Sashe 21
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na tsinkayo wata baƙuwar murya ta sauƙa a kunnuwana na cira kai ina kallon matar ba tare da na ce komai ba. Zan tashi ta riƙe mini hannu"ki koma ki kwanta har yanzu jikinki babu ƙwari sosai".
"Ina ne sannan wace ce ke?".
Ta faÉ—aÉ—a annurin fuskarta kafin ta so daidai saitin kunnuna ta ce"sunana Zinariya".
"Me ya kawo ni cikin É—akin nan?".
"Faɗo wa kika yi a tsakar gida babu wanda ya kula ki balle ya kawo miki ɗauki, haka na shigo na ganki yashe a ƙasa na ja shigo da ke cikin ɗakin na kwantar da ke. Shi ne tun ɗazun kike bacci sai yanzu kika tashi".
Na buÉ—e baki zan yi magana kukan da ya kufce mini ya hana ni damar furzo da zancen da na yake kan harshena.
Ta dafa kafaɗana"ki na jin wani ciwo a jikinki ne? Na girgiza kaina alamar a'a na tashi na zauna da ƙyar har zuwa lokacin hawayen suna zuba daga idanuna.
"Don Allah zan sama ruwa na yi alwala?".
Sai da ta bi ni da kallo kafin ta furta"a cikin wannan yanayin za ki yi salla?". Na gyaÉ—a mata kaina alamar e da hakan ya ba ta lasisin ci gaba da maganan cikin mamakin da ya bayyana har a cikin furucinta.
"Ga buta ki É—auka sai ki je ki yi alwalan".
"Na gode". Na amsa da shi a taƙaice ina dirowa daga kan katifar na sauƙo ƙasa na mayar da ɗan kwalina da ya same kaina, na ɗauki butan na fita waje na je na yi alawan sanda na shigo na tarar da ita tana waya na ajiye wayar ba tare da na yi mata godiya ba.
ÆŠakina na wuce na tarar da ita har yanzu tana baccin ga sautin yana tashi sai dai amon bai kai na É—azu tashi ba.
Na ayi sallan na zauna a wajen ba tare da na tashi har sai da na yi sallan asr kana na fara yin wani irin yunwa yana ƙwalulan hancin cikina, na jawo ledar kayan nan na gama da ragowar sauran lemukan. Sai a lokacin da hankalina ya dawo jikina na tuna da cewar haka na fito daga gidan ba tare da na sanar da Hajiya Muhibbat halin da nake ciki ba.
Na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya ina jin har yanzu kunnuwana sun yi mini wani dum tamkar wacce aka ɗurawa wuta a ciki. Na tuna marin da cin mutuncin da Altine ta yi mini take na ji raina yana soyiwa tamkar yadda ake soya gyaɗa marau-marau a cikin toka. Na ja dogon gashin na fesar daga bakina ina jin wani hawaye suna ciko mini kurmin idaniyata tabbas na yarda rayuwa ba za ta yiyuwa a haka ba dole ni ma sai na tashi na soma nema wa kaina ƴanci, na fara tsaya wa kaina a cikin ko wani irin yanayi don tabbatar da zaman lafiya da jin daɗina.
Dafo kafaɗana da na ji an yi shi ya dawo sa ni cikin hayyacina daga karatun wasiƙar jakin da na faɗa, na ɗago kaina ina kallon La'aniyatu da take tsaye a kaina tana kallona.
"Ki zo Hajiya tana ƙiranki". Kaina kawai na gyaɗa mata na tashi na bi ta a baya har zuwa cikin ɗakin Hajiyar ta shige cikin uwar ɗaka yayin da ni kuma na zube a falo ina na iske Hajiya Babba da kuma Aminu zaune. Cikin girmamawa na gaishe da su sai dai cikin su babu wanda ya tanka mini illa bi na da kallo suke yi kamar yau suka fara tozali da ni.
"Amatullah".
"Na'am ranki ya daÉ—e".
"ÆŠaga idonki ki kalle ni da kyau kuma ki saurara abin da zan faÉ—a miki da kunnen basira". Na cira kaina a hankali ina kallon ta da hakan ya ba ta damar ci gaba da zancen da take yi.
"Gidan nan da kike gani ba wajen sauƙan baƙi ba ne. Gidana gidan gudanar da kasuwanci ne da za ki iya gudanar da su ko kina daga kwance akan katifarki, ba zai yiyuwa ki zauna ki miƙe ƙafa da sunan ki na fita aikin bautan da sai wata ya ƙare kafin a ba ki kuɗi ba, don waɗannan kuɗaɗen ba za su ishe ki ɗaukar ɗawainiyyar kanki ba ma balle har ki biya kuɗin hayan ɗakin da kike zaune a cikinsa har ki yi sauran buƙatunki. Ki kama sana'ar da ƴan matan gidan nan suke yi ko kuma ki shirya barin cikin gidan nan. Tun da kika zo cikin gidan nan ba ki sauya ba kullum jiya i yau ko takalmin takawa ba ki da fitacce balle kuma suturar kirki". Tun da ta fara yin maganan na ji zuffa ya jiƙa jikina sharaf ƙirjina ya soma dakan lugudan-lugudan tara-tara sau tara, daman mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin akuya ai kuwa tunin na soma sakin hawaye.
"Don Allah Hajiya ki taimake ni ki taimaki rayuwata ki yi mini rai, kar ki ce na bar cikin gidan nan. Don wallahi ban san inda zan cusa kaina ba inda na bar nan ki tausaya mini.......".Tun kafin na dire zancen ta dakatar da ni.
"Dakata ki ji ni yarinya nan gidan ba tausayi ko kuma jin ƙai nake yi ba, gidan na zo kin zo ne ki baje hajarki ki kwashe ƴan sulallanki. Ki yi hidimar kanki har ma ki yi kyauta ki yi sadaka, idan tausayi kike buƙata sai ki bari sai ranar juma'a ki tafi ƙofar babban masallaci na gidan mai martaba wataƙila ki yi dace ki sama masu taimaka miki bila adadin. Amma a cikin gidan nan dai kam jikinki ne da ƙoƙarinki zai ƙwace ki har ya yi miki riga da wando har da singileti". Ta juya tana kallon Aminu"daman ba ka sanar da ita dokoki da ƙa'idodin cikin gidan nan ba ne?".
"Aradu na sanar da ita komai in detail in ji ƴan boko. Ita ɗin ce akwai ta da daurin kai yadda kika san jinjirin haihuwar jaki, babu irin bayanin da ban yi mata ba amma kanta ya ƙi ɗauka ta dage akan ba za ta aikata zina ba. Na sanar da ita cewar akwai hanyoyi da yawa da za ta sama ƴan kuɗaɗenta ba ma tare da sun yi ido huɗu da na mijin ba amma ta ƙi amincewa".
Da alama bayyanin da Amimu ya yi mata ya taimaka wajen rura wutar takaicin halina da yake ci a cikin ranta.
"Zan ba ki zaɓi biyu wanda a ciki dole ki zaɓa ɗaya kafin nan zuwa ƙarfe goma sha biyun daren yau. Ko dai ki bi hanyar da ko wacce yarinya take bi ko kuma ki haɗa komatsanki ki setawa kanki hanya".
Gabaɗaya na ji jikina ya yi sany tamkar kazar da aka jefa da ruwan gishiri, na kasa cewa komai na tsawon wasu daƙiƙu kafin na yi ƙarfin halin faɗin"Hajiya kafin wa'adin lokacin da kika ɗauka mini in sha Allah zan zo miki da abin da na yanke cikin zaɓin da kika ba ni".
"Da kuwa kin yi wa kanki adalci yarinya. Yadda kike da suran nan ai za ki ci abinci sosai a harkan nan".
"Amatullah ki nutsu ki yanke shawarar da za ta fishshe ki kar ki yi wa kanki baƙin ciki. Ki na da sura da dirin da ko wani ɗa na miji in ya ganki sai kin tafi da hankalinsa. Ke ɗin matar manya ce kalar shiga gaban mota irin matan da suke ba za taro su tashi kan kowa".
Galla masa harara na yi sa boda haushi da takaicin da kalamansa suka cusa mini na miƙe da nufin barin cikin ɗakin na ji ya furta"tabbas Allah ya yi halitta a nan wajen. Irin wannan zubin kamar kika zama surarki".
Ban tanka masa ba na fice daga ɗakin na faɗa cikin ɗakinmu na zube akan tabarman kwanciyata, duk yadda zuciyata take suya da raɗaɗi idanuna sun daina zubar da hawaye sai sa'ilin na yarda wani tashin hankali ya fi ƙarfin a yi masa kuka sai da kukan zuciya wanda ya fi ciwo gami da raɗaɗi.
Na yi shuru ina sauraran bugawan zuciyata da yake ɓat ɓat. Na koma sauƙe numfarfashi mai ɗumi ina lumshe idanun yayin da zantukan Hajiya Babba da na Aminu suka dawowa mini cikin kaina tiryan-tiryan.
Tabbas rayuwa za ta yi mini matuƙar wahala har ma sai na gwammace wataƙila gwara mutuwa akan rayuwa, sai dai duk rintsin da na yi wa kaina alƙawarin cewar ba zan ƙara aikata wani aikin zunubi da zai sanya Ubangiji ya yi fushi da ni ina cikin sani da hankalina ba. Sai dai in ban bi hanyar da suke so ba ina zan sama kuɗin da zan nema wa kaina matsuguni?.Na cire leɓena ina ci gaba da tunanin zucin da nake yi yayin da na sama salamar zubda da hawaye a daidai lokacin.
"To fa! Ikon Allah wai na kwance ya faɗi. Ke kuma kukan me ye kike yi? Ai tun da kika sako ƙafarki kika shigo duniyar bariki duk daga lokacin za ki sabar wa zuciyarki dakiya, juriya da kuma shan duk irin yanayin da kika tsinci kanki. In ki ka ce kuka za ki dinga yi ina mai tabbatar miki da cewar sai an wayi gari watarana kin rasa hawayen da za ki tsiyayar, ni na fita sai kuma Allah ya yi dawowata zan je na kafa na tsare a bakin manyan ma'aikatu har sai na samu nawa rabon".
Na ɗaga kai ina bin ta da kallo ta shirya tsaf cikin shirgar ƙananan kayan da suka kama jikinta tamau kamar fatanta. Da wani uban gashin kantin da ta watsa wa kanta ta sha kwalliya kamar mai shirin zuwa gasar tantance sarauniyar kyau.
"Ki yi rayuwarki na tawa babu ruwan biri da gada. Zaman kanki kike yi haka ni ma shi nake yi". Na mayar mata da zancen muryata a dake.
"To Allah ya kyauta".