← Book details Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 65

Sashe 33

Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tana shiga bedroom din Ni kuma na fito da kayana dana boye Bayan labulai..."Ja in ja nake da akwatina da bakkona..."Sauri-sauri gudu-gudu nake Tafiya zuciya ta na bugawa..."Cikin Sa'a na fito get din gidan gashi Mai gadin shima baya nan Yana masallaci Aykuwa da sauri na qarasa Titin Estate din..."Nan nasamu Napep ta kawo wata Mata da sauri na shiga nace Masa Shehu shagari Zai kaini..."Sai da muka fita estate din naji wani sanyi da nutsuwa..."Wayata na fito da ita tare da dannawa Esha Kira..."Nace su fito bakin get din hostel gani Nan zuwa yanzun...."

"Bayan an kammala sallar magrip kamar kullum Tsayawa sukeyi a masallacin Ana gaisawa atsakanin su makota..."Yau ma hakan CE Tafaru Shiyasa ya dan jima Bai koma gida ba!"

"Mai gadi ya Kama hanyar gidan..."A bakin kofa ya samu Hajiya jalilah da mamanta da kanwarta tsaye kamar itatuwa.."

"Mudi yace"Ah Hajiya sannunku an dawo...Ay gidan abude Yake ku shiga Mana Daga ciki oga yana masallaci.."

"Harara Rasheeda ta watsa Masa tare da cewa BA ZAMU shiga ba!"

"Tsaki Hajiya tayi tare da Duba agogon wayarta.."Tace"Shi kuma Tahir ya jima Bai zo ba, ko me ya tsaya oho?"

"Mama kin san lokacin magrip yayi Ina ga Shiyasa basu karaso da Wuri ba!"Inji Rasheeda tana tauna chewing gum tare da Danna wayarta..."

"Mudi asawaki KAWAI Yake Yana hararen su ta gefen ido...Aransa yaji haushin dawowar Hajiya wato Jalila..tun Wuri hakan..."

"Juyawa yayi da yanayin ko in kula.. "Ya ce to akawo maku benci? Naga Hajiya zaune kasa Yana nuna Jalila da abinda duniya ya dameta,wanda ya hanata magana..."Ya Koma cewa"Kunsan ban iya hakurin barin Hajiyarmu zaune ga banza!"

"Kai bama buqata munafuki! in Banda iskanci akace maka mun gaji NE!?ko Dole NE zaman!?"Ita Jalila tagaya maka tagaji NE!?Hajiya Tace cikin masifa!"

"Ya numfasa kenan domin ya fesowa Hajiya Amsa, sai dai Jiniyar motar Yan sandan da yaji tana shigowa estate din ne tayi sanadin katse Masa hanzari...."Cike da mamaki ya fito da Ido!abinda Bai taba faruwa ba acikin Estate din Jiniyar Yan sanda sai dai su jiyo a waje...."

"Bai qara mamaki ba sai lokacin da yaga motar tana qarasowa wurin su tana tada kura!ay da gudunsa ya shige gidan tare da rufe get din..."Saboda tsoro!"Yana mamaki abinda Yan sanda suka zo yi akofar gidan..Yana cewa Hajiya kuyi ta kanku tiyagas!!!"Tuni yaran da suka dawo masallaci harda matasa sukayi tsaye suna kallon Hajiya da ke faman baiwa Yan sanda Labari harda na karya da kazafi!"

"Tun Daga nesa ya hango mutane akofar Gidansa..Bai Kara tabbatar wa sai da ya qarasou..."Yan sanda ne da motarsu ya hango..."Sakin hannun Mufeed yayi tare da dafe kansa da ya Sara yayinda ya hango Yan Gidansu Jalila atsaye kofar gidan..."

"Jiki a mace ya iso..tare da masu Sallama.."

"Hajiya Ina wuni yace muryarsa asanyaye..."

"Tsaki Hajiya tayi tare da dauke Kai!"

"Tahir da Rasheeda, Sai hararen shi sukeyi..."

"Tahir ya CE"Yawwa officer Gashi Nan tare da nuna Saddiq.."

"Mufeed wurin momynsa yaje Yana surutu wacce Kuka kawai takeyi..."Suka Rungume juna..."

"I.D card Officer Bashir ya nunawa Saddiq tare da cewa Daman sun kawo karar Kane ka daki Yar uwarsu harda jimata ciwo!"Hakane Kaine kayi Mata dukan har da targade!?"

"Cike da sanyin murya da kunyar jama'ar da ke wurin suna SAURAREN su, yace"Eh.. yallabai na daketa Amma bansan da targaden ba!"Inji Saddiq

"Good"Officer yace, tare da cewa ka shige Mota..zamuje Office da Kai akwai sauran jawabi..."

"Yallabai a kashe maganar Nan anan, Dan Allah ba sai munje ko'ina ba!"

"Wallahi sai ka kwana acell anki akashe matsiyaci Dan ba jaka na Haifa ba! ...Inji Hajiya.."

********* "Murmushi yayi Wanda yafi Kuka!ciwo yau shi ne matsiyaci Bayan goma na Arziki da ya ke masu.

Ya dubi Dan sanda ya ce "ba damuwa yallabai Zan bi ku amma Ina son kabani dama in gayawa kanwata abinda ke faruwa shima yarona ya shiga gida kafin mutafi...."

"Yallabai harda yarinyar da yake magana akai ya kamata afitou da ita domin ba kanwarsa bace Yar iska CE!ya ajiye agidan!"Akanta ne ma ya daki yayata harda saki! Kuma ita CE silar lamarin... Rasheeda Tace da masifa!"

"Duk da abin ya yi Masa zafi!Amma ya kasa magana saboda Yana son adaina maganar a INDA ake masa kallon mai mutunci, Duk da ko yanzu girma ya Fadi!"

"Officer yace wa saura Yan sandan biyu...KU bishi afito da kowa da ke gidan..."Sara Masa sukayi tare da bin Saddiq din..."Sai da yayi magana sannan Mai gadin ya bude get atsorace,shiga Saddiq da police din."Tuni Mai gadi ya shige Dakinsa ya boye!"Kar kaftu ta kafto shi.''

********** "A hankali ya bud'e Idonsa da suka yimasa nauyi tare da karewa Dakin nasa kallon..."

"Hannunsa yaji a hade da na abokinsa, ya kalle shi acikin yanayin irin na ciwo da damuwa.."

"Yace saif meyake faruwa da Ni!?"

"Jawad...Baka jin Dadi NE!Yanzu ya kake jin jikin naka!?" yace Cikin damuwa.

"Hmnnnn..Saif kenan kafi kowa sani damuwata ai Dole na kamu da cuta!Saboda Naga Zan cuci Kaina da kaina!A gaskiya nayi Dana sanin Wannan mataki da zan dauka!"tayaya ma zan auri makiyiyata!?"wai Wacce nafi tsana adunia.."Sai naji sam bana son ganinta bare mu zAuna agida daya...da ace na d'auki mummunan mataki a kanta da yanzu komai ya wuce Amma yanzu idan na aureta ai ko Bayan rabuwar mu Kai da ma ace ta mutu labari zai Cigaba da Tafiya ta tab'a Zama matata!Ni Kuma Bana son a dangantani da Wacce ta kirani marar tarbiyya,maccen da ta zabga min mari har uku."Tashi yayi tare da jingina bayansa jikin gadon...Ya qara da cewa Inda na sani tun farko maganinta Zan sa Yan ta'adda suyi!"ko Kuma nasa ayi Mata dukan tsiyah a karyata a halakata!"A nakasa Mata rayuwa!Ka ga Zan debe haushinta Da yanzu ba ni da mugun tabonta a Rain.."Amma yanzu idan na aureta Saif,ai ta kwareni.

"Gyara zamansa yayi tare da fuskantar Jawad, yace Wannan ba mafita bace!"Ka daina Tunani irin Wannan karfa ka manta da abinda Ta kiraka!"Ay ka aureta ka gasata Kai Mata azaba shine fansa Daga Nan zata koyi sawa bakinta linzami idan zatayi furuci!" Sannan akarshe ka sata Dole sai ta koyar da Kai *TARBIYYAR* saboda Kai ba Mai ita ba NE..."Kamar yadda ta fad'a,Itama za'a kirata bazawara."Kaga anan ka gasata!Kuma ka lalata Mata rayuwa,

"Zan iya sata tayi min hakan ko da ban aureta ba..!

"Tayaya!?"ya tambaya

"Ta hanyar SA asato min ita,Zan iya boyeta sai lokacin da naso na fito da ita Kuma masara idan taji wuta ita ke nunawa."

"Ka daina Wannan zancen abokina ai mafita daya CE ka auri Nadiya domin huce haushinta..."Saif yace Yana kallon Jawad.."

"Numfashi ya sauke tare da furzou iska abakinsa yace "Shi kenan Saif na gamsu Kuma na amince.."

"yace"Yawwa Dan Allah ka cire Wannan aranka kaga mom ta damu da rashin lafiyar Nan naka"Ka manta da komai.."

"Yanzu Ina momyn!?"

"Tana sashenta Bari ka ci abinci kasha magani sai muje kadan motsa jikinka...Ba tama Jima da fita ba!Ba ka ganta ba!"Duk ta damu sai da na lallabata nace damuwar rashin Abbu ne ranka, Saboda lokacin aurenka ya zo bashi a duniya.."

"Allah SARKI Mamana Jawad yace afili..A ransa Kuma tunanin irin kaunar da mahaifiyarsa ke Masa yake..."Allah dai yasa ya Gama da momynsa lafiya shine burinsa..''

*********"Yana gaba 'yan sandan na bayansa bakin falon suka tsaya tare da cewa ka fito da kowa a gidan idan ba haka zamu shigo da Kan mu..."Baice komai ba ya shiga Daga ciki...Mufeeda ya samu zaune tana Kuka!"

"Ke Kuma me akai Miki!?"Ya tambayata

"Da gudu ta isa wurinsa Tace"Abba tsoro nikeji Ni kadai CE agidan.."

"Ke kadai Ina Nadiya!?"

"Nima ban ganta ba!tun dazu fah nake nemanta na Duba banganta harda Kayanta ta kwashe!"

"Diiiif...ya dauke wuta!Ana wata ga wata kenan!To Ina Nadiya ta tafi!?"Kenan ta gudu!?"

"Abba ko ka ganta a waje?Mufeeda ta tambaya!?"

"A'ah...Bari na Duba da Kaina Mufeeda wakil shirmen ki NE..."Nan Saddiq ya rawaye gidan kaf ba Nadiya ba ko tsinken ta..."

"Jikinsa a sanyaye ya janyo Hannun Mufeeda tare da rufo gidan...Ko kallon yan sandan baiyi ba!"Ya wuce suka biyo shi baya.."

"Inda Mai gadi ya tsaya "Bacin ransa ya bayyana ran maza ya baci...Fuska turmuqe yace"Mudi zanje in dawo ka kula da gidan..."

"Angama Mai gida Allah ya tsare ka ya kareka Daga sharrin mahassada.."

"AMIN yace agajarce..Ya fara Tafiya tsam ya tsaya tare da waigowa..Mudi."

"Na'am yallabai yace tare da qarasowa da gudu."

"Ko kaga fitan Nadiya daga gidan Nan!?"

"Gaskiya yallabai Banga malama Nadiya ba.."

"Okay..saina dawo Saddiq yace suka wuce.."

"Adawo lafiya Mai gida, ba dai mutum ko Aljan ba!"Wallahi Tama zaka dawo gidan Nan mu Cigaba da zaman mu,Allah ya rabamu da sharrin bakar shiga.."Inji mudi

"Inda suke tsaye har yanzu suna Nan.."

"Officer yace Kai sajaan..Ku wai..wad'an me irin shashashai NE kunje kunyi zamanku kamar Kun bar itatuwa a waje!"

Fad'a masu yallabai....Inji Tahir

"Sara Masa sukayi tare da cewa sorry sir!"

Saddiq yace yallabai motarku bazata ishemu ba har yarana Ina ga bara na Dauko tawa Muje ko?

Ba damuwa go ahead.inji officer

"Nan Saddiq ya KOMA Cikin gidan ya fito da motarsa,Mufeed da Mufeeda ya dauka amotarsa...Su kuma Hajiya da Jalila da Rasheeda amotar police suka shiga Tahir da Yan sandan biyu abayan motar.."Saddiq NE agaba police na binsa Abaya sai jiniya ke tashi..."Wasu zafafan Hawaye suka zubo Masa yanzu shine police suka Taso gaba!"Lalle ya hadou da irin wahala!"Jalila ba Alheri bace arayuwarsa,Silarta ya shiga wata rayuwa..."Ga tarin kunyar mutane da dama masu ganin girmansa a kansa.."Wannan kazafi da tonon silili da Hajiyar su Jalila tayi Masa..A gaban idon makotansa da Yara..."

"Maganar Mufeeda ta dawo da shi hayyacinsa...Abba Ina zamuje Naga Yan sanda na bin mu Kama mu ZASUYI?"

"Mufeed yace Abba Ni tsoronsu..nakeji,kuma mummy Tace min ka zasu Kama su dakeka kamar yadda ka daketa!"Da gaskiya ne?

"Kuyi shiru bana son surutu.. Saddiq yace ahasale wayarsa ya dauko tare da Kiran layin abokinsa Ali.."

"Cikin Sa'a Ali ya Daga Nan yayi Masa bayani tare da cewa yasa me shi a station din.."

"Rai ba Dadi Ali yace to Yana zuwa.."Da Yake Yana cikin unguwar juya akalar motarsa yayi zuwa police station din."

"A Mota Hajiya Atika sai zagin Saddiq take tare da fadin karerayi domin Officer yaji ya Basu gaskiya.."
Chapter 33 · 0% Book details