Sashe 43
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Haka nake kwana na tashi da tunanin halin da Zinariya take ciki, tabbas da na san garin Abuja ko kuma na taɓa zuwa cikinsa babu abin da zai hana ni tashi takanas na je neman Zinariya. Sai dai na ji an ce mini babban gari da ya tara manya da hamshaƙan mutane neman mutum a cikin irin wannan garin ba ƙaramin aiki ba ne.
Ina ƙwance a ɗaki ina ta saƙa da warwara a cikin raina yayin da wani sashin zuciyata yake hasko mini rayuwarta ta baya mussamman yadda muka rayu da Abba, ta tabbata a gare ni ba ni da wani masoyin da ya wuce shi haka nan babu wani wanda zai nuna mini ƙauna kwatankwacin irin wanda ya gwada mini. Murmushi kawai na yi ina jinjina kaina don izuwa yanzu a zo bijiren da zuciyata ta bushe ta zama tamkar dutse wajen dake wa, babu abin da yake sani fargaba balle tsoro ko kuma tausayi haka nan hawaye ba za zuba daga idanuna. Maimaikon lokacin da suka shuɗe da ba na sanin sa'ilin da suke cin gashin kansu.
Babu shiri na tashi daga kwanciyar da na yi sa boda hayaniyar da na ji yana tashi a tsakar gidan ana ta ruwan shariya tamkar dangin maguzawa. Diro wa na yi daga kan katifar Zinariya da nake kwance na bayyano waje.
"To ƴaƴan kaji dangin karnuka wani gurmin kuma aka haɗo da sanyin safiyar nan?". Na yi zancen yayin da nake iso wa inda na ga su a tsaye cirko-cirko tamkar sun haɗiyi taɓarma.
"Wai don tsabar iskanci da rainin wayon mutanen cikin gidan nan, na É—aura girki daga na fito na shiga banÉ—aki na dawo na samu an sace tukunyar gabaÉ—aya, sa boda rashin ta kunya da tsiya. Wallahi a fito mini
Sabuwar yarinyar da aka kawo da na bi ya mata littafin sirrin zaman bariki babi-babi, kuma aka yi karati yarinyar kanta yana É—auka uwa uba kuma a wayenta ta shigo harkar.
"Ke Kyawawa shi ne kika hargitsa gidan haka da sassafen nan? Ko da yake ban ga laifinki ba a É—auke tukunya sukutum ai dole ki tada jijiyoyin wuya. Yarinya ci gaba da masifa har sai an fito miki da kayanki ai bala'i da masifa babu uwar wacce ta kashe".
Ina rufe bakina Aminu da shigowar sa ke nan ya amshe zancen"ina gaida uwar haɗa gurmi, yarinyar nan kin san kan tsiya kuma kin san wassulanta. Kin san har yanzu kaina ya ƙasa yarda cewar ki na da haddar alƙur'ani a cikin wannan kan nakin".
Na saki shewa har da tafa hannu kana na ce"ai kuwa ya kamata ka yarda don yadda nake murza wulaƙanci na tofar. Haka nake sarrafa ayoyin cin alƙur'ani yayin rera su". Ya kwashe da dariya mai sauti"Mahaddaciya ga sani ga ilmi kuma ga shagala". Ban ce da shi komai illa murmushin da na sakar masa yayin da nake juya wa na koma cikin ɗakin.
Na zauna na yi shuru tunanai kala-kala suna ziyartar cikin kwanyanta, tun da na sa ka ƙafata na fito daga cikin gidanmu daidai da rana guda ban taɓa jin ina son na ƙara kallon fuskar Umma ba balle har na yi kewarta ko na ji sha'awar son kasancewa a tare da ita, kamar yadda nake ji a cikin ƴan kwanakin. Wani tsananin kewarta da son ganinta nake yi.
Haka na wuni ina wannan tunanin bayan na yi sallan asr na kwanta a nan inda na yi sallan, take wani bacci mai nauyin gaske ya yi awon gaba da ni. Irin da baccin da zan iya bugan ƙirji na ce rabo na da bacci cikin kwanciyar hankali irin sa tun kafin rasuwan Abba.
A firgice na farka jikina gabaɗaya yana karkarwa ga wani uban zuffan da ya jiƙa mini jiki lajab kamar wacce aka kwarawa ruwa. Ƙirjina ya na dakan lugudan-lugudan tara-tara tara cikin daƙiƙu tara. Na buɗe baki zan kurma ihu sai kuma na yi hanzarin tufe bakina da tafukan hannayena. Allah ya ba ni ikon karato addu'ar da ta yi nasarar fara zuba kaina a cikin wannan rikitaccen yanayin mai kama da almara.
"Hasbunallahu wa ni'iman wakil".
Na furta har izuwa lokacin ilahirin jikina yana rawa sa boda munin mafarkin da na yi da Ummata. Mafarki na yi wai ga ni ga ita a gaban Allah ya na yi masa hisabi yayin da yake tuhumarta akan amanarta da ya ba ta ta yi masa riƙon sakainan kashi ta kuma wofartar da nauyin da yake bi sa wuyanta, wai Ummata ta gaza kare kanta Mala'ikun azaba suka saka mata sarƙan wuta su ka nannaɗe mata jikinta suka jefa can cikin ƙasan wuta, ina ji ta na ihu ta na kururuwar neman ceto da agaji na yunƙura zan je na taimaka mata wai sai Abba da yake sanye da fararen kaya tas ya riƙe mini hannuna. Ya jijjiga mini kansa alamar kar na je, haka na durƙushe a wajen ina kuka ta na ta aikin lallashina.
Shewa da ihun da na ji an saka a filin tsakar gidan shi ya yi nasarar dawo da ni cikin hayyacina daga nisan zangon da na yi a cikin kogin tunanin da na faɗa. Na kai hannuna na kawar da hawayen da suka ɓata mini fuskana na yunƙura zan tashi na ga an shigo da ledan kaya cikin ɗakin.
"Ledar nan fa, na wane ne?".
Sha'awanatu da ta shigo da akwatin ta washe baki ta na kallona, don tun bayar faruwar wancan abun tsakanina da ita ta shiga taitayinta ba ita kaÉ—ai ba ma har wasu daga cikin matan gidan, silar da ya sa suke shakka ta kenan.
Mun ɗinke ni da ita don ta zama cikakkiyar ƴar fadata mai lasisi. Duk wani jagwal da ta taro yake neman girmewa lissafin ƙwaƙwalwarta ni take tunkarowa na warware mata shi sala-sala.
"Ai Zinariya ce ta dawo yanzu haka ma ta na tsakar gida".
Ba ta rufe bakinta na daka tsalle na tsallake ledan da ta shigo da shi É—in, na fito tsakar gidan. Muna ganin juna ni da Zinariya habawa! Sai murna muka rumgume juna ana yaushe gamo. Na ja hannunta suka cikin É—aki na zaunar da ita a bakin katifar ina faÉ—in"ke kuma da muka yi da ke ba za ki wuce wasu kwanaki ba. Kika je kika share waje kika yi zamanki. Ki ka bar ni nan cikin fargaba da zulumi".
Ta ɗan murmuss tare da sadda kanta ƙasa kafin ta ce"dalili ne mai girma ya kawo hakan Amatullah, yanzu dai ba n ruwa na yi wanka tukunna don wallahi duk wani gaɓa a cikin jikina ciwo yake min". Kaina kawai na jinjina mata na ɗauki bokati na fita waje, ɗakin duk wacce na yi niyya da ra'ayi na faɗa na kamfato ruwa na yi fito babu mai ce wa da ni uffan tambaya na ba'asi. Na kai mata ruwan banɗaki ta shiga wankan na dawo na kallafawa duk wata wanda ta yi girki sai ta kawo mini plate guda ɗakina Zinariya ta ci ta yi haniƙan. Babu mai cewa da ni ko kanzil don na isa har na yi yawa, Hajiya Babba ma sai dai ta ganni ta jijjiga kaina don na zame mata ƙadangaruwar bakin tulu a bar ni na ɓata ruwa, a kashe ni a yi asarar tulu. Dole ƙanwar naƙi ta na ji tana gani sai idanuna ta kawo ta zuba mini.
Sai da na bari ta yi wankan ta ci abincin, ta je ɗakin Hajiya Babba ta gaishe ta sannan ta dawo ta kwanta. Na zo kusa da ita na zauna na ce"na ta ƙiran layinki kullum a rufe, ga shi kuma yanzu na ga kin dawo babu waya a hannunki. An ya lafiya kuwa wannan tafiyar?". Kamar wacce na tsikara mata allura ko kuma wacce na sosa mata inda yake mata ƙaiƙaiyi ta yi zumbur ta tashi ta zauna tana fuskana.
"Kin gan ni nan tsabar rashin hankalin da na shiga har ma na manta da wani abu a duniyar nan wai shi waya. Tun da na ba ro ofishin Æ´an sanda da aka ba ni wayar na kashe ta na jefa a cikin ledan har yanzu da nake yi miki wannan maganar, ban sama nutsuwar da zan É—auko ta ba".