← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 72

Sashe 62

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yayanki Amir ne ya ba ni layin. Ina fatan bai yi laifi ba?". Numfashi mai zafi na furzar daga bakina kafin na ce"sanar da ni dalilin ƙiran don ba ni da lokaci". Ina iya jiyo sakakken ajiyar zuciya da ya sauƙe kafin ya sama zarafin faɗin"kawai na ƙira na ne na ji yadda kika wuni". Wani bambarakwai na ji lamarin ya zo mini a bazata mamaki da al'ajabi ya hana ni cewa komai illa jujjuya zancen nasan da nake ta ci a can cikin ƙasan raina.
Tamkar ya san abin da nake tunanin ya ce"ki na mamaki zantukana ko? Uhmm! Ni ma kaina idan na zauna mamakin kaina nake yi Amatullah ban taɓa tunanin zan iya furta irin waɗannan furucin da nake yi miki yanzu a kaf cikin rayuwa. Sa boda tun tasowa ta na tashi ni ban kasance mutum mai yawan magana ki shiga hayaniya ba, haka nan mata ba sa gabana harkan da ta sha min kai shi kaɗai nake mayar da hankalina a kansa".

"Uhmm". Na amsa da shi a taƙaice ina ɗaukar wayar na kara a kunnena bayan na cire ta daga amsa-kuwwar ina ci gaba da sauraron abin da yake furta wa.
"Amatullah ban zo gare ki da yaudara, mugunta ko kuma cutarwa ba. Hasalima zuciyata a wanke take babu wani mummunan abu a cikinta. Ba zan gaji da sanar da ke cewa ina sonki ba idan har kika ba ni dama babu abin da zai hana ni aurenki ko da kuwa duk mutanen duniya za su taru a kaina".
Cike da ƙosawa da zancen nasan na kawar da zancen ta hanyar faɗin"ina su Aryan?". Sai da ya yi ɗan jim kafin can ya ce"suna nan lafiya, Amatullah ki ba ni dama na nuna miki irin soyayyar da nake yi miki".

"Wai har yaushe ka fara son nawan ne? Da kake ta ikirarin soyayya haka?".

Na jefa masa tambayar raina a ƙunzume ina jin wani ɓacin rai yana cika mini zuciyata taf. Sai da ya ɗauki mintuna a ƙalla uku kafin ya dawo mini da amsa.
"Tun daga lokacin da na daina sanya ki a cikin idona, tun daga lokacin na fahimci sonki ya yi min mamaya a cikin zuciyata ba tare da na farga ba". Na yi luf tamkar wacce ruwa ya cinye ta.
"Wataƙila ki ji zantukana tamkar waƙan shata ta yadda za su shiga ta kunnenki su fita ta ɗaya. Na riga da na sanar da ke iya gaskiyar abin da yake cikin zuciyata, ke ma ki je ki yi shawara da na ki zuciyarki da dul waɗannan kike ganin kin aminta da su, sannan abu mafi muhimmanci ki yi sallan istikara. Kar ki ji shakka, nauyi, ko tsoron sanar da ni duk abin da kuke ji a ranki a game da ni. Kin gan ni nan a cikin rayuwar nan babu wani abun da yake ba ni tsoro, sa boda duk abin da nake tsoron faruwarsa ya riga da ya faru da ni. Duk abin da nake tsoron rasawa na rasa su kuma na ci gaba da rayuwa. Duk waɗannan nake tsananin so da ƙauna sun tafi sun bar ni irin tafiyar da babu waiwaye balle dawowa, rayuwa ta koyar da ni haƙurin dole da kuma juriyan ɗaukan duk abin ya faru da ni walau na shirya masa ko kuma akasin hakan. Don haka duk abin da kike ji a ranki game da ni kar ki yi shakkan sanar da ni da tunanin wai za ki ɓata min rai ko kuma na yi fushi".

Tabbas zantukan sun sama matsuguni a cikin kwanyata sun yi zaman dirsham, jikina ya yi sanyi ƙalau tamkar kazar da aka tsoma ta a cikin ruwan gishiri. Na ƙare matse wayar a kunnena yayin da wasu hawaye suke zuba daga gefe da gefen idanuna. Babu abin da yake yi mini yawo a cikin ƙwaƙwalwata face maganganun da muka yi da Muhammad Taufik ɗazu.
"Ki na ji na kuwa?". Tambayar da ya yi mini shi ya dawo da ni cikin duniyar zahiri.
"Ina jinka kuma ina so na roƙi wani alfarma a gare ta". Tun kafin na rufe bakina ya ce"faɗi dukkan abin da kike buƙata, matuƙar bai fi ƙarfina ba to tabbas kin riga da kin same shi".

"Ina so ka ba ni lokaci na yi tunani kuma na yi addu'o'i, kai a naka ɓangaren ka gabatar da abubuwan da suka dace wanda addini ya sharraɗanta a yi yayin nema. Sannan ina so har zuwa lokacin da zan gama kar ka ƙara yi mini wani maganan da ya danganci soyayya". Haƙiƙa na fahimci zantukan sun yi masa nauyi don sai da ya ɗauki tsawon lokacin kafin ya dawo mini da amsa cikin sanyin jiki.
"Ban yi zaton wannan alfarman za ku roƙo amma sai dai ba na fatan zuwan ranar da za ki nema wani abu a waje ki rasa. Don zan yi kamar yadda kika buƙata in sha Allah zan ba ki cikakken lokaci ki yi duk tunani da addu'o'inki, kuma ba zan ƙara yi miki maganar soyayyar ba har sai ke da kanki kin buƙata hakan. Sai dai ni ma zan roƙe ki alfarman".

Jikina a sanyaye na ce"ina jinka".

"Ina so kar ki hana ni ƙiranki, kar ki hana ni ganinki, kar ki hana ni zuwa inda kike. Sannan inna ƙira ki ko ba za ki ce komai ba".
Ba tare da wani dogon tunani ba balle nazari na ce"na yarda".
"To ina godiya ranki ya daÉ—e, bari na bar ki ki kwanta ki huta. Sai da safenmu a tashi lafiya".
"Allah ya kai mu".
"Amin ya hayyu ya ƙayyum". Daga haka na katse ƙiran na rumgume wayar a ƙirjina tare da lumshe idanuna, na daɗe a haka kafin na tashi na fito na yi alwala na koma na je na yi sallan raka'a biyu na ɗaga hannuna sama zan roƙi Allah sai dai na kasa magana, da zaran na buɗe baki kuka ne kawai yake fitowa haka na kifa kaina a wajen ina tilawan karatun haddan da yake kaina, a wajen baccin wahala ya ɗauke ni.
[12/25, 6:59 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

____________________________________

Page 7️⃣9️⃣

Washe garin ranar da ƙyar na tashi sa boda wani azababben ciwon kan da ya addabe ni idanuna ma ba na don buɗe wa balle na ga gilawan haske komai ƙanƙantansa. Tun safe ban fito daga cikin ɗaki ba ina kwance har sai da Anty Zulaihatu ta zo ta kana na tashi daga kwanciyan da na yi, na gaishe ta yayin da idanuna suke a lumshe, ta amsa mini cike da kulawa sa'ilin da take kai hannunta saman goshina ta ji ya ɗauki zafi garau tamkar garwashin da ke ƙasan tukuban tsire.
Cike da kulawa da ya gauraye da lallashi gami da lallama ta soma faɗin"Amatullah me ya yi zafi ne haka alhalin shi ba wuta ba? Me yasa kike so ki jefa kanki cikin wani irin yanayi da zai shafe mu daga ke har mu. Rayuwar nan fa da kike ji da gani ba ta taɓa tafiya a miƙe tsalin ƙalin dole sai an bi ta tudu da gangare sai an haɗu da ƙalubanale kala-kala, sai an yi katari da jarabawa mai sanya rauni a cikin zuciya. Ko wani Bawa da irin na shi salon ƙaddaran a cikin wannnan rayuwa. Don Allah na roƙe ki cire komai daga cikin ranki ki fawwalawa Allah dukkan lamuranki ki miƙa wuya gare shi ki sakankance cewa duk abin da ya zartar a gare ki hakan shi ne daidai, domin babu kuskure a cikin hukuncinsa". Tun da ta fara zancen na sadda kaina ƙasa ina sauraron ta ba tare da na katse ta har sai da ta kai aya.

Muryata ba ta fita yadda ya kamata na ce"Anty Zulaihatu abin da nake ta ƙoƙari ke nan, na cire damuwar da ya yi kane-kane a cikin zuciyata ni ma ina so na yi rayuwa cikin walwala da annashuwa kamar yadda kowa yake yi. Sai dai wallahi ko na ɗauko aniyar aikata hakan sai na ji na kasa, ba na ma sanin lokacin da tunanin yake zuwa mini balle na ankare da sa'ilin da ruwan hawaye yake kwaranya daga koramar idanuna". A raunane na ƙarshe zancen ina jin ƙirjina ya yi mini nauyin gaske tamkar wacce aka yi wa ajiyan wani gingimemen dutse.

"Haƙuri za ki yi Amatullah watarana sai na labari, komai zai zo ya wuce tamkar bai taɓa faruwa". Kaina kawai na gyaɗa mata ina kwantar da kaina a bisa kafaɗanta da hakan ya ba ta damar kai hannunta tana shafa sumar kaina a hankali.

"Yanzu da na zo ni Umma take sanar da ni wani abun alkhairi da farin ciki kuma". Cike da tashin fahimtan zantukan natan na ce"wani abu ke nan?". Sai da ta murmusa kafin ta furta"ta sanar da ni cewar akwai wanda ya zo cikin gidan nan neman soyyayarki ko kuma kai tsaye na ce aure ne ya kawo sa, don bai zo da wasa. Amatullah kin ga duk mutumin da ba ya shakkan haɗuwa da magabatan yarinya to haƙiƙa wannan mutumin ɗan gidan mutunci ne kuma zai yi wahala ya yaudare ta. Ki ba shi dama ki fahimcie shi ta nan ne za ki gano cancantarsa ko kuma akasin hakan, idan har kika ji ya kwanta miki a cikin rai to kawai ki amince masa ya turo a zo a yi magana". Tun da ta soma magana na yi laƙwas ban ce komai ba har sai da ta kai aya.

Cikin raunin da ya bayyana har a cikin kalaman da bakina ke furtawa na soma magana cikin rawar murya da ya haddasa rashin fitar sautina sosai.
"Anty yanzu ke ma ki na goyan bayan na yi aure a cikin wannan yanayin da nake ciki? Ina buƙatar kwanciya da nutsuwa kafin a kawo mini wani maganar da ya danganci aure ko soyayya, sannan wannan mutumin ya wulaƙanta a lokutan baya ya zarge ni da abin da ban aikata shi hasalima ko kusantansa ban yi ba".
Chapter 62 · 0% Book details