← Book details Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 65

Sashe 18

Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" saboda ya lura a Yan kwanakin nan na kara wayewa a kwayar idona da kuma yanayi na ya fahimci hakan."Amma azuciyarsa cewa yayi zai yiwa tufkar hanci."Mota ya shiga mukayi sallama da su ya wuce."

"Ajiyar zuciya na sauke saboda yadda Naga Yaya ya canja min na tsorata sosai."Hanyar hostel nayi,A hanya sai gaisawa nake da masu kaunar min magana,saboda Ni ban damu da kowa ba!" Ina tafiya Ina zancen zuci har na Isa Dakin namu."

"Fira sukeyi...Amma da na shiga Dakin sai shiru ya biyo baya..kamar da wata akasa."Littafaina na dauko Ina Dubawa."Nan suka canja fira ban dai koma ta kansu ba,Duk da ayanzu Ina shiga cikinsu muyi fira tare muna cin abinci tare kuma har dinkuna sun fara yimin Ni da su har wani suna naji ake Kiran mu da shi Wai 4Stars,A yanzun dai zance nasamu canji sosai na sutura da hijabai da takalma har akwati Mai Taya sun saya min Yanzu dai Nima Ina Jan wankana Kuma Duk abinda na saka ajikina Yana amsana sosai."Nan take na Kara kyau da haske ba laifi sai dai har Yanzu bana fita Daga cikin makaranta Kuma ban daina karatu na ba,sannan ko sun bani Kudi bana karba,Sutura da abinci dai Ina amfani da su Kuma muna mutunci sosai da su tun ranar da sukayi min taron dangi wurin bani Shawara da mafita."Sai dai banaji araina zan iya yin watsi da *TARBIYYAR* da iyayena suka bani akan Abin duniya."

"Bayan na gama karatu abinci mukaci sannan na fita sallar magrib sai da nayi isha na dawo."Sabon karatu nake saboda gobe Litinin muna da gwajin EDU 113."

"Jin Naddy ta katse kiranta da sauri yasa taji haushi da takaicin Domin tasan nata ne sila wato(Yaya Saddiq) mamaki sosai takeyi ko dai baya son alaqarta da kanwarsa,Yana Mata wulaqanci! shin me mutumen Nan ke nufi!?"Ko Naddy CE ta katse Kiran!?"Shin Yanzu shi Bai fahimci cewa na fad'a sonsa ba!?"Kullum ina kiransa Domin in gaida shi but ya kasa fahimta ta!?"Cap lalle akwai aiki agabana saboda Ni kam Duk duniya ba Wanda zai iya rabani da Yaya Saddiq dina."Da nakeso da kauna Wanda cutar Sonsa ta hanani watayawa."Tabbas na dauki damara kuma na shirya fad'a da kowaye akansa,dole NE ya so ni kodai Domin kissata da kisisinata nayi alqawarin sai na sanya soyayyarta abirnin zuciyarsa."Duk wannan zancen zucin mansurah ce ke yinsa Wacce Abin duniya ya taro akanta yayi Mata katutu azucia."A karshe tunanin mafita take sai zarya take a Dakin su."

"Ko da suka koma gida sun Sami Anty Jalila tana kallon Zee world Inda ake series dinnan Amma."

"Tayi zurfi wurin kallon ko Jin Kira batayi..."

"Yaran da murna sukazo gareta suna nuna Mata kayan da aka basu Amma cewa tayi tagani suje su Sha Batare da ta ko kalle su bare Abbansu."T.v ya kalla kana ya dubeta tsaki yayi ya wuce abinsa."

"Takaici NE fal azuciyarsa ace macce takai macce amma batasan yadda zata Kula da mijinta da yaranta saboda dakarchi da lalachi...."Allah wadai yake da rayuwar matarsa saboda wani bangare na rayuwarta Sam baiyi ba!"Wanda basai an fad'a Masa ba!"Yasan abinda ya shuka NE yake girba!Saboda ya san gidan da ya dauko ta!"Ba *TARBIYYA* ne da su ba!"Bare ta koya!"Bariki da kyaunta ne ya rudesa har ya aurota, Ashe tuni yayi zaben tumun dare!"Bai ankare ba sai Yanzu..."Da Dana sani ya fad'a toilet yayi wanka ya fito ya shirya."Falon ya dawo ya zauna."

"Kallonta yayi Tama gyara sabon Zama tana kallon wani sabon series da suka sa married again."Wanda Shakka bayayi magrip da Isha na Nan kanta batayi ba!"Saboda sai zata kwanta take ramakon sallolin."Ya lura duk lokacin sallar magrip da Isha Jalila batayin su saboda sannan NE ake saka Sabon series."

"Yaran ya kalla da sukayi bacci Duk sun hargitsa falon da ledojin minti da biscuits."Ko kayan jikinsu basu cire ba!"

"Jalila....ya Kira sunanta."

"Ehyeeeeh....Tace tana kallonta "

"Idan kin dafa abinci ki kawo min..yace ahasale!"saboda ya fahimci hankalinta baya gareshi."

"Habibi ban dafa komai ba!"Naga yaran basa Nan Kuma Kai kanaci awaje Nima tea da biredi nagama Sha yanzun Nan kagama cup ..Tace tare da nuna Masa saman stool dinda ke gabanta..."

"Tsaki yayi Akan haushi baice komai ba! tashi tsaye yayi tare da nunata!"Ya ce''Nagaji da iskancin ki jalilah wai ke wace irin macce ce da batasan ya kamata ba!"Me Kika daukeni!?"Ya dace ace zuwa Yanzu na huta saboda akwai yara!"Idan da can mu kadai ne zan iya hakuri!" Amma Banda Yanzu Kisani dole kiyi girki bazan lamunci Zama da yunwa ba nida yara ga abinci agida."Shi kenan Ni kullum ahanyar restaurant kamar tuzuru!!"to Nagaji Kuma ba Inda zan Kara zuwa sayen abinci Bayan komai akwai agidana."ki Duba kiga yaranki sun kwanta da yunwa!"Wallahi sai hakkinmu ya kamaki!"Ke kice Daga bacci sai Kallo kamar ibada Kiji tsoron Allah ki daina barin Jin dadin dunia na hanaki aikin lada."Kuma Daga yau abinci wajibi ne agidana..."Ya karashe zancen tare da wucewa daki ya banko kofar azuciye!" gado ya fad'a ransa abace Yana neman mafita da abinyi!!!"

"Ko agefen zaninta Bata ji shi ba!" Domin da Harara ta bishi!"Tare da tsaki saboda surutunsa ya hanata jin me ake."Sai da tagama kalonta tsaf...sannan ta kwashe yaran ta Kai Dakin su..."Haka Nan ta shinfide su da sabbin kayan nasu ajiki." ta wuce Abinta( _Ni Kuma nace ko addu'a bazata shafa masu ba!saboda neman tsari Daga shaitanun aljannu,Hattara iyaye masu halin Jalila,musani addu a wa yaranmu babban makami ce agaresu_)

"Da kyar ta Isa Dakin su Bata tsaya komai ba ta fad'a gadon tana wash!"Alamar ta gaji da Zaman, ga hamma da tabiyo baya sai jerawa takeyi saboda yunwa Nan ta kwanta bacci Abinta Batare da tunanin komai aranta ba!."( _Ni Kuma tunanin sallolin da ake bin Jalila nake Anya ko ta rankasu fans!?"Tabbas Mata da yawa Kallo na hanasu sallah acikin lokacin ta musamman series din nan da ake sawa time din sallah,Ya kamata muji tsoron Allah mu dinga ajiye komai alokacin ibada har sai mun kammala IDAN KUNNE YAJI......_ )

"Zaune suke suna fira da Rabin ransa!"Sai dariya da shewa sukeyi cike da kaunar JUNA!"

"Kallonsa tayi tace yaushe zamuje duba bawan Allah nan nasan dai Yanzu ya dawo."Inji mom tare da kafe sa da idonta masu saurin Kama zaren zance."

"Gabansa ya Fadi!"Ya kalleta tsaf shi take Kallo..."Murmushi yayi yace mom sai..sai....ki saka ra...rana muje mugani idan sun dawo!"Jawad yace cike da inda-inda na rashin gaskiyar Nan!"

"To na saka Rana,gobe zamuje ka shirya da yamma."mum tace."

"To,Allah ya kaimu tare da tashi..."Ya ce"Zanje na kwantar mom..sai da safe."

"Allah ya kaimu...My son mom Tace tana Murmushi cike da kaunar danta."

"Yana shiga Dakinsa wayar Saif yake Kira sai dai akashe!!"Ya rasa me Zaiyi!"Saboda shikam Yanzu baisan meye mafita ba!"

*'YAR MUTAN DIKKAWA CE*[2/18, 7:25 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲

*NA*
*NABEELA DIKKO*

*PEN WRITERS ASSOCIATION*

*SHAFI NA 12*

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_

____________________________________

"Da Misalin karfe shidda na yamma ranar litinin yayi min ne. Abakin kofar hostel dinmu."Idona duk sun kumbura!" Su Eshaa ne suka taimaka min na kwashe kayana!..."Nayi bankwana da makotan Dakin mu nagaya masu zan koma cikin gari da Zama!."Muna nan tsaye muka hango motar Yaya Saddiq na tahowa wajenmu..."Nan take Deeyart ta juya baya suka Esha da Deeja suka bita!"A gurguje mukayi sallama da su suka bace Daga gurina!"da zummar zamu hadu gobe!"

"Wurinsa na karasa na dinga zuba kayana but da yake ya bude Amma Yana Daga cikin motar..."Bayan nasa na shiga motar tare da gaida shi."

"Amsawa yayi batare da ya dubeni ba!"sannan muka wuce."

"Mun dauki lokaci muna Tafiya babu abinda ke tashi sai sautin karatun sheik Ahmad suleiman...Inda yake karanta Amanarrasulu..."Da kuma sheshsheqar Kukana da ke tashi...ko ci kanki Yaya Saddiq baice min ba!"

"Yau dai mom ta tusa kewar saif da Jawad agaba sai gidan Mallam Balarabe domin taje Duba lafiyrsa."

"Da yake sun kirashi awaya kafin su zo shiyasa suke da Tabbas akan Baba Yana gidan Kuma sun samu bakin zaren."

"Da Sallama suka shiga gidan,Dukkansu."

"Amsa masu Innarei tayi tana maraba da su."

"Tabarma ta shimfada masu tare da kawo masu ruwan leda da Baba ya sayo masu kafin ya shigo."Ta ajiye fuska asake tana maraba da Mom."

"Momy ta yaba da halin mutanen duk da Kasancewar su talakawa Amma suna da halin GIRMA."

"Musayar Gaisuwa sukayi.."Da mom da su Baba."

"Nan mom Tace"Baba ya gida ya karfin jiki."Da fatan kasamu lafiya."

"Lafiya qlaw Hajiya jiki da sauki ay naji dama sosai!" Yaran Nan suna kokari sosai...Allah dai yayi albarka."

"Ameen...innerie."Tace tana Murmushi."

Jawad da Saif kallon JUNA sukayi...Tare da yake na Jin Dadi domin sun sami mafita..."Dayake shi malam Balarabe kwanakin baya yayi maleria har ya sanarda su Jawad Lokacin da sukazo gaida shi."Shiyasa ya dauki shine suka sanarda mom tazo masa ya jikin."

"Mom taji dadin zantukan Baba"Ta CE Ba komai Baba yiwa Kaine domin azatonta ko wani dattijo ne mai shekaru." batasan cewa wahala da rashin hutu tare da cutar talauci ne ya tsofar da Mallam Balarabe tun Wuri."

"Innerei Tace Hajiya ayni nasamu yarana masu son mu,Su jawad kaam Akwai mutunci."

"Raaas gaban mom ya Fadi domin Innerie CE,mutum ta FARKO da ta ambaci mutunci tattare da su Jawad."

"Mom mamaki take yadda su Jawad suka canja suka koma kalar kirki tun Daga shigarsu gidan har kawowa yanzu...Ba suyi wani abin rashin mutuncin ba!"Ko meye sila!?"Amma dai Akwai wata akasa Tunda har taga sun Sanya sutura ta mutunci,Wato Kaftan da hula..."Abinda Bata taba ganin sun sanya ba!"

"Jawad ne ya dawo da mom Daga duniyar tunanin da take."Ya ce mom mu wuce Koh!?"

''Dariya tayi tace"To mutafi Baba Allah Kara sauki Kudi ta mike masa 10k Daman sun shigo da manyan ledojin kayan fruits ahannunsu sun ajiye."Tace aci da Hakuri Allah ya baka lafiya ya tsare gaba!"

"Ameen,Baba yace Yana ta jera GODIYA da fatan Alheri wa mom da yaranta."

" Saif yace to Baba sai mun dawo fira jibi."Yana Dariya

"Malam Balarabe yace yawwa saifullahi sai na ganku fa Hajiya angode Allah ya saka da alkhairi,Muhammad sai kunzo cewa da Jawad."."

"Ameen..mom Tace."

"Jawad yace Baba sai mun dawo,"

"Innarei tace gaskiya kuna kokari mun gode ay ba Haka ake ba!"Gashi 'yarta ki tana makaranta har yau ba ta dawo ba."
Chapter 18 · 0% Book details