← Book details Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 65

Sashe 27

Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Saddiq bafa inda zakaje!!"Na gaya maka!fita tare da ita tamkar fitar numfashi na ne!!"Wallahi bazan barka ba! Macuci kawai!!"Wato in barka akara cin amanata agama da rayuwata!!"Hmnnnn tace tare da riqe kugu da cimuimuye masa wuyan rigar da ta yage!!"Tace waini zakuci amana!!"Harda zancen aure bana da labari! To ni ai gwara ka sakeni!!" sai ka aureta amma kasani amanata baza barku ba har abada!!!"

"Da karfi ya kwace kansa daga jalila!"Yace mtwsss!!!kin haukace!!"Ke Nadiya mutafi...Tafiya nafarayi...Banyi aune ba!sai jin saukar sandar humtiyata da nayi akaina wanda Anty jalila ta ratsa min..."Tuni na fadi wurin somammiya!!"

"Tana huci tace idan na kasheta zaka san sonka ne silar haukata!!"Kuma kishinka zai iya SA na aikata!komai

"Jalilah!ya fada da karfi!"tare da duban Nadiya akasa ba rai!"Ganin hakan Ya sanya jikin su Anty talatu da rasheeda rawa da faduwar gaba!!"Amma Anty jalila ko ajikinta fatan ta yarinyar nan ta mutu ita kuma zata iya jure zaman gidan kasou har karshen rayuwarta!!"

"Yaran kuka sukeyi suna kallon iyayen su....Amma jalila hawayen farin ciki take!!"Kallonta yayi yace kibi yan uwanki sai na nemeki "sannan ki saurari sammaci!!"

"Wallahi ba inda zanje ina gidan nan...Ba'a haifi wata da zan bar gidan nan akanta ba!"Babu ta aduniya ni da kai mutu ka raba takalmin dan kaza!!Ayi arziki tare da ni aci da wata banza...wannan mafarki ne!!!"Jalila ta qarashe zancen tana surfa masifa!!"

"Hannun yaran sa yaja zuwa mota!"tare da kinkimar Nadiya wacce tuni numfashi ya dauke!" da sauri ya ajiyeta mota yaja zuwa specialist hospital...."Yaran sai kuka sukeyi...." ( _Hattara iyaye mu sani duk abinda mukeyi yaran mu suna fa kallon mu,A matsayin ki na uwa bai dace kina wasu abubuwa akan idon yara ba!Shi yaro baisan dacewa da rashin dacewa ba,Zaki iya manta kin aikata abi sai yaronki ya tunatar da ke ko labarin ya maimaita kansa hairan ko sharran Akiyaye!_)

_A cigaba da zubou min zafafan commets_

*'YAR MUTAN DIKKAWA CE*😍
[2/18, 7:25 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲

*NA*
*NABEELA DIKKO*

*PEN WRITERS ASSOCIATION*

*SHAFI NA 18*

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_

_SADAUKARWA A GAREKU 'YAN UWANA 'YA'YAH MATA NIKAM DAI BAZAN RAINA MATA BA ADUK INDA KUKE ALLAH YA SANYAWA RAYUWAR KU ALBARKA YA KAWO CIGABA MAI DAUREWA ARAYUWAR MU AMEEN._

______________________________________
"Da zarar ka kunno kanka a unguwar sama road, da ke garin sokoto, kunnuwan ka zasuyi arbah da sautin kid'a da ke tashi..."A katafaren gidan Alh.Badamasi Dan canji,Attajirin gaske ne Wanda naira ta zaunawa atafin hannun sa..

"Muryar fasihin mawakin nan KB show ke tashi Wanda ke ta faman wake Hajiya Asabe wato uwar gidan Haji Badamasin wacce dubban jama'a suka zo murnar tayata bukin cika shekaru Hamsin Aduniya..."

"Manyan kujeru ne na Alfarma naji na gani da fad'a aka jera....sai kayan makwalashe da abinci da drinks da aka jera akan ... teburan"Manyan mata ne zaune Cikin shiga ta Alfarma hakan harabar filin gidan Sai chasu yaran na Hajiya Asabe keyi da qawayen su tare da sauran Dangi Yan uwa da Abokan arziki...."

"Mansura sai kwasar shoyki ake Ana karairaya Ana juyi...Cikin shigar material green da white head kusan su shidda ne da Wannan dressing din iri daya sunyi kyau matuka an Kuma matse Cikin dinkin taaam..."

"Hajiya Asabe da kawayenta sai liki suke masu hakan mawakin shima sai azama yake wurin wake uwar gayya Mai Birthday wato Hajiya Asabe Badamasi."

"Mansura rawa take tana juyi!"Juyowar da zatayi idonta yayi tozali da matar da ta tsaya Mata arai!"Wacce ko a mafarki bazata rasa tantance ta ba!"

"A hankali ta dinga fitowa Daga Cikin filin rawar...karaf taji an Kama hannunta...tare da cewa Ina zakije mansura Bayan kinsan kice Mai jagorantar rawar Nan ko zuman naki yazo NE!?..."

"Murmushi tayi tare da dafata tace ko daya.." Ina zuwa Safna yanzun Nan zan dawo Kinga Daman wata Yaya ta na hango zanje mu gaisa da ita ne...."Inji mansura

"Owk...karfa ki makale kin sanki da zuba kamar ruwa...Safna Tace tana dariya."

"Aha Ina zuwa bazan juma ba... Mansura Tace tare da hanzari tabar Safna wurin tana kwasar rawa ummanta nayi mata liki da Yake ita ce autar gidan.."

"Cikin kwarewa da kwarkwasar take Tafiya daki-daki kamar hawainiya da yake takalmanta masu tsini ne SOSAI..."Ga kayan jikinta duk sun matseta..."A Inda take zaune tana kallon duk shagalin da ake..."Abinci take ci tare da motsa baki." mansura....ta nufota Cikin sanyin murya Tace Ina wuni Anty..

"Kamar bazata kalleta baa domin ta hangota tana zuwa wurinta Kuma ita Sam yarinyar Bata burgeta!"Tun haduwar su ta FARKO taji Bata yinta!...sai dai sadda Kai tayi tare da cigaba da Danna wayarta Tace "Lafiya!Ina gajiya agajarce..."

"Yake tayi tare da janyo kujera ta zAuna Sannan Tace Lafiya qlaw Anty,Hmnnnnn
mansura ce faah ko baki gane Ni ba!?"Inji mansura

"Uw... gaskiya ban gane ba!Daga Ina kenan!?"Ta tambaya

"Haba!?"Kinga nikam na ganeki ya gida yasu Mufeeda da Yaya Saddiq!?"

"Duuuumnnnn gabanta ya buga Nan take ta canja sauyin walwalar fuskarta Tace lafiya..."A Dan kufule!!"

"Madallah Daman kinsan su Safna kenan Ay kawata ce tare muke karatu a university...Daga can ne ma na hango ki nace Bari nakawo gaisuwa gurin babbar Anty..."

"Allah sarki..Nako gode...Niema dai Hajiyar su Safna nan Kawar Mamana CE SOSAI mun shigo bukin tare da Yan gidan mu..."Inji Anty Jalila."

"Am Bari na tashi na tafi,Anty Ashe Naddy tana gida na dauka Kuna tare da ita ne ko da Yake ba magana take min ba!ko da ace mun hadu anan ba Amfanin hakan.."

"AshSha!meke faruwa ke kuwa!?"Ba kawarki bace!?"Inji Anty Jalila da mamaki."

"Hmnnnnn Anty kenan Ada can baya Naddy kawata ce amma Banda yanzu domin tafi karfina saboda nikam bana goyon Bayan cin amana Wannan daliline yasa muka ware!..."mansura ta karashe zancen cike da kissa da makirchi."

"Cin Amana kuma ita Nadiya CE taci amanarki!?"Inji Anty Jalila cike da tuhuma."

"Gyara zamanta tayi tare da fuskantar Anty Jalila fuskarta dauke da damuwa...Tace kiyi Hakuri da Abinda Zakiji Daga gareni Anty Amma tsakani da Allah taimakon zanyi domin ki fita Cikin matsala Kuma ki kwatou mijinki Daga shu'umancin Naddy..."

"Fidda ido tayi waje da mamaki Tace wama kike!?Bangane ba!?"Me kike nufi!?"Mijina Kuma!?"

"Mansura sunana....."Hmnnnnn Anty kenan me kike ci nabaka na zuba...Ki saurareni da kyau Kiji." aranar da Kika ganni agidan KU Daga wurin malamin Naddy muke!"Inda yabata kullin mallakar Yaya Saddiq Wanda sanadin hakan ke kuma za'ayi waje da ke!"Ganin hakan Bai Dace ba yasa na nunawa Naddy ta dai aure shi Tunda sun Dade tare da shi Saddiq din Kuma suna son juna Wanda azahiri ita Naddy ce ta mutu Sonsa domin Tasha gaya min."Shiyasa nace Mata zata iya auren Saddiq Ba sai tarabaki da yaranki da mijinki ba!"To fa Daga Fadan gaskiya fa Anty...sai kawai Naddy ta ci mutuncina ta koreni Daga falon! Ina Fitowa na ci karou da Saddiq Kuna dawowa anan shima ya Kara min wani wulaqanci harda nunawa get man Ni Wai kada yaqara barina na shiga gidan..."Saboda daman Saddiq Yasan cewa bana goyon Bayan cin amanarki da sukeyi Bayan ke da zuciya daya kike zaune da su musamman Naddy da Kika dauka tamkar kanwarki!!"

"Daman Ina nemanki na warware maki zare da abawa Kuma na nemi alfarmar ki yafeni na tuba domin wani wa'azi naji akan zuwa neman magani ba kyau,Akan hakan na dauki alqawari aduk Inda na ganki zan Gaya Miki gaskiya Kuma ashirye nake domin na kaiki har Inda mukaje muka amso maganin Nan."Domin a walwale kullin asirin..."Hawayenta da ke Mata zuba ta goge cike da kicihi Tace Anty Jalila na kasa nutsuwa saboda mun cuceki..."Nidai Dan Allah ki yafe min."

"Tamkar mahaukaciya Sabon kamu Haka Anty Jalila ta hargitse duk ta rikece ta tashi tsaye! tana huci sai gumi da ke fetsou Mata ta kowacce kusurwa ta jikinta!!!!"Hawaye ne sharaf a fuskarta Tace yanzu Ni yarinyar Nan zata zalunta!"Ni Jalila za'aci Amana!Wallahi sai tagane shayi ruwa NE yau ba sai gobe ba!zatayi laushi Kuma tabar min gidana...Ina Mata kallon kirki Ashe Yar iska CE! marar mutunci! to da shi har ita zanyi maganin su...."Jikarta ta dauka ta kalli mansura tace Nagode kinji...yanzu ya za'ayi muje gidan Mallam din!?"KOMA muje yanzun nan kinji Dan Allah mansura ki taimakeni!!!"Ni nayafe maki ke Mesona CE.."

"Numfashi ta sauke tare da cewa yanzu yamma tayi sai dai gobe mu hadou na kaiki Anty yanzu dai kibani lambarki sai muyi waya!"Kinsan bazanje gidanki domin gudun wulaqanci!!"

"Karki ji komai mansura Ni yanzu Kaina ya dauki zafi!bansan ya zanyi ba!"wucewa zanyi bazan iya jiran su Hajiya ta ba!"Inji Anty Jalila hankalinta atashe

"Musayar lambobin juna sukayi har Anty Jalila tafara Tafiya mansura ta cimmata Tace Anty ko gobe Ina baki shawara ki daina sakewa kowa ragamar gidanki da amanar mijinki domin yanzu Babu Amana kingani wacce kikewa kallon kirki itace ke kokarin cutar da ke tare da ci Miki Amana sai ki kiyaye gaba..."

"Wasu zafafan Hawaye ta hadiye tare da Girgiza Kai Tace hakane mansura Nagode..."

"Nan SUKA rabou mansura ko farin ciki NE fal aranta domin hakarta ta kusa cimma ruwa hakan ta Koma filin rawa ta Cigaba da rakashewa "itama Anty Jalila da kyar tasamu taxi din zuwa gida sai rusa Kuka takeyi ga bakin kishinta ya motsa Jin takeyi tamkar ta hadiye zuciyarta ta mutunci saboda kunar rai!"A daddafe ta Isa gidanta da ke BAFARAWA ESTATE ta sallami Mai taxi din tana shiga gidan faduwa tayi a tsakar falonta ta dinga Kuka kamar wacce aka aikowa sakon mutuwar iyayenta...A zuciyarta takasa shirya irin bala'i da masifar da zatayi da Saddiq!"agefe Kuma Tasha alwashin halaka Nadiya idan ta shigo gidan..."

"Sautin dariyar su da shewa ke tashi a falon da karar spoons da suke cin abinci a dining place."

"Yanzu dai mom an kawo karshen zancen...Jawad yace Yana murmushi..."

"Wane zance kuwa yazou karshe Bayan an Saba Alqawari..."Ayni kaji abinda na fad'a bazan Kara cewa akawo ta ba..."

"Mom...ki yarda da mu agaskiya Ranar da mukaso kawo maki Nadiya aranar aka Aiko ta koma makaranta."Amma bazata wani Dade ba zata dawo sai akawo ta...Saif yace Yana Cigaba da cin abinci..."

"Lemu mom ta kurba tare da lunshe idanuwanta...Tace to Saif Ni yanzu ai sai Ranar da na ganta..."

"Jawad ya ce''Yanzu dai mom ayi kokari kafin ta dawo atura magabatana agidan su ay komai agama Kinga da ta kammala karatu Shi kenan..."
Chapter 27 · 0% Book details