← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 72

Sashe 70

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Umma daman su na son junansu ne?". Amir ya yi tambayar cikin tsananin buƙatar amsar.
"Amincewar su kawai nake nema, matuƙar suka amince to komai zai zo da sauƙi. Amatullah zo nan kusa da ni". Cikin rawar jiki na ja jiki na je gabanta na gurbana ta riƙo hannayena ta riƙe tare da umartana akan na ɗaga idona na kalle ta sai dai duk yadda na so ƙarfafa kaina na cira kaina lamarin ya gagare ni.

"Ina so ba ki dama ki faɗi abin da yake cikin ranki don ki na da wannan ƴancin. Shin kin amince da auren Alhassan?". Take na ji zuciyar da take dashe a cikin farfajiyar ƙirjina ya harba sai da na ɗau sakanni kafin na furta"Anty ba na fatan zuwan ranar da za ki buƙata wani abu a wajena na kasa yi miki matuƙar ina da ikon yin sa. Ko wani mutum daban kika zaɓo mini a matsayin miji tabbas zan aure shi komai munin hali da ɗabi'unsa don na yi imanin ba za ki taɓa zaɓa mini abin da zai cutar da ni ba, balle kuma Yaya Alhassan da ni ma kai na shaida ce akan kyawawan halayensa. Na amince da aurensa har cikin raina matuƙar yin hakan zai faranta miki".

"Na gode sosai Uwata Allah ya yi miki albarka yadda kika faranta min in sha Allah ba za ki taɓa yin ƙunci a rayuwa, Allah ya ji ƙan iyayenki ya kyautata makwancinki".

"Amin". Duk muka haÉ—e baki waje amsa addu'ar da Anty Sawwama ta yi kafin ta juya ga Yaya Alhassan.
"Alhassan ka amince da wannan zaɓin?". Sai da ya furzar iska daga bakinsa kafin ya ce"Umma ba zan iya bijire wa duk wani abun da kika zaɓa min, don na ba za ki ba ni abin da zai cutar da ni ba. Na amince zan auri Amatullah na kuma riƙe ta bisa amana, adalci da kuma tausayawa. Ni daman na ri ga da na san genotype ɗinsa tun da daɗe wa AA ne don haka ba wani matsala in sha Allah".

"Alhamdulillah! Allah na gode da ka azurta ni da ƴaƴan masu ladabi da biyayya. Allah Ubangiji ya yi muku albarka ya albarkacin rayuwarku ya kare gabanku da bayanku ya ƙara haɗa kawunanku waje guda".

"Amin". Muka dinga amsa wa da shi, haka Anty Sawwama ta din ga zubo mana addu'o'i kala-kala, daga bisani ma kawai fashe wa ta yi da kuka muka din ga lallashinta tare da ba ta haƙuri. Ƙiran sallan isha'i shi ya tursasawa su Yaya Alhassan fita bayan sun tsara yadda ɗaurin auren zai kasance, Yaya Mu'azzam ne waliyina a ɓangaren Yaya Alhassan kuwa wani ƙanin mahaifinsu Anty Sawwama ta riƙa ta sanar da shi komai, ya yi farin ciki matuƙa tare da balbale mu da ruwan addu'o'i. Ya kuma taso domin yi wa Yaya Alhassan waliyanci bayan ya yi alƙawarin biyan sadaki.

Tun da na yi sallan isha'i na zauna nan kan sallayan na zabga wani uban tagumi, rurin da wayata take yi shi ya ja hankalina zuwa gare ta na ɗauko na kafe ta da idanuna sakamakon ganin lambar Saif ya fito cikin wayar, ban ɗauka ba har ƙiran ya katse ban ɗauko, don ban yi tsammanin ganin ƙiran sa a wannan lokacin ba, ya ƙara ƙira a karo na biyu kana na ɗauka cikin sanyin murya na yi sallama ya amsa kana na gaishe shi.

"Ya na ji muryannki wani irin ko dai ba ki da lafiya ne?".

"Lafiya ƙalau".

Ya ɗan yi shuru kafin ya ci gaba"na ƙira ne daman mu yi wani magana idan ba kya yin wani aikin". Sai da na kawar da hawayen da suka kwaranyo mini kafin na ce"babu abin da nake yi, yi magananka ina sauraronka".
"Ban san yadda zuciyarki za ta ɗauki maganar ba Amatullah, ba na so kuma ki yi tunanin ko ban yarda da ƙaddaran da ta tsara tsakaninmu ba ne. Ina so ki yi wa lamarin duba na tsanaki wallahi tsananin son ganin rayuwarki ta inganta kuma ta ci gaba ne ya sanya ni aikata wannan abun". Na katse shi"tafi kai tsaye ka yi magananka Yaya Saif".

"So nake yi ki ba wa Sultan dama ya nema aurenki. Tun da lamarin ya afku nake ta tunani da zulumi ina tsoron ki faɗa hannun wanda bai dace ba, ina tsoron ki je inda za a yi miki gori akan rayuwarki ta baya, ina tsoron ki je inda ba a san mutuncinki ba balle a mutunta ki, ina tsoron ki je inda za a wulaƙanta ki ko a tozarta ki shi yasa nake ganin kamar Sultan shi ya dace da ya aure ki idan har kin amince. Sa boda shi na san dukkan halayensa na san shi ɗin mutumin kirki kuma duk wasu kyawun hali ya fi ni".

Na buɗe bakina zan yi masa bayani kawai wani kuka ya kwace mini don yadda na so na hana sautinsa bayyana, sai da lamarin ya gagare ni wai ƙoƙarin cire wando ta kai.
"Subhanallahi! Kuka kuma Amatullah? Me ya faru?". Ya watsa mini tambayar cikin kiɗima sai da na yi da gaske wajen daidaita fitar numfashina da yake maƙale mini a ƙirji kafin ina yi furzo da zancen wajen"Saif yanzu haka taron ɗauri aurena ake yi a masallacin ƙofan gidanmu".

"Aurenki kuma? To auren ki da waye?".

"Aure na da Yaya Alhassan wataƙila ma yanzu haka har aikin gama ya gama an ɗaura". Na yi zancen wasu hawayen suna gudun famfalaƙi a bisa kuncina.
Ya ɗauki tsawon wasu mintuna kafin ya yi magana"alhamdulillah! Na ji daɗi da ya kasace cewar Alhassan ne ya aure ki ba wani ba, don ina da yaƙinin ba za ki tozarta ba a hannunsa. Duk inda ake neman mutumin kirki mai ƙoƙarin sauƙe haƙƙin ƴan uwantaka tabbas Alhassan ya kai, ina yi muku fatan dawwamanmen zaman lafiya da kuma samun zuri'a ɗayyaba".
Ban iya amsa addu'ar ba illa furta sunansa da na yi cikin wani irin sanyin murya.

"Saif".

"Na'am Amatullah".

"Ban san ina sonka ba sai da wannan lamarin ya faru, kai ne mutum na farko da ya taɓa nuna mini soyayya babu dangin uwa balle na uba, tabbas littafin tarihin rayuwata ba zai taɓa cika ba ba tare da an rubuta sunanka a cikin shafin farko ba. Na gode da dukkanin abubuwan da ka yi mini a cikin rayuwa, Allah ya saka maka kuma ya yi maka tagomashi da samun mace ta gari wacce za ta ƙaunace ka domin Allah".

"Amin ya Allah, wannan shi ne ƙirana na ƙarshe da za ki gani ya shigo cikin wayanki. Don daga yanzu shari'a ta ja layi tsakanina da ke, in sha Allah zan zo na taya Alhassan murnar samun mace ta gari, ina yi muku fatan samu zaman lafiya. Allah ya haɗa fuskokinm da alkhairi".

Ya na gama maganar kit! Ya datse ƙiran ya bar ni da ɓarin hawaye ji da na yi an dafa kafaɗana shi ya sanya ji waiga cikin sauri, idanuna suka sauƙa akan fuskan Anty Zulaihatu wanda da dukkan alamu ta daɗe a cikin ɗakin kuma ta saurari duk maganganun da ta yi. Da kallo na bi ta har ta iso gabana ta zauna tana fuskantana.

"Amatullah".

"Na'am". Na amsa ina sadda kaina ƙasa.
"Ko dai zan yi wa Umma magana ne a dakata da yin wannan auren nan? Don na ga kamar duk kin shiga damuwa, na lura kuma kaman kawai kara da alkunya kika yi ki ka amsa ba wai don ki na son Yaya Alhassan ba".
"Ba buƙatan hakan Anty ki sanar da ita komai. Ai shi zaman aure ba a yi masa kara, kawaici ko kuma alkunya da ba na son sa ko kuma ban yarda da jagorancin da zai yi mini a cikin gidan aure ba, tabbas da zan san hanyar da zan bi wajen na fahimtar da Umma hakan. Sai dai ina ji har cikin zuciyata cewa zan sama dukkanin gata da kulawan da ya dace a cikin gidan Yaya Alhassan, roƙona ɗaya a gare ki shi ne ki bi mu da addu'a kawai".

"Haƙiƙa Amatullah kin cika ƴar halak, in sha Allah wannan auren zai zamu silar wanzuwar farin ciki a cikin rayuwarki". Ban iya amsa mata ba illa kwantar da kaina da na ji akan cinyarta tare da lumshe idanuna daidai lokacin da wayarta ta yi ƙara ta ɗaga ƙira, a amsa-kuwwa take don ina jin sa'ilin da Yaya Mu'azzam yake shaida mata aure ya ɗauru nan ta din ha hamdala tana gode wa Ubangiji.
Washe gari da safe tun kafin gari ya yi haske Anty Sawwama ta ƙira ɗakinta sadakina Naira dubu ɗari da hamsin ta damƙa mini, na nuna mata cewar babu abin da zan yi da shi ita ya kamata ta riƙe a yi wasu buƙatun da shi, amma ta nuna mini rashin yiyuwan hakan ta ce da ni a addinance ma ni nake da iko da sadakina, don haka na riƙe na je na yi tunanin abin da zan yi da shi.
Tun ranar nake wasan ɓoya tsakanina da Yaya Alhassan duk abin da yake yi inna shi shigowarsa bari nake yi na shige cikin ɗakin ba na fito wa har sai ya tafi, cikin sati ɗayan da ya rage Yaya Alhassan ya ƙarisa aikin gidan da yake ginawa da yake can gangare daman fenti ne kawai ya rage sai ruwa da za a ja, kiwonta da yake ƙauye Anty Sawwama ta ɗaga ta sayar aka yi mini kayan ɗakin da na kitchen yayin da Yaya Mu'azzam ma ya raka rawar gani matuƙa. Duk halin matsin rayuwar da Amira suke ciki hakan bai hana Mansur dunƙulo Naira dubu hamsin ya ba ni ba a matsayin gudumawansa da farko na ƙi karɓa har sai da Amira ta nuna mini ɓacin ranta kafin na amsa.
Chapter 70 · 0% Book details