← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 72

Sashe 45

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Idan ya yi hakan to shi ne kuskuren farko da zai yi da zai yi silar tonuwar aisirinsa ga duniya gabaɗaya. Sai dai ya yi hakan ma akwai ɓoyayyar hanyar da zan ɓullo masa".
Ajiyar zuciya mai nauyi da sauti ta saka yayin da take bi na da kallo, ko ba ta furta mini ba na fahimta kuma na kallon shakku game da maganan da na furta kwance a cikin idanunta da suka ƙanƙance. Na riƙo dukka hannayenta na sanya cikin nawa ina murzawa a hankali.

"Ki kwantar da hankalinki in sha Allah ina ji a jikina Allah zai ba mu nasara akan wannan abun. Kamar jahadi ne fa za mu yi wajen tona asirin abin da yake aikatawa a ɓoye wanda haramci ne hakan".

"In sha Allah zan kasance da ke tun daga farkon wannan lamarin, har zuwa ƙarshensa. Zan ba ki dukkan wani gudamawar da za ki buƙata daga gare ni".
Murmushin jin daɗi na sakar mata muka ƙara rumgume juna cikin farin ciki, haka muka kwana a zaune mu na tsara yadda za mu tafiyar da komai gudun afkuwar matsala. Ba mu muka kwantar da haƙarƙarinmu ba sai bayan sallan asubahi. Sai dai ni kam na kasa yin bacci iya juyin da na dinga yi raina cike fal da tarin damuwar da ya hana ni sakat, na juya ina kallon Zinariya da take baccinta hankali kawai sai na ji ina ma ni ce nake wannan baccin cikin kwanciyar hankali da nutsuwar ruhi, sai dai kash! So ba samu ba ne.

Kafin hantsi har na yi wanka na yi duk wani abun da zan yi, na ɗauki kuɗi na ba ya wa Aminu ya sayo mini ƙwayar da take bugar da hankali. A cewarsa duk wanda ya sha maganin a cikin abin sha akwai yiyuwar ya yi awannin biyar cur yana bacci ba tare da ya san inda kansa yake ba, balle wanda yake tsaye a kansa, haka nan ko yankan naman jikinsa za a yi a wannan yanayin ba zai san ana yi ba wai kunu a maƙwabta. Hatta ƙananan kayan da zan saka na gama tanadinsu kafin mu tafi, Zinariya na tashi na kai mata ruwa bayi ta yi wanka na yi masa abin karin kumallo muka ci muna yi muna ƙara tattaunawa har muka kammala. Muna cikin cin abincin wayarta ta yi ruri ta kai hannu ta jawo wayar ba tare da ta tsaya duba mai ƙiran ba ta kata a kunnenta.

Ban san me ye aka ce mata daga ɗayan ɓangaren ba sai ji na yi ta ce"Oga Deeno ke nan tun da na ce maka ba komai ai na tabbatar da cewar babu ɗin ne. Ni da kai ai ba a jin kanmu, yanzu dai yaushe ya kamata mu zo mu?".

Ta ɗan yi shuru kafin can ta ce"to shikenan in mun shigo zan ƙira ka". Daga haka ta kashe wayar ta mayar da idanunta gare ni.
"Ya ce mu je mu kaman ƙarfe takwas na dare".

Na jinjina kaina cike da gamsuwa"to Allah ya kaimu".
"Amin". Ta amsa da shi a taƙaice muka ci gaba da cin abincin, ji nake yi kamar a ranar lokaci ba ya yi gudu. Ina zaune bayan na gabatar da sallan zuhur a ƙofar ɗaki na yi sallan na zauna akan sallayan na buga tagumi, lokacin Zinariya ta fita za ta je ciro kuɗi.

Kyawawa ta zo ta tsaya a kaina na cira kaina ina kallonta tare da sauraron abin da take cewa" Ranki ya daɗe ki na ba baƙo a waje yana jiranki".
"Baƙo kuma?". Ta gyaɗa mini kanta cike da tabbatarwa tana ƙara wa da faɗin"ƙwarai kuwa ya ma daɗe ya na amfani jiranki da alama. Yana nan da motarsa mai zafi". Na taɓe bakina ina faɗin"babu wanda nake tsammanin zuwansa wataƙila wata yake nema ba ni ba".

"Amatullah fa ya ce yana nema. Kuma duk gidan nan babu wata mai irin sunan nan face ke É—in dai".
A kufule na ce"ki je ki ce da shi ba na nan". Na yi maganar ina miƙe wa tsaye tare da ninke sallayar da na yi salla akan sa na yi shigewa ta cikin ɗaki na bar ta tsaye a wajen. Na zauna ina ta tunanai kala-kala babu jimawa ta ƙara dawowa ta shigo cikin ɗakin.

"Ranki ya daɗe mutumin nan fa ya dage akan ba zai bar ƙofar gidan nan ba har sai ya ganki, ya yi magana da ke".
Na buga tsaki"ai kuwa zai kwana a wajen, tun da ba shi da aikin yi".
Ta riƙe haɓa"ai kuwa ya yi kirarin in ba ki fito ba har shigowa ciki sai ya yi".
"Don Allah ki fita daga cikin É—akin nan ki je ki sanar da shi abin da na faÉ—a miki".

"To shi kenan". Ta amsa da shi a gajarce tare da juya wa ta fice wa daga cikin É—akin, na dinga buga tsaki kamar zan yi aman zuciyata tsabar takaicin da ya cika muni rai da ruhina.
Kamar wacce aka jefo cikin É—akin Kyawawa ta faÉ—o cikin É—akin kamar wacce aka wurgo ta. Na watsa mata harara"mene ne kuma?".

"Wallahi Ranki ya daɗe ya ƙi tafiya ga shi nan ma ya na shigo wa".
Ta na rufe bakinta na ga mutum zamgan-zamgan ya shigo cikin ɗakin, na yi zumbur na tashi tsaye da zummar ɗura ashariya sai dai mu na haɗa ido da shi na nema zancen na rasa ji na yi tamkar an rufe min baki baki. Na nuna shi da ƴar manuniyar ƴatsata cikin rawar murya da sarƙafewar harshe na furta"Saifullah kai ne? Me ya kawo ka cikin ɗakina?".

Bai amsa mini ba illa zara hannayensa da ya yi a cikin aljihun wandon farin shaddar jamfar da yake jikinsa ya zuba mini idanu, kafin daga bisani ya soma bin É—akin da kallo.
Ya jinjina kansa kafin ya ce"a nan kike rayuwa ke nan?".

"Wannan ba abin da ya shafe ka ba ne ka fice miji daga cikin É—aki, tun kafin na tara maka mutane na yi maka tijara".

"Magana na zo mu yi ki saurare ni". Ya yi maganar yayin da na ga yana ƙoƙarin zama akan kujerar roban da yake cikin ɗakin, na yi wuf na janye kujerar ina huci.
"Za ka yi kuskure idan ka sake ka ɗauki kalamaina a matsayin wasa, wallahil azim zan tara maka mutane idan ba ka fita daga cikin ɗakin nan ba. Me ye ya rage tsakanina da ku? Bayan kai ne mutum na farko da ka yi silar kawo komai ƙarshe. Me ya kawo ka cikin ɗakin karuwa mai zaman kanta mace mai mungun nufi? Ka fita daga cikin ɗakin nan kafin na yi mata akuyanci". Na ƙare zancen cikin ɗaga amo tare da runtse idanuna jikina yana cigaba da jijjiga tamkar ana jona mini shock ɗin wutar lantarki. Na ji an dafa kafaɗata na yi azama ture hannuna.

"Kar ka sake ka yi kuskuren ɗaura hannunka a jikina don sai na tabbatar maka da hakan a matsayi mafi kuskure girma da za ka yi a cikin rayuwarka na duniya. Ka fita daga cikin ɗakin nan ba na fatan Allah ya ƙara haɗa ni da wani daga cikin ahalinku balle har mu zauna inuwa ɗaya".

"Ke Amatullah wai me ye yake damunki ne? Da waye kike wannan batutuwan? Sannan waye ne ba kya fatan Allah ya ƙara haɗa ku da shi?". Na tsinkayo muryar Zinariya da hakan ya dawo ni cikin duniyar zahiri na buɗe idanuna da na runtse su na ga dai da gaske ita ɗin ce tsaye a gabana ta na kallo na kamar yadda ni ma nake kallonta. Sai da na yarce ruwan gumin da ya kwanta a saman goshina kafin na sama lasisin faɗin"ba kowa har kin dawo ke nan?". Na yi zancen ina wuce wa na zauna a bakin katifar ina ta faman mayar da numfashi.

"Wai me ye kike ɓoye min ne Amatullah? Na zo na same ki sai wasu suturai kike yi marasa kan gado ga kuma firgici a fuskarki amma ki na ce min ba komai".

Cike da ƙosawa da sauraron zancenta na ce"ba komai na ce miki in akwai a zan gaya miki". Daga haka na kwanta na juya mata baya na lumshe idanuna kamar mai bacci, sai dai musayar wuƙaƙe da mashin wutan da ake yi a cikin farfajiyar ƙirjina ba zai taɓa sauƙar mini da nutsuwar da zan iya runtsawa ko da na sankan guda ba ne. Ban ankara ba na ji wasu hawaye masu ɗumi su na sauƙar akan fatan fuskana. Abubuwan da suka wakana suka soma dawo mini cikin kwanyata.
Ko da na tashi na yi sallan asr ban ba wa Zinariya fuskar da za ta ƙara yi mini wani tambaya, sai da na yi har sallan isha'i kafin muka haramar tafiya otel muka shirya duk abin da mu buƙata muka rufe ɗakin muka tafi.

Muna sauƙa a bakin otel ɗin ƙiran Oga Deeno yana shigowa cikin wayar Zinariya ta ɗaga ta sanar da shi ga mu mun iso ya fito ya yi mana jagoranci har zuwa cikin wani garden muka zazzauna, ya soma yi mana jawabi.

"Yanzu haka shi da tawagarsa su fita zuwa gidan mai martaba amma ina da tabbacin zuwa karfe tara ko goma za su dawo, don haka zan san yadda zan yi na buɗe miki ɗaki ki shiga cikin kafin ya dawo, daga nan kuma ke kike san abin da za ki yi, san a kashe CCTV cameras ɗin dukka sashin. Ni da Zinariya kuma mu ma za mu keɓe". Cike da gamsu na ce"ba damuwa".
Ya ɗan sausata amon muryarsa"don Allah duk abin da za ku yi kar ki cutar da shi, kar ki yi silar da za ki ɓata min aikina ki wargaza min burin da na daɗe ina ginawa".
Chapter 45 · 0% Book details