← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 72

Sashe 4

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Aminu mana tauraro mai wutsiya ganin ki ba alkhairi ba". Na saki taƙaitaccen murmushi ba tare da na ce da ita komai ba.
"Kin ga mutumin kusan rabi da kwatan matan gidan nan shi ya kawo su, kuma duk wanda suka kwanta da shi ya biya su sai an cire masa nasa kason mai tsoka a ciki. Wani zubin har ɗaukan su yake yi ya kai su wajen manyan mutane su yi haramtacciyar mu'amala, akan kuɗi babu abin da ba zai iya aikatawa ba. Kuma ke ma ina tabbatar miki da cewar duk wannan rawan ƙafa da ɗawainiyyar da yake yi a kanki zzi fanshe su tsaf har da riba". Na yi shuru na kasa cewa komai sai can na furta"Allah ya kyauta shi kuma Allah ya ganar da shi". Ba ta amsa ba illa taɓe bakin da ta yi tana ɗauke kanta gefe guda.

"Tun ɗazu ina ta zaune a nan ina jiran ƙiran salla amma shuru".

"Ƙiran salla dai? To ai ko za ki shekara a nan ba za ki taɓa jin ƙiran salla ba. Tun daga farkon layin nan har ƙarshenta babu masallaci, islamiyya ko kuma wani majalasin da ake koyar da faɗin Allah da Manzonsa. Ke in taƙaice miki bayani babu wani ɗan arzikin da yake biyo wa a layin nan don duk mutumci da kimarka idan aka ganka a layin daga ranar ba za a ƙara yi maka kallon mutumci ba. Idan kin ji ana faɗin layin jahannama to layin nan kenan".
[12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

_________________________________

Page 4️⃣3️⃣

Na sauƙe ƙatuwar ajiyar zuciya ina dafe ƙirjina da ya bugawa tamkar zai faso nama da fatana ya bayyano waje, ta kalle ni ta saki murmushi"mamaki kike yi ko?". Na gyaɗa mata kaina da hakan ya ba ta daman zarcewa da faɗin"indai mamaki kike yi to yanzu kika fara don sai an wayi gari watarana kin daina ma jin mamakin wasu abubuwan".
"Allah ya kyauta". Na furta a taƙaice ba ta amsa mini ba har sai da na ƙara cewa"don Allah yanzu ƙarfe nawa ne?".

"Fitowa na daga ɗaki dai ƙarfe huɗu saura". Na yi zumbur na miƙe ina tada iƙaman sallan asr, har na iddar da sallan tana zaune tana kallona na shafa addu'ar da na yi kana na fuskanto ta.
"Don Allah ina neman wani taimako".

"Faɗi kanki tsaye, matuƙar zan iya to kin same shi kin huta".
"Ina so na zagaya cikin unguwan nan don kafin wa'adin da Aminu ya ɗebar mini na ciyar da ni ya cika. Ina so na tsaya da ƙafafuna ba tare da na bi hanyar da ragowar sauran mutanen gidan nan suka bi ba".
"Za ki sha wahala ne kawai don a kaf unguwan ba na tunanin za ki sama aikin da za ki kare mutumcinki da shi. Idan har kin san cewar ba bariki kika fito yi ba me yasa tun farko kika baro gaban iyayenki?". Na ja dogon numfashi na fesar kafin na furta"wannan wani labari ne mai zaman kansa watarana zan ba ki labarina. Yanzu dai ina so na fita don na lura zama bai kama ni ba".

"Bari na duba idan Ummanta ta yi bacci sai mu fita na raka ki". Ba ta jira abin da zancen ba ta tashi ta fita da sauri, babu jimawa ta dawo" mu yi sauri mu fita, ta yi bacci na san kuma ba za ta tashi ba wataƙila sai nan da zuwa dare. Don ta shawo ta yi tatil". Na yi sakeke ina kallonta ganin ba ni da niyyan motsawa ya sa ta jan hannuna ta jijjiga ni na dawo cikin hayyacina daga kogin mamakin da na faɗa, ta ɗauki ɗan makullin ta muka fito ta ja ƙofan ɗakin ta rufe da makulin muka fita a zaure muka yi kiciɓus da wasu samari su biyu suna shigowa. Kamar za mu gogi juna da su amma duk da hakan sun ƙi matsawa sai ma ƙara matso mu da suke yi.

"Gambo ka ba ni hanya na wuce tun kafin na yi maka rashi mutumci mai wasali".
Ya fashe da dariya"to ki yi mana wani dare ne jamage mai gani ba La'aniyatu? Ni fa babu wani nau'in rashin mutumcin da ban ga ni ba, to don kin yi na ki a matsayinki na ƙaramar ƴar bariki ma ai ba zai yi nasarar ɗaɗani da ƙasa ba".
Ɗayan ya saki tsaki yana banka mana harara"ni wallahi na rasa abin da ka gani a jikin wannan ƙwailan yarinyar da ka ji ka nace mata. Na rantse da Sarkin dake busan numfashi ko a yau na yi niyyan kwanciya da yarinyar nan babu makawa sai na yi ko da amincewarta ko babu. Bar ganin wai uwarki tana ba ki tsaro da kariya yarinya".

"Kanku ake ji wai mahaukaci ya faɗa rijiya ya ce ni wanka na nake yi". La'aniyatu ta yi zancen cikin matsanancin ɓacin ran tana jan hannuna muak raɓa ta gefensu muka wuce tun da muka fito ba ta ce da ni komai kuma ba mu fasa tafiya ba kamar yadda ba ta sanar da ni inda muka nufa ba. Sai da muka yi nisa kafin na ce"na ga kaman ranki ya ɓaci bisa abin da samarin can suka yi miki ko?".

"Kar ki damu zan koya musu hankali É—aya bayan É—aya". Na saci kallonta kafin na ce"su waye ne su É—in? Sannan me yasa suke cin irin wannan alwashin a kanki?". Ta ja dogon numfashi ta fesar sai da ta shafe wasu mintuna ba ta yi magana ba.
"Ki yi haƙuri idan abin da na faɗa ya sosa miki rai ko kuma ba ki ji daɗinsa ba".

"Kar ki damu babu komai. Ba kowa ba ne su ɗin face irin ƴan iskan garin da suke taruwa a cikin gidanmu, gani suke yi don kasancewata ƴar magajiyar karuwai da ƴan daudu shikenan ni ma ƴar iska ce ba su san cewar baƙar tukunya ta kan iya fitar da farin tuwo ba". Na jinjina kaina alamar gamsuwa da dukkan zantukanta"haka ne kam kin san lamarin mutane sai haƙuri".
"Kin gan ni nan tun da na yi wayau na iya bambamce tsakanin launin fari da baƙi daidai da rana guda ban taɓa jin rayuwar da mahaifiyata take yi yana burge ni ba. Tun ina ƙarama na tashi da tsana da ƙyaman irin rayuwar da take yi, tun kafin san haramcin abun a addinance nake jin tsanarsa a cikin raina. Mutane da yawa sun sha kawo min farmaƙi Allah yana kuɓutar da ni, da kuma taimakon Ummata don ita ma ba ta yarda na yi irin rayuwar da take yi ba tana ba n tsaro da kariya ta kowacce fuska".

Ƙirjina ya yi mini nauyin gaske da na kasa cewa komai illa bin ta da ido nake yi, ganin yanayin da na shiga ya sa ta sauya maganan.
"Ina ta suturu ma na mance ba na nuna miki wuraren". Na saki taƙaitaccen murmushi da hakan ya ba ta damar ɗaura daga inda ta tsaya"kin ga layin nan shi ne layin na isa. Duk wanda kika gani ya fito daga cikin layin nan to ya ci ya tada kai ne, don duk wanda ya zo ya gina muhalli a cikin layin wani ƙusa ne daga gwamnatin ko kuma wani hamshaƙin ɗan kasuwa, ko kuwa irin wanda iyayensu suke sato kuɗin gwamnatin su tara musu idan aka rasa abin da a yi da shi sai a zo nan a gidan gidaje da shi, ana zuwa hutawa duk ranakun ƙarshen mako mafi yawan ƴan matan gidanmu nan suke zuwa suna sheƙe ayarsu da zaran yamma ta kawo kai za ki ga kowacce yarinya mai ji da kanta ta ci kwalliya ta zo bakin layin nan ta tsaya daidai lokacin da masu gidajen suke dawowa daga aiki, idan kin kasance cikin masu rabo daga nan sai ki dace wani Alhajin ya yi wuf da ke shikenan kakarki ta yanke saƙa".

Na sauƙe numfashi mai nauyi ina ƙarewa faɗin layin kallo sai da na ƙare masa kallon tsaf kafin na furta"Lalle kuwa layin na isa, ga tankama-tankaman gidaje da shimfiɗaɗɗun tituna".
"Sai ma kin ga cikin gidansu aljannar duniya kenan, ga faffaÉ—an filin tsakar gida ya kai rabin wani unguwan".

"To su ina matayensu da suke cin karensu babu babbaka, ko ba su da iyali ne?".
"Su na da su wasu sun su ma har da ƴaƴansu. Sai dai mataye da ƴaƴansu duk suna can Abuja birnin tarayya wasu ma ba sa ƙasar gabaɗaya. Nan gidan kawai wajen shaƙatawa ne da more rayuwar duniya". Na ji shuru ina ƙara bin layin da kallo shuru yake ko'ina babu hayaniyar kowa da alama kowa yana cikin gidajensu ba sa fitowa sai da wani dalili mai ƙwari. Muka ci gaba da tafiya ina ta kallon layin da manyan gidajensu, haka muka karaɗe dukkan girman layin daga nan suka gargaɗa har cikin kasuwa ta nuna mini wurare da yawa, ba mu dawo ba sai da gari ta soma duhu daga yanayin duhun garin na tabbatar da cewa an yi ƙiran sallan magrib.
Muna dawowa gidan muka iske manyan motoci a ƙofan gidan tamkar ana gudanar da gagarumin biki ko kuma walima.
Chapter 4 · 0% Book details