← Book details Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 65

Sashe 55

Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kaga sadaki sha biyar kudin shiga gida dubu biyar Ina son Yanzu Bai sai anjuma ba zaman ku da tsarinku da salonku duk su sauya ina nufin ku aura da Mana Aure Ni da mansbaby!"

"A zabure kawun Mansura ya tasowa su Bimboy Yana fad'a da su har da zaginsu,yana cewa KU Wad'an me marasa hankali da *TARBIYYA* ne,"A Ranar aurenta Ana batun daura aure zaku wani ce Kun kawo kud'in aurenta saboda KU marasa hankali...."

"DakAta Mallam karfa ka manta KU Mutane ke saurare saura sakan talatin lokaci Yayi cip!"Ba sa'insa ya kawo mu ba,kaga tawagar mu can..."Adams ya nuna abokansu da ke zazzaune agefe Duk da kananan Kaya,"Ya ce"

Ya dubi Sadiq yace lallen Ango to karbi Wad'an nan takardun ka karanta!"Nasan Dole ka hakura da amaryarka ka barwa Mai rabo!"

"Takardar Ali ya karba suka karanta shi da Saddiq,"

"Innalillahi Wa'Inna ilaihir Raju'un!!!"Shine abinda suke maimaitawa Alhamdulillah, Saddiq yace"Tare da mikawa Adams takardar....yace ko da abokinka bai zo ba,Kuma Banga Wannan takardar ba!Ayna fasa auren mansura!"Saboda ta cuceni!"

"Murmushi Bimboy yayi yace mansura mayaudariya ce alqawarin aure NE atsakanin mu,Amma ta gujeni sai da naji labarin aurenta da Kai,Bayan duk abinda na Tara ta lashe,kudin gadona ta cinye idan sata nayi ita ke Moran kudin Kai har kidnapping din wani Alhaji saurayinta tasa mukayi Wallahi duk ita ta cinye kudaden da aka bamu,Amma yanzu tazo ta gujeni!"

"Adams yace kai Hakuri bimboy ai bazata yaudareka taci bulus ba, ya dubesu yace Yawwa Kawu wannan takardar da kuke gani ta asibiti CE,wacce da ta mansura da Abdul Rahman CE, kuma an shaida masu da dadewa suna dauke da cutar HIV AIDS,"sannan Wallahi idan ba'a daura auren Nan yanzu ba!"zamu amshi microphones mu shaidawa kowa meke faruwa!"tun farko har karshe!"

"Dariyar iskanci Adams yayi yace"Shin Bimboy Zaki iya tuna iya adadin Cikin mansura!?"

"To zan iya tuna wad'anda nakeda masaniya akai kamar bakwai NE!"Inji Bimboy

"Wata Dariyar Adams yayi inda maroki ya nufa ai da gudu kawun Mansura ya kwasa ya cafkoshi yace"tufa Mana Asiri Dan Nan......!!!!"

"Asirinku atufe Yake Amma ayi a daura auren Nan,lokaci yayi,"nine waliyin Ango...Adams ya ce cike da Jin Dadi!"yadda Duk Yan uwan

"Mahaifin mansura da yayyansa sai sunkuyar da Kai sukayi Saboda kunya!"Kawun ta ko fifita Yake Saboda zufa!yace"Ai ga irinta Nan.....ya dubi Yan uwansa Cikin Jin haushi da takaici!"Yace"Yaya me kuke Ganin yadace!"Kunji saddiq ya fasa auren!"Wad'annan kadagarun barikin Kuma zasu iya tona Mana Asiri wallahi...."Saboda basuda kunya,...."

"Ay tun Kan ya qarasa Adams ya Tashi Rai bace!"Ya karbi abin sanarwa ga wani marobi...hurawa Yayi sannan yace To jama'ah!!"

"Nan dayan marokin yace"To jama'ah kowa ya SAURARA..."

"Adams cike da Daga murya yace"Ango yace ya fasa!"

"Azabure Wasu Mutane suka tAshi..suna kallon Adams Nan hayaniyar ta kaure!"

"Marokin...yace"To fa Ana wata ga wata Wai Ango ya fasa!"

"Adams yace Amma baza a fasa d'aurin auren ba!"

"Marokin yace"kowa ya zauna KU kwantarda hankalinku rabo ya rantse sai Mai shi Domin take away bazai wuce mu ba!"Aure dai sai an d'aura.

" Adams yace sai abu na gaba da Baku Sani ba.... "kawun mansura NE ya rufewa Adams Baki ya jashi izuwa inda suke zaune Yana Hawaye!yace ka taimaka ka rufe Karla tona."Yace liman a d'aura dasu kawai ai duk tsuntsun da yaja ruwa shi ruwan Kan doka.

"Suna Zama Liman yace ayi Salati,Nan aka fara gudanar da daurin Aure,"

"Mutane sai Rabon Ido suke da baza kunne Domin Cikin kowa ya cika fam da gulma,"Da mamaki da kuma Al'ajabi to ya Abin yake.....?."

"A hankali numfashin Mallam BALARABE ya dawo,"sanda ya bude Idonsa Ganin an kewaye shi yasa ya fara tunawa da abinda ke faruwa,

"Jawad da saif tallafo shi sukayi zuwa babbar kujerar da ke falon,Har Yanzu Hawaye yakeyi Yana kallon hoton...!"

"Innerie da Sauran jama'ar falon sai sannu suke faman jera Masa,"

"Inda yake na zauna Ina kwallah!"Nace Baba lafiya meke faruwa!?"

"Alh.malami sambo ruwa yaba Baba yasha kana yace"sannu Mallam ko Kasan Marigayi Husamaddin NE!?"

"Wasu zafafan Hawaye suka zubowa Mallam BALARABE ya Nuna hoton da yatsa Cikin k'unar rai yace hakika nasan shi!"farin sani kunga Wannan hoton....yace tare da nuna masu dayan hoton da ke manne ajikin bangon...na farar kala NE,na Yara kanana uku,sai gudan na yaran su BIYU kamar Yaya da Kane,"Sai Kuma dayan na Babban mutim wato All.husamaddin Wanda yayi alokacin Yana Cikin ganiyar kudin SA gab da rasuwar SA,"

"Kowa hotunan ya duba..."sannan Mallam BALARABE yace"To Wannan hoton na Yara uku Ni da husama,da Aram ne,"

"Dukkan su shi suke kallo da mamaki... "

"Muryar momy na rawa Tace Kar dai kace min Kaine Yaya Bello!?"Yayansa!"

"Girgiza kansa Yayi yace nine Yayansa Bello....Hajiya nine...Yanzu Ashe Jawad jinana NE..."sannan kanena Husamaddin ya rasu!"kaicoh na dunia lallai nayi kewar gida da dangina!"wani sabon Kuka Mallam BALARABE ya bude!"

"Momy da Jawad ma Kuka suke!"

"Nikam Tuni na daskare Domin bakin CIKI Saboda banso makiyina ya Zama jinina ba Wai ma Yana daga Cikin ahlina da na Dade Ina son Gani!"

"Alh.malami da Hajiya Maryam Alhamdulillah suketa faman nanatawa!"

"Saif da Innarei sunji Dadi sosai sai hawayen murna suke!"

"Momy Tace"Wallahi Marigayi ya mutu da son ganinka arayuwarsa.

Nan dai momy ta labartawa Mallam BALARABE komai da tasani tun farko har karshe,"Tashi tayi ta dauko wata tsohowar ajiyar da marigayi mijinta yayi,ta kawowa Mallam BALARABE,"Tace"Wannan shine amanar da ya bani Kuma sirri CE,Daga Ni sai shi,yace min duk RANAR da Naga Yaya Bello na bashi..."

"Jiki na rawa Mallam BALARABE ya bude akwatin,duk hotunan su ne Dana iyayensu,har da tufafin Mallam BALARABE da ya Bari agida SUDAN, Alokacin da ya Gudu zuwa Nigeria,"

"Kuka sosai Mallam BALARABE keyi!!"Har ya Gama ganin kayan akarshe takardun kudaden SA ne,Wanda aka raba aka ba marigayi Husamaddin nashi da na Yayansa Alokacin da mahaifiyarsu ta rasu,Wacce Yar kasuwa CE sosai Mai dinbim dukiyar zinarai,

"Allah sarki Mallam BALARABE yayi Kuka shi da iyalansa sosai,saboda ya rasa uwa da kaninsa,"

"Momy Kam hankalinta ya kwanta yau ta sauke nauyin da ke kanta!"Tace"Yaya Bello sanadin nemanka marigayi ya dawo Nigeria har ya mutu anan,Kuma yaje da buri akanka!"ya shaida min watarana zamu hadou,Gashi dalilin Nadiya da jawad mun hadu!"saboda mun Sha nemanka,Rashin sani akace yafi duhu!"ashema muna gari Daya da KU..."

"Goge hawayensa yayi yace"Allah ya jikan ummu da Husama,"

"Ameen kowa yace"Sai share kwallan Tausayi ake!"

"Jawad ya rarrafo tare da rike kafafun Mallam Balarabe yace Baba Shi kenan na cutar da kanwata!"jinina!"Daman ance idan zaka Gina...Ramin mugunta Gina karami..." Gashi Ni na Gina ya farmin...na yaudare ku iyayena na cutar da kanwata Nadiya..."Ashe jinana ce jinin da muka Abbu na da mommyna su ka sha wahala Ni da wurin nema,"

"Dan Allah Nadiya kiyi Hakuri ki yafe min....Baba na tuba ku yafeni Jawad yace"Yana rusa Kuka!"

"Mallam Balarabe yace"Ka DAINA Kuka!yarona komai ya wuce!"Kuma laifinta NE ba naka b....."

"A'ah Baba Nadiya batada laifi mune masu laifi Ni da Abokina saif domin mun shirya mata gadar zare, Kuma mun yaudareku duk a Dalilin kalmar tarbiyya "Nan jawad ya labartawa iyayensa komai tun haduwarsa da Nadiya,har had'a bakin da sukayi da M Bala yasa aka koreta!Daga makaranta,Da kuma zuwan da sukayi Wurin Mallam yunus suka aibata tah!"Dan kawai Ya ce ya fasa aurenta!"Da irin can mutunci da muzguna Mata da yayi har zuwa karshe dukan da yayi Mata....."

"A hasale momy ta taso ta dinga zabga Masa Mari!"Ta ko'ina tana Kuka ta CE,Ashe haka ka zalince ta batare da kowa ya Sani ba?"

"Da kyar aka banbari hannunta arigar Jawad da ta cumuimuye!Tace Wallahi sai ka saki Nadiya,"Kaje ga Saif Nan ya isheka rayuwa..."Hakuri Hajiya Maryam da Alh.malami ke ba momy Amma sai surfa ruwan masifa take!"

"Nikam jikin mamana na shige Ina rera Kuka!"Akan abinda su Jawad su Kai min Domin sun cuceni sun Zama Silar rushewar karatuna ga sunana da suka b'ata! A gurin malamina"Rarrashi na mama keyi tana share min kwallah!!!"

"Kukan momy yaja hankalin kowa afalon kalar tausayi...."Muryarta na rawa Cikin kunar rai!"Tace"Daman marigayi ya guje min hakan!ya guje min irin Wannan Ranar da Jawad zai Sani Kuka!"Gashi abinda ake guje min Bana gani ya faru yanzu sanadin soyyayar da nake nunawa Jawad ya kaini ga Kuka!"TABBAS duk Wanda baiji Bari ba!"yaji hoho!"

"Duk kulawa da soyyaya har gatan da nake nuna maka Jawad, Ashe akwai Ranar da zaka yaudareni? da karyan Labari,Ni ka yaudara!?"Ni kai yima karya!?"

"Wato ka zabi aboki da shawarar SA akaina!?"Saboda baka gudun zuciyata!nice ke gudun zuciyar ka da bacin ranka!"

"Na yarda na amince *TARBIYYA* ita kadai CE gatan da zaka yiwa yarou wataran ya taso Yasan gatane kayi Masa arayuwa........!"Kuka NE ya ci karfinta!"Hajiya Maryam Hakuri take bata!"

"Alh.malami ya numfasa yace kiyi Hakuri Hajiya!"agaskiya Jawad Bai kyauta ba!"Kuma ya aikata komai saboda Yasan zaki tsaya Masa domin yadda kike Sonsa kike gudun fushinsa!"

"Alhaji Nima nayi mamakin yadda Allah yabani iko na tsawata Masa a al'amarin Nan saboda Ni awurina komai Jawad yayi bana damuwa Kuma daidai Bana son in takura Masa ko in shiga rayuwar SA abinda duk yakeso ko yaga dama agurina shine daidai!"Wannan NE karou na farko da na nuna Masa bacin Raina,na tsawatarmasa a rayuwata da shi!"Har na daure na Masa hukunci!"Abinda Abbansa ya kosa yaga nafara aikatawa....tun yana da rai.

"Hajiya Maryam Tace"Yanzu dai Kinga illar sangarta yaro, Gashi Nan D'an mu ya aikata laifuka da dama sabadin haka ya ci Amana,yayi k'arya sannan ya yaudari mutane!"

Wannan ba hujja bace Domin daga farko har karshe shi ne basida gaskiya,Dan Yana takama da dukiya sai ya wulakanta talaka har Yake ganin titin nasu ne Bana Al'umma ba!"Shiyasa ta kirashi da maras *TARBIYYA* shine ya yi kokarin auren huce haushi da Daukar fansa Wannan ya Kara tabbatarwa da Nadiyan da gaske shi din bayada kirki.''

"Sai Kuma akayi Dace ya hadou da abokin da ba na kwarai ba wato Kai Saifullahi duk jirgi Daya ya dauko KU "Daman Annabi (SAW)ya ce _"Kwatankwachin Wanda ke zaune da mutanen kirki,da maras kirki,kamar yadda kake zaune da mai turaren Almiski da mai zugazugi ne,Ko dai kaji kamshi ko kuma kaji kaurin wuta.,"_
Chapter 55 · 0% Book details