.
A gajiye tulus na isa ƙofar gidan na ƙwanƙwasa mai gadi ya fito ya buɗe mini na tsuguna har ƙasa na gaishe shi ya amsa mini fuskansa tamkar gonan auduga. Kaina a ƙasa na shiga cikin gidan ina tafiya a hankali ban yi aune ba na ji na yi karo da wani abu har sai da na yi baya kaman zan faɗi.
Da sauri na ɗago kaina idanuna suka sauƙa akan sa yana tsaye cikin shigar ƙananan kaya, irin na ƴan wasan ƙwallo sai dai na shi wandon dogo ne har ƙasa, ƙafafunsa ne sanye cikin takalmi sau ciki kansa da hula kamar na sanyi. Bai ce da ni komai ba ya juya ya ci gaba da tafiyansa na bi shi da kallo na ga ya shiga wani sashi wanda bai kai na Hajiya girma ba.
[12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE*
Â©ï¸ Maimuna Tijjani Iyam
________________________________________
Page 5ï¸âƒ£1ï¸âƒ£
Na daɗe tsaye a wajen kafin na ja jikina na ƙarisa shiga cikin gidan, tun daga falo nake nake yin sallama amma ba a amsa mini ba, tamkar gidan babu mutane masu numfashi. A buɗe baki a karo na uku da nufin ƙara rangaɗa sallamar na ji yo muryar Altine a bayana.
"Malama wannan sallama haka sai ka ce wacce kike bin mu bashi ko kuma tara. Idan kika yi É—aya kika ji ba a amsa miki ba ai sai ki tsagaita".
Na tsuguna akan gwiwoyina"na ga kamar ba kowa a gidan nan ashe ku na ciki. Ina kwana an tashi lafiya?". Ta galla mini wani uban harara kafin ta ce"da ban kwana ba za ki gan ni ne?, Ba na son kinibibi da iyayin banza da na wofi in za ki tashi ki kama aikin da ya kallafa akanki tun wuri ki tashi in kuma za ki ci gaba da zama anan ne to bismillah". Tana dire zancen ta juya ta shige kicin ta bar ni durƙushe a wajen, sai da na ja dogon numfashi mai nauyi na fesar kafin na sama zarafin miƙewa na bi bayanta na ɗauko tsintsiya da mopper na fito falon, na share ko'ina tsaf kana na soma yin mopping. Sai da na gama na shiga ɗakin su Aryan shi ma na gyara shi na fito na koma kicin ɗin.
Tana tsaye tana soyar ƙosai da ƙamshinsa ya cika ko'ina, na zo gefenta na tsaya cike da girmamawa na furta"na gama sharan shi ne na ce bari na shigo na tambaya, ko akwai wani aikin da zan yi miki?". Kamar ba za ta amsa mini ba sai kuma can ta ce da ni"karɓin soyan ƙosan nan bari na haɗa kunun". Cikin sauri na amsa matsamin da take miƙo mini na ci gaba daga inda ta tsaya.
Gwangwani madarar ruwa huɗu ta ɗauko duk ta ɓula su ban da madarar garin da ta ɗauko saket guda ta yanke bakinsu da almakashi. Ta ɗauko wani ƙaramin kwanon tangaran ta juye madarar garin a cikin ta dame shi da ruwa sannan ta juye cikin ruwan da yake tafasa akan wutan ta yi ta juya shi har sai da ya fara yin kauri, ta juye madarar ruwan gwangwani biyu ragowar biyun kuma ta ajiye su a gefe, ruwan flavour na ga ta tarfa a ƙadan a cikin kafin ta sauƙe shi.
Ta É—auko kofi mai marfi ta juye madarar ruwan guda biyu a ciki, gwangwanin huÉ—um gabaÉ—aya ta haÉ—a ta mayar da su inda ta É—auko su. Tana juyo wa muka haÉ—a ido.
"Wannan kallon fa?".
Ta jefa mini tambayar cikin tsawa da ɗaga murya, na yi hanzarin rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa tare da faɗin"ki yi haƙuri". Kafin ta kai ga furta wani kalma Hajiya Muhibbat ta shigo cikin kicin ɗin duk muka haɗe bakin wajen gaishe ta ta amsa mana fuskarta ɗauke da annurin da ya ƙara fitowa da kyawunta.
"Sannunku da aiki". Ta yi furucin yayin da take sa hannu ta ɗauki ƙosan da yake gabana ta kai bakinta.
"Amma ƙosan nan ba dai laushi ba, ke kika yi haɗa ƙullin ne?". Na jijjiga mata kaina alamar a'a tare da faɗin"ba ni ba ce".
"Amma kuwa ya yi daÉ—i sosai. Na tabbatar Saif zai ji daÉ—insa". Ta juya tana kallon Altine"ki shirya abincin a dinnig table, Amatullah kuma ta je sashin Saif ta É—auko su Aryan ta yi musu wanka kafin ki gama".
"To ranki ya daÉ—e uwarmu maganin kukanmu".
Ba ta amsa mata ba ta juye ta fice daga cikin kicin ɗin tana amsa ƙiran da ya shigo cikin wayarta. Bayan fitanta mun fi mintuna uku cikinmu babu wanda ya yi magana, har na kammala tuyar ƙosan na sauƙar da man.
Ganin shurun ya yi yawa ya sani kawar da shi ta hanyar faÉ—in"Anty ina ne sashin nasan na je na É—auko su....". Tun kafin na rufe bakina take gallo mini harara wani na bin wani tamkar wacce na watsa garwashin wuta, ko na faÉ—i wani abun da bai yi mata daÉ—in ji a kunnuwanta ba.
"Daman can ba ki san sashin nasan ba kika bari ta tafi daga nan ba ki tambaye ba?. Sai ki fita yanzu kam ai ki tambayo". Yadda ta furzo da zancen shi ya fi komai ƙona mini rai da har ban san lokacin da bakina ya suɓuce na furta kalaman da suka shayar da ita giyan mamaki ba.
"Don na tambaye ki laifi ne? Na da ke ɗin gabaɗaya a ƙarƙashin Hajiyar muke kuma aiki muke yi don a biya mu".
Ban tsaya sauraron amsar da za ta ba ni ba na fice daga cikin kicin ɗin zuciyata har wani tafasa take yi tsabar ɓacin ran da nake cikinsa. A rayuwata ta duniya na tsani a wulaƙanta ni balle a zo gandon da za tozarta ni. Sai da na fito cikin harabar gidan na riƙe ƙuguna ina tunanin inda ya kamata na nufa da zai sada ni sashin nasan, jiya dai lokacin da ya ce a shirya su Aryan za su fita wata ƙofa na ga ya shiga a cikin falon Hajiya babu jimawa kuma ya fito a shirye tana ba za ƙamshi. Na sauƙe ajiyan numfashi a hankali ina ƙara ɗaga kaina sama, idanuna suka sauƙa akan Baba mai gadi da yake nufo inda nake tsaye, hannunsa riƙe da bokatin ruwa. Da sauri na isa gare shi na kai hannu zan karɓa bokatin ya hana ni.
"A'a ɗiyata bar shi ai ba za ki iya ba ma, wai bayi ne nake so na yi a shukokin nan mai musu bayin yau bai sama zuwa ba". Na saki taƙaitaccen murmushi kafin na ce"Allah sarki! Ni ma wai Hajiya ce ta ce a je sashin Saif a ɗauko su Aryan, kuma na kasa tantance wanne ne sashin na san".
Da hannunsa ya yi mini nufi da sashin kafin ya furta"kin gan sa can shi ne sashin na san".
"Ai kuwa Baba na gode sosai da sosai, Baba na ga zanen kanurai a fuskanka na ce ko kai ma kanuri ne?". Sai da ya murmusa kafin ya ce"gaba da baya ma kuwa, ni haifaffen jihar Borno ne cikin garin bama. Uwa da ubana duk kanurai ne".
"Ni ma kuwa mahaifina kanuri ne sai dai ko kaÉ—an ban iya yaren ba".
"Kuma ai ba shi ma da wahala idan aiyukan cikin gidan sun yi miki sauƙi ki dinga zuwa ina koya miki. Ko kuma ki zagaya wajen mai ɗakina". Cike da jin daɗi na furta"na gode sosai Allah ya saka da alkhairi".
"Amin".
Ya amsa da shi yana ƙara yalwata annurin dake kan fuskarsa, ya wuce wajen bayin shukansa ni ma na ɗauki hanyar sashin da na ya nuna mini. Wannan sashin da na ga ya shiga da safe ne. An ƙawata ƙofan sashin da shuke-shuken wasu turanni masu kyau da ɗaukar hankali da suka kasance launin gore da ruwan ɗorawa. Wasu a cikin wani abu kamar tukunyan ƙasa an taraye a sama. A hankali na isa bakin ƙofan na soma ƙwankwasa tare da rafza sallama. Har sai da na gaji da tsayiwar na juya zan tafi na ji an buɗe ƙofar na waigo na ga Aryan ne ko Ayan oho don ban iya tantance wane ne a cikin su ba.
"Ayan ina Aryan É—in?".
Ta tsaya yana kallona"ba Ayan ba ne Aryan ne".
"To ina shi Ayan ɗin? Mamanku ne ta ce ku zo a yi muku wanka". Kamar ba da Hausa na yi masa zancen ba ya tsaya yana ta kallona sai can ya ce"Umminmu?". Na gyaɗa masa kaina alamar e kafin ya ce da ni wani abu Saif ya iso wajen hannunsa saƙale cikin na Ayan. Ganin sa ya sanya ni na rusana ina gaishe shi sai dai bai amsa mini ba. Kwarjini da cika idon da ya yi mini ya sanya jikina fara karkarwa da ƙyar na haɗo kalmomin da zan furta suka zauna a bisa harshena.
"Daman Hajiya ce ta ce su Ayan su zo a yi musu wanka".
"Ki je abin ki za su zo".
"To".