Sashe 22
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Amin". Na amsa da shi a taƙaice da hakan ya ba ta lasisin fita ta tafi gararambana. Haka na ci gaba da zama a haka har na tashi na yi fita na yi alwala na dawo cikin ɗakin na yi sallan magrib, ban tashi daga inda na yi sallan ba har sai da na yi sallan isha'i. Na bi kayan jikina da kallo tun da na zo garin jafari ban sauya wasu kayan ba, balle hijabi da takalmin da wannan mai gadin ya taimaka mini da su. Jikina ya soma rawa ina jin wani zafi yana ratsa wa har cikin naman jikina.
"Allah na tuba ka yafe mini sannan ka kawo mini É—auki da mafita akan halin da nake ciki".
Na furta a bayyane yayin da nake miƙe wa tsaye na fita daga cikin ɗakin na nufi ɗakin Hajiya Babba tana zaune a falon tana irga wasu tulin kuɗaɗen da suke gabanta, na durƙusa na yi mata sannu ta amsa mini ba tare da ta kalle ni ba.
"Hajiya daman na zo na sanar da ke hukuncin da na yanke akan zaɓin da kika ba ni ne".
"Ina jinki".
Sai da na sauƙe wai gauron ajiyar zuciya kafin na furta"na amince zan bi hanyar da kuke so".
[12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE*
Â©ï¸ Maimuna Tijjani Iyam
_________________________________________
Page 5ï¸âƒ£5ï¸âƒ£
Tun da na so zancen ta kafe ni da ido har na kai aya, cike da mamaki ta furta"abin da kike faɗa ɗin nan ya kai har cikin zuciyarki kuwa? Sa idonki a cikin nawa ni ɗin nan da kike ji da gani cikakkiyar ƴar bariki ce mai lasisi babu inda ƙafafuna ɗin nan ba su taka ba a cikin duniyar bariki. Duk wani salon munafukarci, luggu da nurƙufanci na san shi tare da alamominsa. Nan cikin gidan nan kwanakin baya wata yarinya ta zo simi-simi da ita kamar ba za a sanya mata hannu a baki ta ciza ba, mun sha fama da ita kafin ta bi layi mutumin farko da ta fara mu'amala da shi babban mutum ne don duk faɗin garin nan babu inda zan shiga ba a san sunansa ko an san shi a fuska ba. Rimi-rimi ya aiko aka ɗauke ta zuwa otel yarinyar nan ta burma masa wuƙa a cikinsa ta ji ajalinsa har lahira ta kwashe masa maƙudan kudaɗe ta tsallake boda, ta bar ni a cikin masifa da ha'ula'i aka yi mini rufgudu na yi trending a cikin garin nan. Da ƙyar aka same ta a can yankin sudan aka cafke ta kafin na sama salama, ke ma na lura wannan simi-simin da kike yi tsabar tsagwaron munafurci da iya ƙulla luggu".
Ilahirin jikina gabaɗaya ya yi sanyi ƙalau sai da na ja dogon numfashi na fesar kafin cikin rauni na furta"Hajiya har cikin raina na yanke wannan hukuncin". Ta ɗan yi jim tana bi na da kallo kafin can cikin wani irin dakakkiyar murya ta ce da ni"ke yarinya sa idonki a cikin nawa ni ɗin nan da kike gani wargi ce daidai ƙugun ko wacce ƴar bariki da take jin karanta ya kai tsaiko". A hankali na cira kai na sanya idanuna a cikin nata sai dai na kasa jurar jimirin haɗa ido da ita babu shiri na rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa ina sauraran zancen da ta ɗaura da shi.
"Ina fatan abin da kika furta su kasance gaskiya don ina mai tabbatar miki da cewar duk abin da kika jangalo a kanki zai ƙare don duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan duka. Akwai sharruɗa da nake gindayawa duk wata yarinyar da take cikin gidan nan, duk wani namijin da kuka yi mu'amala da shi ina da kaso ɗaya cikin uku na abin da ya sallame ki ina fatan ki na saurarana?". Na gyaɗa mata kaina alamar e da hakan ya ba ta damar cewa"ki na da mutane a ƙasa ko kuma mu nema miki duk yadda kike da suran nan babu wanda zai gan ki ya ji ba ki burge shi ba balle har ya kau da kai".
"Babu wasu a ƙasa".
Na amsa mata muryata can ƙasa kamar an dannen kwaɓo a cikin ruwan zafi.
"To ku shirya da dare bayan misalin ƙarfe takwas za ki yi baƙo". Kaina kawai na jin wani irin abu yana tasowa tun daga ɗan yatsana yana bin dukkan sassan jikina, na tashi cikin rashin kuzari da ƙwarin jiki zan fita na ji an ƙira sunana da hakan ya tilasta mini tsaya wa ba tare da na waigo ba.
"Ke kuma La'aniyatu me ye ya fito da ke daga cikin É—akin? Ke da kika ce ba ki da lafiya kanki yana yi miki ciwo".
"Umma ni fa na warke. Sai ki yi ta garƙame ni a ɗaki kamar wata ƙaramar yarinya kuma na daɗe da gane manufarki akan hakan. Harkar da kike jawo ƴaƴan wasu cikinta ne ni ba kya so na bi wannan layin, ai an ce duk abin da ka shuka Umma shi za ka girba". Tsam Hajiya Babba ta miƙe"ke La'aniyatu ki san irin maganan da za ki na furta domin ni ɗin uwarki ce. Kuma duk lalacewa ta ba za ki sauya ni a matsayin mahaifiyarki ba kamar yadda duk lalacewar tuwo ba a sauya masa suna".
"Ni ban ce zan sauya ki a matsayinki ba amma ina gaya miki abin da yake zahiri ne wanda ko ba ji ma ko ba daɗe ko kuma raye ko ba ma ciki rayayyu, babu makawa sai hakan ya faru....". Ba ta ƙarishe zancen ba Hajiya Babba ta zuga mata mari mai matuƙar sauri har sai da hancin cikina ya kaɗa.
"Tsinanniya wacce ba ta san haƙƙin uwa ba, in sha Allahu ke kam ba za ki gama da wannan duniyar salin ƙalin ba. Da ba a cikin ɗakin nan na haife ki ba sai na ce sauya min ke aka yi a asibiti, duk ƙoƙarin da nake yi wajen inganta rayuwarki da ganin ba ki nema komai kin rasa ba La'aniyatu ba kya gani?" Ta ƙarƙare zancen cikin sanyin amon.
Kasa motsawa na yi daga inda nake tsaye munanan kalaman Hajiya Babba suka jirkita mini tunanina, na tuna da Ummanta a lokacin da take jifa na da makamantan irin waɗannan kalaman wanda ina da yaƙinin su suka yi tasiri a kaina har na tsinci kai a cikin gidan karuwai da ƴan daudu. Ji na yi an ja hannun aka fizgo ni muka fice daga cikin ɗakin ba mu tsaya a ko'ina ba sai cikin ɗakina. Na fizge hannuna daga cikin riƙon da ta yi mini.
"La'aniyatu me ye haka kike yi?".
A zafafe ta mayar min da tambaya"me ye kika ga na yi?". Na watsa mata wani kallo don ban taɓa raina wayo, hankali da hangen nisanta ba irin na yau.
"Hajiya fa mahaifiyarki ce ko me ye take aikatawa hakan ba shi zai ba ki damar da za ki na faÉ—a mata duk wani abun da ya zo bakinki, ba tare da kin tauna kalaman ba".
"Ni yanzu ba wannan ba shin da gaske kike za ki bi hanyar da suke so?".
Na harare ta da wutsiyar idanuna kafin na ce"ƙwarai kuwa". Ina dasa aya na wuce zan zauna ta jayo gefen hijabina.
"Me yasa za ki aminci bayan kin yi wa kanki alƙawarin ba za ki aikata ɓarna ba? Ke ma kenan za ki zama ba ki da bambamci da ragowar matan gidan nan? Kin san yadda suke yin wulaƙantaccen ƙarshe kuwa? Wasun su su kamo da jinyar da za ta yi ajalinsu, wasu shaye-shaye ya haukatar da su yayin da wasu kuma tsufa yake cim musu duk waɗanda suke mu'amala da shi su yi ɓatan gado su gudu ko sama ko ƙasa. Idan ba ki yi sa'a ba kuma har da kuzurin cuta za ta jajiɓowa kansu wasu kuma su haifa shegu waɗanda ba su da uba, haka rayuwarsu da ta yaran za ta faɗa garari su zama abin wulaƙantawa da tozarwa a tsakanin al'umma".
Na cire hannunta daga jikina na je na yi zamana ina cire hijabin da yake kaina"duk na san da hakan, me ye zan zauna na yi bayan ga abin da ya kawo ni nan ban yi shi ba. La'aniyatu duk matan cikin gidan nan ƙaryan bariki suke yi yanzu ne zan nuna musu ainihin abin da kalmar ta ƙunsa, domin zan warware musu zare da abawa. Ke dai kawai ki zuba mini ido ki kuma bi ni da fatan alkhairi".
"Mata da yawa da haka suke fara har su zarje su zama jan wuya. Amatullah ina jiye miki tsoron abin da kike shirin aikatawa zai haifar miki a nan gaba, kin ga muranen nan ba su da tausayi balle imami da zarar sun fara nannaÉ—a garÉ—in mace to ba sa barin ta haka banza wallahi har malamai da bokaye suna bi, don wasu ba a cin kuÉ—insu a zauna lafiya".
Taƙaitaccen murmushi na yi kafin na ce da ita"ni kuwa zan ci kuɗin kuma lafiya sumul".
"Amatullah".
Ta ƙira sunana cikin wani irin yanayi da ya fi kama da na zallan mamakin da ba sirka shi da komai. Na ɗage mata idona guda alamar lafiya? Ta zo ta zauna a kusa da ni tare da riƙo hannuna za ta yi magana na dakatar da ita.
"Ki zuba mini ido kawai na ce da ke, na fahimci wani abu guda cewar in dan har ba ka tashi ka nema wa kanka ƴanci ba haka za ka dawwama a cikin ƙasƙanci". Da alama mamaki da al'ajabi ne ya hana ta cewa komai illa kallon da take bi na da shi na sakar mata da murmushi ina miƙe wa tsaye ina ƙoƙarin mayar da hijabina na ce"bari ki ga na yi salla don ina da babban baƙo. Har ya zo ban gama kimtsa wa". Ba ta ce da ni uffan ba har na yi sallan na iddar na shafa dogon addu'ar da na yi, na waigo ina kallonta ta yi jigum da ita kamar majinyaciya.
"Ba ki tambaye ni gidan aikina ba?".