← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 72

Sashe 20

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Na gama duk wani aikin da ya kamata na yi shi yasa na zo nan na kwanta ina hutawa. Wallahi gabaɗaya gaɓobina ciwo yake yi mini.....". Kafin na gama zancen na ji ta sauƙe mini mari a gefen fuskana na hago da har ban san sa'ilin na saki ƙara ba ina dafe kuncina cikin jin zafi da raɗaɗin da ya ratsa har cikin kwanyata.
"Har kin isa ina magana ban yi wannan lalacewar ba. Tun farko daman na lura kaman kanki yana fisga sai na gyara miki zama tukunnan a cikin gidan nan kafin mu daidai". Tana ƙare zancen ta hankaɗe ni na sauƙa daga kan katifar zuwa ƙasa ta haye ta yi kwanciyarta. Na daɗe zaune a wajen ina jin raina yana yi mini wani irin zogi, yawun bakina ya jirkice ya koma mini tamkar maɗaci, zan iya cewa tun da nake a cikin duniya ba a taɓa cin zarafina an wulaƙanta ni irin na yau ba, na bi kayan jikina da ido da suka jiƙe sosai ina jin wani sanyi yana ratsa cikin jikina. A hankali na tashi na fita daga cikin ɗakin ina ɗaga ƙafata da ƙyar har na fito cikin harabar gidan na nema wani dakali na zauna ina shan hantsi tare da haɗa kaina da gwiwa.

Take zuciyata ta soma karatu mini tsohon karatun da na daÉ—e da haddace shi a cikin kaina. Tabbas gata da mutumcin duk wata É—iya mace shi ne gidan iyayenta haka nan babu inda za ta je a kanta da kima da daraja kamar a zo a tarar da ita a cikin gidan iyayenta. Na tuna da wani magana mai cike da hikima da darrusa masu yawan gaske.

Inda yake ce wa da mu a wurare uku ya dace a sama mace wacce ta amsa sunan mace ba wacce ta rako mata zuwa duniya ba. Wuri na farko shi ne a same ta a gaban iyayenta, in ba a same ta a nan ba to a same ta a cikin gidan mijinta in ba ta gidan mijinta to a same ta a cikin kabarinta. WaÉ—annan wurare guda uku su ne suka fi dace da mazaunin mace, in ba ta gaban iyayenta, to ta kasance tana gidan mijinta tana bautar Ubangijinta domin neman aljannarta. In kuwa duk ba a same ta a nan ba to zai fi kyautuwa da saya mata daraja, mutumci, martaba da kuma kima idan aka tarar da ita a cikin kabarinta.
Ban san lokacin da hawaye suka zarya a kan fuskata ba sai jin É—umin su na yi akan fatan fuskana da har yanzu yake yi mini zogi sa boda da na sha a hannun Altine.

Na ɗago kaina ina ƙarewa girman filin tsakar gidan kallo da Altine ta yi mini umarnin sharewa. Babu shiri na sauƙe wani shirgegen ajiyan zuciya don a girman filin ko tun ƙarfe shidan safe na fara sharan akwai yiyuwar na wuni ina yi ba tare da na kammala ba. Na taɓa kayan jikina na ji ya bushe ƙarau na tashi na ji jiri yana ƙoƙarin nanani da ƙasa babu shiri na koma na zauna na dafe kaina da yake juyawa, ina karanto duk wani addu'ar da ya zo bakina a sa'ilin.

Ji da na yi zafin ranar yana takura ni ya tilasta mini tashi daga wajen na je wajen rumfar ajiye motoci kasancewar wajen intalok ne aka layyale ko'ina da shi, na shimfiɗa ɗan kwalina na kwanta a kai ina ta rawar sanyi ban san lokacin da baccin wahala ya yi gaba da ni ba. Sai jin wani gigitaccen ƙara na yi a cikin kunnena da ya tursasa mini tashi ba tare da na shirya wa hakan ba. Sai da na daina jin sauti da motsin komai na tsawon wasu mintuna sa boda yadda ƙaran ya kiɗima ni.
Kallon shi kawai nake yi yayin da ya fito daga cikin motan ya zo gabana ya tsaya tare da zura dukkan hannayensa cikin aljihun wandonsa. Bai yi mana ba na tabbatar da hakan ne sa boda ko kaɗan laɓɓansa ba su motsawa. Na kasa motsawa balle na yi yunƙurin tashi daga wajen da hakan zai ba shi daman shigo wa da motar ma'ajinta. Daidai lokacin da jina ya dawo na ji ya saki wani tsaki mai dogon zango kana ya juya ya bar wajen.

Da ƙyar na iya tashi tsaye na tsaya akan ƙafafuna da suke rawa da alamta gajiyar su ga jimirin ɗaukar nauyin saƙararren gangar jikina. Na mayar da ɗankwalina kaina na saka na soma tafiya, hanyar gate na nufi don a yadda nake jin jikina ba na tunanin zan iya tsinana komai na zaɓi na koma gida akan na ci gaba da zama a nan.
Na yi sa'a ban tarar da Baba Mai gadi a ƙofan ba balle ya hana ni tafiya ko kuma ya tsare ni da tambayoyi me ye yake faruwa. Kai tsaye na fita na soma tafiya ina haɗa hanya tamkar wacce ta yi tatil da kayan maye cikin wannan yanayin har na isa gida lokacin idanuna har wani dishi-dishi suke kallon abubuwan. Na ji wani daɗi a cikin raina da na hango ƙofar ɗakin a buɗe don tsayawa buɗe ta ma galabaitar da ni zai ƙara ni sosai. Kai tsaye na afka cikin ɗakin sai dai abin da na gan ya sanya ni dole na ja na tsaya.

Wata budurwa na tarar a cikin É—akin tana sauya kaya, gefe guda kuma an saka katifa, akwati da ragowar sauran kayan amfanin yau da kullum.
"Wace ce ke kuma? Me ye kike yi a nan?". Na watsa mata tambayoyin a tare, ta bi ni da wani malalacin kallo kafin ta
ce"ko ke ce Amatullah É—in?". Na gyaÉ—a mata kaina alamar e da hakan ya ba ta damar ci gaba da maganar.

"Yanzu wannan É—akin ba mallakinki ba ne mallakinmu ne ni da ke".

"Ban gane abin da kike son faÉ—a ba".

Ta yi fari da idonta kafin ta furta"kamar yadda kika ji na faÉ—a wannan É—akunan mallakinmu ne ni dake. Tare za mu rayu a cikinsa na kama hayar rabin É—akin kamar yadda idanunki suke nuna miki".
A kufule na ce"hakan ba mai yiyuwa ba ne, don duk ɗakunan cikin gidan nan ai mutum ɗaɗɗaya ne a cikinsa". Ta galla mini harara"ba kya buƙatar sai na ba ki amsa da kalmomin baki tun ga shi idanunki sun ga ne miki zahiri".
[12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

________________________________________

Page 5️⃣4️⃣

Na yi tsaye mamaki da al'ajabi ya na yi motsawa daga inda nake tsaye kamar gunkin ƙasar india. Na ja dogon numfashi na fesar daga bakina ina jin wani abu yana tasowa tun daga ƙasan ƙirjina har zuwa tsakiyar kaina. Ban kuma cewa da ita komai ba na ja ƙafafuna da suka sake na isa kan taburmana na zauna na ɗaura kaina a bisa gwiwoyina ina mayar da numfashi kamar wacce ta yi gudun ceton rai, ji nake yi kamar ɗakin yana juyawa na lumshe idanuna ina cije leɓena haɗe da sauƙe wani gauron ajiyar zuciya mai matuƙar sauti.
Kaina wani irin ciwo yake yi kamar zai faɗo ƙasa na zame na kwanta akan bayana ina kallon rufin ɗakin ina karanto suratul Yusuf daga cikin kaina, ban yi nisa ina yi ba na ji an kunna sauti an ƙure sauti a cikin ɗakin.
Sai da na firgita na tashi na zauna gaba ɗaya na manta da cewar yanzu ba ni kaɗai ba ce a cikin ɗakin, har cikin tsakiyar kaina nake jin sautin yana ratsawa. Ƙaran sauti da kiɗe-kiɗe suna daga cikin abubuwan da suke sautin kiɗima ni tare da saurin juya mini ƙwaƙwalwa da damalmala mini dukkan lissafi gami da hautsina mini hankali.

Na kai hannuna na toshe kunnuwana tare da runtse idanuna da ƙarfi, duk ina daurewa har lamarin ya gagare ni wai cire wando ta kai. Ba tare da na buɗe idanuna ba na ce"don Allah ki yi haƙuri baiwar Allah ki tage ƙaran sautin nan".
Ba ta tanka mini hakan ya sanya ni buÉ—e idanuna ina hango inda take na ga tana kwance a bisa katifarta tana ta sharara baccinta cikin kwanciyar hankali da nutsuwa ga sautin yana ta tashi a cikin É—akin.
Na tashi na ina jin hajijiya yana É—eba na dafe gefen gini ina tafiyan a haka har na isa wajen da ta ajiye MP na kai hannu na É—auka na kashe ta na mayar na ajiye.
Ko barin wajen ban yi ba ta farka tamkar sautin MPn da baccin da take yi tare suke tafiya, ta murtsike idanunta tana kallona.

"Bura uban can! Uban waye ne ya saki kashe min MP?".

"Amma kin san ai ɗakin ba ke ɗaya ba ne, kin san da cewa da ƙaran sautin nan ki na shiga cikin hayyacina".

Kamar na watsa mata tafasasshen ruwan zafi a jikinta ta miƙe zumbur ta tsaya akan ƙafafunta ta riƙe ƙugu.
"Ke bari na fito miki a mutum kuɗi fa na cake na biya na kama ɗakin nan ba wai kyauta nake zaune ba ko kuma alfarma aka yi min ba. Kin gan ni nan ni ba na iya bacci ba tare da na kunna sauti ba, don haka tun wuri gwara ki saba". Tana dasa aya a nan ta kunna MP ɗin ta koma ta yi kwanciyarta tana kaɗai ƙafa, na kasa motsawa daga wajen balle na koma inda na taso duk da jirin da yake ɗauka ta. Sai da na saki dogon numfashi na fesar kafin na ja ƙafafuna na koma inda na taso na zauna na zabga wani uban tagumi tamkar wacce aka yi wa rasuwa ta wani babban makusancinta.
Tun yana damuna har na zubar da komai na tashi na É—auki buta na fita na je banÉ—aki na yi tsarki, na fito ina isowa tsakar gidan na yanke jiki na faÉ—i jirif kamar kayan wanki.
Ban ƙara sanin inda kaina yake ba sai buɗe idanuna na yi na gan ni kwance a cikin wani ɗakin da ban ga ne wajen ba, na yunƙura zan tashi na ji na kasa dole na komo na kwanta ina tunano abin da ya faru kafin faduwar hakan.

"Sannu kin tashi ne?".
Chapter 20 · 0% Book details