← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 72

Sashe 48

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tabbas wannan abun babban lamari ne. Hakiƙa kin yi abin da ya dace a yaba miki". Deeno ya yi zancen cikin jinjin girman ƙoƙarin da na yi. Zinariya ta ɗago ni daga kwancen da nake na zauna kana ta zuba mini ido muryarta cike da rauni ta ce"Amatullah da gaske a rayuwarki ta baya kin taɓa zubar da ciki? Sannan baƙin cikinki ne ya yi sanadiyyar rayuwar mahaifinki? Mahaifiyarki kuma ta sallamaki ga duniya?". Ta watsa miji tambayoyin a dunƙule kuma a lokaci guda, sai da na ja dogon numfashi mai nisan zangon kafin na sama zarafin warware mata tsakanin zare da abawa, babu abin da na ɓoye mata game da gurɓataccen tarihin rayuwata na sanar da ita komai ba tare da na rufe wani abun ko na kwaskware shi ba.

Tun da na soma ba ta labarin take zubar da hawaye har na kai aya ina ƙarewa da faɗin"to yau dai kin sauraru tarihin rayuwata kin san wace ce ni...". Ba ta bar ni na ƙarisa ba ta rumgume ni duk mu biyu muka tuntsire da wani irin kuka mai matuƙar cin rai da azabtar da ruhi.
"Tabbas bakin uwa masifa ne ga ƴaƴanta abin da da yawa-yawan iyaye matan wannan zamanin ba su fahimta ba ke nan. Kaifin harshen Ummanki akan ki shi ne abin da yake bibiyar rayuwarki Amatullah, shi yasa ake ce wa DAFIN HARSHE ya zarce dafin maciji cutar wa da gurɓata duk wani abun da ya soma baki a ciki". Ban iya amsa mata da kalmomin da baki kan iya furtawa ba sa boda nauyin da bakina ya yi mini, harshena ya cika mini bakina da hakan ya taka rawar ganin wajen hana maganata fita. Deeno ne ke ta ba mu haƙuri har muka tsagaita da kukan da muke yi lokacin har ƙarfe biyar ɗin asubahi ya yi har an fara haramar ƙiran sallan asubahi.

Na tashi na shiga cikin banɗakin da take cikin ɗakin na yi alwala na zo na gabatar da sallan a zaune sa boda gabaɗaya jikina babu ƙwari, ba na zato da tunanin ƙafafuna za su iya jure ɗaukar nauyin gangar jikina. Ko da na iddar da sallan na yi dogon addu'an kafin na tashi daga wajen lokacin kusan ƙarfe shida saura, muka fara haramar tafiya Deeno ya kawo mana face mask ya ce mu saka haka kuwa muka yi muka saka kafin muka fito muka yi sallama da Deeno muka hau adaidaita zuwa gida, tun da muka shiga ban ce komai ba illa lumshe idanuna da na yi ji na nake yi tamkar majinyanci don ba na iya aikawatar da komai.
Ko da muka iso gida sai da Zinariya ta taɓo kafaɗuna kafin na ankare da cewar mun iso na sauƙa, ta miƙa masa kuɗinsa ya ja napep ɗinsa ya bar wajen, Zinariya ta kallo ni tare da cewa"wannan damuwar duk na mene ne Amatullah? Na yi tunanin tun da yanzu kam kin cika burinki ai komai ya zo ƙarshe babu abin da ya dace da ke face farin ciki da kuma murna cikar muradinki".

"Ni ma kaina hakan na yi tsammani sai dai ban san dalilin da ya sa na tsinci kaina cikin wannan damuwar ba".

Cike da ƙarfafawa ta ce"mu shiga ciki ki huta, da yardan Allah yanzu kam komai ya zo ƙarshe". Ta riƙo hannuna muka shiga ciki kai tsaye ɗakinta muka nufo ta buɗe mana ƙofar muka shiga ciki, a nan ɗin ma kwanciya na yi na rufe jikina ruf sa boda yadda nake jin wani sanyi yana ratsa jini da gaɓoɓin jikina. Ina kwance na ji Zinariya na magana.

"Ki tashi mu je wajen Hajiya Babba ki yi mata wannan babban albishiri É—in, ina da tabbacin ita da kanta ma sai ta sara miki balle kuma fadawan natan".

Furucinta ya tilasta mini yaye bangon da na lulluɓe har kaina da shi sai a lokacin na ga har rana ta fito ta dalle ko'ina da haskenta. Na yi miƙa haɗe da faɗin"wai har gari ya waye haka?".
"Tun yaushe kuwa, yanzu fa kusan ƙarfe goma ake nema ba". Na waro idanuna waje cike da mamaki na tashi daga kan katifar ta miƙo mini wayar na amsa muka nufi ɗakin Hajiya Babba tare.
Tana kishingiÉ—e muka iske ta muka gaishe ta ta amsa mana fuskarta babu yabo babu fallasa. Kafin mu ce komai ta tare mu da faÉ—in"ina fatan dai ki na lissafin ragowar kwanakin da suka rage miki ko?"
Na kaɗa ina murmushi kana na furta"ai in sha Allah ma daga yanzu duk wani lissafi ya ƙare, yau na zo gabanki da cikakkun shaidun da za su tabbatar miki da cewar duk wani alwashin da na yi na cika sa tsaf". Na lallasa wayar na shiga fegin hotunan da muka yi na miƙa wayar ta sa hannu ta amsa tana kallo sai da ta kalle su tsaf kafin ta ce"amma ai satan ɗaukar hoton aka yi tun da gashi ma kwance yake yana bacci, aka yi hoton".

"Hajiya idan kin tuna a cikin yarjejeniyarmu ba ki gindaya mini sharaɗin cewar sai na farke zan yi hoto da shi ba, don haka ko yanzu aka tashi tabbas ni na ci wannan wasan". Ta ɗan yi shuru ta na ta ƙare wa hoton kallo kafin ta ce"wannan hoton anya kuwa ba haɗa wa aka yi ba?".

"Hajiya ki dai ƙara duba wa sa kyau". Zinariya ta ba ta amsa, wayarta ta ɗauka ta ƙira Aminu ta ce duk inda yake ya zo yanzu ta na son ganinsa, ya kuma amsa mata da cewar ga shi tafe daman ba nisa ya yi ba. Cikin ƙasa da mintuna ashirin ya bayyana a cikin ɗakin ta miƙa masa wayar ta na faɗin"karɓi ka duba hoton nan ka gane min haɗa wa aka yi ko kuma na gaske ne". Na amshi wayar yana kallon hoton tare da yin zooming ɗinsa ciki da waje, sai da ya gama ƙure basirarsa kafin ya ce"billahillazi Hajiya wannan hoton na gaske ne ba haɗa wa aka yi ba, sannan ba aikin AI ba ne wannan na'urar zamani mai ƙwaƙwalwar nan. Wannan hoton na gaske ne". Ya mayar da idanunsa kaina.
"Tabbas kin cika mai cika duk wata maganar da ta furta kin kuma cancanci a jinjina miki bisa wannan na mijin ƙoƙarin da kika yi, yanzu kam ai sai ki kama harka babu kama hannun yaro ko?".
Na ɗan murmusa kafin na ce"ina buƙatan lokaci na yi tunani akan hakan, kafin na fara aiwatar da komai".

"Duk yadda kika ce haka za a yi ranki ya daɗe. Amatullahi mai abin mamaki ga sani fal ga kuma shagala". Duk mu ukun muka yi dariya ban da Hajiya Babba ta da murtuƙe fuskarta tamkar magribar ɗinya ta soma faɗin"akwai wasu maza biyu da suka zo neman ki jiya cikin gidan nan in taƙaice miki bayani a jiyan kawai sai da suka zo sau kusa biyar. Na shaida musu cewar ba za ki kwana a gida ba jiya ki na can otel don haka su dawo yau da misalin ƙarfe biyu na rana, don haka sai ki shirya tabar baƙi. Duk da ma dai na ga ba wani tsiyar ba ne a tare da su".

Ban kawo komai a cikin raina ba don na ɗauki zantukan natan kamar ƙidan shata don haka na ce"Allah ya kawo su lafiya ina nan ina jiran su". Da haka muka yi mata sallama muka koma ɗakinmu Zinariya ta yi mana girki muka ci na kwanta bayan na sha maganin zazzaɓi da na ciwon kai take bacci mai nauyi ya yi awon gaba da ni ba ni na tashi ba har sai da aka yi sallan zuhur, Zinariya ta tashe ni na yi salla bayan na iddar ta zo ta zauna da inda nake zaune.
"Yanzu me ya tsarinmu na gaba? A tunanin a waye ya dace mu turawa wannan sautin muryar da kuma hotunan nan?". Na ja dogon numfashi mai nauyi da sauti na fesar kafin na sama lasisin faÉ—in"tunanin da ni ma nake yi ke nan, amma zuciyata ta fi aminta da cewar mu nema lambar Muhammad Taufik mu tura masa sautin muryar. Hotunan kuma mu goge su tun da daman sa boda mu gamsar da Hajiya muka yi su". Ina rufe bakina Aminu ya É—ago labulen É—akin ya shigo ya zauna duk muka bi shi da kallo.

"Ga can baƙinki fa sun iso, su na falon Hajiya su na jiranki".

"Wai daman da gaske ne an zo nema na? Ni kuwa waye na sane da zai taso takanas ya zo cikin gidan nemana?". Ya É—age mini kafaÉ—arsa alamar shi ma ba shi da masaniya akan hakan.
"Ke kuwa ki tashi mana ki je ki ga su wane ne. Tun da an ce gani ya kori ji". Zinariya ta yi zancen da ya kama hankalina, ba cire hijabina da yake kaina da na yi sallan da shi ba na tashi na nufi ɗakin Hajiya Babba. Na bi takalaman maza da suke ƙofar ɗakin kafin na shiga ciki.

"Hajiya ga ni". Na furta ina daga tsaye tare da tsayar da ƙwayoyin idanuna akan ta.
Ta taɓe baki"ba ni nake nemanki ba. Baƙinki ne ga su can". Ta ƙare zancen tana yi muni nuni da samari biyu da suke zaune a cikin falon da sai a lokacin idanuna suka kai kansu.
Take numfashina ya É—auke na wuce gadi sakamako tozali da na yi da mutanen da ba na tunanin sake ganin su a nan kusa a cikin rayuwata. Jikina ya na rawa tamkar mazari na nuna su da Æ´ar manuniyar Æ´atsata.

"Yaya Alhassan da Amir ku ne?". Na yi zancen cikin rawar jiki da na murya, duk su biyun suka tashi tsaye muna kallon juna.
Yaya Alhassan ya ce"Amatullah ke ce kika dawo haka? Ke ce kike rayuwa a cikin gidan nan". A raunane ya ƙarishe zancen kamar zai yi ƙwalla. Na ji kaina ya soma juya idanuna suna hango mini abin da yake gabana bibiyu, ƙafafuna suka soma karkarwa na yi lu na faɗi a wajen babu wani gaɓar da take motsa wa a cikin gangar jikina.
[12/18, 3:30 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

______________________________________

Page 7️⃣2️⃣
Chapter 48 · 0% Book details