← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 72

Sashe 61

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ka ga ne Sultan ba ri na je waje ba zan iya jure ganin zuban hawaye daga idanunta ba". Saif ya yi furucin cikin sanyin jiki da na murya bai jira amsar da zai ba shi ba ya tashi ya fita. Daga ni har Muhammad Taufik muka yi shuru na tsawon mintuna kafin can ya kawar da shurun ta hnayar cewa"Amatullah in dai ba ni damuwa kuma ba za ki takura ba. Don Allah ki ba wa Saifullah dama ina yaƙinin ba za ki taɓa yin dana sanin zaɓinsa ba, ba zai taɓa yin gangancin jefa ki a cikin wani halin da za ki yi tir da kasancewarki da shi a cikin inuwa ɗaya ba".

"Me yasa ka gaza fahimtar cewa ban dace da shi? Ba na so na gurɓata masa tarihi ta hanyar haɗa jini da shi. Na yarda aure bautar Ubangiji sai Allah bai kallabafawa Bawansa yin sa dole ba hasalima akwai hanyoyin neman aljanna bila adadin. Zan rayu kuma na tsayu akan hanyar bautar Allah da neman yardansa ba dole sai na yi aure ba".

"Ko da kuwa aure bai kasance dole ba amma shi ne cikar mutunci da kimar duk wata mace. Aure rufin asiri ne ga ƴaƴan mata, ko ba Saifullah ba ina tabbatar miki da in lokaci ya yi dole ne ki yi aure". A sanyaye ya ƙare zancen muryarsa har ta na riƙe wa, alamar akwai wani abun a ƙunshe a ƙasan zuciyarsa da yake ɓoye wa.
"Me yasa kake yin duk wannan ƙoƙarin akan kawai na amince da Abokinka?". Kamar jira yake yi na yi masa tambayar ya yi hanzarin ba ni amsa.
"Sa boda na tabbatar da soyayyar da yake yi miki babu yaudara a cikinta, kuma zai riƙe ki amana tare da ƙoƙarin faranta miki har ƙarshen rayuwarsa".

Na jinjina kaina tare da ƙarfin halin cilla ƙwayoyin idanuna cikin na sa kafin na furta"ka na nufin ke nan kai ba so na kake yi ba?". Babu shiri ya ɗago idanunsa da suke bayyanar da maɗaukakin mamaki ya kafe ni da su. Hakan ya ba ni ƙarfin gwiwan ci gaba da furzo da magana"kar ka musa abin da ya riga ya bayyana a cikin idanunka. Muhammad tun ranar da Allah ya haɗa mu kana so ka ce mini ba sona kake yi ba? Idan ba so na kake yi ba me yasa ka shigo rayuwata ka yi tsamo-tsamo a cikinta a wancan lokacin". Ya yi saurin katse mini hanzari"Amatullah ni ban so ki ba, na san dai tabbas akwai tausayinki da yake maƙale a ƙasan raina". Yana ƙare zancen ya miƙe tsaye ni ma na tashi na je na tsaya a gabansa.

"Ka kalla cikin idanuna Muhammad Taufik sai ka sanar da ni cewar ba ka taɓa jin soyayyata a cikin ranka ba, ta hakan ne kawai zan yarda da kai. Har na iya amincewa abokinka".

"Ya isa haka Amatullah ya isa mana". Ya yi zancen cikin wani iriyar sarƙarƙiyar amo mai bayyanar da tarin damuwar da yake tattare da shi, ya kai hannu ya shafo suman fuskarsa yana saki ajiyar zuciya mai nauyi.
"Na ji Amatullah a lokacin na ji soyayyarki a cikin raina, na ji a raina cewan zan iya rayuwa da ke a cikin ko wani hali kika tsinci kanki a cikinsa. Wannan dalilin ne ya sanya na dage tsayin daka wajen ganin na nemo ki har kin dawo cikin ƴan uwanki. Na yarda har yanzu akwai soyyayarki a cikin raina sai dai tun lokacin da Saifullah ya zo min da batun yana sonki tun daga lokacin na shiga ba wa zuciyata haƙuri, don ba zan iya gasa da Saif akan komai ba ko ya kuwa nake tsananin so da ƙaunar abun ya kai ƙololuwa. Zan iya sadaukar da komai akan Saifullah raina ne kawai ba zan iya zarewa na ba shi ba shi ma ɗin don ba ni da iko akan hakan ne".
Ya yi shuru na tsawon wasu mintuna kafin ya matso dab da ni idanunsa akaina ya ci gaba da furzo da sirrin take taskace cikin tsokar zuciyarsa.

"Ba zan iya hana zuciyata son ki Amatullah har abada, kuma komai za ki yi ko ki zama hakan ba zai taɓa sanya soyayyar da nake yi miki ta sauya ba. Sai dai dole na danne abin da nake so don wanzuwar farin cikin aminina, zan taya sa yaƙin neman soyayyarki har sai na ga ya yi nasara. Sannan ina roƙonki don Allah kar ki fitar da wannan maganan, ina so yadda muka yi ta a nan mu burne ta a nan".
Yana dasa aya a zancen ya sa kai ya fice yana ɗan lumshe idanunsa da suka cika da ruwan ƙwalla, da ido na raka shi har ya fice daga cikin falon daidai sa'ilin fitarsa daidai lokacin da na durƙushe akan gwiwoyina ina jero wani kuka marar sauti.
Haka Anty Sawwama ta zo ta same ni ta ɗago ni daga inda nake durƙushe ta kwantar da ni a jikinta yayin da take shafa kaina cike da kulawa ta soma faɗin"Uwata ki daina wannan kukan ya isa haka, kuka ba ya magani da yana magani tabbas da yanzu ya kawar miki da dukkan matsalolinki. Kuka ba mafita ba ne sai dai ma ya haddasa miki wani ciwon kamata ya yi ki ɗaga hannu ki gode wa Allah da ya yi miki wannan suturan, har ya kawo miki mai sonki kuma ɗan gidan mutunci da nutsuwa. Ki yi istikara ki nema zaɓin Allah ya yi miki zaɓin da babu nadama, dana sani balle kuma cizon ɗan yatsa a cikinsa. In sha Allah ina ji a jikina rayuwarki ta kusa sauyawa farin ciki zai maye gurbin dukkan wasu baƙaƙen abubuwan da suka wakana a cikin rayuwarki".

Luf! Na kwantar da kaina a jikinta ina cikin gaba da sauraron tarin nasihan da take yi mini, a haka ina kwance a jikinta har bacci ya ɗauke ni ba tare da na sani ba. Dogon bacci na yi ban tashi ba sai can yamma lilis na tashi na yi wanka na zo na gabatar da salla a makare, na daɗe kan sallayan ina ta tunani kafin na tashi na fito waje na yi wasu ayyukan kana na soma kici-kicin ɗaura girkin dare. Sai dab sallan magrib na gama girkin na sauƙe tare da yin alwala na shiga ciki na yi salla, ban tashi daga inda na yi sallan ba na ɗauko alƙur'ani na soma karanta cikin nutsuwa da fitar da haƙƙin ko wani harafi bisa ƙa'ida. Sai da na yi sallan isha'i kana na tashi na fito daga ɗakin lokacin har su Yaya Alhassan sun dawo, na zubo mana abinci tare da Anty Sawwama yayin da Yaya Alhassan, Amir da Umar suka ci nasu tare a kwano ɗaya kamar yadda al'adan gidan yake, bayan mun kama cin abincin na tattare kwanukan na je na wanke su ina doso ƙofan falon na ji Anty Sawwama tana sanar da Yaya Alhassan yadda suka yi da su Saifullah.
Kaina a ƙasa na shigo cikin falon na wuce ɗaki daidai lokacin da nake jiyo muryar Yaya Alhassan yana faɗin"tabbas kam mutumin kirki ne, sai ta ya ta da addu'a in shi ne alkhairi gare ta Allah ya tabbatar...". Bai ƙarisa zancen ba sakamakon wani tarin da ya sarƙafe shi ya fara yin sa tamkar zai shiɗe, da sauri na juyo na fita waje na je na ɗebo masa ruwa na miƙa masa.

Amsa ya yi ya ɗan sha kaɗan kafin tarin ya lafa muka haɗa ido da shi na ga ya yi hanzarin ɗauke na shi. Yana amsa sannun da Amir da Umar suka haɗe bakin wajen yi masa. Ya miƙe da hakan ya sa ni bin shi da kallo sai dai ko kaɗan ya ƙi yarda mu haɗa ido da shi, a taƙaice ya furta"Umma zan je na kwanta gabaɗaya ba na jin daɗin jikina". Bai jira amsar da za mu ba shi ba ya juya ya fice daga cikin falon, ya bar mu da tarin tambayoyi a ƙunshe a cikin ranmu. Ganin hawaye ya na ƙoƙarin ƙwace mini ya sanya ni na yi wuf na shige cikin ɗaki na zube akan katifa ina sakin hawayen tamkar bakin indararo, na daɗe ina kukan yayin da nake tuno zancen da muka yi na ƙarshe da Yaya Alhassan kafin sheiɗan ya yi nasara a kaina na sa ƙafata na guje wa gida da ƴan uwana masu tsananin ƙaunata.
Tashi na yi na zauna tare da tafka wani uban tagumi cikin duhu dulum da ya mamaye cikin ɗakin ko tafin hannuna ba na iya gani, gabaɗaya na rasa mafita da yadda zan ɓullo wa lamarin balle har na sama matsaya guda da zan tsaya akan sa.

Jin ƙaran waya na yi sai dai da yake ban saba da riƙe wayan ba, har ta gama rurin neman agaji ta yi shuru ban bi ta kanta ba, sai da aka ƙara ƙira a karo na biyu kafin na kai hannu na jawo wayar na zuba wa fuskar wayar kallo.
Baƙuwan lamba ne babu suna, kuma a cikin maganganun da muka yi da Amir bai ce mini ya ba da lambar a kowa ba, hana ƙarya dai ya ce da ni ya sanya mini lambobin duk wanda ya dace a ciki. Ina ganin ƙiran har ya katse aka ƙara ƙira a karo na uku kafin na ɗaga na sanya ta a amsa-kuwwa na ajiye a gabana.

Cikin wani irin sanyin murya mai ratsa jini da jijiyoyin ya bi har ta cikin ɓargo na ji an yi sallama, ba tare da na ɗauki muryar ba na amsa sallamar daga nan na yi shuru ɗaya ɓangaren ma aka yi shuru har sai da na yi zaton ƙiran ya katse kafin na ji an yi magana.

"Na san ba ki gane mai magana ba ko?".

"E". Na amsa da shi a taƙaice.
"Saifullah ne". Ban san lokacin da na maimaita sunan cikin É—aga sauti ba.
"Saifullah kuma? A ina ka sama layina?".
Chapter 61 · 0% Book details