← Book details Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 65

Sashe 10

Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Abinci kowa ke ci cike da raha da Jin dadi musamman Yaya Saddiq da yaransa, duk da nidai taliyar ta Anty batayi min wani dadi ba,Duk da Tasha kayan lambu da magi bare man gyada."Ba a ko magana."A zuciata nace da ace nice na girka kila zan iya ci Kuma bazan Bata kayan da ta suburbuda aciki ba!Wai duk Domin tayi dadi."Hmnnnnn nikuma nace girki tsari da kwarewa yake buqata ba zambada kayan kamshi ba.."Ina amfanin kyau a fili babu abaki akula lol."Sai dai Nadiya bata sani ba ko daga bakinta ne fans ku dandana kuji😀."

"A gurguje ni kam na dan tsakura naci na tashi saboda ban Saba da cin irin wannan kalar abinci ba!"A hankali nabar wurin Dakin Wanda ga alama na yaranta ne, na koma na zauna Ina jiran sallar Isha."Tunanin Malam yunus ya darsu azuciyata na tabbata shima yau zaiyi kewa ta rashin ganina a makaranta

"Cikin sa'a ko ya samu Abokin sa alambun gidan su kamar yadda yadda yadda sanar masa."da yake kafin ya zo sunyi waya."

"Bayan ya zauna,yasha ruwa da lemu sun danbtaba raha."Shi ne Jawad ya zayyanewa Saif duk abinda ke faruwa atsakaninsa Yarinyar da ta mare shi!"Sai dai ya boye zancen marukan da ya Sha saboda tsarou😄"Ya dai gayawa, Saif ta kirasa Maras *TARBIYYA* Abin ya daki zuciyarsa!!"Sannan yarinyar ta masa rashin mutunci ta zazzage shi"Shiyasa yanzu yake so yayi mata wulakanci naji nagani na fada agari!!!."Amma fa ba Wanda zaisa mom ta gane ba!"tayi magana akai..."Nan shaidawa Saif karya!Da tsarinda yayiwa mom."

"Nazari Saif yayi kana ya kalli Jawad Yana murmushi ya ce"ya naga ka wani had'e fuska kamar tana agaban ka."

"Bana son rainin hankali,Shawara nazo nema wurinka ba iskanci ba!"Jawad yace yana kallon Saif tare da Harara."

"Mai da wuqar nawan, yanzu dai mafita d'aya ce nake ganin zamu bi muyi maganin iskancin ta shine mu nemi sanin gidan su,iyayenta akarshe muje masu a mutanen kirki!"Daga nan zamu daura su akan tarkon mu da zarar ya Kama su Ina da tabbacin zamuyi nasara akanta,"Abokina Albishirinka."Daga ranar na tabbata ta tashi da aiki domin ba makawa zamuyi maganinta!" sauran bayani Kuma basai na gaya maka ba yanzun sai zuwa gaba."

"Da wata irin dariyar k'eta Saif ya kalli Jawad da ke wani Shan kunu Yana huci da hura hanci!"Yace Baba you hakuri! tare da miko da shi tsaye....muje yakin neman Gidansu yarinyar domin mu santa da labarinta, Allah ya taimake mu yasa iyayenta kashe money ne.. "

"Ameen,yace."
"Tsaki!"Jawad yayi azuciyarsa yana tuna maruka, Amma afili yace waton Saif idan har ta shigo hannu na banma san irin kalar wulakanci da zanyi Mata ba!"

"Jawad ay babu babi ko days ko Kuma labarin irin abinda zansa ka aikata mata aduk cikin labaran rashin mutuncin wannan zamani..."Inji Saif yana kokari shiga Mota..."

"Da motar Saif din suka fita yayinda Jawad ya bar tashin agidan su Saif har su dawo Kai tsaye unguwar tudun wada suka shiga sai dai Jawad bai Bari suka tsaya inda abin ya faru jiya ba!"gaba suka Kara hanyar da ya ga yarinyar na bi."

"Sai da sukayi Danyi tafiya sannan suka tsaya "Wani shago da ake dinkin tela suka nufa."Suna tambayar yarinyar!?"Sai dai matsala daya!basu San sunanta ba!"Wanda duk kowa shi yake tambaya ko na mahaifintA."Wuri uku suna zuwa babu nasara..."Har sun hakura sun jiyo suna cikin tafiya a motar sai Jawad ya hango yaro daya Daga cikin yaran da ya tab'a gani tare da wancan yarinyar." Yana ta wasa tare da abokansa yara."

"Da sauri Jawad yace DakAta Saif!"Na hango makamin tafiyar Nan."

"Da mamaki ya dubeshi yace a Ina!?"Jawad

"Ga yaro daya ce daga cikin kannanta muje mu tambaye shi."Jawad yace da sauri

"Fitowa sukayi Daga Mota wurin yaran suka nufa...tunda yaron ya hango su tafe ya gane Jawad...nan take yaron ya fiddo ido cike da tsoro yacewa abokan sa ku!!! mu gudu!!!ga mugu Nan tafe!...Nan take Duk yaran suka archeee da gudu."

"Jawad Bai San sanda shima ya archeee ba ya kamo yaron da tuni ya Kama kuka!"

"Saif dariya abin ya bashi yadda Duk miskilanci da iskancin Jawad ya sheqa da gudu."

"Jawad yace "yanzu zanyi maka allura ko kana son mu tafi da kai ne!"

"Ah'ah!"yaron yace Yana girgiza Kai.

"To ka fada min gaskiya idan na tambaye ka! Ina wacce na ganku tare ranar!?"Inji Jawad

"Yaron,yace taje shakkwato makalanta,cikin maganarsa ta yarinta."Yana hawaye

"Ya sunan ta ne!?"

"malama Nadiya!."Yaron yace cikin tsoro domin yashiga tsoron Jawad Jikinsa har Bari yake!"

"Jawad ya ce kasan gidan su?"

"Eh,nasani."Inji yaron.

"To yanzu muje ka nuna Mana sai kadawo Kai wasan Ka."Saif da ke tsaye yace."

"Nan suka saka shi gaba Yana tafe suna binsa har kofar wani gida na laka Wanda daga gani
Basai an fada ba kasan tufin Asiri ne agidan."

"Saif ya kalli yaron tare da dauko naira dubu ya bashi yace maza kaje ka kashe."

"Washe baki yaron yayi jiki na Bari yaje ya kashe kudin."( _Sabo akace turken Wawa Daga Ni yaron ya Saba da kashin kudi_ )

"Sai dai saif rikoshi yayi yace''Sarkin son kudi!!"Ay sai ka tsaya mana..."Ya sunan babanta ita Malama Nadiya?"

"Mallam Balarafe(Balarabe),Inji yaron"

"To ya sunan mamanta?"

''yannere(Innerei)Mai manja"

"Yawwa yaro to jeka mun gode."

"Da gudu yaron yabar gurinsu Yana munna da tsalle sai kanti...."Dariya saif yayi yace shege Dan talaka ya ga Kudi."

"Kallon junan su sukayi Bayan yaron ya wuce,sun gama mamakinsa."

"Sannan suka dubi kodadden gidan cike da haushi!!!."

"Saif yace "cikin sigar rarrashi Babban yaro da ka hakura da wannan kwailar ka yafe Mata me zamuyi awannan gidan ba girman mu bane!"Ka barta iyaka mu dauki hayar Yan iska suyi maganin iskancin ta kawai!!!"

"Wannan zancen Bai taso ba!Domin na dauki alqawarin wulaqanta ta da kaina."Tabbas ba girman na bane in tsaya ma awannan kofar gidan Amma kaddara ta riga fata!"Dan kuwa dole na dauki fansa!!!"

"To shi kenan Baabaa muje can shagon mu Gaya masu sunanta da na babanta musha Labari."

"Suka shiga shagon Kudi suka raba musu 1k Duk Wanda ke shagon Nan take shagon ya dauki shewa suna GODIYA...Nan ne Saif ya tambaye su labarin Nadiya da iyayenta."

"Cikin mintuna suka basu labarin KOMAI tsaf hadda karerayi da kare Karen Dan gishiri...."Sai dai babu abin ashsha ko ki acikin labarinsu da halayensu sai ma furuci da shaidu na Alheri."

"Nan suka bar shagon jiki yayi sanyi saboda kowa yace tanada kirki Amma shi gashi tayi masa rashin mutunci!!!"

"A hanyar su ta dawowa sai mamaki suke yadda hakan tafaru,yarinyar ta masa hakan!"Bayan ance musu tana da kirki Shi kam saif sai yake ganin kamar laifin Jawad din ne."

"Jawad a zuciyarsa sai tusushin baki ciki da damuwa yakeji yadda yar talakawa ta wulaqanta shi!"A gaban mutane!!!"Ashe ma ba Yar gidan kowa ba CE!Jin Motar ta tsaya ne yasa ya fahimci an kawo gidan su Amininsa Saifullahi galadima Wanda hali da rayuwar su kusan daya."Sallama sukayi nan tare da Alqawari gobe zasuyi shiga ta Alfarma su ziyarci Mallam Balarabe wato mahaifin Nadiya."Daga Nan Tunda ba wani haline da su ba,suyi masa barin naira domin cikar burin su."

"Bayan na kammala Shirin bacci Addu'ar azkhar na karanto kana na kwanta bacci saboda nasan gobe litinin makaranta zanje...Nan naji wasu zafafan hawaye na ambaliya a saman lafiyayyar fuskata."Kukan rashin sabo,kewa da soyayya ne nake rusawa Amma fa marar sauti saboda yaran Duk sunyi bacci."

"Duk lokacin da na tuna iyayenah da irin rayuwar su sai naji nakara kujan can na tuna sayyadi Nan ma kukan ya Kara kwaceni!!!"sai da muryata ta daina fita ga ciwon kai idanuwana Duk sun kumbura saboda Kuka."

"Ina son in bacci Amma na kasa har karfe dayan dare sabod tunani da kawa zucin mamana...Hakan yasa na tashi nayi Alwala nayi sallah bayanna idar karatun alqurni na fara,Tabbas Alqur ani rahma ne Kuma maganin komai ne,Nan wurin na samu nutsuwa na shigo ni ahankali,Lazimi na dinga yi da hannu na daga nan bacci barawo ya saceni Ni."( _LITTAFIN manzon tsira rahma ne Kuma saukine Sannan waraka ne Daga dukkan komai_)

"Ana wata ga wata kenan domin Yana cikin bacci ya dinga jiyo sautin karatun Alqur ani ahankali Yana tashi acikin gidan,sabon lamari kenan saboda abinda Bai tab'a faruwa ba agidan,sautin muryar mace tana karatu....Juyowa yayi ya kalleta tana gefensa tana sharar baccinta azuciyarsa yace Daman nasan ba anan ba ne..."A hankali ya isa bakin kofar dakin da yake tsammani...Yana sauraro tun Yana tsaye har ya Kai zaune,muryata ta na shiga jinin Jikinsa Yana wurin har sai da yaji Shurin nata Sannan ya tashi ya koma dakinsu cike da tunani azuciyarsa agaskiya Ina son macce Mai addini yarinyar ta burgeshi,Ina ma ace jalilarsa ce ta ia karatun alqur a ni hakaaan....."Yaya Saddiq shima Alwala yayi ya tada sallah,Abinda ya dade baiyi ba!"Domin A Da Yana da kokarin ibada,Azumin nafila tsayuwar dare da tilawar alqur'ani sai yanzu akan yasamu macce marar addini batayi kuma shi idan yanayi tace Yana takurata hakan dai shima ahankali shaitan ya rinjaye shi!!"Amma gashi yau yaji komai ya dawo masa, Jin da yayi Nadiya tana rera karatu kamar balarabiya...Nan shima ya dinga nafilfili da istigfari har wajajen uku da rabi Sannan ya kwanta... Jalila ta farka bayi ta shiga da ta ganshi zaune Yana Jan carbi tsaki tayi tace Hmnnnnn su Huda Huda sarkin sallah yau an tuna da ibadar Ni Motsin ka ma ya hanani baccin kirki!"Kwanciyar ta tayi tare da Cigaba da baccinta."( _Tabbas akwai Mata kawayen Jalila masu wannan irin wannan halin! ya kamata mu gyara!idan kinsamu miji Mai addini da ibada to yi kokari kibi sahunsa ki Kara karfafa masa gwuiwa KU Cigaba da ibadar atare domin KU tsira atare,idan ma sabanin hakan ne kiyi kokari kiga Yazan mai ibada yadda ya kamata,Saboda da yawa mazan wannan karnin suna da raunin ibada ko ta farilla bare nafilar Allah yasa MUDACE Amin._!")

*'YAR MUTAN DIKKAWA CE*
[2/18, 7:25 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲

*NA*

*NABEELA DIKKO*

*PEN WRITERS ASSOCIATION*

*SHAFI NA TARA*

_SADAUKARWA GA AMAREN 👰🏻DECEMBER🌙,DA KUMA NA SABUWAR SHEKARA📆 INA MAKU FATAN ALKHAIRI ALLAH YASA AYI LAFIYA A WATSE TAROU LAFIYA_
Chapter 10 · 0% Book details