← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 72

Sashe 28

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Na riga da na faɗa miki iya gaskiyata, ya rage na ki ki yarda da abin da na faɗa ko akasin hakan". Ina dasa aya a zancen na raɓa ta gefenta na yi tafiyata, da farko gida na yi niyyan wucewa amma yadda na ga Altine ta ɗaura idonta a kaina ya sa ni sauya shawara, na je wajen Baba Mai gadi na zauna. Ta fi mintuna goma sha biyar a tsaye a wajen ita ba ta yi gaba balle baya tana ta aikin banko mini harara tamkar ƙwayoyin idanunta za su faɗo ƙasa.
"Lafiya kuwa yau me ye yake faruwa tsakaninki da uwar-gijiyartakin?". Furucin Baba Mai gadi ya dawo da ni izuwa cikin duniyar zahiri daga karatun wasiƙan jakin da na afka na wucen gadin.

"Babu komai Baba, daman wajenka na zo neman wani taimako".

Ya gyara zamansa yana fuskantana da kyau da hakan ya ba ni ƙarfin gwiwa da karsashin ci gaba da zancen.
"Akwai wani babban malamin addini da ya yi shura a gefensa kuma sunansa ya ɗaukaka ya zagaye ko'ina a cikin ƙasar nan har ma da kewayenta." Tun kafin na dire zancen ya katse mini hanzari ta hanyar faɗin"wannan ba kowa kike magana a kansa ba fa ce baƙin Balarabe".

"Anya kuwa shi ne? Wannan ɗin fa sunansa Sheikh Dawood aka yi masa kirari da gaskiya dokin ƙarfe". Ya murmusa kafin ya furta"ai mu a nan cikin jarafi an fi sanin sa da sunan baƙin Balarabe. Yana zuwa tafsirin alƙur'ani sosai a cikin garin nan. Ina tunanin babu garin da ya tara masoya fiye da wannan garin namun indan ya zo hatta mai martaba Sarki dakatar da komai yake yi ya je ya saurari wa'azinsa, kusancin da yake da shi da mai martaba ya sa shi ba shi auran ƙanwarsa ƴar autarsu ya aure ta sai dai ta rasu shekaru biyu da suka wuce, mutum ne mai tarin ilmin addini har ma da na zamani don na taɓa jin an ce yana shugabanci a wata jami'a".
"Don Allah Baba kaman da wani irin lokaci yake zuwa garin nan É—in? Sannan in ya zo yana yin kamar kwana nawa kafin ya tafi?".

Sai da ya kalle ni kafin ya ce"yana iya zuwa a ko wani lokaci sai dai ta fi zuwa a lokacin sanyi kamar irin yanayin da muke ciki yanzu. Sannan idan ya zo yana gabatar da wa'azi a wurare daban-daban kuma a mabanbantan lokuta hatta wa'azin mata yana gabatarwa a masallacin Sarki".
Na ɗan yi jim kafin can na ce"shin ko yana da wani alaƙa ne tsakanin shi da wannan baƙon da ya zo cikin gidan nan?".

"Wai Sultan?".

"Sultan kuma?".

"Ƙwarai da gaske sunansa Sultan don tun sanin da na yi masa haka ake ƙiransa da shi. Amma asalin sunansa Muhammad".

Mamakin zantukansa suka gana ni samun damar cewa komai illa sadda kaina ƙasa da na yi ina tufka da warwara a cikin raina. Ta ya ya Muhammad Taufik ɗin da na sani zai ya rikiɗe ya koma amsa sunan Sultan?. Sannan me ye haƙiƙanin alaƙarsa da Sheik Dawood da har na ga hoton su tare? Hoto ne da aka yi shi cikin lokacin zallan farin ciki da annashuwa da har ya bayyana akan fuskokinsu. Kuma a cikin gida aka yi sa balle ma na ce a wajen gabatar da wa'azi suka haɗu aka yi hoton.
"Amma Æ´ar nan lafiya kike ta yi min wannan tambayoyin?".

"Lafiya ƙalau Baba, tun ranar da na ga wannan baƙon ne na ga suna kama da shi Sheikh ɗin to shi ne nake ta tunanin ko sun haɗa jini da shi ne. Ko wani dangantaka ta kusa ko ta nisa?". Na ƙarƙare zancen cikin sigar jefa masa tambaya a faƙaice.
"Ban ma taɓa lura da kaman da suke yi ba sai yanzu da kika furta nake zumo kamar a idanuna. Sultan dai kam abokin Saifullahi tun na ƙuruciya wani sa'ilin ma a nan cikin gidan suke ƙarar da hutun makaranta, ban taɓa jin labarin akwai alaƙa tsakaninsa da Sheikhi ta kusa ko ta nisa ba. Na san dai Sheikhi yana da azurki ƴaƴa sai da mafi yawansu mata ne ɗansa na miji ɗaya ne tal kuma bai cika bayyana fuskarsa ba".

"To shi Sultan bayan abokan da yake tsakaninsu da Saif su na da wani alaƙa da masu gidan nan ne?".

Kallon da ya watsa mini ya sani tabbatar wa kaina cewar na kwafsa kuma na wuce gona da iri har ina ƙoƙarin tsallake iyaka ba tare da na farga ko na ankare ba.
"Wannan irin tambayoyin Æ´ar nan sai ka ce ina gaban alkali".
Na murmusa kafin na ce"yi haƙuri Baba kawai na ga kamar ta sun ne ta yi tsananin yawa shi yasa nake tambaya".

"Ba laifi kika yi don kin tambayi abin da ya shige miki duhu ko ya jefa ki cikin shakku ba, ai magabata sun ce tambaya mabuɗin ilmi ce. Sai dai a wannan gaɓar zan iya ce miki ba ni da amsar ko guda ɗaya daga cikin tambayoyin da kika yi min hasalima yadda kike gan sa a cikin gidan nan ya zo, ni ma haka nake ganinsa tun yana yaro ban taɓa damuwa da na san mene ne alaƙarsa da masu gidan ba don wannan ba hurumina ba ne kuma bai shafe ni ba". Na jinjina kaina cike da gamsuwa da zantukansa da dukkan suke kan gwadaben gaskiya.
"Haka ne kam Baba to Allah ya kyauta".

"Amin ya Allah".

"Zan nem takarda da biro na zo ana ɗaura mini darasi. Ko gaisuwa ya kamata na koya daga cikin yaren nan tun da ban iya furta ko kalma guda a ciki ba". Ya dara sosai kafin ya ce"ba girin-girin ba dai ta yi maiƙo, kullum haka kike ce har na gaji da gafara sa ba tare da na ga ƙaho ba". Kafin na kai ga cewa wani abu Aryan ya iso wajen.
"Wai ki zo in ji Umminmu". Haka kawai na ji gabana ya faɗi zuciyata ta buga da ƙarfi. Jikina a sanyaye na ce"lafiya?". Ya ɗage mini kafaɗunsa alamar bai sa ni ba daga haka ya dura da gudu ya koma ciki.

"Tashi ki je Æ´ar nan kar ki yi sanya don ba a bori da sanyin jiki". Kaina kawai na gyaÉ—a masa na tashi na nufi cikin gidan ba tare da na san abin da zan je na tarar a ciki ba.

Ina doso cikin falon idanuna suka soma sauƙa aka fuskar Altine da take zaune kusa da ƙafafun Hajiya Muhibbat gefe guda kuma Aryan da Ayan ne suke wasan mota. Na durƙusa kana na ce"Barka da hutawa Hajiya, ga ni an ce ki na nema na".
Ta É—au lokacin kafin ta ce"me ya kai ki wajen mai gadi?".

"Hajiya gaisawa kawai muke yi da shi, sai kuma yaren kanuranci da na roƙi ya dinga koya mini kasance yarena ne kuma nan yi ba". Ta ɗan yi shiru kafin ta ce"to ba na son na ƙara ganin kin ce wajensa ko da wasa ne kuwa, ki yi aikinki shi ma ya yi nasa".

"In sha Allah hakan ba zai ƙara faruwa za a kiyaye".

"Good". Ta amsa da shi a taƙaice, jikina ya yi sanyi ƙalau don na kasa gano inda maganganun natan suka dosa da kuma abin da take nufi da kar na ƙara zuwa wajensa ko da kuwa da wasa ne.
"Hajiya rana tana yi me ye za a girka ne?". Furucin da Altine ta yi kenan da ya tilasta mini cira kai na yi mata kallo guda tare da janye idanuna daga gare ta.
"Fita ni zan yi zuwa anjima can da yamma. Ku dafa abin da za ku ji don ba na jin ma su Saif za su dawo nan kusa". Tana dasa aya ta tashi ta bar cikin falon sa boda ƙirar wyarta da aka yi ta hau sama zuwa ɗakin da kallo na raka ta har ta ɓace wa ganina daidai lokacin da sautin Altine ya sauƙa a masarrafar naɗar sautina.
"Idan kunne ya ji jiki ya tsira". Duk yanayin da nake ciki hakan bai hana ni sakar mata da murmushin ba duk da kuwa bai kai har cikin ƙasan zuciyata ba. Ta tashi ta bar ni a gantale a cikin falon ba tare da ta sanar da ni abin da zan yi ba, zafafan iska na fesar daga bakina ina ɗan lumshe idanuna da nake jin har wani zafi-zafi suke yi mini.

Jin an fado kafaÉ—una ya sa ni buÉ—e lumshashshun idanuna ina tsayar da su akan Ayan da yake tsaye a gabana yana rungume da dokin wasa a hannunsa.
"Kuka kike yi?". Na girgiza masa kaina ina kai hannuna ina share hawayena da ya zubo daga idanunta don ban san lokacin da suka zubo ba.
"Ummi ce ta yi miki faÉ—a shi ne kike kuka ko?".

Na riƙo hannuna ina jinjina kaifin tunanin yaron na furta"Ummi ai duk ta fi mu shi yasa idan muka yi ba daidai ba za yi mana faɗa, sa boda rayuwarmu ta gyaru ba don ba ta son mu ba". Kallon da ya tsare ni da shi ya sa ni fahimtar kalaman da na yi amfani da su sun yi girme wa shekarun da har ya hana sa fahimtar saƙon da nake son a isar masa a cikin zancen.

Na kai hannuna na shafo sumar kansa"ba faÉ—a Ummi ta yi mini ba ka ji?" Ya gyaÉ—a mini kansa alamar ya ji, daidai lokacin da Aryan ya iso wajen ya zo ya tsaya kawai yana kallona.
Na ƙirƙiro murmushin dole na dasa a bisa fuskana kafin na kai ga furta"lafiya ka tsaya haka?". Ya yi rau-rau da ido yana ta faman dube-dube ya matso saitin kunnena kamar mai raɗa ya ce"Anti don Allah ki yi mana wanka jikinmu gabaɗaya ƙaiƙayi yake yi mana".

"Wanka kuma? Ba a yi muku ba ne?". Da sauri Ayan ya janye Aryan daga kusa da ni yana faÉ—in"Aryan Uncle Saif ba ya hana ka yawan magana ba, ka zo mu yi wasan mu". Na cafko hannayensu gabaÉ—ayan su ina kallon Ayan da gaba É—aya ya bi ya firgice na lura ya fi Ayan tsoro nisa ba kusa ba.
"Me yasa za ka ce ya yi shuru?".
Chapter 28 · 0% Book details