← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 72

Sashe 12

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun da ta fara maganar ya yi shuru yana kallon ƙasa bai ɗago kansa ba har ta gama maganar ta kai aya, kafin ya furzar da dogon numfashi a taƙaice ya furta"shikenan Anty amma dole zan yi bincike akan ta, idan na same ta da wani aibu tabbas dole a sauya ta a nemo wata".
"To ubana yadda ka ce haka za a yi". Sadda kai ƙasa ya yi yana ɗan sosa ƙeyarsa ya ce"Anty ni fa ba haka nake nufi ba, zan tafi wajen aiki sai na dawo don Allah a kula da yaran nan".
Murmushi kawai ta yi ba tare da ta ce da shi komai ba ya juya ya fice sai da ya fita kafin ta ce da ni"sai kin yi haƙuri da Saifullah haka yake, miskili ne na buga wa a jarida. Yana da wuyar sha'ani ga wanda bai san halinsa ba amma da zaran kun saba da shi za ki fahimci yana da daɗin zama da sauƙin kai uwa uba yana da tausayi da son taimakawa na ƙasa da shi".

Kaina kawai na iya jinjina mata don bakina ya yi mini nauyin da na kasa cewa komai, ta yi gaba ina biye da ita muka zagaya ko'ina a cikin gidan nan, kicin É—inta tsaf-tsaf da shi ga wani uban faÉ—i da girma. Girmansa ya kai a haÉ—a falo da É—akinmu da muka yi rayuwa a cikinsa kafin Abba ya rasu.

"Hajiya ban iya amfani da irin wannan abubuwan na zamani ba". Na yi zancen ina ƙara ƙare wa girman kicin ɗin kallo. Ta dafo kafaɗana tare da faɗin"a hankali zan koya miki komai idan na sama lokaci, kafin nan za ki na yi shara da mopping ɗin ko'ina a cikin gidan nan, amma ban da harabar gidan iya ɗakuna da falo ne sai wanke banɗakuna".
"Na gode sosai".

"Ki godewa Allah, ni yanzu zan fita wajen sana'ata amma ba zan daɗe ba zan dawo. Don haka za ki zauna da tare da Altine da su Aryan kafin na dawo". Kaina na jinjina mata kana na ce"a dawo lafiya Allah ya tsare ya ba da abin da aka fita nema". Cike da jin daɗin addu'ata ta amsa da faɗin"Amin ya Allah". Muka dawo falo ta shaida wa Altine za ta fita ta yi mata addu'ar a dawo lafiya, ta kwashe Aryan da Ayan suka yi mata rakiya har waje kana suka dawo. Ina zaune a cikin falon Altine ta dawo daga rakiyar da suka yi mata muka kalla juna ta banko mini harara kamar idanunta za su faɗo ƙasa, ba ta zauna a inda nake ba sai ta ja gefe ta zauna suna wasa da su Aryan, haka na ci gaba da zama shuru babu wanda zan yi magana da shi balle taɗi. Muna zaune a wajen har aka yi ƙiran sallan zuhur Altine ta tashi da yaran suka hau sama babu jimawa sosai suka sauƙa. Za ta wuce su fita na dakatar da ita ta hanyar faɗin.

"Anty ina zan sama ruwa na yi alwala na yi salla kar lokaci ya ƙure?". Ta watsa mini wani kallon uku saura kwata kan ta mayar mini da martani a zafafe"tun ɗazu da na tashi na je na yi sallan ba ki yi min magana ba sai yanzu? Ai na yi tunanin ba za ki yi sallar ba ne". Na rusunar da kaina ƙasa ina ci gaba da sauran abin da take faɗa daki-daki.
"Sai ki fita ta ƙofan can za ki ga fanfo ki yi alwalan ki dawo ki yi sallan a nan".

"Sallaya fa?".

"Ki yi akan ɗan kwalinki don ban yarda da tsarki da tsaftan jikinki ba". Tana gama faɗin haka ta ja hannun yaran suka fita, ƙofar da ta nuna mini na bi na yi alwalan na dawo na shimfiɗa ɗan kwalina na yi sallan akai. Ina raka'ar ƙarshe suka dawo suka zube akan kujera, na iddar da sallan na shafa addu'ar da na yi kana na juya ina duban ta"Anty akwai aikin za da a yi ne?".

"Ban sani ba wannan kuma sai dai ki jira matar gidan ta dawo, sai ta yi miki wannan bayanin da bakinta".

Tun da ta yaɓa mini wannan maganar ban ƙara cewa da ita komai ba, Ayan ya soma jan hannunta yana cewa"Anty ki tashi mu je ki yi mana alwala mu yi salla, Uncle Saif ya ce idan an ƙira salla mu na yi kar Allah ya ƙona mu a wuta". Hankaɗe shi ta yi ya faɗi bakinsa ya saki hannun kujera.
"Wai ku kam wasu irin jarababbun ƴaƴa ne haka? Babu dama ku ga mutum ya zauna yana huta wa sai kun addabe shi da jaraba, ku dai ku na gaba da ku ganni ina zaune ina hutawa. An gaya muku ni ɗin jakar uwarku ce ko ta ubanku ko kuma ni inji ce da ba na buƙatar hutu? Ubanku na can wata uwa duniya na kuma ta tsallake ku ta tafi neman duniya ni da ban haifa ba an bar ni da jalala".
Ta yi zancen tana miƙewa ta bar cikin falon, ganin yadda bakin Ayan yake zubar da jini ya tilasta mini tashi na je na ɗago sa, don tun da ya faɗi ya kasa tashi daga wajen. Ƙofar da na bi na je na yi alwala nan na nufo na wanke masa bakinsa sannan na cire masa rigarsa don ita ma ta ɓaci da jini muka dawo cikin falon, na zaunar da shi akan kujera kusa da ɗan uwansa na je na ɗauko mopper na gyara wajen.

Na zo na zauna a kusa da ni ina duban Ayan da yake ta sauƙe ajiyan zuciya akai akai. Na riƙo hannunsa kana na ce"a ina ake ajiye muku kayanku?".

"A É—akinmu yake".

"Ina ne ɗakin nakun?". Da hannunsa ya yi mini da wata ƙofa ya ce"wancan ne". Na tashi na shiga komai guda bibbiyu ne a cikin ɗakin kala ne kawai ya bambanta su. Na buɗe sit na ɗauko masa wata riga na juya zan fita na hango Altine tsaye a ƙofar ɗakin ta naɗe hannayenta a ƙirjinta tana yi mini wani irin kallon da na gaza cewa ma'anarsa.

"Me ye kike yi a nan?".

"Riga na zo É—aukawa Ayan".

"Saboda ke kike kula da su ko?".

Da saurina na ce"A'a Anty na jikin nasan ne ya ɓaci da jini shi ne na cire masa na zo ɗauka masa wani." Ina rufe bakina ta ƙariso cikin ɗakin ta wafce rigar daga hannuna.
"To ba zai sa wata rigar ba, haka zai wuni ba riga tun da an sa masa ya ɓata. Ai ni ba jakar gidansu ba ne da kullum ba ni da aiki sai hidimarsu".

Na yi mutuwar tsaye ina bin ta da kallo ganin yadda ta zage tana zazzago masifar babu kwama balle fulsutop. Cike da maÉ—aukakin mamaki na ce"amma na yi tunanin ai an É—auke ni saboda hidimansu. To me ye ba za ki yi aikin da ya kallafa akanki ba ko don ki ci halaliyarki?".
Ta riƙe ƙugu tana kallona"madalla tun da har kin fahimci cewa an ɗauke ni domin na yi musu hidima, to na haɗa ki da girman mai yi mana ruwa da ƙanƙara ki bar ni na yi aikina kar ki yi min shishshigi akan lamarin da bai shafe ki ba. Ki yi aikinki ni ma na yi nawa don haka ki fita daga ɗakin nan".

Ban kuma cewa da ita komai ba na fita daga É—akin cikin tsananin mamakin da ya bayyana har a kan fuskata ina fitowa na ga har sun yi bacci akan kujerar sun manne da junansu. Na bi su da kallo cike da mamakin abin da Altine ta aikata gare su.
Na koma gefe na zauna a inda na yi salla na kifa kaina akan gwiwana ban yi aune ba ni ma bacci ya kwashe ni don daren jiya ban samu na yi bacci mai kyau ba. Ƙiran sallan asr shi ya tilasta mini tashi na ina karanto sunanyen mahaliccina tsarkaka guda ɗari babu ɗaya, na fita na je na yi alwala na zo na yi zama, tun ina sallan nake jin cikina yana kukan yunwa har na iddar na shafa addu'ar da na yi.
Na kafe yaran da ido ina ta kallonsu tun ranar farko da na fara tozali da yaran na ji sun shiga raina can ƙololowa, mussamman yadda na ga suna da nutsuwa sosai kamar ba yara ba sannan ba su ƙiriniya ko kaɗan.
Ban ji sallamarsa sai gani na yi ya zauna kusa da yaran yana shafa kansu, na yi saurin gyara zamana rare da É—aukan É—an kwalina na É—aura a kaina.

Na rusuna ina faÉ—in"sannu da dawowa ranka ya daÉ—e". Bai amsa mini ba ya ci gaba da shafa kan yaran ya kai hannunsa wuyan Ayan babu shiri ya waigo yana kallona haÉ—e da faÉ—in"me ya same shi na ji jikinsa da zafi gau haka?".

Na yi ƙasa da idanuna na rasa me ye zan ce da shi sai kame-kame nake yi, kafin na kai da cewa wani abun Altine ta fito fuskarta kamar gonar auduga bakinta har kunne ta zo ta zube a gabansa"Barka da dawowa Alhaji ƙarami sannunka da shigowa".
Bai amsa ba ta ya jefa mata makamamcin tambayar da ya yi mini.

"Me ya sa Ayan na ji jikinsa da zafi haka gau, kuma jikinsa babu riga?".

Ta ɗago kai muka haɗa ido da ita ta yi hanzarin kawar da nata tana faɗin"sun yi wasa a baya ne wajen bayin shuke-shuke shi ne ya jiƙa rigar, na cire masa na shiga domin ɗauka masa wani kuma sai na fito na tarar ya yi bacci. Ni kuma ban son tashin su shi yasa ban ɗaga sa ba".

Ya cije leɓansa"sun ci abinci sun yi salla?".
Chapter 12 · 0% Book details