← Book details Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 65

Sashe 8

Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kwanan su hud'u da zancen aka samu bizar su ta zuwa kasar India dukan su...Daren ranar da washe gari zasubi jirgin India Alhaji ya ce ga garinku!!!"Sun shiga tashin hankali na tsawon shekara daya basa cikin hayyacin su sai daga bisani suka hakura da hukuncin ubangiji Duk sun rame sunyi baki sun canja saboda damuwa."Nan karatun Jawad ya dawo Nigeria saboda ba zai iya barin mom ba ita kadai!"Itama agefenta Bata iya rabuwa da Jawad shi kadai ne da ita ahalin yanzu."Sonsa sai karuwa yake,ko taso tayi masa fada Bata iyawa,shikam idan ya tuna da hudubar Abi da ta shigesa sai yayi laushi saboda ya daina wasu abubuwan wasun ma ahankali yafara dainawa."A hakan ya kammala Degree dinsa fannin Accounting har yayi service ya dawo,suna zaune da mom cikin tufin asiri tana kasuwancin ta,"

"Amma shi jawwad har yau baisan aynihin kasar iyayensa ba!"Da dalilin zuwan su Nigeria."Iyayensa sunki su gaya masa sirrin boye."Wannan kenan

"A yanzu dai jawad kokarin zuwa masters yakeyi."shi da Abokinsa Saifullahi waziri."Wannan ita CE rayuwar Jawad da Iyayensa ta baya har kawowa yanzun ."Da Yake suna da dukiya Kuma Kullum acikin Kasuwancin kudin suke, shiyasa Bai damu da ko da yafara neman aiki da degree dinsa ba!"

*'YAR MUTAN DIKKAWA CE*😍

[2/18, 7:25 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲

*NA*
*NABEELA DIKKO*

*PEN WRITERS ASSOCIATION*

*SHAFI NA TAKWAS*AYI HAKURI SHAFI NA BAKWAI YANA K'ASA WURIN HADAWA NE AKASAMU MATSALA!

_Kyauta ce ga Daukachin 'yan uwa da Abokan Arziki Ina maku fatan Alkhairi Allah yabar zumunchi AMEEN_

_Appee Bufday🎂 Kawar Aminchi Fatty Musa tare da ta hannun damanki Pynah Buhari Ina maku fatan Alkhairi Allah ya qarou shekaru masu Albarka,Da 'yah'yah nagari,Ya barmu tare,Ameen"_

_My Cweet Baby Mufeeda ta ce"A gaida ku Fans Ana tare iya wuya."😍

______________________________________
"Tunda na farka asuba ban koma bacci ba!"Karatun Alqur ani nayi tare da azkhar."Bayan na kammala wanka nayi da misalin karfe bakwai na ta da yaran saboda nasan cewa suna zuwa makaranta domin jiya kafin su bacci sun sanar min."Da kyar Mufeeda da ke gefena ta tashi can na koma agadon Mufeed Ina tashe shi ahankalin ya tashi wanka nayi masu daya bayan daya."Sannan nace suyi Alwala Amma wai basu iya ba!"Da taimakona sukayi cikakkiyar Alwala...Sai na shirya su tare da saka masu uniform dinsu da suka dauko a lokarsu."Cewa nayi suyi sallah Nan take Mufeeda ta Bata rai!"

"Wai ba za tayi sallar ba,''Saboda mumyn su Tace Basu Isa sallah ba!"sai sun girma,"

"Shi kam Mufeed ta da sallar yayi domin ya Gaya min Abbansa Yana zuwa masallaci da shi magrip da ishaa kawai idan yadawo aiki amma ranakun mako yanayi duka."

"Nadai lura dukkan su basu son sallar domin Nan da nan Mufeed ya gama tashi sallar."Ya dinga zuba kamar famfo, banji ko Aya Daya abakinsu Amma Nasha surutu da labarin series da wakoki abakinsu."

"Da kyar da wa'azi da Komai na samu Mufeeda tayi sallar nan tana fushi!"Da taga ma har da hawayenta Domin na takurata ne sai da tayi dole!

"Bayan sun kammala nasiha nayi musu akan duk Wanda baya sallah Dan wuta ne!"RANAR tashin alqiyama wutar jahannama za'a SA Maras sallah,"Kuma Yara ma suna sallah basai an girma kamar yadda momynsu ta fad'a,"Domin idan sunyi Abbansu da momy za'a sakawa Lada."

"Sun tsorata matuka,suna hada baki sukace zasu dinga yin sallah kullum ka da Allah yasa su wuta bal-bal!!"( _Hattara iyaye mafi yawa bama tilasta yara sallah musamman asuba akwai wata yarinya da nagani tace ita Sam batasan akwai sallar asuba ba!acikin salloli,ko da na bincika Ashe Bata taba ganin sanda iyayenta ke sallar ba,A lokacin tana bacci Kuma idan an tasheta ba za'ace tayi ba,Mu sani ana koyawa yara sallah tun suna kanana domin ta shiga Jikinsu sosai basai sun GIRMA ba!"Shi Icce tun yana danye ake tankwara shi )

"Bayan mun shirya tsaf nasa atamfata Riga da zane da hijab masu dama saboda yau ne shigar farko da zanyi Dolene Nima in kure wanka,"Kar araina Ni naji ance Yan jami'a akwai wankan,"Hijabina sabo Shima na zuba Mai yalwataccen girma,daga cikin turaren da malam yunus ya kawo min na bude daya arebian ne jamylah na saka Ni da yaran sunyi kyau sosai acikin uniforms dinsu black and blue,"sannan muka fito falon suna rike da school bag din su."

"Anty Jalila muka Fara Cin karou da ita wanda tun jiya Bayan shigowarmu Ni da Yaya ban sake daurata a idona ba! afalon take tana kokarin shigowa Dakin mu, tashin ta kenan Daga bacci tana idar da sallah komawa takeyi bacci sai yanzu ta fito.."murmushin Jin dadi tayi da ta gansu tsaf!!Tare da sauke ajiyar zuciya."ta kalleni tace, Nadiya kice har kun shirya gaskiya kinyi kokarin Shirin su day wuya!.....kullum fa sai sunyi latti akan kafin na shirya su lokaci ya kure!"Tunanin ma nake yanda zan shirya su yanzun!!"

"Mufeed oya jeka Kichen ka dauko basket din KU...Anty Jalila tace.."

"Mamaki abin ya bani yadda ko gaishe da maman nasu basuyi ba,Ni kadai na gaida ita Kuma Bata damu ba!"( _Zamu ga yara da dama basa gaida iyayensu,wasu har baki suka Gani baza su gaishe da bakin ba,Sai dai suji ana fira su sakou bakinsu su amshe zancen!"Wai anan iyayen suna dubin abin duk yarinta ce, ba za'a tilasta yara ba akoyarda su gaisuwa,"Iyaye na ganin idan sun GIRMA zasu daina................,_)

"Mufeed ne ya dawo falon hannunsa dauke da basket biyu ya ba Mufeeda nata."Ya CE momy yau waina mukeso..."

"Ni bana son waina doya da kwai Abba zai saya min..."

"Nidai waina..mufeed yace Yana ma Mufeeda dariya."

"Mufeeda Tace mumy Ni bana so tana kokarin kuka!"

"Zo Nan kiji."Mufeeda taje wurin da momyn take zaune...ta wani hade fuska..."Tace Kinga Mufeeda duk abinda kikeso ki gayawa Abba zai saya maki kibar Mufeed Baya Jin magana.."Doya kike so ko!!"

"Eh,mumy da Indomie ko Zaki dafa Mana..!?"

"Kin jiki da rigama Mufeeda wane indomie Kuma Ana zaune kalau,Kinsan ban samun lokacin dafa maku abincin zuwa makaranta."Wa yayi min bacci wa ya shirya min ku,Mufeeda Tunda aka sakaku amakaranta ban Kara samun nutsuwa ba!"Ni wallahi na k'osa ayi maku hutun Nan ko na ji sarari Ina lokacin dafa indomie gareni idan ita kikeso ki gayawa Abba kubiyata teburin Mai shayi sai asoya maki kinji Yar mama"Inji Anty jalila tana ma mufeeda cakulkuli
"Kyalkyala Dariya Mufeeda keyi tana momy...."

"Nidai sai saurare da Kallo NE aiki na Ina gefe zaune..."

"Yaya Saddiq ne ya shigo ga alamu ya shirya Dan har jakar zuwa aiki ya ratayo a kafadarsa yayi kyau sosai..."A hankali na gaida shi ya Kuma amsa min fuska asake...Yana mamakin yau anyi saurin shirya yaran ko ba'a fada ba yasan nice Dan gimbiyar bata dade da fitowa ba."

"Kayan shayi Anty Jalila ta hada daman akwai ruwan zafi!"Tea ta hadawa Yaya da yaran Ni Kuma tace na hadawa kaina ita Kuma dakinta ta nufa Domin tashin ta kenan Daga bacci!"Haka muka Sha sayin da biredi...Ina mamakin Anty Jalila duk da ban waye ba Amma dai nasan a karin safe ana cin Doya da kwai..Wanda na gani zube acikin Kichen dinta Wasu har sun Fara lalacewar Musamman dankalin turawa harda hunhuna "ko indomie katin katin nagani jere ga yaranta naso amma saboda tsabar son jikin tsiya da lalaci bazata iya girkawa ba!"Nace araina saboda koni dai bakuwa Ina son na lasa,"

"Haka muka gama Karin muka fita,Anty Jalila fitowa tayi tana Mana Allah ya kiyaye!"Sai mun dawo...Domin ta k'osa mu wuce ta tafi zuwa bacci!"

"Yaya tambayata yayi na dauko duk takarduna?"

"Eh,na amsa masa saboda komai nawa Yana acikin jikata tana GIRMA..

"Sai da muka fara biyawa aka sayawa yaran abinci da yake akwai biscuits da drinks acikin school bags dinsu sai suka had'a..."Daga nan Hanan Academy muka nufa da ke kan titin Ali bagodu...Aka sauke su a makaranta.."Sai hannu suke min suna cewa.....bye-bye Anty,ahakan muka rabu nima Ina murmushi,Yaya cewa yayi na dawo gaba,saboda daman Mufeed ne agaban.."Ni da Mufeeda abayan."Nan na dawo gaban muka wuce,"

"Tunda muka dauki hanya Yaya Saddiq ke min nasiha akan nayi karatu sosai kada nasa wasa Kuma kada na kuskura ya ganni da abokai barkatai."Ya CE in Sami qawa d'aya wacce na yaba da hankalin ta da kamun kanta kuma wacce ke karatu sosai."Sannan ya Kara da cewa zai samu dalibi daya namiji Mai hankali ya hadani shi ya dinga koya Mana karatu muna group Assignment."Haka dai Yaya Saddiq ya dinga min Bayanin komai yadda zangane...."Zuciyata Bata Kara tsinkewa sai da muka shigo get din makarantar."

"Ba laifi makarantar tana da kyau Inda aka rubuta admin da manyan bakake can muka nufa parking place yaya ya nufa ya tsaya."

"Bayan mun fito Mota,Inda office dinsu Yaya yake muka nufa."Bayan mun shiga office din nasa."Mai tsari, wasu Takardu ya d'auko acikin file."Sannan muka fito Nan ya dinga gaisawa da Yan uwansa malammai da muke haduwa da su Nima Gaida su nake ba Dan nasansu ba."Da muka fito harabar makarantar muka nufa Ina bayansa, Dalibai sai gaida shi suke..."Nima fa na zama Abin Kallo awurin su irin yadda muke tafiya da Yaya Saddiq."Gwanin burgewa Ina Jin Wasu na gulmar mu..Wasu na fad'in ai matar mallam ce,ko budurwa sa ce, can wani yace ko dai kanwarsa ba! Ina jinsu saboda shi Yaya waya yakeyi Tunda muka fito Admin din."Nidai komai banayi sai aikin kallon makaranta..."
"Bayan Yaya ya kammala wayarsa, magana yayi min Amma Ni nayi nisa wurin kallon 'ya'yan duniya Wasu da shigar mutunci maza da Mata wasun ko tamkar mahaukata idan Naga wasun Kuma kamar ba yaran Mallam bahaushe ba."Kabilun ma sun fisu shigar mutunci."Wani nayi murmushi wanin Kuma nayi tsaki,"
"Ke hankalinki na Ina!?"Inji Yaya."
"Sunkuyar da kaina nayi cike da kunya...Ya ce ga to ga faculty DINKU Nan."Eng/Sos aka baki Adm.no gata nan 22741/18/Sk."karbi wannan Takardun komai naki na aciki computer form da clearance Duka."

"Amsa nayi da girmamawa Nace to Yaya nagode,"Is okay!yaya yace atak'aice Yana Cigaba da Danna wayarsa tare da dubin agogon da ke daure a tsintsiyar hannunsa.."

"Wani matashi ne...ya iso wurin mu cike da ladabi.."ya gaida Yaya tare da musabaha atsakanin su."

"Nima gaisawa mukayi da shi....Nan Yaya Saddiq yace'' Naseer ga kanwata nan Nadiya da nayi maka bayanin zata zo."A kula sosai kamar yadda nayi maka Bayani."
Chapter 8 · 0% Book details