Sashe 14
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ga shi nan sai ki ɗeba ki ci". Daga haka ta haye kan katifa ta yi kwanciyarta. Na fi mintuna biyar ban ce komai ba kafin na buɗe kulan sai dai da mamakina sai na ga ba abin da muka girka ba ne a cikin kulan, shinkafa muka girka da ta amsa sunanta sai dai a nan fara ce da mai da yaji ko wake babu wata yajin ƴan ɗis a saman shinkafan kamar an roƙo daga maƙota.
Ban ce da ita komai ba na sa hannu na soma cin abincin duk daga loman farko na sha jinin jikina, don da ƙyar na haɗiye shinkafan ya wuce ta cikin maƙoshina tsabar bushewa da sanƙarewan da ya yi da alama ya shafe tsawon awannin a dafe.
Haka na ci gaba da cin abincin ina ji kamar ina haɗiyan ƙarangiya, ba don yunwan da nake ji ba tabbas da na haƙura da abincin amma babu yadda na iya dole na ci tun da ba ni da wani zaɓi. Na gama ci na tashe zan je na mayar da kwana ta dakatar da ni.
"Ki ajiye kulan a nan ki yi tafiyarki". Duk da kalamanta sun ba ni mamaki ainun amma ban nuna mata hakan ba, na yi kamar yadda ta ce na ajiye kulan na shiga banÉ—akin dake cikin É—akin na wanke hannuna na fito.
"To Anty ni zan tafi, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu".
Kamar wacce aka yi wa dole ta ce"Allah ya tashi mai gaskiya". Na saki taƙaitaccen murmushi kana na ce"Amin ya Allah". Na bar cikin ɗakin na iske Hajiya a inda muka bar ta har yanzu tana latsa wayarta ta saka wani waƙan yaren turanci tana bi tamkar tare da mawaƙin suka rera waƙar tsabar ƙwarewar bin dukkan baitukan waƙan da ta yi.
Na iso na durƙusa a gaban ta"Hajiya na fito zan tafi".
"To ki gaida gida, ga wannan sai ki yi kuɗin mota da shi". Ta ƙarƙashin zancen tana miƙo mini naira ɗari biyar na kuɗin ƙasata Nigeria.
"Na gode sosai Hajiya amma ba zan iya karɓan wannan kyautar ba ba kuma don na raina ba. Zan fi so duk ƙarshen wata a ba ni haƙƙina na yi amfani da shi, ina ga kamar hakan zai fi amma idan maganganuna sun ɓata miki rai to ina mai ba ki haƙuri".
Kafin ta ce wani abu Aryan da Ayan suka shigo da gudu suna rige-rigen isowa gare ta, ta buɗe hannayenta suka faɗo jikinta suka ƙyalƙyalewa da dariya. Ina ɗago kaina muka haɗa ido da shi yana shigowa hannunsa riƙe da wasu manyan ledodi guda biyu, na yi hanzarin rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa. Ya shigo ya zauna kafin ya yi magana Hajiya ta riga sa"ina kuka je ne haka?".
"Kun fita wani waje ne".
"Wajen bai da suna?".
Kafin ya yi magana Aryan ya karɓe zancen"Ammi wajen wasan yara muke ce, daga nan muke je muka ci abinci sannan ya kai mu ya yi mana siyayya, muka tsaya a masallaci muka yi salla kafin muka dawo gida".
"To kin ji amsa daga bakin uban masu gidan". Dariya duk su biyun suka yi kafin ya miƙe"sai da safenku ni kam zan wuce sashina".
"Kafin nan ga Amatullah ka mayar da ita gida na ga dare ya yi za ta sha wahala kafin ta sama abin hawa. Daga nan ma sai ka gano gidansu ko don gaba".
Ya tsaya sakeke kafin ya furta"wace ce kuma Amatullah?".
"Ga ta". Ta amsa masa tana masa nuni da inda nake durƙushe, ya ɗan shafo sumar kansa kana ya ce"har yanzu fa akwai ababen hawa suna hada-hadan su, tana fita za ta samo har ƙofan gidan". Cikin kakkauran murya da tsare gida Hajiya ta ce"Saifullah in ba za ka yi ka fito fili ka sanar da ni, ba sai ka yi wani kwana-kwana ba".
Ya sunkuyar da kansa ƙasa ciki-ciki ya ce"ina jiranta a waje". Tana gama faɗin haka ya juya ya fice daga cikin falon.
"Tashi ki je yana jiran ki". Na É—ago kaina zan yi magana ta tari numfashina"kar ki ce komai, idan ba hakan zai zama takura a gare ku ba ne to kawai ki je ya kai ki".
Jikina a sanyaye na tashi na yi mata sai da safe na fita, ina fitowa na hango sa tsaye a jikin mota yana danna waya muna haɗa ido da shi ya buɗe ƙofar motar ya shiga. A hankali na iso na buɗe ƙofan motar zan shiga ya dakatar da ni ta hanyar cewa"gidan gaba za ki shiga". Na mayar da ƙofan na rufe na buɗe na mai zaman banza na shiga na zauna, ina rufe ƙofan ya ja motar tunin daman mai gadi ya wangale gate ɗin, a hankali yake tafiya akan shimfiɗaɗɗan titin da babu cunkoson ababen hawa balle hayaniya. A ƙalla ya yi tafiyan da ya kai na mintuna ashirin ba tare da ya tambaye ni ina unguwanmu ko kuma inda zai ajiye ni ba.
Gabaɗaya na ƙagu da zaman ga wani tarin gajiyan da nake ji a cikin jikina kamar an yi mini dukan tsiya, muryata cike da tarin tsoron da ya yi mini dabaibayi na ce"idan ka sama waje zan sauƙa".
Kamar ba zai amsa ba sai kuma ya ce"har mun iso gidan nakun ke nan?".
"A'a zan ƙarisa nan ne ba wani nisa ba ne sosai".
Yana kayar kwana ya ce"akan idonki amma aka ce na kai ki gida, na ga gidan gudun watarana".
Daga nan ban ƙara cewa da shi komai na zuba masa idanuna domin na ga gudun ruwansa, haka ya ci gaba da tafiyan har gyagyaɗi ya soma ɗeba ba. Hawayen takaici da dana-d shiga motarsa da na yi suka kwaranyo mini. Na kai hannu na goge su ina jin zuciyata tana tafasa kamar talge na ji ya taka birki motar ta tsaya.
"Fita".
Na yi ya furta muryarsa babu alamar wasa balle wargi, na ɗago ido domin ganin inda ya tsaya. Da mamakina ina ɗago ido na hango ƙofar gidan Hajiya Babba da ya cika ya yi maƙi da samari da ƴan mata suna sheƙe ayarsu tare da cin karensu babu babbaka.
"Ki fita mana. Ko ba nan ba ne ƙofar gidan?".
Na sadda kaina ƙasa"nan ne, na gode".
"Ki gode wa Allah".
Ban iya amsa wa saboda mamakin da ya shayar da ni. Na fito na tsaya na kasa gaba na kasa baya idanuna akan motan har sai da ya ɓace wa ganina. Na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya tare da jefa wa kaina tambayar da na kasa amsa wa.
Ya ya aka yi ya san cewa a cikin gidan nan nake rayuwa, har ya kawo ni?.
[12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE*
Â©ï¸ Maimuna Tijjani Iyam
___________________________________________
Page 5ï¸âƒ£0ï¸âƒ£
Na daɗe tsaye a wajen ina saƙa da warwara a cikin raina, kafin na ja ƙafafuna na bar wajen sai da na raɓa tamkar zan shige cikin gini kafin na sama hanyar da zan wuce saboda kuncoson da yake ƙofar gidan, mutane kamar ana kaɗa ƙararrawa suna fitowa sun cika wajen sun yi maƙil. Ga wanda bai sa ni ba sai yi tunani da zaton wani gagarumin taro ake yi a wajen.
Har cikin tsakar gidan da mutane kamar ba dare ba ina shigowa na hango La'aniyatu zaune a ƙofan ɗakinsu, na isa kusa da ita na zauna ina kafa hannayena wajen guda da hakan ya ba da wani ɗan sautin da ya dawo da ita cikin hayyacinta daga tunanin da ta yi nisan kiwo a cikinsa.
"Yaushe kika dawo?".
"Lokacin da kika yi nisa cikin tunanin da kike yi na shigo". Ta miƙe ba tare da ta ce komai ba ta shiga cikin ɗakinsu babu jima wa ta dawo ta miƙo mini ɗan makulina. Na karɓa ba tare da mun ce da juna ko kanzil ba na je na buɗe ƙofana na shiga buta na ɗauka na fito na yi alwala kana na koma ciki na gabatar da sallan isha'i, ban gusa daga inda na yi sallan ba na zabga uban tagumi ina tunanin abubuwan da suka wakana a cikin wunin yau gabaɗaya. Babu shiri na sauƙe numfashi mai zafi ina cije naman leɓena. Ban san sa'ilin da hawaye suka fara tsere a bisa fuskana ba suna sauƙa har izuwa saman haɓana tare da zarcewa zuwa tudun wuyana, ban share su ba kamar yadda ban yi wani yunƙurin hana su kwaranya ba don na yi imanin zubar da su ne kawai zai sanya na ji sanyin tafasar da zuciyata take yi mini da kuma ɗacin da nake ji a cikin maƙoƙarona tamkar an shayar da ni ruwan maɗaci.
Ina zaune cikin wannan halin Aminu ya faɗo cikin ɗakin ban ji shigowarsa ba sai ji na yi an zubo mini wani irin hayaƙi a daidai saitin fuskana take tari ya sarƙafe ni na soma yin sa babu ƙaƙƙautawa, da ƙyar tarin ya tsaya wanda hakan ya ba ni damar bin sa da idanuna yayin da yake zama akan tabarman da nake zaune, yana busa tabar sigari cikin ƙwarewa hayaƙin yana fita ta baki da hancinsa.
"Tunanin me ye kike haka Æ´an mata?".
Na yi masa wani kallo ta wutsiyar idona kana na ce"amma ka san bai dace ka faÉ—o mini cikin É—aki haka ba tare da sallama ko neman izni ba ko?".
Ya ƙura mini idanuna tamkar ba da yaren Hausa na yi zancen ba"ban gane ba me ye kike nufi da waɗannan kalaman nakin?".
Idona a cikin nasa na ba sa amsa"ina nufi bai dace ta na shigo mini cikin É—aki haka garangatsau ba, ko ba komai wani lokacin akwai yiyuwar ka same ni cikin wani hali".
"Wani irin hali ke nan?". Na galla masa harara tare da É—auke idona daga kansa ba tare da na ba shi amsar tambayar da ya yi mini ba.
"ÆŠazu na zo ba kya nan ina kike je?".