Sashe 6
Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Mom bana buqatar komai yanzu idan dawo zanci nayi faam,."
"Allah ya dawo min da Kai lafiya son,Akula adinga tuki ahankula....mom tace,
"Ameen."sai na dawo!"
"Hanyar kofar fita ya nufa dai-dai da shigowar Inna Mai aikin gidan..A tsorace ta gaida shi cikin girmamawa ko kallonta baiyi ba ya amsa."
"Komawa Inna tayi da Baya ta bashi hanya ya wuce,sannan ita Kuma ta shigo daga cikin falon jikinta na rawa!"saboda tsoron Jawad,da take! tun ranar da ya sharara mata Mari ya karyewa jikarta Habi kafa!"ta shiga tsoronsa saboda Baya da kirki Ko kadan!!"Da sauri ta qaraso falon,tana gaida Mom tare da Bata Aiken da tayi mata."Amsa mom tayi ba tare da ta kalleta ba!"Inna madafa ta nufa Domin Cigaba da aikinta." Mom ko cigaba da jimamin abinda ya faru da su Jawad take cike da gasgata labarin d'anta( _A matsayinki na uwa ya kamata ace kina iyah banbamce zancen gaskia da karya a bakin yaranki,Ko afuskar SA,Bai kamata ace Duk abinda yara zasu fada ki yarda ba,A gaskiya muna sakaci iyaye sai mun gyara, mu daina karbar zancen yaran mu har sai mun raigaye_)
"Shi Kuma jawad din Yana fita,Hamdala yayi da mom, Bata gane komai na gaskiya a zantukan sa"Domin tuni ya kwarai wurin tsara mom,Duk hanyar da zai daurata akai hakan take hayewa!!"Dariya yayi yana tafawa kansa yadda ya tsara zancen karya ya shimfadawa Mom,Daga nan Gidansu saif ya nufa Domin warware Masa zare da abawa."
*WANENE MUH'D JAWAD.........?*
Ku hakuri da wannan fans banajin dadi!Ina neman AAddu'arku pls!!!!!INA SONKU MASOYANAAH
*'YAR MUTAN DIKKAWA CE😍*
🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲
*NA*
*NABEELA DIKKO*
*PEN WRITERS ASSOCIATION*
*Wannan Shafin kyauta ce,Ga kungiyata Mai albarka,(PEWA)Allah yaqara daukaka mu ya Sanya haske a alqamin mu,ya qarou baseera da kaifin ido,ya Kuma dauramu mu akan turba ta gaskiya Ameen.*
_INA YIWA DUKKAN 'YAN UWANA MARUBUTA FATAN ALKHAIRI A DUK INDA SUKE, ALBARKOKIN ALLAH SU YAWAITA GARESU AMIN._
_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_
*SHAFI NA SHIDA*
_____________________________________
"Tafiyar kimanin awa d'aya da rabi da 'yan mintoci,Ta kaimu sakkwato birnin shehu..."Inda ake ajiye mutane, a nan aka sauke mu.."Duk muka fito kowa ya Kama gabansa,masu Kaya,tsayawa mukayi direban ya sauke Mana kayan mu."
"Nawa kayan na d'auke na ajiye gefe,ina sallama da mutanen da mukayi Dan fira a motar, da yake mata munfi yawa amotar.."Lambar da Baba ya bani ta Mallam Saddiq ce na Ciro acikin jakata.."Mansura wacce muka zauna tare itama tsaye take agefena tana jiran napep."
"Takardar ke hannu na na duba kana na kalleta...."A sanyaye nace Mansura ko da akwai waya hannunki."
"Eh,Ina da waya Nadiya."Ta amsa min
"Yawwa..dan Allah Kinga Lambar Nan ki taimaka ki Kira min ita."
"Ayyah...gashi banida Kati,Kinsan nayita waya amota! Amma Bari naciyo bashin MTN na Kira maki..."INJI Mansura..."
"Ba za ayi Haka ba!"mansura Daman Yaya na ne,zai zou daukana to tunda na taso Babana ya kirashi yace Masa na taso, Domin ni Banda waya, Shine Baba yace idan na iso nan sai naje shagon masu sayarda Kati na biya Kudi akira min shi muyi magana."Shine Naga ke Yar uwata macce ce zaifi sauki ki Kira min,Da naje gurin mazan can!"Kinga ga kudin saimu sayi katin akirashi da wayarki."
"Murmushi Mansura tayi tace Da ki barshi..."katse ta nayi da cewa ba'ayi haka ba."Ina zuwa."
"Nan na tsalka titi naje nasayo katin dari 200 aka loda Lambar na baiwa Mansura tasa awayarta takira kusan sai akira na biyun aka d'aga"
"Wayar ta bani,Na karba da sallama,sannan na gaida shi,tare da masa bayanin in da muke ayanzu."Da taimakon Mansura har ya gane."Yaya Sadiq kenan
"Amsawa yayi da to Yana zuwa yanzun najira shi,tareda katse Kiran."
"Kallona tayi cike da mamaki irin yadda ta fahimci ko wayar ban iya ba bare karata a kunnena irin na Yan gayu...Tace Wai ni na tambayeki Nadiya Sam ke bakya da waya ne?ko kuwa lalacewa tayi!?"
"Yake nayi Tace ban taba rika waya ba, ta kaina dai gaskiya Mansura.......,saboda Iyayena basa so Kuma Ni kaina Bata dameni ba...."na Bata amsa Ina dariya."
"Hmnnnn...Lalle nikam ban San yadda za'ayi nayi rayuwa babu waya ba Naddy,Ay ko basa Bari Zaki iya riqe abirki aboye!"Tunda su aganinsu wai...Ita ke lalata yara ko."Nikam Ina ganin ba haka bane!" Kin ganni nan wayoyin da nayi sun Kai biyar ba tare da sanin Dattijai ba!duk da mamana ba ruwanta tsohonne dansa ido"Mansura Tace tana juya wayarta da ni ban ma San sunanta ba."Amma da ganinta tana da kyau da tsada."
"Numfashi na sauke nace to Allah ya kyauta."
"Amma Bazasu maki fad'a idan suka Gane!?
"Fad'a fa ai ita mama ba ruwanta!shi Kuma Baba ko ya fara fad'an nasa, mama ke tare min Domin ta tsani bacin ranmu Kinga Ni ko ahabar Zane na!"Yayi ya Gama Idan ya gaji ya fita.. "Mansura tace tana Dariya
"Nace to Lalle Mansura Allah dai ya shiryaki,"Baki kyautawa,"
"Wani kallon banza ta bini da shi Tace to Ameen,Ni Kinga Nadiya zan wuce."Tana Cin chewing gum kallo D'aya zakai Mata ka fahimci Kai ya waye."
"Cike da damuwa nace Ah'ah kiyi hakuri har Yaya yazo,mana!nasan idan ya karaso zai K'ara Kiranki Kinga idan kin wuce ya kenan zanyi."
"Toufaah Nadiya kin fara ganin Amfanin wayar!"Hmnnnn ai wallahi kije ki nemi waya tun wuri domin tana da amfani bazaki gane ba sai kinje jami'a."Inji mansura tana juya Ido!
"Dariya nayi Ina kallonta Nace Nima zan roki Babana alfarma da yayi Hakuri, ya saya min,Domin nima na shigo gari,sanan mansura ai karatun ne ya kawoni garin nan."
"Da mamaki ta kalleni da kayana ta kwashe da dariya Tace makaranta faa,Nadiya!?tare da dukan kirjinta"Tace Nifa na dauka ko sakandare ne zakije ko kuma hutu Kika zo."Lalle Nadiya kina cikin duhun Kai!"yoo Nan kayan Yar jami'a ne bako !? Yar trolley din Nan ma bakisan ki saya ba ki da kudin samari!Duk kyaun nan ya tashi abanza!?Ko kinsan yanzu irin KU ke da kasuwa da farinjini."Hmnnnnnn abin mamaki kenan Inji mansura
"To wace makaranta acikin makarantun?"Ta tambayeni tana Murmushi
"Nace shehu shagari(COE) tare da Bata fuska saboda naga tana son kawo min raini!"da wulak'anci
"Kiyi hakuri da ni Nadiya akwai ni da hegen baki da yawan magana ko,Amma Bari Kiji Kinga kayan Nan naki,ta nuna ni.."Sannan Tace karki Bari ki shiga da su ahaka harabar school, saboda akwai Yan sa ido! dan basuyi Kama da na yam Mata wayayyi ba!"Idan Kika kuskura Kika saki layi wallahi zasu gane ke JJC ce,Ke Kinsan Zane..to zasu zanaki tsaf da kayanki da Kuma abinda kinkayi ko Kika fada kowa ya gani."ga Yar kauye Mai zumbulum hijab ta shigo makaranta,"Mansura Tace tana wani kaudi,Nikam cewa nayi to ai kinsan Kowa da halinsa mansura,"
"Mansura cap KE nifa Nan da kike gani na Yar makarantar ce,"Nan take ta gaya min ita a Danfodiyo take karatu,Daga birnin kebbi take yanzu hakan Tana shekara ta karshe,daga nan zataje bautar kasa idan ta kammala karatu Sannan tayi aure...."Nan dai mukayi ta Fira tana ta zuba har tarihin iyayenta da komai ta labarta min acikin kankanin lokaci,Kiran Yaya Saddiq ne ya shigo,Nan muka Kara fitowa abakin titin ya hango mu Bayan mun dauki wayar......"
"Inda muke ya tsaya,bayan ya fito Gaida shi mukayi dukkan mu,Mansura har da wani canja murya.."Amsawa yayi yace mu shigo motar."Nan ya bude but muka zuba kayan."
"A rab'e muke cikin motar Mai kyau ga kamshi ni gaba Mansura Baya,wacce tuni ta mutu wurin kallon Yaya Saddiq Domin matashi ne Mai cikar zati da haiba Yana da kyau sai dai baki ne wulik Amma Mai sheki."Shi Kuma sai tambayata yake ya nabaro mutanen gida."Ni Kuma Ina ba shi amsa."Nan yake tambayar Mansura Ina zai ajiyeta."Saboda tun farko na masa bayani itace na aro min wayanta makaranta zataje."Tafiya mukayi Mai Dan nisa ba Mai magana sai sautin wakar ashanty ke tashi a motar asanyaye har muka karaso..."
"Cike da yanga mansura Tace Nan ma ya isa yayah sadiq, cikin sigar kissa,nikam mamaki ma take bani yadda take canja salon muryarta kamar sarewa..."
"Nan dai Yaya ya ajiyeta bakin kofar makarantar,akwatinta Mai tayoyi baka tajanyo ta dawo gefena Tace Nady zanyi saving Lambar Yayanmu,sai munyi yawa ko Nagode kawata,"Wani iri naji Amma yake nayi nace To...mansura nagode!"Domin na kosa ta tafi ganin yadda Mai motar yasha kunu...karya murya tayi tayi masa sallama tare da ma shi godiya tana lankwasa murya."Bakomai yace da ita."yaja Mota muka tafi."ko kallon ta bai kara ba.''
"Kallona yayi ya watsar a Dan fusace!yace Wannan yarinyar na lura Idonta ya bude!ta cika kaudi da rawar Kai!Daga yau bake ba ita!"
"To Yaya Daman a Mota muka hadu nace Ina Wasa da yatsunta!"Bayani yayi min sosai Kan adimishin Dina da Kuma tsarin yadda karatuna zai kasance!"Yace sai gobe zanje makaranta,Kasancewar yau kinga lahadi ne ba aiki sai na karasa Shirin....."kiransa da akayi awaya ne ya tsayarda Zancen,Ashe Baba ne, Yaya Sadiq ya shaida masa na sauka lafiya,Yanzu ma muna hanya zai kaini gidansa har gobe ko jibi idan an samamin daki a hostel, ya gama komai sai na koma."Godiya Baba yayi masa Yaya Sadiq yace''Baba bakomai Nadiya kanwata ce...Nan ya bani Baban muka gaisa da shi tare da Mana fatan alheri....."A hankali muka shigo unguwar da naga an rubuta BAFARAWA ESTATE daga farkon get din."Hancin motarsa ya kunna aciki ahankali yake tafiya....Layi na biyu muka shiga dai-dai wani gida mai lamba sha biyu muka tsaya sai da Mai gadi ya wangale get."Babu abinda nakeji sai fargaba!da tsoro azuciyata!Yau kwana ba dasu Mama ba!"Kayana Yaya Sadiq ya fito da su tare da daukar min leda guda jikkata na kinkimo Sannan ya rufe motarsa Yana gaba Ina biye abayansa."