← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 72

Sashe 5

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ga mutane maza da mata tsaye cirko-cirko a ƙofar gidan, maza kama daga kan samari, tsaka tsakiya da kuma dattawa babban wani abin takaici har wa manyan mutane da aƙalla za su kai sa'an Abbana a shekaru. Sai da muka rarraɓe kafin muka sama hanyar shiga cikin gidan kowacce budurwa ta ci wanka ta caɓa ado kamar za su tafi gasar kyau na duniya. Kowacce ta tsuke cikin ɗamammun kayan da ba su tamaika da komai wacce rufe tsiraicinsu ba, ga ƙarin gashi da farata rututu a hannayensu kamar masu cin moshe.
Na buɗe ƙofar ɗakina na shiga na hango wasu baƙaƙen ledodi guda biyu na saki hamdala don na kwaso yunwa kamar zan ci babu, na zauna na jawo ledar ina buɗe wa biredi ne da wainar fulawa guda biyar a leda sai kuma ruwan shayi ƙulle a leda, gefe guda kuma ga can ledar pure water an jingine a gefe. Na san babu wanda zai kawo mini wannan abun face Aminu don haka ban yi wata-wata na ɓula ruwan shayin na tsoma zuƙa ina haɗawa da buredi ina danne wa da wainar fulawan sai da na ci wainar guda uku na zuƙe ruwan shayin na ɗaura da ruwan pure water ɗaya na yi hamdala na tashi na ɗauri pure water ɗaya na zuba a buta na fito na yi alwala na koma ciki.

Sallan magrib na yi ban tashi daga wajen ba har sai da na yi sallan isha'i, na zauna na zabga tagumi tamkar wacce aka aikowa da saƙon mutuwar uwa da ubanta. Tunani barkatai suka dinga yi mini yawa a cikin kaina suna kai kawo a cikin kwanyata.
Tunanin gida da ƴan uwana suka faɗo mini a raina tamkar faɗuwar aradu, ban san sa'ilin da hawaye suka fara kwaranyo mini daga idanuna ba kamar da bakin ƙwarya.
"Anty Sawwama ki gafarce ni babu yadda zan yi ne ba ni da wani mafita saman da wannan. Ya zama dole ne na yi nisa da ku ko don kwanciyar hankalinku da nawa rayuwata ta gama tarwatsewa don haka ba zan zama matsala a cikin taku rayuwar ba".

A bayyane na yi maganar wasu hawayen suna rige-rigen fitowa daga idanuna suna wanke mini fuska yayin da suke sauƙa har izuwa tudun wuyana, na daɗe ina kukan da dukkan ƙarfina har sai da numfashina ya soma sarkafewa kafin na zame na kwanta akan bayana ina kallon rufin ɗakin da ya zama shamaki tsakanina da sararin samaniya.
Kamar daga sama na ji sauƙar muryan La'aniyatu a na'urar naɗan sautina.

"Har kin kwanta ne?".

Na tashi na zauna"a'a yaushe kika shigo ban ji ko sallamarki ba?". Ba ta amsa mini ba har sai da ta nema waje ta zauna kana ta ce"ban yi sallamar ba ne, daman na zo ne mu yi hira don Ummata ta yi baƙi daga wata ƙasa daban sun tafi otel za su gana". Na waro idanuna waje cike da mamaki"a cikin daren nan?".
Ta riƙe haɓa"yo mai ma aka yi da maza? Ai duk wani taron da za a yi wanda manyan mutane za su halarce shi to cikin duhun daren yin sa tare da taƙaitattun mutane".
Na jinjina kai tare da kawar da zancen ta hanyar faÉ—in"ina so na nema aikin da zan yi na dinga rufawa kaina asiri, ni wallahi ko wankau ne ma ko surfe zan yi". Ta bi ni da wani irin kallo kwatankwacin irin kallon da mai hankali yake yi wa zautacce.

"Yanzu ke a layin nan kin ga alamar wanda gidan da za su kawo surfe? Ai tuni bature ya kawo sauƙi ban ƙi ba dai wankau ɗin". Na yi saurin faɗin"don Allah ina san samu wankau ɗin?". Ta ɗan yi shuru kafin ta ce"gaskiya ba na ce ba don gidajen layin nan ma ba su cika zama ba amma dai ba za a rasa ba, wataƙila sai dai ki dinga bin gida-gida ki za a dace".
Jikina gabaɗaya ya yi sanyi ƙalau kamar kazar da aka watsawa ruwan gishiri na tuna rayuwata ta baya lokacin da Abba yake raye a cikin duniya, rayuwa kenan wai yau a ce nake neman aikin wankau don na ciyar da kaina, hasali a lokacin baya ba a taɓa sauƙe tukunya a cikin gidanmu sai dai ba daɗi amma tabbas za mu ci mu ƙoshi. Ko ruwan da za mu jiƙa maƙoshinmu bai taɓa yanke mana ba. Na ja dogon numfashi na fesar ina zabga tagumi.

"Lafiya kuwa na ga duk yanayinki ya sauya?". Kalaman La'aniyatu ya dawo da ni cikin hayyacina.
"Babu komai kawai wani abun na tuna. Na gode da kulawarki a gare ni, mu tashi lafiya". Murmushi kawai ta sakar mini ba tare da ta ce da ni komai ta tashi ta fice.
Na zauna na yi jigum ina ta tunanin abin duniya, wasu hawayen masu zafi suka ciko mini kurmin idaniyata, na tuna Umma lokacin da ta yi watsi da ni ta ƙi ba ni ko wani irin ƙofar da zan yi mata bayyana balle har ta fahimce ni. Na daɗe zaune ina tunanin na ji an bankaɗo labulen ɗakin an shigo na cira kai ina kallon Aminu har ya shigo ya zauna.

"Na ga saƙo na gode sosai Allah ya saka da alkhairi".
Ya ɗago ya kalle ni"in ce dai ki na lissa adadin kwanakin da kika yi a cikin gidan nan yanzu ko?". Na bi shi da kallon mamaki sai dai na danne mamakin da kalamansa suka shayar da ni na ce"ina sake da yawan kwanakin. Kuma in sha Allah kwanan nan zan nema aikin da zan dinga ɗaukan ɗawainiyya kaina da shi". Ya yi ƙuri yana kallona"wani irin aiki ke nan?".

"Wankau ko kuma aikatau".

Cikin maÉ—aukakin mamaki ya ce"da kuÉ—in wankau da aikatau É—in za ki É—auki nauyin kanki?".
"In sha Allah". Na amsa da shi cike da dukkanin ƙwarin gwiwa.
"Kar ki yaudari kanki Amatullah babu ta inda sana'ar wankau zai riƙe. Yadda kiken nan mace iya mace sura iya sura diri iya diri, ki na da kyawun sura ta yadda duk wani lafiyayyen namijin da ya yi ido huɗu da ke dole sha'awarsa ta motsa. Idan kin iya allonki to tabbas za ki yi moriyar bariki za ki ja zarenki shekaru aru-aru, don yanzu haka ma akwai hamshaƙan mazan da suke ganin gilmawarki a cikin gidan nan kuma sun yaba za su saki baki aljihu matuƙar kika ba su dama".
Na runtse idanuna"ba zan taɓa aikata zina ba a cikin rayuwata". Ya yi saurin taran numfashina"ba ki shirya aikata zina ba kika shigo bariki". Ya miƙe tsaye ya tsaya"ki yi wa kanki karatun ta nutsu. Don tallafina gare ki na sati guda ne kuma yau an ci kwana biyu saura kwanaki biyar". Yana dasa aya a nan ya cika bujensa da iska ya fice ya bar ni zaune na kasa ƙwaƙwƙwaran motsi.

Na ja dogon numfashi na fesar ina yi wa zantukansa tankaɗe da rairaya. Na cije leɓansa saboda bugawan da ƙirjina yake yi. Dole ne zai na yi zina kafin na sama abin da zan ɗauki nauyin kaina da shi? Tambayar da na jefawa kaina ke nan da tsawon daren na gaza samun amsarsa.
[12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

__________________________________

Page 4️⃣4️⃣

Haka na ƙarar da dukkan tsawon daren ina tunanin ina saƙa da warwara a cikin raina. Tabbas dole na tashi na nema na kaina in bay haka kuma na ji ana yi, sai dai ta ina zan fara wai ƙoƙarin cire wando ta kai. Ina zaune a inda na iddar da sallan asubahi ina ƙarewa ɗakin kallo cikin dubu, haƙiƙa ina buƙatar wasu abubuwan buƙatan rayuwa kamar kayan sawa, abinci da wasu ƙananun abubuwan. ban yi aune ba na ji wasu hawaye suna zubo miji daga idanuna wanda ban san dalilin zubar su ba, ban goge su ba kamar yadda ban yi wani yuƙurin haka su zuba ba.
"Anty Sawwama ku yafe ni na san ba jefa ku cikin tashin hankali na rashina. Na san na shayar da ruhinku ɗacin baƙin ciki, sai dai na yi muku alƙawarin ba zan taɓa sauƙa daga turban da kuka ɗaura ni a kai ba zan ci gaba da kare mutumcina da tsayawa akan gwadaben da na taso a kai". Ina rufe bakina na kai hannu ina goge fuskana tare da miƙe wa tsaye na ci ragowar abin da na bari jiya. Sai da gari ya yi haske na fito waje so nake yi na yi wanka amma ba ni da abubuwa da yawa da za su taimaka mini wajen gudanar da hakan, sai na tsaya ruwa, na nema bokiti, soso da kuma sabulu uwa uba kayan da zan sauya idan na yi wankan.

Ina dab da fitowa daga cikin ɗakin muka yi kiciɓus da La'aniyatu tana shigo wa na matsa mata ta shigo, muka tsaya muna kallon juna ina da ita kafin ta ce"ina za ki je kuma da safiyar nan? Na yi tunanin ma zan zo na samu ba ki tashi daga bacci ba".

"Ina so na fita ne na je neman aiki don na ga rayuwar ba za ta yiyu a haka ba".
Ta yi ƙuri tana kallona"kin dade dai sai kin nema aikin nan?".

"To ya ya kike so na yi, Aminu ya shaida mini cewar ɗawainiyyar ciyar da ni na tsawon sati guda kawai zai yi wanda yanzu haka ya rage kwanaki huɗu rak, idan ban fita na nema ba ya ya kike so na yi da raina a lokacin da ya janye tallafinsa a gare ni". Na yi maganar ina ƙoƙarin ficewa ta riƙo hannuna"ki bi a hankali dai mutanen unguwan nan ba ababen yarda ba ne". Kaina kawai na jinjina mata na yi ficewa ta na bar ta a cikin ɗakin, sai da na fito ƙofar gidan na sauƙe numfashi mai zafi ina ƙarewa gabar da yamma kudu da arewa kallo.
Chapter 5 · 0% Book details