Sashe 6
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ya Zuljalali wal ikram ga baiwarka nan". Na yi furucin a bayyane cikin sanyin jiki haɗe da na murya, na salwantar da aƙalla mintuna uku a tsaye kafin na ja ƙafafuna na bar ƙofan gidan na yi dogon tafiya kafin na iso bakin wani tankamemen gidan da aka ƙawata da shukayen koren fure. Na ƙarar da mintuna ina kallon gidan kafin na isa na ƙwanƙwasa gate ɗin wani mutum ya fito ya buɗe ƙaramin ƙofan gidan gare ɗin yana jefa na da wani irin kallo.
Na tsuguna har ƙasa na gaishe shi sai dai maimakon ya amsa mini sai ya jefo mini wats tambayar cikin zafin rai.
"Ke me ye kike yi a nan wajen?".
"Na zo neman aiki ne?". Ya watsa mini wani ƙazamin kallo"ce miki aka yi ana neman masu aiki a gidan nan? To su masu aikinsu tun daga Abuja ake kawo musu kamfani suke zuwa su cike takarda su zayyana irin wacce suke so a kawo musu su zaɓa, ki tashi ki bar ƙofar gidan nan tun kafin na ɓata miki rai". Na haɗe hannayena waje guda alamar roƙo"don Allah ka taimaka mini na shiga cikin gidan na yi musu magana da kaina, wallahi ina tsananin buƙatar aikin nan ne".
"Ke zan haɗa da Allah ai ki taimake ni ki tashi daga nan wajen tun kafin masu gidan su fito. Don idan suka fito da ni da ke duk ba za mu ji daɗi ba". Yana rufe bakinsa aka buɗo ƙofar gidan yana faɗin"wai ina ka shiga ne ina ta ƙiranka?". Cikin rawar jiki ya ce"Allah ya huce zuciyarka ranka ya daɗe ka daɗe ka yi shekaru irin na dabino, na ɗan fito waje ne amma ban yi nisa ba".
"Ka zo ka buÉ—e min gate zan fita amma ba zan daÉ—e ba zan dawo".
"To ranka ya daɗe a dawo lafiya". Har sun juya za su koma ciki idanun mai gidan ya sauƙa a kaina ya tsaya cak yana ƙare mini kallon tsaf.
"Wannan yarinyar fa me ye take yi a nan wajen?".
"Irin masu zuwa neman aikin nan ne, na ce da ita gidan nan ba a buƙatar wata mai aiki amma ta ƙi tafiya sai magiya take ta faman yi min". Maigidan ya ɗan matso kusa da n tare da zura dukkan hannayensa cikin aljihun doguwar rigar jallabiyar da take jikinsa fara sol, har izuwa lokacin idanunsa a kaina ya furta"ƴan mata me ye kike buƙata?".
"Aiki nake nema ranka ya daɗe ni wallahi ko wankau ne ma ko raino zan yi". Ya yi shuru yana ci gaba da kallo na har sai da na tsargu da kaina na yi ƙasa da ƙwayoyin idanuna ƙasa kafin ya ce"to shigo daga ciki mana sai mu yi magana". Raina a wanke fes ban kawo komai a cikin zuciyata ba na yi masa godiya muka shiga cikin gidan.
Babban gida ne iyakar kallona ban hango ƙarshensa ba, ga wajen ajiye motoci da aka jera wasu rantsatstsun motoci. Duk girman gidan talis ne mamaye a ƙasa ga wasu shuke-shuke masu ɗaukar hankali da daɗin ƙamshi. Yana gaba ina bin sa a baya har muka isa cikin falon da aka ƙawata da duk wasu nau'in ababen jin daɗi da more rayuwar gidan duniya.
"Ga waje ki zauna bari na ƙira Madam ɗin". Ya yi zancen yana nuna mini kujerar zama, na zauna a ƙasa dirshan ina jiran dawowar da tare da matarta san babu jimawa ya dawo hannunsa ɗauke da wani tray ya ajiye mini a gabana, ruwan gora ne da lemon kwali sai kuma kofi su kenan a bisa kan trayn ɗin.
"Ga ruwa ki jiƙa maƙoshinki kafin ta fito, ta ɗan shiga wanka ne amma babu jimawa za ta fito sai ku yi magana da ita wataƙila ba za'a rasa gurbin da za a ba ki aiki ba. Don na ga alamar kamar a buƙace kike da aikin ko?".
Na yi hanzarin gyaÉ—a masa kaina"e wallahi ina son aikin. In dai har Allah ya sa na dace da samunsa".
Ya murmusa kafin ya ce"ki jira ta fito bari na shiga na ba ku waje". Kaina kawai na gyaɗa masa kai ya tashi ya taka wasu matakala ya haye sama, na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya tare da runtse idanuna na ɗaga hannayena sama ina zabgawa Allah godiya da ya tarfawa garina nono na dace da samun aikin da nake biɗa.
Na ji an dafo kafaÉ—ana ta baya na yi saurin buÉ—e lumshashshun idanuna tare da waigawa, cak numfashina ya tsaya cak na wucen gadi bisa mummunan gamon da idanuna suka yi.
Maigidan na gani tsaye a gabana daga shi dai ɗan bante zandardar da shi mai faffaɗan ƙirji. Na yi zumbur na miƙe tamkar wacce aka tsigarawa matsilli jikina gabaɗaya yana rawa na ce"ranka ya daɗe ko zan je na jira ta a waje ne?".
"Ai babu wanda mace ma a cikin gidan nan, ni kaÉ—ai nake rayuwa a cikin gidan, amma zan ji daÉ—i idan ke kika amince kika ba ni abin da mace take ba wa mijinta".
"Amma ka san ba mace a cikin gidan ka ce na shigo har da cewa na jira ta tana zuwa?". Cike da tashin damuwa balle kunyar abin da ya aikata ya ɗage kafaɗa ya ce"to hakan laifi ne don na gayyato kyakykyawar mace kamar cikin gidana?". Ya ƙare zancen yana ƙara nufo inda nake, na ɗaura hannu a ka na kurma ihu.
"Idan ka matso inda nake sai na yi mata ihu wallahi".
Da mamakina sai na ga ya bushe da dariya yana faɗin"ai ko lasifika za ki ɗauko babu wanda zai ji sautinki balle har ya kawo miki ɗauki. Ki ba ni haɗin kai kawai mu yi abun ne dukka ba zai wuce mintuna ashirin zuwa talatinsa ƙarƙarinta mu yi awa ɗaya, sannan zan ba ki duk adadin kuɗin da kike buƙata ki je ki kashe wutar gabanki".
Hawaye suka fara zuba daga idanuna"ka ji tsoron Allah ka sani duk abin da kake yi yana sama yana kallonka. Sannan akwai ranar da za a haska duk abin da ka aikata lokacin da kake raye a gaban dukkan halittun duniya daga na farko har zuwa na ƙarshe, shin kai ba ka tsoron irin wannan ranar?".
Ya yi sakeke yana kallo na"kin ga Malama duk wannan maganganun nakin ba su za su saka na ƙi aiwatar da abin da na yi niyya a kanki ba". Da sauri na juya zan fita ya riƙo gefen hijabina, ban yi wata-wata ba na fice hijabin na bar masa na fantsala da gudu na yi wajen ƙofa Allah ya rufa mini asiri na ji ƙofar a buɗe na fice ƙafata tamkar zai taɓo ƙeyata tsabar saurin da nake falfalawa.
"Baiwar Allah lafiya na ga kin fito cikin tashin hankali?". Mai gadin ya tare ni da zancen da na kasa samun sukunin amsa masa. Na soma jan gate É—in kamar zan cire ta.
"Ki yi a hankali bari na buÉ—e miki".
Ya zare sakaran jikin ƙofan ya buɗe na fita sai da na fito na lura da yanayin da nake ciki, na ware ɗan kwalin kaina na yafa a kaina na lulluɓe wuyana zuwa ƙirjina da shi, ko takalmina ban ɗauko ba na fita tsabar kiɗima da ruɗewar da nake cikinsa. Na ji an buɗe ƙofar na yi saurin waigawa, mai gadin ne ya fito ya zuba mini ido cikin takaici yake faɗin"wannan dalilin ne ya sa tun farko na ce ki bar ƙofar gidan nan don in har Allah ya fito ya kan ki na san abin da zai faru kenan. Gidan nan da kike babu wata mace a cikinsa shi kaɗai yake zaune shi ma kuma sai ya ɗebi lokaci bai zo ba. Idan kuwa ya zo to har ya tafi duk daren duniya sai ya kawo mace wacce za su kwana tare. Kin gan ni nan ni ma da nake wannan aikin ba a son raina ba ne kawai dai don ba yadda zan yi ne, wannan ne hanyar cin abincina. Ƙarbi wannan ki hijabin ki saka na matata ne na ƙarbo miki a ciki".
Hawaye suna gudun famfalaƙi a fuskana na miƙa hannu na ƙarba hijabin na saka na suturta jikina. Na tsuguna har ƙasa ina yi masa godiya ya amsa yana ta saka mini albarka. Har na tashi zan tafi ya tsayar da ni.
"Ƴata ki kasance mai taka tsantsan don duk yawancin gidajen unguwan nan ba mutanen Allah ba ne a cikinsu. Idan har ba ku rasa abin da za su sanya a baki salati ba ke da iyayenki to ki yi haƙuri da wannan neman aiki don akwai hatsari a cikinsa sosai. Gwara ki zauna a gida tare da iyayenki idan ma ya zama dole neman aiki to mahaifinki ki ya fi dace ya fita ya nema ya kawo muku".
"To Baba na gode sosai". Na amsa masa har zuwa lokacin hawaye suna wanke mini fuskana, ya cire silifas ɗin ƙafarsa ya ba ni na saka ya umarce ni da har na ƙara ko da bin layin balle na zo kusa da gidan. Haka na bar ƙofar gidan ina kuka da takaicin abin da ya faru.
Ina cikin tafiya takalmin ya tsinke na ji kamar na ɗaura hannu a ka na ta zabga ihu ko zan ji sauƙi halin da nake ciki. Haka na riƙo takalmin a hannu ga rana ga yunwar da take ƙwaƙular ƴaƴan hanjina na dawo gida, na sama ƙofar ɗakin a kulle da makulin na san La'aniyatu ce ta rufe ɗakin don ita na bari a cikinsa.
Kafin na shiga ɗakinsu ta fito kamar ta san abin da zan tambaye ta ta miƙo mini ɗan makullina, na karɓa ba tare da na ce da ita komai ba na buɗe ɗakin na shiga na zube akan tabarma kamar kayan wanki ina sakin wani irin kuka mai ratsa zuciyar mai saurare.
"Wai me ya faru ne kin fita kuma kin dawo ki na kuka?". Ban iya cewa da ita komai ba saboda yadda kukan ya gama galabaitar da ni. Ta ɗago ni tare da kwantar da kaina a bisa cinyoyinta tana ƙara maimata mini tambayar a karo na biyu.
"Wai me yake faruwa ne Amatullah?".