Sashe 15
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A taƙaice na ce"wajen aiki".
"Aiki?". Ya maimaita cikin sigar tambaya na gyaÉ—a masa kaina cike da tabbatarwa.
"Ina mai tabbatar miki da cewan babu wani aikin da zai riƙe ki balle har ki ɗauki ɗauwaniyyan kanki da shi. Amatullah ki buɗe idanunki ki farka daga baccin da kike yi da yake haddasa miki yin wannan mafarkin mara gindi balle tushe, kin san me ye bariki kuwa balle yadda ake gudanar da rayuwa a cikinta? Kin san yadda zaman bariki yake kuwa? To billahillazi duk wanda kike ga yana zaman kansa ko zaman kanka a cikin duniyar bariki sai ya yi da gaske kafin yake ɗaukan dukkan ɗawainiyyansa, a namiji ma ke nan balle kuma ɗiya mace da take rauni a bayyane. Kin ga duniyar bariki ya wuce duk yadda kike tunani kallon kitse kike yi wa goro, tun wuri idan za ki zubar da makamanki ki kama gaskiya da hanyar da za ta miƙar da ke ɗoɗar ki yi kafin lokaci ya ƙure miki. Ban da toshewar basira ina ke ina wani zuwa aikatau aikin da sai kin saka ƙarfi kin sadaukar da lokacinki wajen yin sa, yadda kike da kyakykyawan suran nan da diri mai kyau da ɗaukar hankali aikin wahala bai kamace ki ba, kamata ya yi a ɗauke miki komai sai dai kawai a kama miki ɗaki a ciyar da ke a shayar da ke duk abin da kike so. Ki ci mai kyau ki sa mai kyau. Ki sha iskan AC ki kwanta ki bi lafiyar gado".
"Na gwammace na yi ko wani irin aiki da na bi hanyar da kake so ka É—aura ni a kai".
Ya yi wata dariyar da na kasa gano manufar da yake ɓoye a tattare da shi kafin ya furta"ina nufin ki ba da kai kawai bori ya hau. Kawai manyan masu kuɗi hamshaƙai da suka ci suka ta da kai, akwai ƴan kasuwanni, akwai ma'aikatan gwamnati, akwai masu aikin ɗamara, akwai ƴan siyasa, akwai manyan malamai da suka yi shura da suna a duniya, akwai waɗanda su ba ma a cikin ƙasar nan suke ba. Waɗannan su ne waɗannan ba su da matsala su hotunan wasu sassan jikinki kawai za ki ɗauka a hoto ki ki dinga tura musu yayin da su kuma za su dinga jiƙa miki account ɗinki da wasu mahaukatan kuɗaɗe masu nauyin gaske. Akwai hanyoyi da yawa da za ki bi don rufa wa kanki asiri ba tare da kin yi aikin wahala ba".
Na kai hannuwana na toshe kunnuwana saboda yadda kalamansa suka jirkita mini tunanina har sun barazanar juyar mini da kaina.
"Ba zan duk abubuwan da ka lissafa ba. Don na yi wa kaina alƙawarin ba zan ƙara aikata wani saɓon Allah a ciki sanina ba, sai dai wataƙila ba na cikin hayyacina amma da hankalina dai kam ba zan iya wannan abun ba".
Ya sake baki da hanci yana kallona"hoton jikinki ne fa kawai za ki É—auka ki na zauna daga cikin É—akinki akan wannan tabarman ki turo, babu wanda ya san kin yi wani abu. Wannan ake yi wa kirari da cewar ka yi kyauta da damanka ba tare da hagunka ya sani ko ya ji labari ba".
"Kar ka canza ma'anar maganar nan domin sam ba haka yake ba. Kuma ina so ka sani ba ka da wasu kalaman da za ka yi mini zai sa na karya alƙawarin da na yi wa kaina". A fusace ya miƙe yana jefa da guntun sigarin da ya gama zuƙa ya take ta kafin ya furta"shikenan ki yi yadda kike so. Daman Hausawa sun ce mai rabon shan duka ai ba ya jin bari, don haka ga fili ga mai doki sai ki yi sukuwarki yadda kike so".
Tana dasa aya a nan ya fice daga cikin ɗakin na bi shi da kallo kamar idanuna za su faɗo a ƙasa, yana fita La'aniyatu tana shigo wa cikin ɗakin kamar zai bangaje ta ya ƙarisa ficewa cikin ɓacin rai.
"Lafiya na ga wannan ya fita cikin ɓakin rai kamar zai duki bango?". Ta jefa mini tambayar yayin da take zauna kusa da ni. Sai da na furzar da zazzafan iska mai ɗumi daga bakina kana na furta"ba komai kawai dai abin da aka saba ne wanda kin riga da kin san shi". Ta jinjina kanta"Allah ya kyauta".
"Amin, na ga ɗazu kaman ranki a ɓace me yake faruwa ne?".
Ta ɗan yi jim kafin ta ce"wallahi Ummata ce ta yi mungun ɓata min rai, sai da na ji kamar na ɗaura hannu akaina na yi rafza kuka tsabar tsagwaron baƙin cikin da ta ƙunsa min". Cike da mamaki game da buƙatan ƙarin bayanin da ta yi mini a dunƙule na ce"me ye ta yi miki haka?".
"Wai fa baƙi ta yi ta san da cewa ina cikin ɗaki ina saka kayana ta shigo da su. Wallahi na ji haushi sosai ta yadda ban ma san lokacin da na rufe ta da masifa ba". Cike da maɗaukakiyar mamaki na waro idanuna waje"Umman nakin kika rufe da masifa?".
"To mene ne?".
"Ai ita ɗin mahaifiya ce ko me ye ta yi miki bai dace ki rufe ɗaga mata murya ba balle har ki rufe ta da faɗa. Iyaye fa suna fa su na da wani irin daraja da kima wanda ba kowa yake da makamancinsa ba, mussamman uwa wanda sai Annabi ya ambace ta sau uku kafin ya ƙira uba sau ɗaya saboda girman haƙƙin da take da shi akan ɗa".
Ta É—an yi shuru kamar abin da na faÉ—a ya ratsa ta sai dai kuma kalamanta suka sani tabbatar da cewa duk abin da na faÉ—a ya shiga ta kunnenta na gefen dama ne ya fita ta gefen hagu.
"Ummanta dole sai ana yi mata haka, dole sai mutum ya zama jan wuya mai iya ƙwacen haƙƙinta kafin ya iya zama da ita. Akwai wani lokaci da ta tsiri kawo maza cikin ɗakinmu su hana n sakat na yi faɗan na yi faɗan ba ta daina ba, har sai da na daina kula ta na daina yi magana na kusa a ƙalla wata guda kafin ta dawo cikin taitayinta, tun daga lokacin na fahimci Umma zuma ce dole a da wuta za a mu'amalance ta".
Zan yi magana ta É—aga mini hannu"mu bar wannan maganan, yanzu dai ba ni labarin ranar ki ta farko a wajen aiki, ya abin ya kasance?".
Na ja numfashi mai nisan zango kana na fesar kafin na sama damar kwashe komai da ya faru na faÉ—a ba. Ta yi É—an jim kafin can ta ce"ke kuma bayan faruwan hakan wani hukunci kika yanke?".
"Wallahi na ji gabaɗaya aikin ya fita daga raina. Duk da ina son aikin amma ba na jin zan iya jure cin zarafi da wulaƙanci". Ta riƙo hannuna ta sanya cikin nata kafin ta soma magana cikin sigar ƙarfafa gwiwa.
"Amatullah ki riƙe aikin nan ƙam. Kar ki bar damuwar wasu a cikin ranki. Ita ma wacce kike ba ni labarin ai ƴar aiki ce matsayinku ɗaya da ita don haka shafawa idanunki toka za ki yi ki karta mata rashin mutunci na rai da motsi, tun da daman an ce idan babba bai ji kunyar hawa jaki ba to jaki ba zai ji kunyar jefar da shi ba. Zake wa za ki yi ki ƙwaci ƴancin kanki da kanki kar ki yarda wata ƴar aiki da kuke matsayi ɗaya da ita ta taka ki". Na furzar da zazzafan iska daga bakina kafin na sama zarafin cewa"to ya ya kike so na yi? Shin kin san adadin shekarun da suka yi tare da ita da kike yin wannan maganar? Kuma daga dukkan alamo na yadda take cin karenta babu babbaka a cikin gidan akwai wani alaƙa a tsakaninsu. Kin ga yadda take yi kowa? Mulki take zuba wa ko matar gidan sai haka, ta na ba da umarni da cikakken izza ta na wani yatsina fuska". Na ƙare zancen ina kwaikwayon yadda Altine take magana.
"Ai duk kar ki yi duba da waɗannan abubuwan, idan ta yi miki kan kara ki yi mata na rodi idan ta ɗaga miki ɗan ƴatsa ki tabbatar da cewa kin karya shi kafin ta sauƙe. Da zaran ta ce miki kule ki ce da ita cas. Ai ƴar aiki ba ta fi ƴar aiki ba, shi kuma wancan mutumin ki manna masa bajin hauka tun da ba shi ya ɗauke ki aiki ba ai ba shi da hurumin sallamarki".
"To shikenan zan duba na ga abin da ya dace na yi".
"Ya fiye miki dai kam kafin kwaɓar ta yi miki ruwa tsalalo". Taƙaitacce murmushi kawai na saka ba tare da na ce da ita komai ba, haka muka yi sallama da ita bayan mun yi wa juna a kwana lafiya. Na raka ta har ƙofa ta fita na rufe ƙofar. Na zo na kwana na runtse idanuna ina karanto karatun haddan da yake cikin kaina har bacci ya yi nasarar ɗauka ta. Washe gari da wuri na farka na yi alwala na yi salla ragowar ruwan da nake da shi na shiga banɗaki da shi zan watsa.
Ina ƙoƙarin cire sutarar da yake jikina na ji an bankaɗo ƙofar banɗakin tamkar za a ɓalle ta. Cikin wani irin gigicewa da ya wuce a misalta shi na yi hanzarin mayar da rigana jikina.
Wani gardeden ƙato ne daga shi sai gajeren wando ga tulelen ciki a gaba kamar randa.
"Ki fita zan yi wanka".
Firgicin da nake ciki na hana ni motsa wa balle samun kuzarin mayar masa da amsa illa kallonsa da na tsaya iya yi. Ya daka mini tsawan da ya sanya jikin rawa tamkar ana jona mini wutar lantarki.
"Ki fita na ce ko ba kya jin Hausa ne?". Ya ƙare zancen yana sanya ƙafa ya yi bol da bokitin ruwan nawan, jikina yana ɓari na ɗauki da yake ta gangarawa na fice da hanzari ban tsaya a ko'ina ba sai cikin ɗakina har zuwa lokacin jikina bai daina rawan da yake yi ba.