← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 72

Sashe 17

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na amsa da shi a gajarce ina ɗaukan hanyar barin wajen, na runtse idanuna a ƙoƙarin daidaita nutsuwata da ta yi nisa da gangar jikina. Ni da uwata Hafsatu ta haife ni ban taɓa ganin mutum mai tsananin kwarjini da cika ido irin wannan bawan Allahn ba. Fuskarsa a sake take duk da ba ya murmushi amma fuskar ba a murtuƙe take ba. Ina tafe ina ta saƙe-saƙe a cikin raina har na isa sashin Hajiya ina shiga Aryan da Ayan suka shigo na kamo hannunsu ina faɗin"mu je na yi muku wanka ko?". Suka gyaɗa mini kansu alamar sun ji. Na ja hannunsa muka nufi cikin ɗakinsu, na cire musu kayansu na ɗaura musu towel muka shiga cikin banɗakin. Fanfon banɗakin irin na gidan Anty Zulaihatu ne mai na ruwan zafi da na sanyi, don haka ban shan wani wahala ba na kunna na ruwan zafin na tara na na tsirka shi da na sanyi daidai yadda mutum zai iya watsawa a fatan jikinsa.
Sabule ne da mayuka kala-kala a banɗakin masu ƙamshin tsiya, na zaɓi guda ɗaya daga ciki na yi musu wankan da shi, na wanke musu suman kansu da mai ɗin na ɗaura musu towel ɗin muka fito.

Zan wuce na ji an riƙo hannuna na juya fuskana ɗauke da murmushi ina kallon yaron na ce"ya ya aka yi?".
"Ke É—in waye ce? Waye ya kawo ki gidan nan?".
Na durƙusa a gabansa ina goge masa ruwan fuskansa da hannuna na ce"ni sunana Amatullah, Umminku ce ta kawo ni don in dinga taya Anty Altine aiyukan cikin gida".
Ɗayan ya yi saurin faɗin"ita kam da ruwa mai ɗan karen sanyi take yi mana wanka, kuma in mun fito ta hana mu lulluɓuwa da komai wai har sai jikinmu ya bushe".

"Ayan".

Ya jijj kansa"Arya ne". Kafin na yi magana Ayan da nake riƙe da hannunsa ya fizge ya zo ya buge bakin Ayan tare da yi masa wani irin kallon da na gaza fahimtar saƙon da ya isar masa. Ɓoyayyan ajiyan zuciya na sauƙe don na lura kamar akwai abin da suke ɓoyewa a tsakaninsu wanda ba sa son kowa ya ji balle a sani.
Na riƙo hannunsu na ɗaura su akan gadon na je gaban madubi daka jere shi da mayuka da turarruka kama ɗakin wata macen. Gefe guda kuma kum ne da mayukam gyaran gashi kamar yadda na fahimci hakan daga hotunan da suke jikin mazubin.
Na shafe musu jikinsu da mai ɗin kana na gyara musu sumar da ake tara musu akan su, na isa gaban wadrode ɗin su kaya ne sosai a ciki kamar ba wadrode ɗin yara ba komai guda bibbi ne a ciki, sai dai mafi akasari ƙananan kayana na ɗauro musu singileti da gajeren wandona na saka musu kana na soma kici-kicin zaɓo musu kayan da za su saka wani shuɗin riga da wando jeans na ciro musu tun kafin na gama Aryan ya zo ya riƙe mini hannu.

"A'a ki ɗauko mana ba wannan ba". Ya ƙare zancen cikin gaurancin Hausarsa da ba ta gama nuna a bakinsa, lokaci guda kuma idanunsa suka ciko da ƙwalla.
"Me yasa?". Na tambaye sa idanuna a kansa.
Bai amsa mini na ya wafce kayan daga hannuna ya mayar cikin wadrode ɗin ya ɗauko wasu, ban ƙara gigin tambayarsa ba na taimaka musu suka saka wanda ya ɗauko ɗin na ɗauko turare na fesa musu sama-sama duk da kasancewar turaren ba mai ƙarfi ba ne sai dai yana da daɗin ƙamshi ainun. Na riƙo hannunsa za mu fita muka yi kiciɓus da Altine za ta shigo cikin ɗakin na matsa na ba ta hanyar shigowa, ta bi su Ayan da kallo da ganinta ya sanya su duk suka yi ƙasa da idanunsu.

Ba ta ce da ni ko kanzil ba illa ƙwafan da ta yi kafin ta fice daga ɗakin da hakan ya sanya kaina ƙara ɗaurewa. Muka fito falon hannuna saƙale cikin da na Ayan suna hango Saif zaune a falon yana latsa laptop suka zame hannunsu daga cikin nawa suka nufo wajensa da gudu, ajiye laptop da yake kan cinyarsa ya yi ya ware hannayensa suka faɗo kan ƙirjinsa suna dariya kamar waɗanda aka yi wa kyauta.

"Kun yi kyau sosai". Ya furta yana shafa suman kansu da na ƙarar da aƙalla mintuna goma ina gyara musu ita.
"Uncle Saif wancan ce ta yi mana wanka yau". Aryan ya yi zancen yana dirowa ƙasa ya zo ya ja hannuna ya kai ni har gabansa. Ya ɗago kai ya yi mini kallo guda tare da kawar da kansa gefe ba tare da ya ce da ni uffan ba.
Ya zaro wayarsa daga aljihunsa ya soma ɗauka musu hoto, cikin sanyin jiki na juya na bar cikin falon na wuce ɗakin Altine na zauna. Na zabga tagumi ina abin da na saba kuma na ƙware a cikinsa watau tunani. Ina zaune ta shigo hannunta ɗauke da plate da kofin roba ta dosara mini a gabana a wulaƙance kamar yadda ake ajiye wa akuya harawa a gabanta.

"Ga karin kumallonki nan". Ta faɗa tana wuce wa ta koma gefe ta zauna, na bi ta da kallo na ga ta jawo wani kula da ƙaramin flask ɗin ruwan shayi na hango wannan kofin da ta tsiyaye madarar a ciki ta zuba ruwan shayin da yake cikin flask ɗin a kai tana juya wa da cokali. Ta kurɓa ta ajiye kana ta buɗe kular na ga ta ɗauko doya soyayya da ƙwai tana dangwala da yaji ta kai bakinta.

Lamarin ya ɗaure mini kai don ni dai ban inda aka soya doya ba hasalima ƙosai na zo na iske ta tana tuyawa. Na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya ina dawo da dubana kan plate ɗin da yake gabana ƙosai ne wanda a lissafina ba su haura guda bakwai ba, gefe guda an ɗan ɗosa na mini yaji.
Kaman ba zan ci ba sai kuma na yi wani tunani na kai hannuna na ɗauki guda ɗaya na sa a bakina, na ɗa kofin kunun na kai bakina. Na kasa haɗiye don ban yi tsammanin jin sa haka ba. Koko ne wanda ko sugarin arzuki babu a cikinsa ga shi ya yi sanyi ƙalau babu daɗi sha, wanda ni kuma dai na gani da idona kunun madara aka dama. Ban. ce da ita komai ba na ci gaba da cin ƙosan ina haɗawa da kokon ba don ina jin daɗinsa ba har sai da na kama tsaf, na tashi zan fitar da plate na ji ta bushe da dariya bai waigo ba kamar yadda ban tambaye dalilin dariyar ba na yi ficewa ta.

A bisa kan dinning table na iske su Hajiya suna yin karin kumallo, na durƙusa na yi musu sannu da hutawa ta amsa mini cike da kulawa. Na tashi zan shige kicin na Saif yana faɗin"Hajiya Anty mu na da baƙo fa a cikin satin nan, da na ce ba zan sanar da ke sai dai kawai na kawo miki shi amma daga baya na sauya shawara".

"To fa! Wane ne haka".

"Abokina ko in ce amina Muhammad Taufik".

Baan lokacin da na saki plate ɗin da ke hannuna zuwa ƙasa ya tarwatsewa ba. Tsabar firgicin da sunan da ya ambata ya jefa ni a ciki.
[12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

___________________________________________

Page 5️⃣2️⃣

"Amatullah lafiyarki me ye ya faru?". Na tsinkayo muryar Hajiya Muhibbat sai dai na kasa cewa da ita komai kamar yadda na kasa motsawa daga inda nake tsaye balle na yi wani yunƙurin tattare plate ɗin da ya tarwatse a wajen.
Ban dawo daidai ba sai da na ji hannun mutum a bisa kafaɗuna da hakan ya sanya ni sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya ina ɗan lumshe idanuna a hankali.
"Me yake faruwa ne?". Ta ƙara jefa mini tambayar a karo na biyu, sai da na furzar da zazzafan iska mai ɗumi daga bakina kafin na sama zarafin faɗin"babu komai Anty, kawai ji na yi kaina ya ɗan sarawa". Ta yi shuru tana kallona na tsawon wasu daƙiƙu kafin ta ce da ni"to ki je ki kwanta ki ɗan hutu a ɗakin Altine". Kaina kawai na gyaɗa mata don ba na tunanin ko na yi ƙoƙarin amsawa mata da kalmomin baka bakina zai ba ni haɗin kai waje aiwatar da hakan a aikatace.

Na nufi kicin na ɗauko tsintsiya da faka na zo na share inda plate ɗin ta tarwatse na je na zubar, a hankali na dawo cikin falon ina tafiya a hankali don haka kawai na ji gabaɗaya ƙafafuna sun riƙe ta yadda da ƙyar nake ɗaga su ina sauƙewa.
"To baƙon nakan yaushe zai zo sai mu fara shiri?".
Na ɗago kai ina satan kallonsa na ga idanunsa suna kan plate ɗin ƙosan da yake gabansa sai dai ban ga sa'ilin da ya kai ko guda cikin bakinsa ba.
"Gobe da yamma in sha Allah zai shigo garin nan tare da mahaifinsa".

"Allah Sarki! Muhammad Taufik ina jin daɗin ganin yadda yake bayar da hankali wajen ba wa addini gudunmawa kamar yadda mahaifinsa yake yi, duk da irin yanayin aikinsa. Shi fa yanzu lokacin kansa ma bai da shi balle kuma na mace daga kai har shi ɗin shi yasa har yanzu kun kasa fito da matayen aure. Ga shi kullum ƙara girma kuke yi shekarunku suna ƙara tafiya".

"Hajiya Antynmu ai komai lokaci ne, idan lokacin mu ya yi babu makawa za mu yi auren nan. Ko kika sa ni ma ba mu daga cikin wanda Allah ya ƙaddarawa za mu yi aure a cikin duniya". Ya ƙare zancen yana miƙe wa tsaye daidai sanda zan shige ɗaki na ji Hajiya Muhibbat tana tambayar sa ya ta ga ya tashi? Ya ce da ita ya ƙoshi ban san yanda suka ƙare ba na shige ɗakin. Ina shiga muka haɗa ido da Altine ta banko mini wata uwar harara tamkar wacce ta yi arba da kashi, na yi hanzarin janye idanuna ina ƙariso na zauna a ƙasa. Mun shafe a ƙalla mintuna talatin ni da ita babu wanda ya ce da wani ko kanzil ina waige-waigena na hango alƙur'ani ajiye a saman akwati.
Chapter 17 · 0% Book details