Sashe 10
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Na gode sosai Allah ya saka da alkhairi". Ba ta amsa ba illa murmushin da ta sakar mini na ɗauki ledodin na fita, duk nisan tafiyan da zafin da ƙafafuwa suke yi mini ban ji su dame ni ba saboda farin cikin samun aikin da na yi ta hanyar da ban taɓa tsammani ba balle zato. Na tarar da La'aniyatu ba ta nan amma ta ajiye mini makulli a kan taga na ɗauka na buɗe ɗakin na shiga na fito na yi alwala na shiga na yi sallan zuhur a nan inda na yi sallan na kwanta wani bacci mai nauyi ya ɗauke ni ban tashi ba sai can yamma na yi sallan asr kana na jawo ledodin da ta ce ni na buɗe su, kayan ƙwalam da maƙulashe ne burji a cikin ledan, ɗayan ledan kuma lemukan gora ne kala daban-daban.
Na ɗeba wasu na soma ci sai da na gama na tashi na ajiye sauran na tashi zan fita kenan La'aniyatu ta shigo. Muka sakar wa juna murmushi yayin da take ƙariso wa cikin ɗakin.
"Ina kika je ne na dawo ban same ki ba?".
"Umma ce ta aike ni. Na ga kin tashi kamar ƙara fita za ki yi?".
Na matso dab da ita"albishirinki".
"Goro fari ƙal".
"Na sama aiki yanzu ma can zan je na ji matsayina".
Cike da farin ciki ta ce"a ina? Zauna mana ki ba da labari kafin ki tafi".
Na jijjiga kaina"a'a ki bari sai na dawo sai ki ji komai, ga makullina nan idan kin fita ki rufe mini ƙofan". Ban tsaya jin abin da ta ci gaba da faɗi ba na fice da sauri. Sai da na iso ƙofar gidan na goge gumin da na haɗa kana na ƙwanƙwasa mai gadi ya fito ya buɗe mini na shiga ciki, na yi sallama aka amsa mini kana na shiga na iske wata mace zaune tare da wasu yara biyu masu tsananin kama da juna dukkan su maza sun yi shiga iri guda. Na tsuguna na gaishe ta ta amsa mini a taƙaice ta na bi na da kallo.
"Hajiyar ta nan kuwa?".
"Lafiya kike neman ta?".
"Ita ta ce na zo".
A wulaƙance ta ce"to sai ki jira ta ta fito".
"To". Na amsa da shi a taƙaice zan zauna akan capet ta ce na sauƙa ƙasa, ban yi mata musu ba na yi kamar yadda ta ce. A ƙalla mun yi fiye da awa ɗaya zaune a wajen muna jira kafin ta fito tana fitowa yaran suka yi wajen ta da gudu suka rumgume ta. Ta riƙo hannunsu suka ƙariso suka zauna kafin ta ce"Altine ku da muka yi da ke za ku yi kwana biyu a can, ya ya kuma na gan ku yau?".
Matar da ta ƙira da altine ta kaɗa baki ta ce"wohoho Hajiya ai Alhaji ƙarami ne ya je gidan gaida Hajiyarki dagan kuma ya ce a dawo da su, ko kuma shi ma ya haɗa kayansa ya koma can ayi hutun ƙarshen makon a shi".
"Saifullah ke nan shi dai ba ƙaunar yaran nan su yi nisa da shi".
"Ƙwarai kuwa Hajiya, ai ni tun da nake ban taɓa ganin ƙauna irin wannan ba. Hajiya ga baƙuwa nan kin yi. Sai a lokacin ta lura da kasantuwana a cikin falon ta kai idon ta kaina"ki ƙariso ki zauna mai kyau mana". Ban ce komai ba na tashi na iso gaban ta na zauna tare da gaishe ta ta amsa tare da zarce wa da faɗin"mun yi magana da shi ya kuma amince don haka za ki iya fara zuwa daga gobe, albashinki naira dubu ashirin ne duk wata sannan aikin da za ki na yi shi ne sharan cikin gida, mopping da kuma girki. Idan na yaba da tsaftan da kuma ƙarewarki akwai yiyuwar na ƙara miki albashi".
Take na durƙusa ina ta jeranta mata godiya kamar zan yi aron baki ta nuna mini cewar babu komai. Ta ba ni naira ɗari biyar ta ce na yi kuɗi mota sai gobe na fara fitowa aiki lokacin har an fara ƙiraye-ƙirayen sallan magriba. Haka muka yi sallama raina fari ƙal kamar nono kindirmo ina ƙoƙarin fitowa daga falon na yi karo da mutum har sai da abin da yake hannunsa ya faɗi ƙasa.
Waya ne da ya faɗi na tsuguna da sauri na ɗago na miƙa masa ina faɗin"ka yi haƙuri wallahi ban lura da kai ba ne.......".
Miɗik na haɗiye ragowar zancen saboda firgitan da na yi. Na tsaya cak ina kallonsa tare da wassafo inda na taɓa ganin fuskarsa. Take na nufa inda na taɓa ganin sa shi ne wanda muka haɗu da shi yau da asuba har ya ba ni sallaya na yi salla a kai.
[12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE*
Â©ï¸ Maimuna Tijjani Iyam
__________________________________
Page 4ï¸âƒ£7ï¸âƒ£
"Ke ce? Me ya kawo ki nan?". Na rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa saboda ba zan iya juran irin kallon da ya katse ni da shi da ya fi kama da na tuhuma ba. Kafin na kai ga ba shi amsa tagwayen yaran suka fito a guje har suna rige-rigen rumgumansa ya tsuguna akan gwiwansa tare da ware hannayensa suka faɗo kan ƙirjinsa.
"Uncle Saif tun ɗazu Inna Altine ta dawo da mu, ba mu gan ka ba". Ya shafa kan yaron da ya yi magana tare da cewa"Aryan na tafi wajen aiki shi yasa, amma ai na je can gidan Hajiya Maman ai na gan ku kafin na tafi". Ɗayan yaron ya yi caraf ya amshe zancen"ai Hajiya Mama ma ta yi ta masifa bayan tafiyanka, Anty Talatu ma cewa ta yi wai....". Kafin ya dirar zancen ya rufe masa bakinsa"Ayan ba na hana ka yawan sutura ba? Kai duk abin da ya faru zai ka kaso ka faɗa. Shi yasa Aryan ya fi ka hankali". Take Ayan ɗin ya cuno baki gaba gami da buga ƙafa yana kai wa Aryan ɗin da yake yi masa gwalo duka ya zame.
"Wallahi bai fi ni hankali ba, ai Mummy ma ta ce ni ne babanta Aryan kuma ba babanta ba ne tun da shi sai kukan banza". Tana ƙare zancen ya bi Aryan ɗin da gudu suka shige cikin gidan, na bi su da kallo don ba ƙaramin burge ni yaran suka yi ba, kamansu guda, yanayinsu, girman jikinsu hatta muryar su kala ɗaya ne. Sai dai abin da na lura da shi ɗaya ya fi ɗaya suturu.
Figigi na dawo cikin hankalina saboda fizge wayarsa da ya yi daga hannuna bai ce da ni komai ba, ya bi bayan yaran yana ƙira sunan Ayan, na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya kafin na ja ƙafafuna da suka sanƙare na bar wajen, kafin na isa gida har an fito daga masallacin sallan magrib ina zuwa na karɓa makuli na buɗe ƙofan ɗakin na shiga na ɗauko buta na zo na yi alwala na koma ciki.
Sallan magrib na yi na haɗa har da na isha'i na zauna a wajen ban motsa ba na zuba uban tagumi, so nake yi na yi karatun alƙur'ani amma na waigo ko ina ban ga alamar alƙur'ani ba.
Na runtse idanuna wasu siraran hawaye suna gangarowa daga gefe da gefen idona, a bayyane na furta"Allah ya jiƙan ka Abba, Allah ya yi maka rahama ya kai haske cikin kabarinka".
"Amin".
Na ji an amsa da shi da hakan ya tursasa mini buÉ—e lumshashshun idanuna, na kafe La'aniyatu da su har ta iso inda nake ta zauna a gaba na.
"Kin dawo kenan?". Na gyaÉ—a mata kaina da hakan ya ba ta lasisin ci gaba da maganan"kin ce za ki ba ni labarin aikin da kika samu idan kika dawo".
Na ja dogon numfashi na fesar kafin na kwashe komai na juye mata tas, sai da na dire zancen ta ce"Allah ya saka mata da alkhairi, amma gaskiya ta kyauta kuma ta na da kirki. Amma har dubu ashirin kuÉ—in da yawa gaskiya".
Na jinjina kaina"ni ma haka na gani, kuma a hakan ma ta ce za ta ƙara mini wani abu idan ta ga yanayin kamun ludayina".
Ta riƙo dukkan hannayena"Allah ya sa a fara a sa'a".
"Amin na gode sosai". Na furta ina ƙoƙarin samar da annuri a bisa fuskana, haka muka ɗan taɓa hira da ita kafin muka yi sallama tare da yi wa juna sai da safe.
Tsabar farin ciki kasa bacci na yi na kwanta kawai ina ta juye-juyen ji nake yi kamar gari ba za ta waye ba balle har na fara fita wajen aikin.
Ina daga kwance na ji an bankaɗo labulen ƙofar ɗakin an faɗo cikin ɗakin, duk da a cikin dubu ne amma ina gani gizon mutum yana nufo inda nake. A kiɗime na rarumo ɗan kwalina da ya zame daga kaina na mayar kaina.
"Waye ne wannan? Waye ne?". Na yi maganar harshena har yana harɗewa, ba a amsa mini ba aka ci gaba da nufo inda nake zaune, babu shiri na tashi na miƙe tsam akan ƙafafuwana da suke rawa, babu wadataccen hasken da zai ba ni kallon fuskarsa balle na iya bambamce wane ne, har lokacin ba a amsa mini ba haka nan ba daina nufo inda nake ba, ya kawo hannu da niyyar kawo mini cakfa na yi hanzarin zamewa ya faɗi akan tabarman ruf da ciki. Yana wani irin numfarfashi kamar ragon layan da aka zarcewa wuya za a yanka shi.
A guje na bazamo waje ina kurma ihu, take waÉ—anda suka rage a cikin gidan ba su fita ba duk suka fiffito suka dallo ni da tocila.
"Ke dalla banza mene ne kika fito ki ma hurmawa mutane ihu?".
Ɗaya daga cikin ƴan matan da suke tsaye a wajen ta furta a zafafe kamar za ta kai mini duka. Hajiya Babba ta fito tana gyara ɗaurin zanin jikinta da yake ƙoƙarin zame wa.
"Wa ye yake son ya tada min da hankali da daren nan?".
"Hajiya wa ye kuwa ban da wannan kucakar yarinyar mai zubin Æ´aÆ´an aljanu, duk ta fi ta fitsine mutane a cikin gidan nan". Hajiya Babba ta nuna wacce ta yi zancen da Æ´atsarta"ke Zuby ba na son É—iban albarka, daman har masu zubin Æ´aÆ´an aljanu ne a cikin gidan nawan ban sa ni ba?".