← Book details Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 65

Sashe 14

Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*TUKUICHI NEH GAH* _Mesona,farin cikinah Hasken idaniyatah Abin alfaharinah Nagode sosai da kulawa Allah yabar zumunchi da Zaman tare Ameen_*FATAN ALKHAIRI*😍

______________________________________
"Ta Kama yau ranar litinin CE,Ranar da ko bature Yana tsoronta!"Tunda na kammala shirina tsaf acikin wata atamfa metro ruwan miyon goro da fari,dinkin riga da siket ne yayi min kyau sosai."Da yake su Eshaa suka dinkama ita dinkin ya amshi jikina sosai."Hijab fari nasa irin wannan da ake daurewa baya."Yayi min kyau,Takalmi na saka sannan na dauki jikata,Na fita da zummar su Esha zasu sameni facultyn mu."Saboda tun adaren jiya na sanarda su zasu rakani Inda Yaya Saddiq muyi masa barka da zuwa."

"Ina fita Inda muke haduwa da Naseer na wuce Banyi minti biyar awurin ba sai gashi ya sameshi Ina duba littafaina."

"Yace "Malama kiyi hakuri kinata jirana ko tare da zaunawa gefena..."

"Murmushi nayi nace bakomai antashi lafiya."

"Yace"Lafiya qlaw yace,Gaskia Nady yau kin fito kamar balarabiya ko dai kin hada Da su ne."Wannan kyaun."

"Dariya nayi wadda sanadinta sai da dimple dina suka lutsa..nace ehhhhh...Ni balarabiya ce...kaga bana son zolaya muje tun ba Kai min format din abinda na rike ba.."

"Naddyh kenan kefa karfe ce..na yadda da karatunki bazai taba zuwa ko'ina ba.."

"Nan dai muka wuce muna Tafiya muna firar da yake jinin mu ya hadu sosai da Naseer...Haduwata da shine na fara rage tunanin malam yunus.."Yana debe min kewa mutum ne Mai mutunci da sanin darajar Dan Adam,"

"Acikin awa Biyu muka kammala gwajin mu(test)."Cikin ikon Allah duk abinda aka tambaya na amsa saboda nayi karatu."Da munna na fito Daga Hall din Ina dubin ko Naseer Ya fito da yake bama Zama guri daya uztaz ne baya chakuda acikin Mata ya zauna sai idan takama dole."

"Bayan ya fito ya sameni zaune Ina jiransa..."tambayoyin juna mukeyi akan test din da yadda malamin ya rikita Mana lissafin saboda tambayar a hikima yayita idn mutum Bai fahimta ba sai ya fad'i."Daga nan Dakin karatu muka shiga muka Duba Wasu littafai acan nabar Naseer saboda munyi da su Esha idan Sha biyu tayi zamu hadu muje Inda Yaya Saddiq."

"Banyi wahalar samun su ba domin nasan Inda sukafi yawan Zama.Nan na samesu sai ciye_ciye kayan kwalaam suke maza da Mata."Da nesa na tsaya ayko Nan take suka tashi suka sameni...Kallon su nayi ba laifi duk jallabiyoyi suka saka..."Sukayi rolling da mayafin rigunan."Sunyi kyau sosai da yake ba karya dukkan suna da kyau ga mayukan gyaran Jiki da suke amfani da su masu tsada kowacce sai sheki take Sunyi tatas da su.

"Deejah tace Nadiya har kin karaso mu Tafi ko,

"Esha ta ce"Ya test din koda yake nasan ku masu kwanya ne zakuci..."

"Murmushi Deeyart tayi batace komai ba."

"Bamuyi doguwar Tafiya ba suka isa admin din."Office din Yaya Saddiq mukayi knocking..."Sai da naqara yin wani sannan yace Mana Yes come in (Alamar mu shiga)"

"Da Sallama muka shiga office din.. "A hankali ya amsa Mana tare da ajiye wasu files a side drower dinsA."

"A hankali muka gaida shi..."

"tuni su Esha suka sha jinin jikin su saboda kwarjininsa da cikar zatinsa Domin shi Sam bada case da Kowa mutum ne mai Kare mutuncinsa" wani irin Kallon yayi Mana ba yabou ba fallasa Yaya Saddiq ya bimu da shi."A lokacin da ya dago kansa ya ganmu..."Tare da amsa gaisuwar mu adakile!"

"Da sanyi nace Yaya Daman mun zo mu gaishe ka ne.."

"Yawwa to kun kyautah..."Ya karatu!?" ya tambaya

"Lafiya qlaw....nace da shi"

"Wad'annan fah!"yace tare da nuna su da hannu.."

"Rass!"Gabana ya fad'i!"Cikina ya dauki duri kada ya wulaqanta su..."Domin sunyi suna da tashen rashin mutunci a makarantar

"Da....Da.....Daman 'yan Dakin mu ne yaya!"na bashi amsa."

"Okay...yayi KU Nagode Kuna iya Tafiya zanyi magana da ita."yace da su Esha

"Kamar jira suke kowaccen su ta tashi Daga kujerar da take zaune.,sum sum suka fita jiki na kyarma!"Saboda duk iskancin basa wasa da irin su Yaya Saddiq."

"Suna fita ya kalleni...sama da kasa!"Ya ce"Da kyau! haba biri yayi Kama da mutum...Shiyasa naganki kin wani canja Ashe da marasa kamun Kai kike rayuwa dasu!"wad'annan yaran da muke gani Kowa ya sansu a makaranta Nan sune abokanki bakisan idan Kuna yawo da su za'ayi maku Dauka D'aya!"Dan an hadaku d'aki D'aya dasu saiki dinga fita dasu meyasa ma Baki gayamin ba ai sai nasa ahadaki da mutanen kirki.... inji Yaya Sadiq a fusace!

"Kina ganin kinyi wa iyayenki Adalci Nadiya!?"To wallahi bazan lamunce ganin ki da wadan Nan 'yan iskan yaran ba!"Sai dai ki koma gida da karatu saboda Baba Ni ya baiwa amanarki!"

"Meye alakarki da su Bayan Zama guri Daya!?"Ya tambayeni a fusace!"

"Kuka!nakeyi yayin hawaye na ke malala a fuskata!"Nace wallahi Yaya Sam bana rayuwa irin tasu Dakin mu ne daya!"Kuma nifa ko yawo bamayi tare ko yanzu Dan kace nakawo su ka gansu ne..."Naqarashe maganar muryata na rawa.."

"Saboda naga kin canja ne ya sanyani tuhumarki!"Shiyasa na nemi ganin su.."hankalina ya tashi alokacin da na hango wayewa da canji a kwayar idonki...sannan tsadar chocolates dinda kika baiwa su Mufeed ne ya bani mamaki...domin Ina sayen irinsu nasan kudin su..."Amma ace Wai kawayenki. Zasu iya KYAUTA da su amatsayinsu na dalibbai."
"Daga yau karna Kara ganinki da yaran nan saboda lectures da dama sun nuna min su amatsayinsu na makaranta."Duk makarantar Nan ansan da labarinsu da Zaman da suke school dinnan."Kina tunanin ba za'ayi muku dauka daya ba!?"To kisani babu ke babu su!"Kuma na baki Nan zuwa yamma ki tattara komai naki Zaki koma gidana da Zama saboda ko an raba maku daki nasan zasu iya binki har Inda kike su canja makin rayuwa kamar Yadda suka fara...."

"Dai-dai Nan nakara fashewa da Kuka saboda na shaku da su Eshaaa,Ban son rabuwa da su..."Jin kukana!ya tsananta yasa Yaya Saddiq yace na fice nabashi guri karfe shidda ya sameni bakin get din hostel da kayana."

"Fita nayi cike da kunci azuciyata!Nasan bana rayuwa irin ta su Eshaa Amma Ina da burin cetou su daga halinda suke ciki!"Ban Kai ga cika burina ba!"Yaya ya yanke min kuduri!!!"Tafiya nake Batare da nasan Inda nake kada kafata ba!"Banyi aune ba sai Jin nayi karaf an rikemin hannu."

"A zabure na dubi gabana ...wani ne. Wanda ga alamu kamar malami ne.."
"Hannuna na kwache a nasan tare da bashi hanya ya wuce!"Haushin rikeni da yayi yasa na watsa Masa harara da tsaki!Nace haba Mallam Bai kamata ka rikeni ba!sai Kai min magana!"

"Murmushi yayi yace"Yammata Kiyi Hakuri Amma laifinki ne,kisani Kuka Bai kamace ki ba!"Kina da kyau hakan har za'a ga hawaye kwance a fuskarki Kuma kina 'yar jami'ah..."

"Ya Kara kallona Yana murmushi yace ki gayamin damuwarki zan taimake ki wanene ya kadake!? ko ya cuceki!?"

"Takaici ya bani bansan sadda nayi na koma tsaki ba!"Na wuce abina saboda yabani haushi tabanin da yayi!"

"Tsaye yayi Yana kallona...."Yace Kai!Ni wannan yarinyar zata yiwa tsaki!"Hmnnnn zan nemoki yarinya Zaki shigo hannu...Tabbas watarana zaki San waye malam Dan Bala!"Ya wuce office dinsa Yana mamakin yadda Mai kyau ta masa tsaki duk yadda yake jin kansa."

"Ko da na fitou fili Banga su Eshaa ba!"Duk da muna da lecture 4_6 ban tsaya ba hostel na wuce saboda ban San abinda ke min Dadi bA!"
"Na Saba da rayuwar hostel tsawon watanni biyu..."Naji dadin rayuwa acikin mutane!"Na fara iya mu'amala da mutane da yadda AKE zama da su Naga wadanda nafi komai Naga Wanda suka fini ilimi,da addini har Ina kwaikwayon su Amma yanzu Yaya Saddiq Yana son ya rabani da su!"Saboda su Eshaa da nasan a mazaunin da na ajiye su arayuwata."

"Da tunanin na isa Dakin mu....Gabana ne ya fad'i alokacin da na kalli fuskokin su...kowacce ba fara'a ita Deeyart har da hawayenta..."

"Banyi kasa agwuiwa ba!"Nace Eshaa, Deeyah, Deejah Dan Allah kuyi hakuri da abinda Yaya Saddiq yayi muku, kunga koni yanzu yayi min! wannan halinsa ne KU kanku kunsani Kuma kunji aschool ana fada!!!"

"Ba komai duk abinda yayi Yana da dama domin mu muka Kai kanmu!"Inji Deeyart da bacikin Rai!"
"Eshaa tace wallahi saboda ke kawai mukaje Naddy..."Kuma Dan kawai kince mu rakaki ne!"ya ganmu a office dinsa but idan yakara ganinmu ya Yankee kafafuwan mu!"

"Inda ba domin Hakan ba! me zai kaimu!? mu da sai ma an gayyace mu muke shiga office!k'oshi sai mun Sami time,Bare shi waye shi!?"Me Kuma ya dauki kan sa"

"Deejah kenan."KU daiyi hakuri koma menene nice sila!"Nace da Deejah wacce ta gama zancenta tana cika tana batsewa.."

"Shiru sukayi Ni Kuma tashi nayi Ina had'a kayana..."

"Eshaaa tace Naddy Ina zakije Naga kina had'a kayanki ba dai akan wannan maganar ce zaki bar Dakin ba!?"

"Hawaye masu zafi!suka zubou min,na dubeta Ina ninke kayana nace Eshaa Yaya Saddiq yace"Gidansa zan koma da Zama duka...!!"

"Menene!Naddy!?cap lalle bawan Allah nan anyi mugun gaske,!"Saboda kawai yaga shi aka baiwa kula da ke shine yake Miki hakan ai Wannan mulkin mallaka ne!..."Inji Eshaa

"Ni kaina Ina son zamana anan Eshaa Gidansa bazan sake ba!"Bazanyi karatun kirki ba!"Amma ya zanyi? Ina gudun ya Kira Babana ya Gaya mashi wani Abu akaina ran iyayena ya baci...Dole nabi umurninsa..."Nace idona ya ciko da kwallah!!"
"Hmnnnn...Tabbas zai Gaya masa kin lalace Tunda kina rayuwa da mu lalatacci!"Inji Deejah

"Ba Haka bane Khadija...."DakAta! Naddy, Hakane mana!"Saboda kowa a makarantar nan ya ajiye mu a marasa kirki da kamun Kai!"Dan kawai muna tafiyarda rayuwar mu irinta zamani!ba Halin wanka da sa kayan zamani,

"Tabbas hakane Deejah!"Nidai duk Wanda ya zarge mu akan abinda bamayi Allah ya isa!Domin baka shaidun mutum Ayau!"

"Tabbas Deeyart!"Inji Esha wacce ta tashi Daga Inda take zuwa wurin da Dan firijin dinsu karami yake!"Ta bude tare da dauko lemun kankana Mai sanyi ta kurba kana Tace" mudai Allah ya wanke mu,Daga zargin da ake Mana!"ke Kuma Naddy kiyi hakuri ki yafe Mana domin Zama da mune yasa ake ganinki kema kin lalace har aka Bata maki Rai!"Daman Zama da madaukin kanwa ke Sanya farin Kai!"

"Nidai Har ga Allah Nady Ina sonki Kuma Ina kaunar Zama da ke ko bakomai muna karuwa da iliminki Inji Deejah .."

"Kuka ne ya kwace Deeyart da yake akwaita da saurin Kuka da hasala!"
Chapter 14 · 0% Book details