Sashe 65
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da suka gama na tambaye shi yadda suka yi ya shaida mini cewa ya yi in su gama su fito su tafi yana jiransu a waje. Kimtsa su na yi na kamo hannunsu muka je wajen Anty Sawwama suka yi mata sallama yayin da take musu leda taf da tarkacen abubuwa dangin su bushashshan kuɓewa, zogale, kanwa da kuwa yajin ƙuli ta ce su kai wa Umminsu. Har bakin ƙofa na rako su sai da na fitan su har suka isa wajensa kafin na jawo ƙofar na koma ciki.
Haka na ƙarar da wunin cikin tsinkewar zuciya da faɗuwan gaba. Bayan na yi sallan isha'i na ɗauko alƙur'ani na soma karantawa sai da na yi izu biyu daga suratul Naba'i zuwa suratul Nasi. Ban jin sha'awan cin komai hakan ya sa ni yin shirin kwanciya na kwanta ina ta saƙe-saƙe a cikin raina. Har bacci ya fara ɗauka ta na jiyo rurin wayata na zabura na tashi na ɗauko ta tare da ɗaga ƙiran don dama shi nake jira har bacci ya sace ni.
"Amatullah ina kika sama sautin muryan nan? Idan ban yi ƙarya ba fa muryanki ne me ya kai ki wajen mutumin nan? Me yasa kika naɗi sautin nan?".
Ko sallama bai yi mini ba illa jerin tambayoyin nan da ya soma jefo mini a jere wani na bin bayan wani.
"Ka tsaya na yi maka bayani". Na zancen cikin sanyi ganin yadda gabaÉ—aya lokaci guda ya birkice.
"Wani irin bayani za ki yi min Amatullah bayan abin da na saurara yanzu?. Tambaya É—aya zan yi miki wanda nake so ki ba ni amsarsa shin da gaske wannan sautin muryan da na ji mallakin Sheik Dawood ne mahaifi ga aminina Muhammad Taufik ko kuma na ce Sultan?".
Cikin ƙwarin gwiwan da ban san ina da shi na furta"ƙwarai kuwa muryarsa ne, kuma duk abin da ya faɗa haka yake babu kuskure a cikinsa. Na ba ka ka saurara ne don ka ceto rayuwar abokinka da har kake ikirarin a zama amini kuma ɗan uwa a gare ka. Na ba ka saurara ne sa boda mu ceto rayuwar ƴaƴan matan da zai iya lalatawa rayuwa a nan gaba" .
"Innalillahi wa inna ilahirin raji'un! Allahuma ajirni fi musibati. Ya Allah ta ina zan fara? Kin san yadda nake ganin girma da darajar Malam kuwa? Wallahil azim kallon uba nake yi masa haka nan shi ma ya ɗauke ni tamkar ɗan da ya haifa a cikinsa. Ina da tabbacin Sultan bai taɓa sanin cewa ba shi ya haife sa sa boda ya ba shi dukkanin kulawan da uba zai ba wa ɗansa". A sanyaye ya ƙare zancen cikin yanayin damuwa da ya haɗe da ruɗani.
"Dole ne kuwa sai na ji hakan ko ba daɗe ko ba jima. Ka fi ni sanin hanyar da ya dace ka sanar da shi wannan ɓoyayyan sirrin". Shuru ya yi na tsawon lokaci mai tsayi har sai da na yi zaton ko ƙiran ya katse ne sai da na duba na ga yana tafiya.
"Hello". Na yi furucin cikin sanyayyan amo.
"Amatullah". Ya ƙira sunana muryarsa ba ta fita sosai.
"Na'am Yaya Saif".
"Tabbas kin zo da babban lamarin da na ji kaina ya gaza É—aukansa, zuciyata ta kasa yarda cewa Sheik É—in da na sani ne ya rikiÉ—a ya zama wannan. Tabbas zan bayyana wannan sirrin ga Sultan sai dai ta ya ya kuma ta ina zan fara?".
Daga ni har shi muka yi shuru don ban san amsar da ta dace na ce da shi ba.
"Zan neman wani layin da bai san ni da shi ba na buɗe what's app da shi sai na tura masa, na tabbatar idan ya saurara ni ne mutum na farko da zai fara tunkara da matsalar daga nan sai mu warware matsalar a tare. Amma kai tsaye kam wallahi ba zan iya tunkararsa na sanar da shi cewar ina zargin Sheik da aikata wannan ɗanyen aikin ba". Shuru ina sauraronsa har ya gama ban iya cewa komai ba. Ina jin sa sai faman maimaita kalmar hasbunallahu wa ni'iman wakil yake yi kafin ya ce"amma me yasa kika zaɓi ni ki ka ba ni wannan memory card ɗin?".
"Ba ni na zaɓe ka zuciyata ce ta zaɓe a bisa wannan aiki don a wannan ɓangaren, tabbas ka sama yardanta".
"Amma da farko me ye kika yi niyyan aikatawa da sautin muryan da kika naÉ—a?".
Babu wani ɓoye-ɓoye balle nuƙu-nuƙu na fito ɓaro-ɓaro na sanar da shi komai har da yadda muka yi da Yaya Alhassan. Ya ɗan yi jim kafin can bayan lokaci mai tsayi ya ce"tabbas kin yi kyan da kai da ba ki bayyana wa duniya wannan sautin muryar ba, Sheikh babban mutum ne a idon jama'a kuma ko ba komai shi ɗin ubana ga ƴayansa, marayu har ma da masu uban. In sha Allah na yi miki alƙawarin shawon kan lamarin nan cikin ruwan sanyi har mu warware komai ba tare da kin shiga cikin wata matsala kamar yadda Alhassan yake tunani ba".
Ji na yi zuciyata ta yi saƙayau nauyin da ƙirjina ya yi mini na ji tamkar ana warware mini shi, ban san sa'ilin da hawaye ya zubo daga idona ba.
"Idan har hakan ya tabbata ni kuma na yi maka alƙawarin babu abin da zai hana ni aurenka, na tare a cikin gidanka a matsayin matarta". Da gaggawa ya katse ni"wannan abun da kike faɗa har cikin zuciyanki haka yake?".
Jikina a sanyaye na ce"ƙwarai kuwa".
"Alhamdulillah! Alhamdulillah Ya Allah".
Kit! Na kashe wayar ba tare da saurari ragowar zancen ba, na kwanta na yi ruf da ciki ina hawaye. Ina jin wayar tana ruri wanda ina da tabbacin Saif ne yake ƙira amma ban ɗauka ba.
[12/26, 8:27 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*
Â©ï¸ Maimuna Tijjani Iyam
____________________________________
Page 8ï¸âƒ£0ï¸âƒ£
Haka na raya tsawon daren da sallan dare sai bayan sallan asubahi na samu na kwantar da haƙarƙarina take wani bacci mai nauyin gaske ya yi awun gaba da ni, cikin baccin na ji ana ƙiran sunana cikin sanyin amo tare da bubbuga matashin da nake kwance akan sa. A hankali na soma buɗe idanuna har na buɗe su tar akan fuskar Anty Sawwama da take zaune kusa da ni. Na murtsike idanuna yayin da nake ƙoƙarin tashi na zauna ina faɗin"har gari ya waye?".
"Wani irin gari ya waye kin san yanzu ƙarfe nawa kuwa? To yanzu kusa ƙarfe sha ɗaya ake nema na rana duba fa ki ga yadda rana ta take haskenta ya mamaye ko'ina". Zumbur na yi na tashi tsaye ina leƙa taga na ga hasken rana ya dalle tar.
"Innalillahi har rana ta fito haka Anty? Da kin tashe ni na yi aikin cikin gidan ai". Taƙaitaccen murmushi ta yi kafin ta ce"kwantar da hankali ai na gama duk wasu aikace-aikacen da ya kamata, hatta girki na yi ke dai abin da nake so da ke ki tashi ki je ki wanka ki zo ki ci abincinki ga shi can a cikin kicin". Daɗin zantukanta da yadda suka faranta mini ruhina ya sanya ni sakar mata da murmushi ina zuwa na rumgume ta ina ta jeranta mata godiya wani na bin wani. Albarka ta din ga sanya mini tamkar za ta yi aron baki.
Haka na fito na yi wanka na shirya sannan na ɗauko abincin na tisa kwanon gabana kafin na saka hannuna wayata ta soma ruri, na ɗauko wayar ƙiran Saif ya shigo cikin wayar ban ɗaga ba har sai da ya katse ya ƙara ƙira a karo na biyu kafin na ɗaga, cikin sanyin murya na yi sallama ya amsa mini cike da kulawa.
"Har kin tashi ke nan?".
"E".
"To ina miki fata da addu'ar Allah ya sanya wannan ranar ta zama rana mafi daraja da alkhairi a gare ki". Cike da jin daÉ—in addu'ar tasan na amsa da faÉ—in"amin ya Allah tare da kai gabaÉ—aya".
"Jiya kin yi min wani furuci wanda nake son ki tabbatar min da shi a yanzu ido yana ganin ido, don na sai na gama sakankancewa akan hakan ashe kuma gigin bacci ne yake É—eban ki san da kika yi zancen".
"Wani zance ke nan?".
"Alƙawarin amincewa da aure na da kika yi mana". Sai da na ja dogon numfashi na fesar da shi daga bakina kafin na sama zarafin cewa"a cikin hayyacina na yi wannan zancen kuma ba a iya fatan bakina ya sanya ya ratsa har cikin zuciyata". Ina iya jiyo sautin ajiyan zuciyan da ya sauƙe kana ya ce"ni kuma in sha Allah zan yi iya ƙoƙarin ganin komai ya tafi daidai". Shuru ya biyo bayan zancensa na ƙarshe kafin can ya kuma cewa"to bari na bar ki ki huta, in sha Allah a yau ba sai gobe ba zan yi duk yadda zan yi na ga sautin muryan nan ya shiga hannun Sultan. Na san duk yadda zan yi memory card ɗin nan ya je hare sa duk da yanzu ba ma tare da shi a gari guda".
"Fatan nasara". Na furta masa a taƙaice da hakan muka yi sallama da shi na ajiye wayar tare da jingina bayana jikin bango na ɗan lumshe idanuna ina sauraron yadda zuciyata take buga wa a hankali hankali. Yayin da wasu tunani kala daban-daban suke ziyartar cikin kwanyata tabbas izuwa yanzu na ji zuciyata ta nutsu da Saif ban san ko hakan ake ƙira da soyayya ba don ban taɓa tsintar kaina cikin irin makamancin wannan yanayin ba.
Haka na gama cin abincin cikin rashin daɗin yanayi na fito na wanke kwanun, na leƙa ɗakin su Yaya Alhassan na ga ba ya nan Umar ne kawai a ciki yana karantu wani littafin turanci.