← Book details Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 65

Sashe 2

Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Mama tace Allah ya saka mata da Alheri...Lantana akwai mutunci Shiyasa zaman mu ya daure da ita akwai kirki, Kuma batada munafunci Shiyasa nake sonta..."Mama tace cikin harshen nan na hausarta da Bata gama zaunawa abakinta sosai ba,

"Ameen nace."Amma Azuciata Ina tuna kazafin da Kishiyarta laraba tayi Mana,Sai dai Banda halin sanar da mamana komai akayi,Domin tun Ina karama ta horeni Akan k'aramar magana, da kawo Mata gulma da sauran kaji ka Gani, Sam Bata saurara kuma da zarar na fara fad'a Mata zata kwabe Ni tare da min fad'a akan ba halin kirki ba NE,"Shiyasa ko Yanzu nayi shiru nabar zancen Dan Nasan gwaleni zatayi,"

"Mama Tace"Bani zobou kinyi zaune kina tunani kamar Mai lissafi...."

"Murmushi nayi tare da kallon mamana cike da kauna.. "

"Nan muka dinga shan zobou,Mama tace adashe ne na kwashe...Ina son in ba malam kudi aqara sayo min kayan Nan.."Saboda naga magi da mangyada sunyi qasa kinga babu dadi,azo sayen kaya babu su."

"Haka ne mama Allah ya kara kawo kasuwa.."Nace Ina kurba kunun Aya,"

"Ameen,Ina son na baiwa malam dubu biyar ya qara wurin biya maki kudin makaranta."

"Allah sarki Mama NAGODE,Allah ya bani abinda zan muku nima..."

"Kedai Kice Allah yaqara tufa asiri kawai nidai fatana kiyi karatu Kuma ki rike addini da *TABIYYAR* da muka baki."Ko yanzu Mungode Allah domin daga ni har malaam,muna da sana'ar da muke tufawa kanmu asiri da ita Kuma akullum muna korewa bakin mu gudaji dai dai gwargadou..."

"Gaskiya ne,mama Allah yakarou arziki,Bari na d'aura sanwar dare naga lokaci na tafiya."Nace tare da azamar tashi na hura wuta."

"Mama tace"nima dai bara na kulla manja da magi da sauran kayan yajin nan kafin ki wuce Islamiyya."Yau naga cinikin ma yayi sanyi yara sun dan tsakaita shigowa to babu kudi ga Mutane sai addu'a."Inji mama

"Nace haka ne mama ko d'azu da safe Islamiyya mallam yace yanzu kusan mako daya Yana mita akawo kudi makaranta,Amma kowa shiru saboda gari yayi zafi!"

"Nan dai muka cigaba da aikin mu muna fira saboda mamana ita ce babbar Aminiyatah batayi karatun boko ba,Amma ta kwankwadi na muhammadiya,Shiyasa take da ilimi da wayewa na ainihi wayo Addini."Domin macece da taso gidan malammai batada wata makosa arayuwarta,"Magana Daya da biyu ta ambaci sunan Allah ko wa'azi."

Mallam Balarabe da abokinsa Mallam musa ne atsaye suna tattaunawa dangane da zuwan Nadiya makaranta da yake Dan gidan malam musa Yana aiki a jami'ar ta shehu shagari da ke garin na sakkwato."Takardun nema min gurbin karatu na aji daya ne."A hannun baba na."Wanda Saddik ya kawo abaiwa Baba na shine mahaifinsa Mallam Musa yaba Babana."Tare da gaya masa Saddiq yace "A tura ni makaranta mako Mai zuwa Domin kuwa dadewa daliban sun fara karatun zango na daya."Lambar wayar Saddiq Baba ya karba Yana kara godewa Abokinsa Mallam Musa abisa namijin kokarinsu."Daga Nan sallama sukayi Baba ya nufo gida."

"Bayan sallar Isha,mun kammala cin abinci,Baba yace Nadiya shiga dakina kina ganin takardu ki dauko min su."

"To,Na amsa da toh tare da cika umurnin Baba."

"Na kawo masa yace"Ki karanta ki gani Takardun ki ne,jibi zakije makaranta."Idan an kara shiryawa

"Da murna mama tace madallah, Allah abin godia Mallam wato yaron nan Saddiq ya samo mata adimishan (Admission)din!?"

"Ni kuma murna kawai nikeyi bakina yaki rufuwa sai jera Alhamdulillahi nakeyi azuciata."Ina ta Duba Takardun fuskata awashe bakina kuwa tamkar gonar auduga."Ina dariyar Mama

"Baba yace"Ay Innerie dazun Nan Mallam Musa ke bani su,Yace Saddiq din yazo to kai tsaye ne,Tare da abokan aikinsa ne sunzo ko wani taro ne a kwalejin can ta Adamu Augie."

"Oho,na gane makarantar, Nan kafin akai asibiti babba ko,Inji mama."

"Eh ita,Wai suna sauri ne Shiyasa, malam Musa ma yace saddikun yaso mu hadu Amma dai yace abani lambarsa da zamu Kira kuma yace idan Nadiya taje da ita zata iya kiransa."

"Allah sarki gaskiya yaron nan akwai kirki....Inji Innerie,ta Kara da cewa to kinji ko Nadiya ki rikesa ki masa biyayya yayanki ne."Kuma nasan ke da shi duk Kuna da hankali da sanin ya kamata Kinga bakisan Kowa ba sai shi,"

"To mama in shaa Allah."Na Bata Amsa Ina murmushi."

"Baba yace Kuma kunga cikin ikon Allah yace gwamnati ta biyawa dalibbai kudin makaranta,Yanzu kudin da zamu bata bazasu wuce dubu ashirin ba ayi duk abin ake buqata,"

"Mama tace Haba dai mallam masha Allah gaskiya naji dadi Allah Mai tufin asirin bawa, Nan ta kwance gefen Zanenta,kudi ta fito da su,ta kirga sannan tace malam ga wannan dubu biyar ne,akara ayi mata sayayyar daman dazu na kwashe adashena na gidan lantana da na fada make kwanan baya, wadannan ragowar kuma gobe kasuwa ayimin sayayyar kayan cefane kamar yadda aka saba Amma Ina da ragowar,kuka,kanwa,da barkono,su bada suba,Uw na manta da gishiri mallam"

"Dariya Baba yayi yace da kin barsu Innarei Ni kaina na hada dubu goma sha biyu Kuma Mallam Musa ya bani dubu uku tun shekaranjiya."Ke ga sai ai Miki cefanen Sana'ar ki,"

"A'ah malam ba komai ai yiwa kaine da kai da kaya duk mallakar wuya ne, Allah dai yaqara tufa asiri."shima mallam Musa Allah yasaka masa da Alheri."

"Ameen nace Ina kallon iyayena cike da tausayin su...hawayen da nike kokarin hadiyewa ne suka kwanta a fuskata."A hankali na share su kasancewar dare ne."Nace Baba!"cikin sanyi naqara da cewa Mama NAGODE Allah ya sadaku da gidan aljanna yaqara tufa asiri."ya bani ikon muku Biyayya,"

"Ameen,Sukace Dukkan su,Baba ya kalleni yace"Kinga dubu goma zan ba Innarei, gobe kije kasuwa kisayo kayan abinci da abubuwan da kike buqata."Dubu biyar ki rike hannun ki,Dubu biyar Kuma naji ance malammai nacewa ku kawo kudin ko awut(handouts)sai ki dinga saye."

"Dariya Baba ya sani Nace to Baba NAGODE," Duk kudaden Mama ya baiwa ta ajiye,"fatan su Nan dai zuwa jibi na gama komai na wuce makaranta."

"Tashi nayi na basu wuri suna ta hirar su."Ni Kuma dakina na fada envelope din da nake boye documents dina na dauko na zuba Takardu na da baba ya bani."sannan na kwanta Ina ta tunanin yadda zanyi rayuwa a jami'ar tare da tunanin irin halin da zan shiga saboda Ban taba nisa da iyayena ba idan dai ba hutu naje garin kakanni na ba dakin gari."Kasancewar makarantar sakandare ta jeka ka dawo nayi anan Argungu."Da hakan nayi addu'a kwanciya bacci barawo ya saceni."

*'Yar mutan Dikkawa ce*

🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲

*NA*

*NABEELA DIKKO*

*PEN WRITERS ASSOCIATION*

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_

*SHAFI NA UKU*
_____________________________________

"Tunda misalin karfe goma na safe na shirya tsaf ciki riga da siket na atamfa super faro kalar miyan goro da fari kayan sun amshi jikina sosai,hoda da man baki na shafa da yake Ni ba ma'abociya son kwalliya bace,nayi kyau matuka,katon hijabina na islamiya na sa ruwan kasa tare da takalmina na roba,Kudi na amsa ga mamana da yake tun kafin baba ya fita kasuwa nagama lissafin komai da zan saye."

"Shiyasa Ina amsar kudin na nufi hanyar kasuwa,Mama tayi min adawo gida lafia,Daga gida banyi wata wahalar tafiya ba, Na samu napep bakin titin makarantar nan shehu kangiwa."Tsayarda shi nayi kana na Shiga, a hanya ya samu wasu yam mata biyu wanda da ba zasu wuce sa'a ta ba,sunci kwalliya, riga da wando ne sanye ajikin su Wanda suka kame jikinsu, sai Dan karamin gyale da kowaccen su ta yafa,Duk surar jikin su abayyane take,kallo daya nayi musu na Kauda kai!"Mai napep sai kallon su yake Yana washe baki Domin irin sune suke nema."Daga ganin su suma dallibai ne Domin handouts ne rike ahannunsu sai jaka da suka rataya(Wankan gefe)."

"Tunda suka Shiga adaidaitan sahun muka gaisa da su ban kara bi takan su ba!",firar su kawai sukeyi ba kunya bare tsoron Allah firar samari suke da malammai(lecturers)...Haka dai muke zaune dasu wannan tace ke yau wane ya sayo min kaza munci, wane yayi min kaza,Kice wane ya kawo maki abi kaza gobe...nikam mamakin su nikeyi kamar ba mata ba!?"

"Ba hankali bare nutsuwa da kamun Kai,Suna aikata zantuka banza kamar marasa *TARBIYYA* wata zuciyar nace min aykam basuda *TARBIYYA* da gani....wannan rashin kamun kai yayi yawa."Allah dai ya shirya nace azuciata"...Dai dai nan aka ajiyeni babbar kofar ko kasuwar kudinsa na tambaya yace naira dari,kudin na bashi ya wuce da su..ko ajikin su suna fira suna shaan rake ga ledojin marhaba super market cike da kayan kwalaam ajikinsu,nikam da mamaki nabar wurin..."

"Addu'ar Shiga kasuwa na karatou kamar haka" _LA ILAHA ILLALLAHU WAHDAHU LA SHARIKAA LAHU LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU YUYYI WA YUMITU WA HUWA HAYYUN LA YAA MUTU WAHUWA ALAA KULLI SHAI'IN QADIR_"sannan na daura kafata na shiga a nutse na Fara abinda ya kaini har na kammala duk sayayyata."Dan dakou na nemo ya tayani daukar kayana bayan na kammala sannan na nemi adaidaita na dawo gida."

"Mamana ta Duba duk kayan da na sawo a kasuwa,daman su gari ne da indomie da sabulun wanka da ta wanki sai karamar tukunya da risho sakanhan na samo masu kyau na sayo, da sauran abubuwan da ba za a rasaba."Ni da mama sai munna muke tana sa albarka."Tace sai Baba ya dawo anuna masa Kudi sunyi albarka,nikam murna ce faal azuciyata."

"Da yamma bayan na idar da sallata ta la'asar Kuma na gama aikina sarai shirin zuwa Islamiyya nayi."

"Sallama nayi da mama na wuce,A hankali nake tafiya kaina kasa sai sauri nake saboda karfe hudu harta gota banaso na makara Domin Nice Amira wato (shugabar dalibai mata)Kuma malamar na kasa da ni, kusan aji biyu nakewa karatu bayan anyi min nawa."Bana sanin inda nake jefa kafata saboda saurin da nake gashi daga gidanmu zuwa makaranta zanyi tafiyar mintuna goma da Dan nisa kadan."A daddafe na isa ko da na Shiga ajinmu Mallam Yunus Yana karatu nan,Nima zama nayi ya karanta min batare da wani korafi ba saboda halin karya dokar makaranta ba hali na bane,Shiyasa yayi min uzuri."Dalibai da dama suna cewa Mallam Yunus Sona yake Amma nidai ban yadda ba sai dai Ina da tabbacin Yana ganin mutuncina Kuma Yana kulawa da ni saboda hazaqa ta."

"Malam yunus karatu yayi min, tare da bani umurnin naje aji biyu da uku na fada masu karatu,idan na kammala nazarin karatuna."

"Lokacin Tashi yayi anan ne nake fadawa malam yunus jibi zanje makaranta a kwalejin shehu shagari da ke sakkwato."
Chapter 2 · 0% Book details