Sashe 30
Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Yace Kinga garin Nan ki dinga turaren wuta da shi...Sannan Wannan na ruwan ki dinga sakawa ajikin ki da yardar Allah ba dai Wannan yarinyar ba!"Zai tsaneta!zai daina sonta!"
"Washe baki Anty Jalila tayi jiki na rawa ta amsa Tace nagode Mallam..."
"Mansura ko kashewa Mallam Ido tayi sukayi murmushi Tace yayi Mallam Aiki dai ya kammala Allah yasa muga sauyi da haske!"Magana tabi hanya...Mungode..."
"Dariya yayi yace"karkiji komai mansura kamar gobe ne..."
"Jalila Tace gaskiya Mallam ka taimakeni ka taimaki rayuwata Allah yaqarou sani..."
"Ameen...Mallam zakiru yace...."Nan SUKA tashi....Anty Jalila kudi ta dauko ta aza Masa asaman kwaryarsa...."
"GODIYA yayi Mata Sannan suka fita...Har sun fara Tafiya mansura Tace lah!"Anty Jalila Allah ya gyara Kinga nabar wayana azauren Mallam Bari nayi sauri na dauko..."
"Anty Jalila.... Dariya tayi domin tana Cikin farin ciki Tace Lalle Mansura kin cika sakarya!to maza jeki ki dauko na tare Mana adaidaita..."
"Wucewa Anty Jalila tayi bakin titin...ita Kuna mansura ta wuce zauren Mallam..."Daman karya takeyi wayarta na Jikarta ta sata a silent..."
"Dawowa tayi da sauri ta zAuna agaban"Mallam tace injin komai ya kammala!?..."
"Kwarai kuwa sai dai ki jira ki ga Aiki da cikawa...Ga Wannan ki tabbata ki Sanya shi atufafinki kije inda yake da tufafin ajikin ki...."
"Amsa mansura tayi tana murna...yayi kyau Mallam nagode ai na fahimci signal dinka Shiyasa nadawo amsar nawa tsarabar....tana dariya... "
"A inda Anty Jalila take tsaye da Mai Napep ta karasa da sauri tana dadin bakinta har suka shiga suka wuce kowanne murna fal aransa...."
***** "A wajen gidan suke zaune karkashin bishiyar cediya..."Suna tattaunawa akan abinda ke tafe da su...."
"Mallam Balarabe yace"To agaskiya ba zan iya amsar Auren Nadiyatu Ni kadai ba."Sai dai ku bari na Kira liman da makocina ayi agabansu da Kuma abokina Mallam musa...Domin sune Yan UWANA a wannan garin bani da kowa sai su...."Alhaji malami Gyaran Murya ya yi yace"Ah bakomai a kirasu,Nan ya kirasu a waya ba dadewa ba!"Sai ga liman ya qaraso Daga bisani Mallam Yusuf da Mallam musa su ka zo...Bayan an gaisa, Nan liman ya bude taro da addu'a. Sannan malami sambo ya KOMA yin jawabi Akan abinda ke tafe da su wato nemawa dansa Jawad Auren Nadiya..."
"Ba tare da wata matsala ba!"Akayi magana suka biya kudin aure naira dubu ashirin kacal kamar yadda liman ya bukata..."Sunyi zancen sadaki sai dai Malam Balarabe baiyi na'am ba!"A cewarsa yafiso sai an saka Ranar aure Sannan a karbi sadaki saboda yanzu yarinya karatu take...Kuma ba kyau yawo da sadaki aka"Sun dai amshi kudin goron baikoh NE,saboda atsayar Mata da mijin..."
"Su Alhaji malami sambo da Haji shehu sun gamsu da bayanin malam Balarabe sosai,Nan aka kammala komai suka wuce Cikin Aminchi..."Suna yabawa da halin dattako na dattijawan, Tabbas yarinyar ta samu cikakkiyar kulawa....idAn dai hakan ne hakika Jawad yayi Dace..."
"Shima Mallam Balarabe GODIYA yayi ma abokansa tare da fatan alkhari... "Cikin gidan ya shiga Yana shaidawa Innarei dukkan abinda ya faru...."
"Itama murna tayi da Sanya Alheri...."
"Kudin ya Bata ta ajiye da zummar Ranar kasuwa zai sayo goro arabawa Yan uwa da Abokan arziki...ita Kuma Nadiyatu ta sayi alawa ta rabawa kawayenta idan tadawo...."
"Da Haka suka cigaba da tattaunawa akarshe fatan Alheri sukayiwa yaran nasu..."
**************
"Hajiya khaltumi ce hakimce a kayataccen falonta tana kallon AREWA 24.. sai ga Kiran waya ko da ta Duba Alh.malami sambo NE....Da fara'ah ta amsa Kiran..."
"Bayan sun gaisa ne Alhaji malami sambo ke sanarda ita dukkan abinda ya farua tsakanin da iyayen yarinyar,ya kuma yaba da halayar mahaifinta...."
"Hajiya khaltumi taji Dadi matuka GODIYA tayiwa Alhajin tare da fatan Alheri Daga Nan Sallama sukayi da shi ta Kara godewa.."
"Da murna takira wayar Jawad tana shaida Masa yau Ranar Murna CE Anyi baikonsa da Nadiya..."
" ya nuna Jin dadinsa a fili sai dai a ransa yaji wani haushi ya Kama shi!tamkar anyi Masa Albishir da mutuwa..."Yanzu amaimakon ace zai fara auren so arayuwarsa da wacce yake so Amma Wai da makiyiyarsa zai fara kafa tarihin aure!"Kuma wacce yafi tsana Aduniya!"....Hmnnn Anya Ni Jawad ban tafka kuskure ba!!!?Ta Ina hakan zata faru!?"Karfa ka manta da kalmar da ta kiraka saboda ta rainaka!"Dole ka koyarda ita darasi arayuwarta,Dole ta Sha wuya!Hmnnnn ka nuna Mata ta tafka Babban kuskure! Zancen zucin ya dinga yi tuni ya manta da waya yakeyi......."
"mom ta fahimci ita kadai ke surutunta....Jawad watakil ya ajiye wayar,Shiyasa not Kira sunansa...Amsawa yayi Nan ta kammala duk zantukan ta da murnarta... akarshe datse Kiran tayi da zummar sai yadawo suyi celebration..."Shi Kam wani Abu yaji ratsa jikinsa,"Wasu Hawaye suka zubou masa wanda baisan ko na menene ba."
******* "Tun da muka shigo unguwar ido na suka kawo kwallah!"Fargabata ta karou!"Ina ji ajikina Babu alheri a Dawowata gidan, sai dai ba yadda Zanyi banajin zan iya Girgizawa umurninsa..."
"Duk da ya lura da irin damuwar da na shiga baisa shi ya nuna min komai ba!"A fuska ko kuma ayanayin sa..."
"A kofar get din gidan muka tsaya Mai gadi ya bude get din muka shige!"
"A hankali ya kunna kan hancin motarsa acikin gidan...Bai tsaya a mazauninta ba saitin kofar falon yabi Sannan ya kashe injin motar..."Fitowa mukayi dukkan mu...."
"Mai gadi barka dawowa Yake Mana tare da min ya jiki!?"
"Amsa Masa Yaya Saddiq din yayi.."Nima da sauki nace Masa..."Ya wuce bakin aikinsa..."
"Kayan da ke motar Yaya da su Mufeeda suka kwashe..."Tsaye nayi Ina rarraba Ido...Har sun Kai KOFA ya juyo inda yabar ni atsayen Ina Nan...."
"Ke anan din Zaki zauna!?" Yaya Saddiq yace da Dan tsawa!"
"Da sanyi nake Tafiya Ina bin bayansu har muka karasa bakin kofar, mukulli yasa ya bude...."
" _Bismillahi Tawakaltu Alallahi_ Na Fadi Sannan na shiga falon...."
"Yaran shiga sukayi sai raba ido suke ko zasu ga momyn su Amma shiru...sai kawai suka basar domin bawani sa su ajiki take ba..bare su damu...wasan su suka cigaba da yi afalon..."
"Yaya Saddiq Kichen ya fad'a Babu komai aciki sai dai ya ga kayan da akayi breakfast da su ajiye awurin....A ransa mamaki yake wato Jalila tana gidan!?"To Ina ta tafi !?"Da tunanin ya daura sanwar jallof na taliya..."
"Ko da ya dawo falon a inda nake zaune kasa atakure Nan ya sameni...Tausayi na bashi cike da rarrashi yace Nadiya Kuka fah!?"Ko baki hakura bane!?"
"Sai alokacin na fahimci kukan nake, hawayena na share Sannan nace Nidai Yaya Dan Allah ka mayarda Ni hostel da Zama, nagode da kokarin...ka saboda hankalina zaifi kwanciya acan......."Katseni yayi
"Yace bana son shirmen banza!"Kece Zaki Gaya min yadda Zanyi!!!?...ki tashi kije kiyi wanka ki sauya kayan jikinki idan kin kammala ki fito ki ci abinci kisha magani sauran idan kinje ki Cigaba da kukan ko kuma ki Bari har sai na Aiko su kifiton!...."Yaya Saddiq ya idar da maganar fuskar sa adaure..."
"A hankali na tashi nabar falon Ina Kukan xuci!!!"Dakin mu na nufa...Toilet na shiga tare da hadawa Kaina ruwan dumi nafara wanka..."
"Su Mufeed da Mufeeda ya tasa agaba sai toilet din bedroom DINSU..." wanka yayi musu tare da sauya masu Kaya...."ya gyara bedroom din da ke hargitse ya kuma wanke toilet din fes.. Sannan NE shima ya fad'a...suna fitowa tsaf acikin shiga Mai kyau...Daning area suka nufa har Ni din dake zaune falo Ina jiran fitowar su....''Yaya Saddiq ne ya zuba kowa abincin"A hankali kowa ke cin abincinsa musamman yaran sai da suka cinye tatas harda Kari...Domin rabon su da abincin kirki tun kafin muje asibitin..."Nima na ci saboda girkin yayi Dadi da Dan yaji ga marar lafiya da son Dan barkono😋ba Dan Kar nace Yaya Saddiq ya karamin ba masoyana suyi min Dariya,Mai ciwo da cin tsiya _Kamar SHATOU Dikko acicih_ Da nace akarou min...Amma Hakuri Zanyi nayi na masu ciwon🤣
************
"Ana sauke mansura a makarantar su...ita Kuma Gidansu aka nufa da ita..."Nan l
Bayan ta Sha ruwa ta huta ta labartawa Mama Atika(Hajiyar su)Labarin daga inda take da maganin da mallamin ya Bata.."Jinjinawa Jalila mama Atika tayi harda Sanya Mata Albarka tare da fatan Samun Nasara Aikin yaci..."(Hattara iyaye a dinga Sara Ana duba bakin gatari,kuso yaranku a lokacin da duniya takisu, hakan ku kisu a lokacin da taso so)
"Cike da Jin Dadi ta tafa da ita tana nuna Mata maganin...Tace Ina ALFAHARI da ke Jalila hakika Kece Kika gajeni...Saboda kina da zuciyar daukarwa kanki fansa..Basai an TAIMAKA maki ba!"Nima Nan ba zAma Zanyi ba!"Zan daura Daga inda Kika tsaya.... "Haka akeso Jalila hakika kin biyani goron haihuwarki da Nayi Allah yasa kifi hakan,."
"Ameen...Hajiyata...Jalila Tace cike da Jin Dadi suka tafe da Hajiyar..."Tana Mata bayanin duka garukan da malam zakiru ya Bata.."
"Anty Talatu da ke kwance Akan gado tana Jin su...sai dai batace masu kanzil ba!"Saboda ta lura idan har Hajiya taga Jalila agidan yanzu zata sauya masu tana yabon Jalilar...domin kawai tana damka Mata yan kudade...."Lumshe Ido tayi tana tunano ita ma alokacin da take zaune agidan nata mijin yadda Hajiyar su ke nuna Mata so...Gashi tayi nasarar kashe mata auren yanzu ta dawo gida zawarci sai wulaqanci take mata da sauran kannanta..."Hmnnnnn rayuwa kenan...wasu Hawaye suka dinga zubowa Anty Talatu..."
"Can sai ga Ga Rasheeda wato Autar gidan...Da fara'ah Tace Anty Jalila saukar yaushe..."Da Dan gyalenta a Hannu.."
"Tace yanzu na shigo na tambayeki ai,Hajiya Tace kina makota sarkin yawo!"Baki dai barin halinki uwar gulma!''..Ita Yaya Babba Naga sai bacci takeyi.." Jalila Tace tare da nuna Anty Talatun da baki tana Dariya..."
"Haba...Anty jalila!Nafa rage gulmar nan..."Nifa banason cin fuska duka yanzu gidaje shidda ko bakwai ne nake shiga kaf layin nan....Hararen wurin gadon Rasheeda tayi tare da tsaki Tace aikinta kenan ita Kuma Wannan Daga bacci sai ci!!"Ko ba Anty Tala ba uhmnnnn!"
"Hajiyar su Hannu ta baiwa Rasheeda suka tafe suna dariya"Tace auta Wannan bakin naki ko!!"Sai ta jiki taci mutuncinki, Ina gefe kin san Sarai kunnen ji ne da ita..."Yanzu hakan kwantou ake Mana Ana daukar rahoto.."
"Hakane kaam...Amma Wallahi Hajiyata. sai dai mu ci mutuncin juna Ni da ita ...rasheeda Tace tana murgudar baki...."