← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 72

Sashe 32

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Lafiya Amatullahi me ye yake faruwa?". Hajiya Babba ta jefo mini tambayar yayin da take ƙoƙarin ƙwace wuƙar da yake hannuna, na turje ina faɗin"Hajiya ki bar ni, ki bar ni na koya musu hankali". Ba ta yi ƙasa a gwiwa ba har sai da ta karɓa wuƙar daga hannuna.
"Wai me ye yake faruwa ne?". Hajiya Babba ta ƙara maimaita mana tambayar a karo na biyu, Sha'awanatu ta kwashe komai ta sanar da ita sai da ta gama sauraron ta kafin ta waigo gare ni"duk abin da ya faɗa haka ne?". Ban iya amsa mata da kalmomin da baki kan iya furtawa ba illa gyaɗa kai da na yi alamar e, don cikin abin da ya faru babu wanda Sha'awanatu ta rage ba tare da ta furta ba.

"Kai solofiyo zo ka fice daga cikin ɗakin nan". Hajiya Babba ta yi zancen tana saitawa saurayin hanya, cikin rawar jiki ya fice. Haka ta sallame kowa daga cikin ɗakin aka fice ana ta ƙananan suturai da yamaɗiɗi.
"Ke Sha'awanatu kin gan ni nan da kike ji da gani duk yadda na yi ƙaurin suna a haɗa gurmi, to ba ba son abin da zai ɗaga min hankali. Ɗakin nan kin san da cewa ba ke ɗaya kike rayuwa a cikinsa don haka duk wani baƙon da za ki yi ko iyakarsa wuni ne babu kwana".

"Amma Hajiya ba ki dubi abin da ita ta yi ba sai ni? Shin idan ban kawo kwastomana cikin É—akina ba ina ake so na kai shi?". Sha'awanatu ta yi zancen cikin É—aga muryar da ina ta tsbbacin shi ya fusata Hajiya Babba ainun.
"Matuƙar ina ƙaunar ci gaba da zama a cikin gidana to ya zama tilas a gare ki ki bi dukkan umarni da sharruɗan da na gindaya miki. Idan kin ga ba za ki iya zama ga ƙofa nan sai ki haɗa kayanki ki san inda dare ya yi miki". Shuru ta yi ba tare da ta ce ko kanzil har Hajiya ta gama zancenta ta waigo gare ni.
"Ke kuma zan ja miki kunne a karo na farko kuma wanda zai kasance shi ne na ƙarshe, kar ki ƙara yin gangancin ɗaukar makami a cikin gidan nan".

"To".

Kawai na amsa mata da shi a taƙaice, ta juya ta bi ta tare da wuƙar da yake hannunta. Kallon-kallo muka yi wa juna ni da Sha'awanatu kafin na wuce zuwa makwancina na kwanta raina a jagule. Ina ta jiran na ji ko za ta kunna sautin da ta yi ikirarin cewar ba ta iya bacci ba tare da ta kunna sa ba, sai na ji shuru kamar Malam ya haɗiye shirya. Na yi ƙwafa ina gyara kwanciyata tare da ƙara tabbatar da cewar wargi ma waje ya samu, kuma maganin biri karen maguzawa.
[12/5, 5:07 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

________________________________________

Page 6️⃣2️⃣

Ban iya runtsawa ba har sai da dare ta raba sosai, sai faman juyi nake yi na kasa yin baccin. Gabaɗaya ba na jin daɗin komai raina ya gama ragulewa yayin da zuciyata ta lalace ainun. Ƙwafa na yi ina tashi na zauna duk da kuwa duhun da ya mamaye cikin ɗakin nan sai dai hasken farin wata yana hasko cikin ɗakin daga tagar da yake a buɗe.
Karatun alƙur'ani na soma yi tun sautina ba ya fita har sai ya soma fita na ɗau tsawon lokaci ina karatun har sai da na ji wani sanyi ta ratsa sashin ruhina, sai da na yi sallan asubahi kana na kwantar da haƙarƙarina wani bacci mai nauyin gaske ya ɗauke ni, sosai na yi baccin ban farka ba sai da hantsi ya fito.

Ina buɗe idanuna na ga ranar ral ta galle, na yi zumbur ina miƙewa tare da murtsike idanuna don tabbatar da sahihancin abin da nake gani. Tabbas rana ta yi saboda yadda ta galle haske da zafinta ya mamaye ko'ina. Kallabina na za ra na ɗaura akaina na saka hijabina na ɗauki buta na fito na wanke fuska da bakina na mayar da ita cikin ɗaki, kana na fito ina fitowa muka haɗu da Zinariya. Muka sakarwa juna murmushi kafin na ce"ranki shi daɗe kin tashi ke nan? Sai yanzu na ki safiyar ta yi ke nan?". Ta yi miƙa kafin ta ce"wallahi ke dai bari daren jiya ban samu na yi bacci da wuri ba ne, na tsaya yin waya ban yi aune ba har sai da lokaci ya ja kin gan ni nan sai yanzu na sama daman tashi da ƙyar".

"To Allah dai ya sa kin yi salla?".

Ta taɓe baki"so nake yi yanzu idan na yi wanka, inna ci abinci sai na samu na yi sallan. Don ina jin sallan daren jiya ma ban yi ta ba na ɓige da yin waya".

"Sallan kike haÉ—a wa a kanki haka?".

"To ya ya zan yi Amatullah ayyuka su yi min yawa, dole wani abun sai ana ajiye shi a gefe idan aka sama sarari sai a É—ago shi".

Shuru na yi don mamaki da al'ajabi ya hana ni furta ko da kalma guda, sai da na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya kana na sama lasisin faɗin"ya dai kamata kam ki samu ki yi sallan, ni na fita wajen aiki".

"In kin dawo za mu yi magana". Ta murmusa"akwai zancen bakinki na ga alama sai na dawo É—in dai kawai sai mu tattaunawa". Dariya ta fashe da shi har ta tafa hannu, ban tsaya jiran abin da za ta faÉ—a ba na fice don ko ban tambaya ba na san cewa na makara.
Gudu-gudu sauri-sauri nake tafiyar ƙafafuna har suna sarƙewa tsabar sautin da nake zuba wa tamkar za tashi sama, kamar daga sama na ji an danna mini horn lamarin da ya yi matuƙar gigita ni. Na ɗaura hannuna aka tare da runtse idanuna ina jiran na ji ta inda motar za ta doke ni da yadda Allah zai yi da ni.
Ji na yi motar ba ta dake ni ba hakan ya ba ni ƙwarin gwiwan buɗe idanuna don ganin abin da yake wakana, take idanuna suka sauƙa akan fuskar Saif da yake tsaye a gabana ya zube dukkan hannayensa a cikin aljihun wandon suit ɗin da yake jikinsa, idanunmu suka sarƙafe cikin na juna na tsawon wasu daƙiƙu kafin na yi ƙarfin halin janye nawa gefe guda.

"Amatullah ko?".

Na gyaÉ—a masa kaina da hakan ya ba shi damar ci gaba da maganar da yake kamar an yi masa dole ko kuma mai ciwon baki.
"Da kin daina wahalar da kanki ki na yin sammakon zuwa wajen aikin da ba zai amfane ki da komai ba, da zan ba ki shawara ki ɗaura da na ce da ke tun wuri da kin ɗauke ƙafarki daga cikin wannan gidan".
Na cira kaina ina kallonsa sai dai kwarjininsa da cika ido ya hana ni ba ni damar yi masa dogon kallo.

"Me ye yake nufi da waÉ—annan maganganun nakan?".

"Ina nufin ba za ki taɓa samun gurbi a cikin zuciyoyin mutanen da suke rayuwa a cikin wannan gidan nan, ba ki da tarbiyya da nagartar da ya dace ki kasance a kusa da mu kasancewarki mai zaman kanta kuma a cikin gidan magajiya cikin tsakiyar karuwai da ƴan daudu. Da babu abin da suka sanya a gabansu face saɓon Allah da kaucewa koyar wa Annabinsa".
Hawaye suka ciko mini kurmin idanuna sa boda zafin kalamansa da na ji, kaina na ƙasa da hakan ya ba wa hawayen damar kwaranya na kuma gaza samun ikon tsayar da su.

"Amma ka san cewar ko wani bawa da irin na shi salon ƙaddarar da Ubangiji yake ƙaddara masa ko....?". Tun kafin na gama zancen ya ɗaga mini hannu alamar ba ya ƙaunar sauraron raguwar zantukan nawan.
"Allah ba ya taɓa ɗaura wa Bawa abin da ba zai iya ba. Kuma duk wani abin alkhairin da kika ga ya sama Bawa to daga Allah ne akasin hakan kuma daga mu ƴan adam ne".

Jinjina kaina na yi ina haɗiya kukan da yake ƙoƙarin kufce mini, na kai hannu na kawar da hawayen da suka ɓata mini fuskana kana na furta"duk kalamanka babu kuskure a cikinsu, amma ka roƙi Allah kar ya jarabce ka da abin da ba za ka iya ba kuma ba ka taɓa tsammanin tsintar kanka a cikin irin rayuwar ba". Ina dasa aya a nan na juya na bar shi tsaye a wajen, na karya kwanar da za ta sada ni da gidan. Baba Mai gadi na iske zaune a bakin gare ɗin na durƙusa har ƙasa na gaishe shi ya amsa mini cike da kulawa, ban bari mun yi wani dogon zance da shi ba na tashi na shiga cikin gidan.
Babu kowa a falon don hakan kaina tsaye na wuce ɗakin Altine na shiga cikin banɗaki na kulle kaina na jingina jikin ƙofar banɗakin yayin da wasu hawaye masu ɗumi suke gudun famfalaƙi a bisa kuncina suna zarce wa har izuwa saman haɓata.

Tabbas juyi-juyi ce in ji kwaɗo ya ce wash! Da ya tsinci kansa tsumgum a cikin ruwan zafi. Haƙiƙa ta kan zo a ko wacce irin siga ba tare da ta yi raunin mutumin da za ta faɗa kansa ba. A zamanin baya idan wani ya kalle ni ya ce wannan yarinyar za ta iya sanya ƙafa ta bar cikin gidan mahaifinta ta shiga duniya ta yi zaman kanta, ilahirin mutanen da suka sanni kuma su ka san wace ce ni, sai sun yi haɗaka sun yi taron dangi sun ƙaryata abin da ya furta cikin babbar murya. Sai ga shi ƙaddara ta jefo ni cikin duniyar da babu kulawar uwa balle uba, babu mai tsawartawa balle ƙwaba, babu mai hana ki balle ya saka ki duk abin da kika ga damar aikatawa shi za ki yi babu mai tambayarki dalili balle har ki sama tagomashin shawara. Babu tswatarwa iyaye balle dangi babu mai tanƙwara ka balle ya tursasa ka ka yi abin da ba kya yi niyya ba.
Chapter 32 · 0% Book details