← Book details Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 65

Sashe 50

Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tashi tayi ta daura Alwala salloli ta dinga jerowa, da nafilfili tare da karanto dukkan Addu'oin da malamin su na islamiyya ya Bata tana Kuka tana jerawa Allah kirari tare da Kai karar mansura awurinsa,Akarshe salatin manzo da istigfari da hailala,"Tayi Nan wani Sanyi da sauki ya ziyarci zuciyarta,"Sannan tayi azkhar ta kwanta."Da zummar da safe ta nemi mafita mafi sauki."

*'YAR MUTAN DIKKAWA CE😍*
[2/18, 7:28 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲

*NA*

*NABEELA DIKKO*

*PEN WRITERS ASSOCIATION*

*SHAFA NA 33*

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_

*Kayi kuskure ba shi ne matsala ba!Ka yarda kayi kuskuren shi ke da muhimmanci,Abinda yafi shi muhimmanci shi ne ka koyi darasi Daga kuskuren ka.*

*Duk mutim bawa ne,Ko ka Zama Bawan Allah,ko Kuma ka Zama Bawan shaid'an ko na son zuciya,Wanda baiyi sharan masallaci ba!Hakika Wataran ya Shari kasuwa.*

_DUNIYA MAKARANTA_
_____________________________________

Bayan gari ya Waye

"Kosawa tayi Rana Bata fito ba, da kyar ta ga karfe Sha biyu na Rana yayi, sauri-sauri, gudu-gudu,take Tafiya a sukwane da kyar ta samu abin Hawa,Tana shiga Napep din sama road,Tace ya Kaita Bayan tsawon lokaci suna Tafiya sai gasu a unguwar,Layin gidan su Umaima suka nufa,A kofar gidan aka sauketa,Nikab din ta janyo ta rufe fuskarta tare da sallamar Mai Adaidaitan,"

"SHIGA tayi gidan,sai dai Mai gadin su tare ta yayi da tambaya!"Saboda kafafunta safane baqaqe,ga Hijab har k'asa,da nik'abi,"

"Yaye Nikab din tayi,sannan ya dubeta tare da gaidata,"Nan yabata hanya ta shiga,"

"Gabanta ya fad'i ganin motar Ali agidan,A hankali ta karasa kofar falon...sai dai canja Shawara tayi sai tabi ta Bayan wacce zata sadata da hanyar Cikin gida,gefen Kichen...."

"Gabanta fad'uwa yake Kar dai yau ne d'aurin Auren can take tuna jumma'a akace..."Kofar tafara bugawa ahankali,Cikin Sa'a sai ga Umaima ta bude hannunta dauke da jug,"Ganin wacce ke bugar kofar yasa taji tsoro yanayin shigarta komai dark blue,"Yasa Umaima jin tsoro,tana Addu'oin acikin zuciyarta Kar dai Aljana CE!"

"Riketa tayi tare da yaye Nikab dinta,Tace nice Umaima karkiji tsorou!"Nice!"

"Da mamaki..ta kalleta tare da Juyawa baya Bataga kowa ba!"Janyo hannun tayi zuwa bedrum dinta,"Tace,Jalila kice da Rana tsaka!lafiya dai!?"

"Babu lafiya Umaima zuciyata tana neman rugujewa Nan zuwa Anjuma jinina zai hau!"Taimakona zakayi!?"Inji Jalila tana zubda Hawaye!"

"Murya kasa-kasa Umaima Tace"Saddiq da Ali suna Falo,Abin Sha ne Zan Kai masu da Abinci,suna jira zAuna Ina zuwa,"Ki kwantar da hankalin Jalila

"Kama hannun Umaima tayi!"Tace Dan Allah Umaima ki taimakeni Domin fad'uwa tazo dai-dai da Zama,Bude jikarta tayi tare da fitou Robar faro da Ruwa aciki,"

"Kallonta Umaima keyi..."

"Tace Umaima ki TAIMAKA min ki zubawa Saddiq ruwan Nan, acikin abin Shansa Dan Allah!"

"Tayaya Jalila gaskiya bazan iya cutar da Saddiq ba!"Kuma tare da Abban Salim suke fa abinci zasuci!"Inaji Ina Gani bazan aikata hakan ba!"Umaima Tace da Dan fushi!"

"Umaima kina nufin ahalin Yanzu Zan iya aikatawa Saddiq wani mugun Abu!?"Ko Zan cutar da shi!?"Wallahi Duk halayena da Kika sani na canja su Sarai!"Ba kamar da ba!nayi hankali Kuma duniya ta koyar da Ni darasi!"Babu cuta Babu CUTARWA acikin ruwan Nan Addu'oin ne akayi da ruwan zam-zam da ma'ul khal,na AYATUL SHIFAH,"Wallahi Umaima na karye sihiri NE,ki taimakeni mansura tayiwa Saddiq Sihirin da Zai tsaneni!!"Mallamin Islamiyyar mu Sheik Affan,Da kansa Yayi istihara Akan lamarin Kuma shine yabani Addu'oin nan na kariya ne da karya Asiri,Ni kaina tayi min Kuma Anyi Nasara nawan ya karye suran nashi"ki taimake Ni sauran bayani Zanyi maki Daga baya,Kuma Dukkan su suna iya sha Bari ma kigani,Nan Jalila ta bude Robar Tasha ruwan,Taba Umaima jiki a sanyaye tace''kema Kisha ki yarda da Ni Umaima bazan cutar da kowa ba!!"Kukane ya ci karfin Jalila ta k'asa karasa maganarta!"

"Umaima Ta hango nadama tsantsa a fuskar Jalila Shiyasa ta amshi ruwan Bismillah tayi ta Kora,Jin tsamin su ya tabbatar Mata da AKWAI ma'ul khal din aciki,"

"Nan ta koma hanyar Kichen zobou ta had'a da ruwan tare da saka kankara,Kayan Abinci ta had'a,Tana sauri taje falon,har Yanzu fira sukeyi!"

"Saddiq yace"mun d'auka an manta da mu!"Yana Dariya"

"Ayyah!kuyi Hakuri Khairat ta motsa Daga bacci ta hanani sukuni Daman yau fitina takeji,"

"Kayan Abinci ta jera masu tsaf,A dining sannan ta koma bedrum su Kuma abincin suka hau ci,"Daman Umaima tasan Aliyu baya Shan zobou Shiyasa ta had'a kadan,Nan fa Saddiq ya Shanye kusan Rabin jug,"Ali ko Drink yasha da Ruwa."

"Tun farkon had'uwar Jalila da Mansura har karshe da yadda neman maganin ya kasance tsaf, Jalila ta labartawa Umaima tana Kuka!"

"Umaima taji haushi da takaicin Jalila matuka saboda tayi sakaci!"Tun farko da ta yarda da Duk plan din mansura ba tare da ta bincika ba!"Amma kaddara ta Riga fata!"

"Jalila Tace"Yanzu Kinga Nidai Duk wani Abu da yafaru Umaima ya Riga da ya wuce!"Nidai burina Saddiq ya samu lafiya, Allah ya kubutar da shi Daga cutar tsanata!"

"Umaima Tace"Jalila tun Ranar da Saddiq ya kawo shegiyar yarinyar Nan naji batayi min ba!"Kinga hotunan su da yaran,kuma jiya fa da kanta ta turo min pics DINSU na aure gobe ma ake dinner jibi aure,"Nan Jalila ta karbi wayar Umaima tana dubawa,Hawaye na Mata zuba!"Tace lalle mansura ta cika mayaudariya!"

"Umaima Tace"Ba zamu barta ba!za tasan ta cutar da ke!"Yanzu Zan sanarda Aliyu komai Daga Nan zamu Sami mafita,Kodai Saddiq ya mayar da ke!Dakinki Kafin jibi Ranar auren!"ko Kuma ya fasa aurenta,nasan Idan yaji Wacece ita zai tsaneta saboda fuska biyu tayi Masa!"kin Shan shi Kuma ya tsani haka in fact BASAI na fad'a Miki halayenta ba kissani baya son munafunci da k'arya.

"Umaima kenan ba zai yarda ba!"zaice sharri nayi Mata!"nasan Waye Saddiq!"Nidai ya mayarda Ni ko da Zai auri mansura saboda na rike yarana na kula da su,"*

"Ajiyar zuciya Umaima tayi tare da daukar Khairat da ta Tashi Daga bacci tana jijjigata Tace"Jalila Addu'a kadai zatayi Mana maganin Wannan Matsalar!saboda Nima nagane Saddiq yayi nisa duniyar son yarinyar nan idan Allah ya nufa ya mayarda ke Jalila sai ki kula Domin ta iya kissa da abubuwa da dama Wanda ke bakida ilimi Akan su!"Ga Kuma neman magani oh ni Yan matan yanzu Abin Tsoro ne.

"Hakane komai gogewarki yanzu kiga karamar yarinya ta fiki iyawa watakil ma tafi ki sanin duniya,Aini ina Cikin tashin hankali da matsala!"Ni da mijina uban yarana amma na koma baran SA!"Kai duniya makaranta Umaima Ni Kam na samu darussan rayuwa!Dan Allah Koda Kun hadu da Nadiya Wurin auren ki nema min gafararta nayi ta kiranta da layin ta da nikeda Bana samunta akashe,kinga saboda rashin sani yasa na cutar da ita,Ni da Yan uwana,Ina Jin kunyar Ido hudu da Nadiya yarinyar kirki,"

"Murmushi Umaima tayi,Ay ina ga satin can ne Saddiq yaje Auren Nadiya,"Tayi aurenta su Mufeeda ance sun Sha shagali,"

"Haba Dai!?"Inji Jalila

"Gaskiya!"Kuma wani Dan Masu kudi ne ta aura kamar Jawad sunansa Dan Saddiq ya kawo Mana littafan aurensu da memo"

"Allah sarki Nadiya ta wajena!"ban kyautawa bautar da kikayi min ba!"Allah ya Basu zaman lafiya!"Kai zargi baiyi ba!"Ashe tana da ma mijinta!"Allah ka rabamu da sharrin zuciya!"Inji Jalila

"Ameen...Shiyasa komai nason Kyakkyawar fahimta,Daman da Dan gari Akan ci gari"Inji Umaima"

"Hakane,Yanzu goben zaku wuce Kebbi ko!?"Jalila ta Tambaya kamar tayi Kuka!"

"Bata fuska tayi,Tace"Jalila a gaskiya niKam bazanje auren Nan ba!"Ko Aliyu Hana shi zuwa Zanyi!"Daman niyyar su muje gobe ayi dinner mu kwana idan anyi walyma da daurin aure sai muzo da Yan kawo Amarya,Kinsan Kun dawo gidanku na Nan unguwar,Kuma har part dinki akwai aciki"Umaima Tace cike da zolaya,"

"Gidan Amarya mansura dai,Domin Ba'a b'ari akwashe dai-dai," niKam Ina gefe,"Hmnnnn... Yanzu har an kammala ginin nan!Allah sarki Dani aka tsara gidan Allah baiyi ashiga Dani ba!"Daman mugunta akace fitsarin fakou,Jalila Tace cikin sanyin murya,"

"In shaa Allah ko ba'a shiga da ke ba!"za'a Ida rayuwar ciki gidan da ke Jalila ki kwantarda hankalinki!"Ba'a taba canjawa tuwo suna!"Har gobe ba za'a iya yanke alakarki da Saddiq ba!"saboda AKWAI gudan jini!"

"Ajiyar zuciya tayi tare da mayar da Nikab dinta Tace"gobe Zan dawo naji yadda ake ciki,ki duba min da yanayin canjin Saddiq,sai munyi waya, Nagode! Umaima TABBAS ke Abokiyar Shawara CE,saboda kin taimakeni na yarda ciki da gaskia wuka Bata iya hudawa...Nayi danasani akan kuskure na nq wargaza alakata da ke kiyi Hakuri."Ni Zan koma Daga Islamiyya nake!"

"Itama Umaima Tashi tayi Tace"Yawwa Jalila karki damu Allah ya bamu nasara,Har kofar da ta biyo Umaima tayi Mata rakiya,Nan Jalila take tambayar Suhaila da yaran "

"Umaima Tace, Suhaila tana makaranta,yaran ko Sunje kitso da Lalle gidan k'awata Amina a rinjin sambo."Nan sukayi Sallama kowa ya wuce da abinda ke cin ransa,"

**********Kaddara ta Riga fata!"a gurin Nadiya Dan kuwa rashin mutuncin Jawad sai abinda ya karu!"Duk yanayi shigarsa ta da ayanzu hakan da ita yake yuni ya kwana acikin gida,sai Idan zai fita yake saka tufafin kirki,"

"Momy(Hajiya khaltumi)tana bani kulawa da sosai komai ta samu ta aiko min Sam batson na wahala,burinta nidai bugun zuciyarta mu kasance acikin Jin Dadi da walwala ba kalar gatan da batayi mana,"Har gidan tazo ta ganeni tare da shaida min Duk abinda nakeso arayuwa,na sanar Mata Abinci ma Tace in daina Masu aiki su dinga dafowa Ana Aiko Mana.

Amma nace Zan iya dafamana hakan tayi zancen kawo min Yan aiki nace a ah a hakan momy ta Hakuri ta barni da ayyukana.

"TABBAS Albasa batayo halin Ruwa ba!"Domin nagane momy tana da girki sosai,"

"Zama na da jawad Sai Kara lalacewa Yake,Domin ya sani agaba!"Duk wani aikin wahala burinsa ya sani!"A wuni sau uku nake Shara da mopping kaf gidan,Ga abinci Yana sani dafa kala hudu biyar ba Wai domin ya ci ba!"Acewarsa ba zai ci girkina ba kwaila Dani kazama!

Har lokacin da ya diba min na adadin zamana agidan ya rubuta ya bani a takarda yace in ajiye Domin aranar zai sakeni ya yi min korar Kare.

IDAN nayi abincin,sai da yaba masu gadi ko yace akaiwa almajiran kan layi,"hakan naketa wahala da fama da ayyukan gidan.

"Na yarda wuya Bata kisa!Domin nayi Hakuri na danne Duk irin wulaqanci!Zagi,Cin zarafina da Jawad ke min,"Ba Wanda ya sani agidan mu,hakan gefen kawayena Saudat CE tasan wani Abu,wanin Kuma Daga Ni sai shi,"
Chapter 50 · 0% Book details