Sashe 1
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
[12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE*
Â©ï¸ Maimuna Tijjani Iyam
_________________________________________
Page 4ï¸âƒ£1ï¸âƒ£
Na daɗe ina kukan har sai da na gaji don kaina na tashi na share hawayena, so nake yi na je na yi alwala na gabatar da salla amma ban san ta inda zan fara ba ga shi ina son shiga banɗaki na tsaftace jikina kafin na yi sallan. Ganin wankin hula yana neman ya kai ni dare ya sani tashi na fito waje, cike gidan yake da mutane jinsin maza da mata kowa yana harkan gabansa daga matan har mazan babu wani shigar arziki balle ta mutunci. Mafi yawan matan zani ne a jikinsu ɗaurin ƙirji mazan kuwa gajeren wando da ya tsaya daidai gwiwansu masu kunya daga ciki suka ƙara da singileti.
Na fi mintuna biyar a tsaye a ƙofar ɗakin na kasa gaba na kasa baya illa bin kowa da nake yi da ido.
"Madam lafiya kin yi tsaye sai ƙare mana kallo kike yi in ce dai lafiya ko?". Na yi an yi zancen a zafafe kamar za a rufe ni da duka, da sauri na waiga don ganin wanda ya yi furucin. Wata matashiyar budurwa ce tsaye ta riƙe ƙunta tana ƙare mi kallon tsaf kamar yadda ni ma nake bin ta da kallo. Kafin na ce wani abu ta daura mini mari na yi saurin dafe kuncina don ba ƙarya marin ya shige ni sosai har sai da na ji idanuna sun kawo ƙwalla.
"Ke waye da har ina yi miki magana za ki tsaya kina kallona maimakon ki ba ni amsa? Yau sai kin faÉ—a min uban da ya tsaya miki a cikin gidan nan da har ya ba ki damar da za ki yi min wannan É—iban albarkan".
"Me na yi miki za ki mare ni?". Na yi zancen har izuwa lokacin ina dafe da kuncina, da alama tambayar ta fusata ta don sai da ta riƙe haɓa kafin ta furzo zancen.
"Kan uban can! Lalle ba ki san da wacce kike magana da ita ba ne shi yasa kika tsaya a gabana ina faɗa ki na mayar mini da martani. To yau zan nuna miki ƙarshen barikinki da iya shegen da kike ji da shi". Ta kacumo wuyan hijabina ta riƙe tamau har sai na soma tari, duk cikin dandazon jama'ar tsakar gidan babu wanda ya taso balle ya kawo mini ɗauki. Kowa ya mayar da hankali kan abin da yake yi.
"Me ye nake gani haka Baraka? Kashe ta za ki yi ko kuwa? Sakar ta na ce". Hajiya Babba ta yi zancen yayin da take fitowa daga É—akinta ta fincike hannun Baraka daga jikina.
"Baraka na sha gaya miki cewar ba na son rigima a cikin gidan nan. Babu wanda nake ajiye kara ya tsallake shi face ke don hakan ba za ka tara min ciwon kai ba. Yanzu ba sai an jima ba ki shiga ki haÉ—o duk abin da yake mallakinki ne ki fice ki bar min cikin gida, tun da ba kuÉ—i muka haÉ—a muka gina gidan tare da ke ba".
Take jikin Baraka ya soma rawa ta zube a ƙasa ta na magiya.
"Don girman Allah Hajiya ki rufa min asiri kar ki bari na tozarta na kunyata a idanun maƙiya. Kin san yanzu ƙiris ake jira ya faru a soma yamaɗiɗi da kai. Hajiya ki rufa min asiri wannan shi ne na farko kuma na ƙarshe".
Cikin zafin rai Hajiya ta soma cewa"sanin kanki ne Baraka ni ba na yafiya kuma ba na sauƙa daga kan maganar da na riga na furta. Don haka ki shiga ki haɗo kayanki ki bar min cikin gidan, daman na sama wanda suke son ɗakin kuma har na dafe ƴan sulallana". Tana dasa aya a nan ta waigo kaina.
"Ke kuma me ye kike buƙata?".
Na yi ƙasa da kaina kafin na ce"banɗaki zan shiga, sai kuma ina so na yi alwala".
Ta nuno ni da ƴar manuniyar ƴatsarta kafin ta furta"zan ɗaga miki ƙafa ne kawai saboda ke baƙuwa ce kuma Aminu ya kawo ki to za ki ci albarkacinsa. Zan ba ki ruwa da buta da bargon kwanciya wanda za ki yi amfani da shi, amma ina so ki sani kuma ki sa a cikin kanki cewa a gidan komai na sayarwa ne komai da kike ji da gani ke za ki nemawa kanki hatta ruwan wanke ido kin ji ni ko?". Jikina yana ɓari na ce"e na ji na gode sosai". Ba ta tanka mini ba ta shige ɗaki babu jimawa ta fito, ta ba ni bango, buta sabuwa sai kuma pure water guda uku. Na karɓa na durƙusa har ƙasa ina yi mata godiya, ba ta bi ta kaina ba ta yi shigewarta cikin ɗakinta bayan ta gama gindawaya Baraka gargaɗin kar ta kuma fitowa ta iske ta ba ta bar cikin gidan ba.
Na shiga ciki na ajiye bangon na zuba ruwan guda biyu a butan na bar É—aga na sha, na fito na rasa gane ina ne banÉ—akin don haka na isa wajen wasu mata na yi musu sallama. Maimakon su amsa sai na ga duk sun kafe ni da idanuna kamar wacce ta zo da wani sabon abu.
"Don Allah ni baƙuwa ce a gidan nan yau na zo. Banɗaki nake nema ina so na shiga". Duk su ukun suka fashe da dariya har da tafa hannu suka mayar da ni kamar magiji da sun kalle ni sai su tuntsire da dariya. Haka na gaji da tsayiwa na bar wajen na koma can gefe na tsaya.
"Ki na neman wani abun ne?". Na ji an furta a kusa da ni. Na ɗaga kaina ina ƙarewa wacce ta yi zancen kallo sanye take da hijabi fari irin wanda ake ƙira da sunan half sunna. Na ja dogon numfashi na fesar kafin na ce"ni baƙuwa ce banɗaki nake nema".
Ta yalwata annurin fuskarta kafin ta ce"mu je mana to na nuna miki". Ta yi gaba ina bin ta a baya har muka isa bakin banɗakin ta yi mini ishara da hannunta alamar na shiga. Na sakeke na tsaya ganin mutane tsaye cirko-cirko a ƙofar banɗakin suna lamarin gabansa babu abin da ya sha musu kai. Fahimtar abin da nake nufi da abin da yake yi mini yawo cikin raina ya sa ta faɗin"kar ki damu ki shiga abin ki, zan tsaya miki a wajen babu wanda zai shigo kanki".
Na waro idanuna waje cikin firgici na ce"a shigo kaina kuma?".
"KaÉ—an ne daga cikin abubuwan da mutanen cikin gidan nan za su iya aikata. Don haka ki shiga abin ki ina tsaye a nan babu wanda zai shigo". Na jinjina kaina ba don na gamsu da abin da ta ce da ni ba, na shiga banÉ—akin na yi abin da zan yi na fito sai dai duk a firgici nake. Na yi alwala muka dawo ciki na yi mata godiya sosai ta nuna mini babu komai na shige É—akin da aka kai ni.
A bisa tabarman na yi sallan magrib da isha'i ko da na shafa addu'ar da na yi na zauna, na zabga tagumi ina tunanin makomar rayuwata da yadda lamura suke sauyawa. Na daɗe a zaune har sau da dare ta yi nisa, kafin yunwa da ba kasancewa ƙanwar uwata ba ta dawo da ni cikin hayyacina. Na dafe cikina da hancina suke kukan yunwa na waigo da nufi ɗauko ledar da Aminu ya kawo mini na ga waje wayam babu shi babu alamarsa.
Ta yi zumbur na miƙe ina ta waige-waige amma ban ga komai ba hatta pure water guda ɗayan da na ajiye ban gani ba. Na durƙushe akan gwiwoyina ina shararo kuka da dukan ƙarfina, ga wani yunwan da nake fama da shi kamar ƴaƴan hanjin cikina za su tsintsinke, tun ina durƙushe sai da na kwanta a ƙasa na dinga juyi riƙe da cikina da yake murɗawa.
Na kasa yin bacci tsabar yunwan da yake nuƙurƙusata take wani zazzaɓi mai zafi da ratsa jiki ya rufe ni na koma sauƙe numfshi da ƙyar.
Da wani irin kuzari Anty Sawwama ta wayi gari ranar ta fito waje ta soma kici-kicin haɗa wuta domin ɗaura abin kari, tana cikin aikin Umar a fito ya iske ta ya durƙusa har ƙasa ya gaishe ta ta amsa fuskarta ɗauke da walwala, tare Yaya Alhassan da Amir ma suka fito suka tsuguna suka gaishe ta ta amsa tare da sanya musu albakar da addu'ar Allah ya datar da su a cikin wunin wannan ranar.
"Umma ke da kanki za ki yi girkin ba za ki ba ri Asma'un ta zo ta taya ki ba".
"Har yaushe zan jira zuwan Asma'u ita ma da sai ta gamo aikin gidansu kafin ta zo. Ina so yau na yi girki na musamman ga Amatullah don tun gabannin faruwar wannan lamarin babu wani abin da take ci na kirki". Ta ja dogon gashin ta fesar kafin ta ci gaba"wallahi yanzu ba ni da wani burin da ya wuce ganin Amatullah cikin farin ciki. Ba ni da wani sauran buri da ya zarce na ga rayuwarta ta gyaru wanda ya aikata mata wannan aika-aikan kuma a hukunta shi daidai da abin da ya aikata".
Cikin jimami Amir ya furta"ai wallahi da zan ga wannan mutumin sai na yi masa lakanin da ko uwar da yi naƙudarsa, idan ta gan shi ba za ta shaida sa ba".
"Babu wannan maganar Amir amma tabbas doka za ta yi aiki akan sa. Ba ma shi kaÉ—ai ba hatta matar da aka yi abun a cikin gidanta sai ta É—anÉ—ana kuÉ—anta".
"Hakan shi ne daidai, Allah ya datar da mu". Anty Sawwama ta yi furucin da duk suka amsa da amin, tare suka yi aikin don daman ta sabar da su akan hakan, sai da suka gama haÉ—a komai aka tattare wajen Umar ya shimfiÉ—a tabarma aka jera kayan karin kumallo.
"Bari na je na taso ta".
Anty Sawwama ta yi zancen tana tashi ta nufi ɗaki wayam ta tarar da ɗakin babu kowa, take ta dafe ƙirjinta cikin tsananin tashin hankali ta dudduba ɗakin hatta katifa sai da ta ɗaga. A fito jikinta yana ta rawa su Yaya Alhassan duk suka taso suna tambayar lafiya.
"Ba ta ciki ban ga Amatullah ba ta cikin É—akin".