← Book details Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 65

Sashe 38

Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Hmnnnn...Jalila kenan Hakuri zakiyi da Duk abinda Zakiji ko ki Gani agidan Nan,Shawarata daya ce ki kwaso kayanki,Abinda ya Kamata ki sayar asayarda shi,kudin kina samun na Jan jari,masu dama a ajiye Miki su,Ki dauko injin wankinki ki dinga wanki da abinki,Kuma Duk shegia ko katou, karki ba dama Dan za'a halaka Miki shi,abarki da cizon yatsa tunda ba mutunci ne da su ba!"

"Yanzu Anty, tala, shi kenan bazan koma gidan Saddiq ba!?"

"To Jalila,Sai naga Yanzu fa an kusan wata d'aya da faruwar abin nan ba labarin komai,kinga ko gara mu hakura,ki kwashe kayanki."har zuwa gaba idan da rabo Zaki Koma.

"Nikam gaskiya ba Zan taba fidda Rai da komawa gidan mijina ba!"Ina Sonsa Ina kaunarsa ban taba zato ko tsammanin saddiq zai iya sakeni ba a yadda nayi imanin Ina so na!"Ban zaci zai iya rabuwa dani Rana Daya ba,Ya Allah kasa ya maidani ko Domin darajar su Mufeeda!!"Jalila ta karashe maganar tana zubda Hawaye masu d'umi.

"Daina Kuka!karki sani zubda Hawaye!Ni Kaina Ina maki fatan hakan ki koma gidanki,saboda ko Yanzu mun ga izinah,kina Gani yadda Hajiya ta saka kayan dakina gaba sai da komai ya Kare!"Badan raina yaso ba!" shi ne nake jiye maki!"kinga tun hankalin ta Bai karkata Kan kayanki ba!Kiyi yadda na Gaya maki,Domin Inda shanuwar gaba Tasha ruwa ko ta baya can ta nufa.......,

"Amma Ina mansura!? ba naji Ranar kamar tace''zata dawo ba!?"

"Anty Tala,Banda labarinta tsawo mako biyu,Kuma ko na Kira wayar mansura akashe nake samunta! Tunda na Gaya Mata nayi amfani da maganin nan,Ta zo gidan nan ta sameni mukayi magana, kina gani Babu ta, ba labarinta Daga lokacin,Kuma munyi da ita, zata yiwa mallam duk bayanin komai."

"Da Naga an dauki lokaci ban ganta ba!Shi ne, na tafi da kaina,Wurinsa na Masa korafi akan magani baiyi ba,To nan nake jin wai mansura ta tafi gida saboda mamanta batada lafiya,Kuma an sace wayarta."Ina ga shine Matsalar!"Inji Mallam."

"To shi Mallam me yace da ke da kika Masa bayanin!?"Anty Talatu ta tambaya

"Yace min Yana Nan Yana iya kokarinsa ba dare ba Rana har sai anyiwa tufkar hanci,yace ba Domin tsari yayi yawa ajikin Saddiq ba da tuni an wuce gurin.Yawan ibadar da Yake da shiyasa abin yaki ya kamashi!Amma yace in Kara Hakuri!"

"Ina gaya maki Anty ban bar wurin Mallam ba, sai da ya tatseni dubu bakwai shiyasa kinka ganni Banda komai,Ranar fa dubu biyar na ba mansura ta Kai mishi,Duk fa Yan kudaden NE da nake tatsar Saddiq na cefane!"Sune na hada kansu,sai ga Matsalar Nan ta samu."Yanzu Duk sun Kare!"

"Yanzu dai Jalila ki raba kanki da yawon neman magani kina Gani duk can takalmina suka tsinke Kuma ba riba,sai tarin asarar arziki,ga dinbim zunubi,meye amfanin shirka!?" Wallahi nikam na tuba na daina saboda ko abin neman maganin banida shi."Daman can rashin ilimi ne,Yanzu Islamiyyar nan da nake zuwa na Gane Gaskiya. Addu'oin azkhar na safe da yamma sunfi duk wani magani da za a Baki Dan haka Ina maki tayin kema ki dinga zuwa islamiyya,zaman gidan nan Kara halaki zaiyi, ba uwa ba riba.

Yanzu zamuyi ta Addu'a Allah ya yafe Mana, kuskuren mu na baya, yasa mazajen mu, su maida mu ga yaranmu Domin mu Basu kulawa Mai kyau."

"Ameen,Hakane Anty,Nima nayi hankali Yanzu!"Abinda ake maki yau Nima shi ake min agidan Nan."Tun farko Mallam (Baban su) yayi Mana gudun hakan shiyasa yaso ya Gina rayuwar mu ta inganta amma Hajiya ta rusheta gashi Yanzu muna nadama Munyi Kuka har da Hawayen mu."Inji Jalila tana goge kwallah!'

"Anty Tala ma,nata Hawayen ta share Tace"Hakane Jalila Allah ya gafartawa mallam."Bari na duba abinci, kin san Da zarar ta dawo gidan nan abin masifa take nema, ta nufi Kichen Inda take dafa abinci,saboda kamar ita CE Mai aikin gidan! Kullum Cikin aiki take."

"Tsaki Jalila tayi Tace"Allah ya raba kowa da zaman irin na gidan Nan..Nima Shara Hajiya ta sani Bari na Tashi."Tsintsiya ta kwasa tun Daga bedrum din Hajiya har nasu da falon ta share tatas Ta kwashe sharar, Taje ta Fara mopping,tana Cikin gogegogen taji ta gaji Tsaki tayi ta ajiye Tace"Wallahi na gaji idan bazan ba! idan banzar can ta dawo Aiki, tayi idan zata iya,tana nufin (Rasheeda) saboda Yanzu tana fita aiki a wata firamare,shiyasa iskanci ya karu tana Jin sakon kudi Duk wata."shiyasa Daga ita sai Tahir akeyi agidan,shi Mahmud Yana MAKARANTA bawan Allah." Hajiya Atika ko sunyi tafiya ita da kawarta Anty saratu,sunje buki agarin shagari su dawo."

"Zara akace bata barin Dame,Yau da gobe Kuma Bata bar komai ba,Cikin ikon Allah, Umaimah an haihu ta samu yarinya barkallah wacce ta ci sunan mahaifiyar Aliyu wato(Asma'u)inda suke Mata alkunya da (Khairat) ."Suhaila kanwar Umaima tazo an Sha shagalin suna an Gama Mai jego da yarinya suna lafiya."

"Suhaila tana da kirki da hankali kamar yayarta,saboda tun asali sun samu tushe Mai kyau Awurin jigon rayuwar su Wato *MAHAIFIYA* Wanda *MAHAIFIN* su yayi nasarar samu a matsayin Macce Tagari ginshik'in gida."

"Tun da Suhaila tazo gidan mafi yawan ayyuka suka dawo hannunta,sanda taga yaran,Nan take kaunar Mufeeda da Mufeed suka d'arsu a zuciyarta, saboda ta lura yaran na da hankali da gasu farare kyawawa barkallah"Ita Kuma Yara shiyasa ta hade su, da su Salim da salima,"Kuma tana kula da su sosai."Rayuwar gidan hakan ta Cigaba da Tafiya lafiya qlaw,gefen su Mufeeda da Mufeed ko Tuni momy Umaima ta maye masu gurbin Momynsu,Haka Anty suhai (da Yake hakan yaran suke kiranta )ta maye masu gurbin Anty Naddy,Dama can Duk Bayan kwana d'aya ko biyu Abbansu Yana zuwa gidan cin abinci,ya kawo masu alawa,Kuma ya gaya masu Momynsu ta kusa dawowa daga tafiyar da yace tayi."A hakan suka yarda tare da jiran dawowar Jalila da tsarabar da zatayo masu ba Adadi."

"Tun lokacin da Anty jalilah ta sanar da ita cewa, Saddiq ya tsaneta,taje gidan sa yayi mata wulaqanci! taji wani Dadi ya mamayeta, saboda Aiki yayi kyau kenan, Daga ranar ta karya sim dinta, ta canja wani,Domin ta Riga da ta Gama da babin Anty Jalila kuma ta huce haushi Nadiya dan ta ci duka,Yanzu ta rufe babinsu na karshe basa gabanta."Kebbi ta tafi weekend asatin, sannan ta dawo"Wannan dawowar da tayi ta zo da Shirin tunkarar Saddiq."Saboda Haka da shirinta ta dawo na musamman,dama can Mallam ya Bata makaman Kare Dangi."

"Duk wasu (C.A) namu mun kammala yanzu jarrabawar karshen zango na biyu ke gaban mu.."Karatu nakeyi sosai saboda naji ance Yan NCE 2 sunfi kowa carryovers a kwalejin,saboda anga zasuje (TP) first semester,Shiyasa na dage ba dare ba Rana Ina karatu,tare da taimakon Naseer."Har lokacin exam yazo,muka fara Cikin ikon Allah duk jarrabawar da na zana sai na amshi tambayoyin duka kamar yadda AKE buqata,daman na shiryawa exams din duka ga Addu'a inayi."

"A yanzu ba abinda Yake damu na, sai yadda yaya Saddiq din ya canja min ga halin ko in kula da yake nunawa akaina,kamar bashi ba!"Sai dai ina masa uzuri Domin Yanzu ba shi da Mata nasan abubuwa NE suka taru su kai Masa yawa."A Cikin Raina har Tausayin SA nakeyi."Fatan mafita mafi Alheri nake Masa akullum."A gefe Kullum Sai Anty Jalila ta turo min texts din tsinuwa da Allah ya isa!"Sai nake ganin Tabbas Haka NE Domin nice sila!!!"Ba abinda nake so arayuwata face Yaya Saddiq ya mayarda Anty Jalila dakinta,shi NE damuwata,Wasu hawaye!Na share afuskata, Allah SARKI su Mufeeda ko Awanne hali suke!?" agaskiya Ina Tausayin yaran.."Nidai Allah ya daidaita Kan iyayensu su shirya Amin."Nace Azuciata cike da rashin Jin dadin Wannan kaddarar."

"Cikin Dan lokaci muka kammala exams Nan aka bamu t.p form dinmu,Domin mu zab'i Inda muke son zuwa." makaranta uku na cika mafi kusa ga unguwar mu,da ke Argungu,Sannan mukayi submitting,Ranar da muka kammala exams, Ban kwana mukayi da abokan karatun mu cike da kewar juna,."

"Muna Tafiya da su Esha zasu rakani Office din Yaya Saddiq Domin na fada Masa Zan wuce gida, na Gama exams dina."

"Ni da su tafiya MUKE muna zancen Duniya,Da Yake Yanzu Ina zuwa Office dinsa da su, shi da kansa Yasan kawayena sun tashi daga watsattsu Marasa ta Ido sun dawo masu hankali da nutsuwwla.

Dan Ni da su ba bambanci tun kan shigarmu har halayen mu iri dayane."Ko munafuki ya dubesu yasan cewa sun canja Kuma sun tuba sun daina komai,"

"A hanya muka hadu da malamin da ake Kira M.Bala,gaida shi mukayi Dukkan mu da girmamawa,Amma Idonsa na Kaina."

"Da kyar ya Amsa Mana gaisuwar muka wuce."

"Ashe kowa acikin mu cike da tsoron sa yake."

"Deeyart Tace Wallahi Ina jin haushin Dan iskan malamin nan!"Idan na ganshi kamar na halaka shi,mugun son Mata da kallon tsiya gare shi,Allah dai ya tsare mu da maitarsa."

"Esha, Tace hmnnnn Amin, inda ke kadai CE da nayi maki Barka!"Bai da mutunci, yafi na hannun Daman shaid'an bala'i!" ya rike mutim har ya manta da Takardunsa na NCE,ba komai ba nei!"A wurinsa saboda shi Sam bai san mutunci ba!"Kinsan ko ya taba turo student affairs wurin mu tun muna FARKON shigowa makarantar Nan ko kin manta!?"

Deeyart tace kwarai kuwa na tuna, a lokacin Muna Cikin hayakin mu, Ammah ko yanzu Allah ya tsare mu da masifarsa."

"Ameen,Wai Kun san me,shi fa" M.Bala da zarar yace Yana sonka kace baka Sonsa, shi kenan,Ka shiga matsala!Ga shi mugu sai a NCE 3 zai fara daukar mu...Inji Deejah

"Hmnnnn,mu akwai Dan iskan malamin da zai Mana iskanci!? sai dai yaba wasu carry-overs ba dai mu ba..ko dan k'ura tayi lafiya gaskiya mun bar recard ko Yanzu"Deeyart Tace tana Dariya."

"Murmushi nayi nace Allah ya shirya."

"Ameen,Ustaziya Nadiya Balarabe ai Mungode maki Dan sanadin ki muka dawo Hala har ake Mana kallon mutanen kirki sabanin a da.."Inji Esha tana Dariya tare da rika hannuna."

"Nan muka Isa Office din Yaya Saddiq da Sallama muka shiga muka zAuna."Tare da gaida shi

"Ko kallon mu baiyi ba fuska ba yabo ba fallasa yace"ya akayi..!?"Yana Cigaba da rubutunsa akan takarda.

"Daman Yaya na Gama zana jarrabawa ta yau,Zan wuce Kebbi shi NE nazo na Gaya maka."

"Okay,muna gaida su Baba idan kinje,yace tare da bude wallet dinsa dubu biyu ya Ciro amshi Wannan ki shiga Mota."

"Da ka barsu Yaya ina da kudi a hannuna, Nace Raina ba Dadi! saboda naga kamar Wanda akayiwa dole!"
Chapter 38 · 0% Book details