← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 72

Sashe 50

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Na amince zan bi ku mu koma gida tare". Na yi furucin muryata a shaƙe tamkar kwaɗon da aka danna kansa a cikin ruwan zafi. Duk su biyun suka yi shuru kafin can Yaya Alhassan ya ce"kin amince da hakan har cikin ranki ko kuwa dai kawai babu yadda kika iya? Don wallahi ba zan ɓoye miki ba tun da na ga kin yi ƙoƙarin guje mana daga cikin asibitin na ji gabaɗaya gwiwoyina sun yin sanyi ba na son mu yi miki tilas kuma daga baya a zo ana dana sani da cizon ɗan ƴatsa". Na zuƙe majinan kukan da ya zo mini kafin na sama damar cewa"na amince wallahi". Na ƙare zancen cikin karyewan zuciya da rashin ƙwarin jiki.
Kafin su ce wani abu aka buɗo ƙofar ɗakin aka shigo tare da yin sallama da tashin farko na gano muryar Zinariya ce, duk sai da ta gaishe su kafin ta tambayi ya ya mai jiki, Amir ne ya amsa da cewar da sauƙi. Duk suka miƙe tsaye Yaya Alhassan yana faɗin"bari na je wajen Likitan ya ba mu sallama". Amir ya rufa masa baya suka fita tare suka bar ni daga ni sai Zinariya zaune a cikin ɗakin, ita ta taimaka mini na tashi na zauna daga durƙushewar da na yi na jingina bayana jikin matashin da ta sanya mini a bayana don na ji daɗin zaman, na lumshe idanuna yayin da wasu hawaye masu zafi suke fitowa daga cikin idanuna da nake jin sauƙar su bisa fatan fuskana tamkar sauƙan tafasasshen ɗanyen ruwan dalma mai turiri.

"Ya ya jikin nakin?".

"Da sauƙi". Na amsa da shi ba tare da na buɗe idanuna na gan ta ba.
"Wallahi gabadayanmu mun tsorita da irin yanayin da kika shiga lokaci guda fa kika fita daga cikin hayyacinki, babu wani wanda zai gan ki a wannan lokacin ya tsammata miki za ki ƙara yin numfashi ko da na sakon ɗaya ne a cikin wannan duniyar. Waɗannan mutanen da suka ikirarin cewar su ƴan uwanki ne su ne suka kawo ki asibiti tare da ni aka yi komai don jiya har sai dare kafin na bar cikin asibitin nan, don Likitotin sun ce babu wanda zai kwana a wajenki. Waɗannan mutane sun nuna miki ƙauna mai ƙarfi da ta amsa sunanta, a dai cikin wannan duniyar da muke rayuwa a cikinsa da mutanen kirki suka yi ƙaranci da wuya a sama masu kirki da tausayinsu. Daman ki na da ƴan uwa maza ne? Don a labarin da kika ba ni kin ce ke ce ɗiya ɗaya tal a wajen iyayenki?".
Na furzar da iska mai zafi daga bakina kafin na soma ba ta amshoshin tambayoyinta.

"Tabbas kam yadda suka ce su ɗin ƴan uwana ne, sai dai ba muharramaina ba ne. Mahaifiyarsu ce yayar mahaifina uwa ɗaya uba ɗaya. Mai farin kayan shi ne Yaya Alhassan wanda aka so haɗa ni aure da shi ɗayan kuma ƙaninsa ne Amir wanda yake bin bayansa, idan ba ki manta ba su ma na ba ki labarinsu".
Cike da mamaki ta riƙe haɓa"yanzu Amatullah wannan zankaɗeɗen saurayin kika ƙi aura? Shi kuwa me ye laifinsa? Ga shi da kyau, ga ƙira da kuma kwarjini da ɗin da ɗawa ga kuma daɗin murya". Jinjina kawai na yi ba tare da na ce da ita uffan ba don na lura da yanayinta ko da na cewa wani abu, ba lalle ba ne ta fahimta balle har ta fahimci halin da zuciyata take ciki.

"To yanzu me ye dalilin wannan zuwan da suka yi? Don fa sai da aka ɗeba ƴan kallo tsakaninsu da Hajiya Babba ta yi musu tijara mai wasali, wannan ƙaramin har sai da ya fusata ainun don har sai da ya yi yunƙurin kai mata mari Aminu ya amshe cikin faɗan. Nan ta tada tijarar sai an biya ta kuɗin hayan ɗakinta da kika zauna a cikin kaf, Aminu ya bijiro da na shi buƙatar sai da aka biya shi wai kuɗin ɗawainiyyar ciyar da ke da ya yi a lokutan baya. Take suka karɓa lamban asusunsu suka tura musu kuɗin, kafin Hajiya ta bari suka kawo ki wannan asibitin ta kuma gindaya musu sharaɗin yadda suka fita da ke a cikin gidan nan, to su tabbatar da cewar kin fita ke nan har abada ko kin dawo sai dai ki nema wani masauƙin amma dai ba cikin gidanta ba".

Cike da damuwar da yake barazanar tarwatsa zuciyar da take kwance a cikin ƙirjina, na kai hannuna na dafe kaina da yake sarawa da ƙarfi.
"Innalillahi wa inna ilahirin raji'un! Me yasa Hajiya kuwa za ta yi mini haka?".
"Babu wani dalili illa na baƙin ciki da tsanar da ta yi miki tun farko, mussamman da kika ƙi bin layin da ragowar ƴan matanta suke bi. Ga ki da diri da kuma sura komai cif-cif kin ga kuwa ai da kin ba da kai bori ya hau ba ƙaramin harka za a buga da ke".

"Ai kuwa in sha Allahu na bar cikin gidanta ke nan har abada". Zinariya ta yi hanzarin tarar numfashina"ban ga ne kin bar gidan har abada ba ina za ki koma ke nan?". Na kwashe duk yadda muka yi da su Yaya Alhassan na sanar da ita, ina gama ba ta bayanin kawai na ga ta fashe da kuka sosai lamarin da ni ma ya saka ni kuka muka rungume junanmu babu mai lallashin wani a cikinmu.
Ni na fara yin ƙarfin halin tsagaita na wa kukan na ɗago kanta ina share mata hawayen fuskanta tare da faɗin"zan koma gida Zinariya Allah ya yanke mini wannan zaman ƙasƙanci da wulaƙancin. Ke ma ina mai ba ki shawara ki yi wa kanki karatun ta nutsu ki koma gida, na tabbatar da cewar iyayenki za su amshe ki".

Cikin muryar kukan da ya gama galabaitar da ita ta ce da ni"Amatullah ba zai yiyu yanzu in ce zan koma gida ba in kuma na yi yunƙurin hakan to ina mai tabbatar miki da cewar sai dai a komar da gawata. Sa boda mun riga da mun shiga cikin ƙungiya mun kuma yarda za mu yi biyayya ga dukkan dokoki da sharaɗoɗinta duk wanda ya ce zai fita to ɗayan biyu ne ko dai ya haukace ko kuma ya bar cikin duniyar gabaɗaya. Ke ma da ba kya cikin ƙungiyar ina jiye miki tsoron abin da Hajiya Babba za ta iya yi a kanki mussamman yadda suka yi musayar yawu da ƴan uwanki".

Gabaɗaya jikina ya yi sanyi ƙalau na kasa cewa komai har sai da ta ci gaba da maganar"ke dai Allah ya ƙaddara ba za ki saɓa masa ba ta hanyar keɓe wa da wani ɗa na mijin da ba halal ɗinki, ƙaddarar rayuwa a barikin ce kawai a kanki amma babu ƙaddarar saɓawa Ubangiji. Na taya ki murna da ba ki bari sheiɗan ya yi nasara akan yi ba haka nan ba ki taka rawa a lokacin da yake buga gangar sheɗancinsa ba, za ki koma gidan iyayenki cikin aminci da kuma mutunci Amatullah. Ga wannan wayar ki tafi da ita idan kin nutsu ki ba wa ƴan uwanki su saurari abin da yake ciki na san cewa za su fahimce ki". Tana gama maganan ta riƙo hannuna ta damƙa mini wayar yayin da ta fashe da wani kuka da ni ma ya tursasa hawaye kwaranya daga idanuna. Ban iya ce mata ko kanzil ba har zuwa lokacin da Yaya Alhassan suka dawo cikin ɗakin tare da Likitan ya duba ni ya kuma tabbatar da cewar jikina ya yi sauƙi ya rubuta mana sallama tare da wasu magungunan da ya ce lalle a saye su, kuma na fara amfani da su da gaggawa.

Haka muka fito har cikin haraban asibitin hannuna saƙale cikin na Zinariya, da Yaya Alhassan yake ta yi mata nasihar ta tuba da koma zuwa ga Allah da ya kasance gafurul rahim. Kanta kawai take gyaɗa masa don da ni da ita mun an cewa akwai ɓoyayyan matsalan da bala'in da yake tattare da hakan.
Ko da muka zo rabuwa da ita ji na yi tamkar raina zai bar gangar jikina. Haka muka sha kukanmu Amir ya din ga ba mu haƙuri da ƙyar muka saki hannun juna, haka muka rabu muka hau adaidaita muka nufi tasha, muna isa muka saka motar garinmu ba mu yi mintuna goma ba ta shiga muka soma tafiya.
Tun da muka soma tafiya ƙirjina yake bugawa har muka isa cikin garin, ina fitowa daga cikin motar na ji gabana ya faɗi da har sai da na runtse idanuna, muka tara adaidaita muka shiga na lura har zuwa wanna lokacin Yaya Alhassan fushi yake yi da ni hatta magana ma sama-sama yake yi mini shi ma sai ya zama dole ne. Mu na iso ƙofar gidan Anty Sawwama na ji wani zazzafan zazzaɓi ya lulluɓe wajen gabaɗaya ya sauya miki tamkar wacce ta yi shekaru goma cur da barin cikin gidan, da ƙyar nake ɗaga ƙafata da na ke jin ta tamkar ba ta kasance ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikina ba yayin da wani jiri yake kwasa ta da barazanar buga Ni da ƙasa haka muka ƙarisa cikin gidan da Anty Zulaihatu da ta fito daga banɗaki na fara tozali.
Chapter 50 · 0% Book details