← Book details Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 65

Sashe 48

Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

********Tun adaren jiya da Jawad ya fita Daga sashen Amaryarsa har Yanzu da gari ya Waye bai Kara waiwayenta ba,"Yana Dakinsa Yana Kuka har bacci ya kwashe shi!"Yanzu ma yana Tashi wanka yayi ya shirya saboda Daga yau Zai fara baza makaman yaki agidansa,"

"A gefena ma tun Daren jiya da nayi kukan bakin ciki har na hakura,"Amma Ina mamaki ace Ango yayi min tsaki ya fice ban kara ganinsa har Yanzu!"Wannan wane irin rayuwa CE!?,wane laifi na aikatawa Jawad da Zai min hakan!?"ko dai duk masu Suna Jawad hakan suke Basu da kirki?

"Jikina ba Dadi na Tashi na fad'a rantsattsen bayina nayi wanka,Bayan nayi sallah,komawa baccin nayi sai kusan 11:00am na Tashi,inda aka ajiye ledojin kaji da lemuka har yanzu Suna gurin ban Kara bi ta kansu ba.

Bayan na Gama shirina tsaf Cikin wani boyel less maroon nayi kwalliya sai zuba kamshi nake, fitowa falon nayi Ina k'ara gyara guri,Nan ne nakara yiwa gidan kallo,ba karya gidan ya tsaru Kuma ya burgeni musamman falona Mai kalar maroon da milk,bedrum Dina Daya milk ,dayan Kuma maroon,ba laifi gidan yayi,Sama ko inaga gefen Jawad NE Shiyasa banyi kokarin hawa saman ba,"Bare naga duniyar da ke can,"

"Bayan na kammala goge da share-sharen K'asan nawa turare gidan nayi ta ko ina ya d'auki k'amshin turaren na Maman QURAISH Yar mutan maidugurin barno wacce ta shahara wurin hade amare da kamshin jiki,tufafi,da gida,"

"Kichen dina na shiga komai atsare,sai dai ba komai na abinci,Shiyasa na dauko flats na Koma dakina kaza Daya na bude naci na koshi sannan na aza lemu.

Daga nan falona na Koma na zauna Ina jiran su Saudat Domin nakira ta Tace min tana Nan zuwa."

"Idona na Kan t.v Ina kallo naji karar takalmi na saukowa Daga saman benen,Ban dauke idona ba!"Saboda ko ba'a fad'a nasan Jawad NE ke kokarin saukowa,"

"Da gadara yake Tafiya,sai wani kamshi Yake Sha,"Yana saukowa Yana waya,"

"Wani faduwar gaba ya riskeni!"Duk da ahankali Yake maganarsa Amma muryar da naji ce taja hankalina zuwa inda yake!"

"Cike da tashin hankali na dubeshi Tabbas Idan idona ba gizou yake min ba shi ne!"Sanye yake da wando 3quarter,da riga ba inda dressing dinsa ya sauya a yanda nasan shi a day duk da yanzu ba Suma akansa Kuma ya rage Jiki Amma tabbas shi ne,"

"Wani kallon banza yayi min up and down,Nima kauda kaina nayi Daga gareshi tare da d'aura kafata d'aya Kan d'aya cike da k'asaitah, na Cigaba da kallon t.v Nan take bugun zuciyata ya tsananta!."

"A k'aramar kujera zaman mutim d'aya ya zauna..."Yana Danna waya, Shi ma ya d'aura kafarsa D'aya Akan dayan, waya yakeyi Yana Dariya da shewa,"Sai da ya Gama ya dubeni yace Amarya Abokin Ango Saif yace agaida ke,"

"Banza nayi da shi!"

"Yace"Ke wace irin banza CE!Ana magana kina kyale mutane saboda bakida hankali ko gaisuwa ma Baki iya ba!"ko ba ayi miki tarbiyyar gaida mutane bane?

"Kallon SA nayi cike da bacin Rai!"Nace Ni zakayiwa magana cike da raini?

"Yace"Eh...Anyi maki marar tarbiyya da ke, da ace kina da ita da kin nuna min alokacin da na shigo!Amma saboda ba'a koya maki ba!"Baki San mutuncin kowa ba!kin kyale mutim,"

"Naji nagode Amma ahakan Yayan naka ya Gani ya auro Ni,"Na karashe zancen muryata na rawa saboda ban zaci Wannan ne kanen mijin nawa!"Amma Kuma shi yayan shi sunan su D'aya Jawad to tayaya hakan ta faru?na tambaya a Raina.

"Kokari Tashi nayi in shige Daga ciki sai dai gabana yasha yana kallona har munajin sautin bugun zuciyoyin mu!"

"Meye haka kabani hanya bana son rainin hankali!"Nace a fusace,"

"Tsaye Yake Yana murmushin mugunta Yana kallona..."Na bude Baki nayi magana Kenan....Sai naji saukar Mari uku zafafa!"A fuskata!"

"Cike da gadara ya qara wanka min wasu biyu...Hankalina tashe na dubeshi idona na zubda kwallah!"Hannayena Duka dafe da fuskata!"A firgice...Ina mamakin iskanci irin na kanen mijina to shi Jawad din Yana Ina NE,da baiji hayaniyar mu ba!"

"Nuna Ni yayi da yatsa yace"Daga Yanzu ki sanyawa bakinki linzami,kisan me kike fad'a Saboda na fahimci bakinki yana sakaki amasifa!Domin nafi karfinki da iskancin ki!"Ni Zaki mayarwa martani!Zaki San koni Waye! bana barin bashin gaba!"

"Kuka nakeyi Ina son bude bakina na bashi Amsa Amma na k'asa irin yadda yake min kallon tsana da takaici na tabbata Zai iya kasheni,Gashi ba kowa agidan!"Shiyasa na dinga rera Kuka Ina Kallonsa kawai!"

"Dariya yayi marar sauti yace"naji Dadi yau gaki agaban mijinki Muhammad Jawad kina Kuka Nadiya abinda nafi kaunar ganin kenan a tare dake wato bacin rai,Kinsani Kuka!kin mareni shekaru biyu da suka wuce,Gashi arana daya na mayar maki da su,harda dauri!"kisani Wannan shine Babban burina,Kuma soman tabine kalolin wuya da azaba marar Adadi na Nan tafe arayuwarki!"Zan nuna Miki nidin cikakken Maras *TARBIYYA* NE kamar yanda Kika fad'a Abaya!"

"Wani jiri ya dinga dibana Jin irin kalaman Jawad,meke faruwa!?"Mafarki NE!?ko Kuma gaske!?"Idan mafarkine Allah ya tasheni Daga nannauyan baccin da nake!"Kaina na dafe! ahankali saman falon ya dinga min yawo, Faduwa nayi k'asa somammiya!"Batare da sani na ba!"

"Murmushin Jin Dadi Jawad yayi,yace farawa ce,Nine hawan jininki!tsallaketa yayi,Saman SA ya wuce abinsa Yana sauraren wakokinsa na Hip-hop,"cike da Jin Dadi."

*'YAR MUTAN DIKKAWA CE😍*

*VOTE,SHARE,AND COMMENTS MY FANS❤*
[2/18, 7:28 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲

*NA*

*NABEELA DIKKO*

*PEN WRITERS ASSOCIATION*

*SHAFA NA 32*

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_

*Hawayen ka Littafinka ne,masu sonka ne kadai suke iya karanta shi Dai-dai.*

*Kada ka zamo kamar alawa a shanyenka,Kuma kada ka zamo kamar madacci a furzar da Kai,mafi alherin al'amurra shi ne na tsakiya.*

*Ka koyi kawaici kamar yadda kake koyon magana, Domin Alokacin da magana ta k'asa amfani kawaici zai iya Kare ka.*
_DUNIYA MAKARANTA_

______________________________________

********

"Knocking.....D'in da ake a falon k'asa ne ya dameshi ahankali ya sauko Daga saman...Turus ya ja ya tsaya!ganin mutim a kwance kamar gawa!" saboda shi har ya manta da akwai somammiya a kwance,Tsaki yayi tare da isa inda fridge din falon yake,"Robar faro ya dauko Mai Sanyin gaske,"Isa yayi gadan-gadan cike da mugunta inda take,"Kara Kwankwasa kofar akayi...."Da hanzari ya Bud'e ruwan ya dinga zuba Mata su,Ta ko'ina ajiki,"A hankali na sauke wani nannauyan Numfashi!tare da bude idona,"Ina duban jikina!"Sunan Ubangijina na kiraya!"

"Wani kallon tsana!na watsa mashi tare da kokarin Tashi sai dai kasa tashin nayi!"ga jikina da ke tsuma Yana kakkarwa saboda Sanyi!"

"Ke banza!ballagaza!!kwaila..kucaka Yar kauye!!Kafin na dawo kin fita daga falon Nan,Jawad yace tare Juyawa zuwa bakin kofar ya bude," Mai aikin momy CE tsaye!"dauke da basket din abinci ta ce inji Hajiya."Tare da gaida shi,"da ladabi,"

"Amsa Jawad yayi tare da cewa ta gaida momy,saboda baya son taga halin da Nadiya take ciki!"yaki barinta ta shigo daga ciki,' Ko da ya dawo na Tashi Daga falon,Dining ya nufa ya zubawa kansa abincin,ya hada tea da chips din da pepper soup din hanta da koda ya dinga ci yana chat har ya koshi sannan ya Cigaba da sha'aninsa,"

"NiKam da kyar na k'arasa dak'ina na kwanta Ina zubda Hawaye!"Wato dai da gaske NE,wannan guy da na tsana shine Jawad Kuma mijina,Abokinsa Saif shine ya yaudareni Yazo min amatsayin Jawad din!"Tabbas sunci amata Kuma ubangijana Zai saka min!"Sallamar su saudat CE ta dawo da Ni hayyacina da sauri na Rufe bedrum Dina,saboda naji su afalo," toilet na fad'a na wanke fuskata sannan na sauya wasu tufafi zuwa atamfa,"Ko da suka karaso bude masu kofar nayi tare da Rungume su naji dad'in zuwan su ita da Mardiyya Ina murna,"

"Abincin suka zuba min Wanda suka zo min da shi,nayi zaune muna ci.''Na lura Saudat na yawan kallona Shiyasa na basar muka dinga fira suna zolayata, Mardiyya Tace munga ango da Saif a falo,Abinci suke ci!"Ke Kika girka?"

"Momy ta Aiko Mana shi!banci ba na karashe zancen Ina kallon Saudat tare da dariyar karfin Hali wacce tafi Kuka zafi!"

"Saudat Tace Hmnnnn...Amarya

"Nan muka ci muka koshi tare d adauko sauran kajin da lemu munci sosai muna fira daga nan Mardiyya ta wuce da Yake wani Buki gareta dangin mamanta shiyasa tayi Mana Sallama ta fita ,Ya Zan daga Ni sai Saudat adakin,"

"Saudat ta kalleni Tace Nadiya kinki ki hakura ko!?"

"Nace"me Kika Gani,"Saudat!?"

"Murmushi tayi ba komai,Naga kamar Baki daina Kuka ba!"But nasan zaki daina yanzu dai muje falo ga Saif da Jawad can,sai muyi fira Mana ya fiye Mana zAma anan Inji Saudat..."

"Bazanje ba!"Na Bata Amsa atak'aice!

"Saboda me!?"ko bazaki girki ba!?"

"Eh...girkin me Zanyi nasan momy zata dinga Aiko Mana da shi,sai Nan da wani mako Zan fara aiki Domin Ina buqatar hutu!"Amma idan ke kina buqata muje ki girka.

"Dariya Saudat tayi tace"to Gimbiya Naddy..Sarkin son hutu,Gashi dai Allah ya yarda Zaki huta,Allah ya samu adanshin ki,niKam a koshe nake.

"Nace...Hmnnnn Saudat kenan wani hutun Alheri wani Kuma cuta ne kedai Allah yasa mudace Ameen."

"Dagewa Saudat tayi da sai mun fita!Shiyasa na hakura,muka nufi falon Aykuwa na shiryawa tunkarar Saif akan tambayar SA meye dalilin sa nayi min karya akan shine Jawad!"

*********"Mansura amaryar wani mako,An shigo sokoto Domin gayyatar Yan uwa da Abokan ARZIKI, musamman kawayen ta da ta Bari a school,Wasun Kuma har gidajen su ta zazzaga ta Basu alawa da katin gayyata,"
Chapter 48 · 0% Book details