← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 72

Sashe 35

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun da ta fara zancen nake bin ta da kallo har ta tsaya a madakata. Ban yi mamaki don izuwa yanzu in da sabo ya ci ace na saba da halinta. Murmushi kawai na yi na ce"yadda kika ce haka za a yi ranki ya daɗe". Ina rufe bakina na tashi na je na yi alwalan sallan zuhur na zo na gabatar da salla a daɗe zaune akan sallayan har sai da na ji wani bacci-bacci ya soma ɗauka ta kana na tashi na ɗauki alƙur'anin na ci gaba da karatuna ban daga wajen ba sai da na yi sallan asr, na fita kicin na haɗa abincin rana na zo na jere shi akan dinning table lokacin Hajiya ba ta cikin falon, haka nan ban ga su Ayan ba Wanda na fi kyautata zaton ko su na can wajen Saif. Don na leƙa ta taga na ga motarsa tana cikin gidan da hakan ya ba ni tabbacin cewar bai fita ba.
Sai da na ci nawa abincin kana na fito falo na kuwa yi sa'a lokacin Hajiya ta fito sai dai da alamar fita za ta yi don mayafinta yana saƙale a bisa kafaɗunta. Na duƙa na yi mata sannu ta amsa mini fuskarta babu yabo babu fallasa.

"Hajiya daman mun gama duk wasu ayyuka ne shi ne nake son na je gida. Inda wani abun zuwa an jima sai na dawo".

"Ba damuwa ni ma daman fita zan yi yanzu, Su Aryan suna É—akina suna bacci sai ki sanarwa Altine ta na duba su".

"To in sha Allah, a dawo lafiya".
Har ta yi gaba sai kuma ya dawo da baya"an kai abincin Saif ne?". Na jijjiga mata kaina alamar a'a da hakan ya ba ta damar zarce wa da faɗin"ya kamata a kai masa sai a fito da kwanukan safen". Kaina kawai na gyaɗa mata da hakan ya ba ta damar ficewa daga cikin falon, na fita da kallo har sai da ta ɓace wa ganina kana na juya na je na haɗa masa abincin na ɗaura akan tray na nufi sashinsa. Haka kawai a duk sa'ilin da na nufi sashin nake tsintar kaina cikin matsanancin faɗuwa gaban da ban san dalilinsa ba.
Sai da na ja dogon numfashi kana na sama ƙwarin gwiwar tura ƙofar falon haɗe da sallama na shiga ciki, yana nan kwance inda na same shi da safe da dukkan alamu tun da na bar shi bai gusa daga wajen ba, na ajiye abincin kana na ɗauki tray ɗin da na kawo da safe. Na ga alamun ko buɗe wa ba ayi ba balle a ci.

"Ranki ya daɗe a fitar da abincin safen nan tun da ga na rana an kawo?". Na yi tambayar jikina yana rawa. Na yi shuru bai tanka mini ba hakan ya sa ni buɗe plate ɗin don gani da idona cikin rashin sa'a ya zame ya faɗi zuwa ƙasa take ya tarwatse ya yi ɗaɗɗaya. Ƙarar ya gigita ni har sai da na runtse idanuna na ajiye tray ɗin hannuna ina tattare wanda ya fashe ɗin.
"Ranka ya daɗe ka yi haƙuri kuskure ba da niyya na yi ba". Tsit na ji ba a amsa mini har na gama tattarawa na zuwa a gefen tray na juyo na ga yana nan inda yake kwance bai motsa.

Haka kawai na ji ƙirjina ya buga na zo na tsaya a gabansa ina ƙiran sunansa amma shuru bai ko motsa ƴatsunsa ba, balle wani gaɓa daga jikinsa.
Ina janye matashin da ya rumgume a ƙirjinsa na ga hannunsa ya faɗo ƙasa jikinsa ya sake, ban san lokacin da na yi jifa da matashin ina sakin salati da sallallami ba tsabar gigicewa da kiɗimewar da na yi.
[12/7, 1:15 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

______________________________________

Page 6️⃣4️⃣

Na rasa abin da ya dace na yi sai kai komo nake yi a cikin falon rumgume da hannayena a bisa ƙirjina, na rasa wanda zan je na sanar wa halin da yake ciki ga shi Hajiya ba ta nan ta fita, na zo na tsuguna a gabansa ina bubbuga hannun kujerar da yake kwance a kaina tare da ƙiran sunansa.
"Ranka ya daɗe don Allah ka tashi ka buɗe idanunka". Shuru bai amsa ba kamar yadda bai motsa ko da ƴatsun hannunsa ba, hakan ya ƙara gigita dukkan nutsuwar da ya yi saura a gangar jikina da har ban san lokacin da hawaye suka ambaliya a bisa dakalin fuskata ba.
Altine ce ta faɗo mini a ciki raina na yi zumbur na miƙe da nufin na je na sanar da ita halin da na zo na iske shi a ciki, har na tashi na ji wayarsa da yake ajiye akan teburin ta soma ruri kamar ba zsn kula ba sai kuma na ɗauki wayar ban tsaya duba wanda yake ƙira ba na kara wayar a kunnena ina magana ciki sarƙafewar harshe da cushewar numfashi.

"Don Allah ku taimaka mini Yallaɓai ne ba shi da lafiya. Gashi nan ko motsawa ba ya yi kamar ma ba ya yin numfashi".

"Ina mai wayar? Ina shi Saifullah É—in?".

Aka jeranta mini tambayar a haÉ—e sai da na juya na kalle shi har yanzu bai motsa ba kafin na ce"ga shi nan a shi da lafiya ne".
"Yana ina yanzu?".
"Yana gida a cikin sashinsa".

Aka ɗan yi shuru kafin can aka ce"ki karanta suratul Baƙara a cikin wuta ki shafa masa a fuskarsa, sannan idan inda yake akwai fanka ki kashe su sannan ki rufe tagogi, ki aiwatar da abin da na ce miki ba tare da kin katse ƙiran ba".

Tamkar ina gabansa haka na gyaɗa kaina alamar duk na saurara abin da ya faɗa kuma na fahimta, na je na ɗauki ruwa na karanta ayoyi goma na farkon Suratul Baƙara na tofa a cikin ruwan, na sa hannuna na ɗeba na yarfa masa a fuskarsa na yi hakan har sau uku amma bai ko motsa ba balle na kai ga saka ran sai buɗe idanunsa har numfashinsa ya dawo.
Ban san lokacin da na fashe da wani kukan ba ina rarumar wayar na mayar da ita kunnena ina faɗin" ka ga har yanzu fa bai tashi ba, ko buɗe idonsa ma bai yi ba". Da ƙyar na ƙare zancen sa boda wani gigitaccen da ya ƙwace mini.

"Ki nutsu ki kwantar da hnakalinki sai mu yi tunanin mafita. Kin rufe tagogin?".
"A'a yanzu zan rufe". Na furta ina miƙe wa na je na rufe tagogin kana na kashe fanka.
"Ki lulluɓe masa jikinsa da bargo mai nauyi sannan ki zauna a kusa da shi ki na ci gaba da karanto masa karatun".

"Ka na ga zsi tashi kuwa?". Na jefa masa tambayar cikin sarewa da kuma cire tsammani.
"In sha Allah ke dai kawai ki yi abin da na ce".

Ban iya amsa masa da kalmomin da baki kan iya furtawa ba, na hanzari na haura sama na shiga cikin ɗakinsa na ɗauko bargon da na gani akan gadon na fita. Garin sauri na zame daga matattakalan benin sai ji na na yi a ƙasa tim, ƙuguna ya bugu sosai da har sai da na runtse idanuna ina cije leɓena sa bosa azabar zafi da zogin da na ji ya ratsa cikin kwanyata.
Da ƙyar na tashi ina dafe jikin gini har na iso inda yake na lulluɓa masa bargo a jikinsa tun daga ƙafarsa har zuwa kafaɗuna, na zauna a ƙasa kusa da kansa ina ci gaba da karatun a hankali cikin muryar kuka.
Ban gushe ina karantun har sai da na ga ya soma motsa ƙafafunsa zuwa hannayensa, sai dai har izuwa lokacin bai buɗe idanunsa ba. Wasu hawayen suka gangaro daga cikin koramar idanuna, zan iya cewa tun da Uwata Hafsatu ta haifo ni cikin wannan duniyar ban taɓa ganin irin wannan rashin lafiyan da numfashin mutum zai ɗauke gabaɗaya, jikinsa ya sandare kamar itace ba. Tun ina karatun da tunani da burin zai buɗe idanunsa har na soma karaya na ɗauki wayar da nufin ƙiran lambar da muka yi waya da mai ita. Na ga wayar da lambobin sirri da hakan yake nufin ba zai iya aiwatar da komai da ita ba, tagwayen ajiyan numfashi na sauƙe tare da ɗaura kaina jikin kujerar da yake kwance akan ta, na koma yin karatun a cikin zuciyata don baki ya yi mini da hakan ya hana ni furta ko da kalma guda.

Rurin da wayar ta soma yi shi ya sanya ni zabura na ɗauko kaina zan ɗauki wayar idanuna suka sauƙa akan fuskarsa. Yana zaune akan kujerar ya jingina bayansa a jikin kujerar tare da cije leɓansa. Idanunmu suka sarƙafe cikin na juna wani kukan ya ƙara kubce mini mai haɗe da farin cikin ganin ya buɗe ido har ya tashi ya zauna.
Wayarsa da yake kusa da ni ya kai hannu ya É—auka da hakan ya tilasta mini janye idanuna daga gare sa.
"Za mu yi magana an jima kaɗan yanzu ba na jin daɗin jikina inna dawo daidai zan ƙira ka".

Ban san me ye aka ce masa daga ɗayan ɓangaren ba sai ji na yi ya furta"waye ya sanar da kai ba ni da lafiya Sultan?". Ban san amsar da aka ba shi ba a taƙaice ya ce"ok". Daga haka ya datse ƙiran ya ajiye wayar yana lumshe idanunsa tare da furzar da zazzafan iska da bakinsa da har sai da na ji sautin fitarsa.
Muryarta a shaƙe na ce"sannu ranka ya daɗe ya jikin?". Bai amsa mini ba illa idanun da ya tsura mini kamar zai cinye ni da ido, dole na rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa sa boda kwarjini da cika idon da yake da shi.
"Za ki iya tafiya". Kalaman da ya saka mini da su kenan bayan sautin maganarsa ya fita raÉ—au, na saci kallonsa na ga ya mayar da idanunsa ya lumshe su, sai dai har yanzu numfashinsa bai daidata.

"Allah ya ƙara sauƙi".
Chapter 35 · 0% Book details