Sashe 31
Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Duk Anty Tala...na jin su da Kuma SAURAREN su Amma sai ta lafe domin idan ta tashi ta samu damar cin mutuncin Rasheeda..."Saboda ko ita ma ba baya ba!wurin rashin mutuncin da masifa,yanzu ne Kura tayi lafiya.."
"Tana Jin su aka bud'e sabuwar tashar zagin Nadiya da Saddiq, a gefe sai yabon mansura ake da irin taimakon da tayi masu tare da yabawa da halayenta..."A karshe Hajiya da Rasheeda shawarwari suka baiwa Jalila tare da koyar da ita wani babin rashin mutunci...."Sannan sukace ta tafi gidanta kawai ba wani abinda zai faru.
zuciyarta fal da murna ta fito da karfin gwuiwa har ta isa gidan..Akan murna ko canji Bata tsaya ta karba ba awurin mai Napep Tace ya wuce kawai ta bar Masa...."
_Hattara iyaye!!!....A gaskiya muna sakaci da izgili!"A yau...,"Tabbas akwai iyaye masu rayuwa irin ta mama Atika...Mu sani fa, Wannan ba rayuwa bace!" Mai Wannan hali na ko in kula Akan yara Kisani watarana zakayi Kuka da idonki biyu!😭" Wai ace lalacewar ta kai yaronka ma alfahari kake da shi idan ya iya aikata rashin mutunci,Da Rashin kunya! ko Kuma wasu halaye na banza!🤔?"Sai dai Kuma ba abin mamaki ba NE,Domin kuwa uwa Tagari kawai CE zata iya haifo d'a nagari,Kuma ita *TARBIYYA* Daga gida ake tasowa da ita,Babban tushe CE,Kuma tubali CE,Wanda tun asali ake samunta...Allah ya shirya mana Ameen_
*NA*
*NABEELA DIKKO*
*PEN WRITERS ASSOCIATION*
*SHAFI NA 22*
_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_
_KYAUTHAH CE GARE KU MANYAN WRITERS INAJI DA KU ALLAH YABAR ZUMUNCHI_
_Anty Murja Na'ikkeh_
_Hassana Dan Larabawa_
_Zuwairah(Ummu Maryam)_
_Nabila Lady(Takwarata)_
_Nabilancy luv(Tawan)_
_Kamal No Luv_
_Nordin_
_Hassan Tanko_
____________________________________
*WACECE JALILA?*
"Jalila Nura gwaranyo 'ya CE awurin Alh.Nura gwaranyo,tsohon principal na Nana girls da ke garin sokoto...."Wanda aiki gwamnati NE ya zaunar da shi sakwatto har ya Tara iyali..."Amma ainihinsu shi matarsa Yan karamar hukumar garin sokoto ne..""Mallam Nura p.c Mutumen kirki NE wanda Tuni matarsa Atika tafi karfinsa acikin gidansa.."Domin irin matan Nan NE marasa sanin ciwon kai Duk da Yana iya bakin kokarinsa wurin tsawatar Matarsa da yiwa yaransa tanadi Mai KYAU arayuwar su..."Amma Tuni ta rinjaye shi saboda shi mutum NE marar son hayaniya.." Zaman SA da Atika Zama NE na wahala da rashin sanin girma da mutuncin juna!"batasan darajar miji ba!bare aure..."Bakin cikinta ne yayi sanadin ciwonsa dake addabar rayuwarsa hawan jini..."Tunda ya kwanta ciwo ba ruwan su da Shi sai abinda suka ga damar yi agidan..Mahmud ne Mai kirki Amma Yana makaranta.."Kuma shine Mai taimakon mahaifinsa.."
"Suna da Yara biyar maza biyu Mata uku..."Anty Hajara wacce suka ma alkunya (Talatu)ita CE tafari...Itama dai rainon Atikan CE bawani kirki ne da ita ba!Rashin biyayya shine silar fitowarta agidan mijinta inda tabar yaran ta uku duka Mata..."Da taimakon Hajiya Atika Anty Talatu ta kashe aurenta saboda kawai mijinta Mustafa yaqara aure...yanzu hakan Amaryar SA Halisa ta rike yaran tamkar nata ta hadasu da yarta ta riqe su gaam.."Yayinda Ita kuma Anty Talatu ke Zaman Dana sani agidansu wato (Zawarchi..)Domin tayi biyar tsohon mijinta ya mayarda ita da sauran igiya daya amman yaki..."Kasancewar ita batayi karatu ba iya sakandare NE da ita..Shiyasa take zaune Zaman banza..."Ba aiki ba sana'a kudin gadonta Tuni suka Zama kashi..."( _Sai naji na tuna da baitin tauraruwata Allah ya jikan Rai...Barmani chogi...In take cewa "kowa ya Kama sana'a wacce Bata sana'a ta boni...Duk wacce ke zaman zaune abata ta boniyh wulaqanchi da takaichi zai ZAMOU ajalinta"_)
"Daga Anty Talatu Sai Jalila ita ke binta..."kyakkyawa CE fara Sol anyi bleaching har angaji...Tana da jiki Mai KYAU idan ba kaga Jalila tana tsiya ba! bazaka taba yarda da ko hannu akasa Mata a Baki zata ciza ba!"saboda (silent in face ce...)"Amma kaf rashin mutuncin Talatu Bata Kai na Jalila ba,domin ita copyn Atika CE harda dauri akan wasu halayen banza..."Tayi karatu a Danfodiyo sai dai har yau result yaki karbou saboda akwai carry-overs da yawa Kullum Cikin process take ko zata Amsa Amma ba labari..."
"Sai Tahir shima dai ba laifi ya dauko halin gado ba SOSAI ba!"Shima ya kammala Degree dinsa Engr.ne Yana aiki a nepa Ya fara gini sai dai Bai fara neman auren ba har yanzu....."( _Ni dai Engr.Tahir ga qawata DANMUSA itama Duk kune 'Yar mutan Dikkawa na center🤣lol_)
"Mah'mud shine na hudu agidan kuma bawan Allah acikinsu Yana da kirki matuka ga Tausayi Duk halayen mahaifin su shine ya kwaso saboda Yana da nutsuwa da hangen nesa..."Shi Kam ya fita daban agidan saboda Yana dama acikinsu."akullum Yana nunawa mahaifiyarsa da Yan uwansa akan abinda sukeyi..."Domin shi sam baya Jin Dadi..."Shima ya kammala karatun sa Mass com..Yana aiki a rima redio.."
"Rasheeda ita CE auta agidan kaf gidan idan ancire Jalila ba Mai nuna Mata rashin mutunci tayi karatun NCE ta kammala shekaru biyu kenan ba aiki ba miji..."
"Tun kafin auren Jalila mahaifin su Mallam Nura Allah ya yi masa..rasuwa,sai dai komai na auren ya tanada tun Yana kwance..."Da Yake yana da tufin asirinsa ga aikinsa da Yake kuma ga kadarori yan kudaden da Yake samu ribar feeding na makaranta da yake..."Shiyasa basu Sha wata wuya ba." suna da gadon su mai tsoka...Gashi Kuma Bayan auren na Jalila kudin sa suka fito Nan aka raba gado kowa yasha sha'aninsa..."Abin yazo masu da sauki saboda marigayi ya Gina rayuwar yaran sa da ilimi kowa yayi karatu..."Daga lokacin ne ragamar kula gidan da yaran tadawo a hannun Hajiya Atika." Daman marigayin NE ke Dan tsawatar masu Duk da ba so take ba Tana nuna bacin ranta saboda ta tsani ayiwa yaranta fad'a ko so kanka!"....."Aykuwa Daga lokacin suka Kara lalacewa gidan ya dawo gidan macce Tuni yaran suka fandare mata saboda ba Mai tsawatar masu..."Mutanen unguwa ba Mai tofawa Hajiyar Atika da yaranta Mata Alheri saboda Sam basu San meye mutunci ba.."Ko an zo nemen auren su idan aka BINCIKI mutan unguwar gaskiya suke Fadi yaran Hajiya Atika irin sakakkon ne sun kasance 'ya'yan macce Komai suke so shi sukeyi..."
"A hakan suka Cigaba da tafiyar da rayuwar su tun Bayan rasuwar mahaifin su har zuwa yanzu ba abinda ya rago saima karuwa..."Domin Hajiya Atika kwadayinta,da dogon buri...tare da son abin duniya sai gaba yakeyi..."Shiyasa har yanzu Rasheeda Bata Sami miji bA!"Itama Talatun shekaru shidda tana zawarchi har abin ya fara damunta...."Hajiya Atika ta shiga ta fita Amma Babu Labari shiru kakeji tamkar an aiki bawa kan saqou garin su..."
Wannan kenan.
*CIGABAN LABARI*
"Tunda abin nan ya faru Bata taba Jin faduwar gaba ba!"sai yanzu da ta shigo gidan kuma taga motarsa a parking place..."
"Da sassarfa ta isa bakin kofar falon..."Murd'a kan kofar tayi gam..."Alamar an rufe Daga ciki...."
"Knocking...Tayi kusan sau uku shiru Nan ta dage ta banki kofar da karfi...."
"Yaran da ke bacci falo azabure suka tashi saboda tsoro!..."
"Mufeeda ta Kama hanyar kofar tana murza idonta da magagin bacci!..."Da sauri ya fito daga Daki shima baccin Yake knocking din ya tashe shi! Yana cewa DakAta Mufeeda...kuje Dakin ku, ku karasa baccin ku inda Nadiya bara na duba..."
"Komawa tayi tsakiyar falon yana tashin su Dakin nasu su ka nufa da sauran baccin a tattare da su..."Shi Kuma kofar ya nufa ya bude...."
"Tsaye take ga alama ta kawo iya wuya!"Wani kallon banza tayi Masa ta watsar!"Shi ma kallonta yake batare da yace Mata uffan ba..."
"A fusace Tace"Dan Allah bani guri na wuce!!"
"Ki wuce kuma!?"Daga ina!?"Ina Kuma zakije!?"Saddiq ya tambaya
"Kamar ya Daga Ina nake!?Ay baka bukatar sanin inda na fito saboda baka damu da Ni ba!"Bare lafiyata!?"Ni ban tambayeka Daga Ina kake ba!?"Awanne Wuri ka kwana!?"Saini zaka tambaya!?""Ai kaine abin tuhuma da zargi ba Ni ba!Kuma Dan wulaqanci za'aje yawon banza harda yarana!?"Kai da Allah!Saddiq Wannan ba Rayuwarka bace!?"An Riga anyi maka asiri!"Nasani...To Bari kaji Abbakar! Wallahi na fad'a na kara fad'a Ni Jalila ka CI amanata Saddiq bazan yafe maka cuta ta da kukeyi!" ta karashe maganar da kumfar Baki..."
"Kokarin tureshi take ta wuce Daga ciki...Amma tureta yayi waje!"Fuskarsa a turmuke ya nunata da yatsa yace"Ke har kin Isa ince ga yadda za'ayi kice Ah'a!waye ke!?"To Bari kiji ki koma inda Kika fito saboda bakida wani sauran muhalli a gidan Nan..."Naji anyi min asiri sai me so ba yau aka Saba samin gari a abinci ba!"Idan so kuddi ta Aiko...."
"Ay Daman na Gaya maki kibi 'yan uwanki sai na nemeki!?"
"Anki abisun ai gwara ni da Azzalumai masu cin amanar aure..."Jalila Tace tana nuna SA da yatsa...."Kuma Kasan wake maka asiri ba dai Ni da Hajiyata ba!"
"Ganin mudi Mai gadi Yana kallon su yasa ya juya ya shige falon tare da kokarin rufe kofar..."
"Iya karfinta ta tattare ta bude kofar kafin yasa key....Tana shiga falon da gudunta ta fad'a Dakin yara... Shima da gudunsa ya bita Yana kwashe jallabiyar sa kada ya Fadi...."Ta Kai hannunta ta chakumou Nadiya kenan ya cafe Mata kafa ta Fadi tif agefen katifar...."Tare da fadin wash!wallahi ko zaka karye!kafar zan kasheta!!!"Da hargagi tana neman damkou Nadiya....."
"A zabure na tashi Cikin tashin hankali Naga Yaya Saddiq da Anty Jalila na kokuwa tana neman damkou Ni....saboda daman Jalila irin matan Nan Yan masifa masu karfin tsiya...."Ido na fitou da su waje ina Salati..."
"Maruka Yaya Saddiq ke sakarmata Amma Taki sakinsa....Nan yaran suka tashi suna kallonsu suna Kuka..."Nima na takure jikin bango Ina Kuka..."
"Janta Yaya Saddiq yayi tare da rufe mu adakin ta waje Ni da yaran..."Ita Kuma sai falo yayi jifa da ita Cikin fushi!" wayar Kebul din t.v ya zarou ya dinga aunawa Anty Jalila ta ko'ina tun tana DAUREWA har tafara kururuwa tana zaginsa Babu mugun furuci kazafi d alkaba'in da Bata jera Masa ba!"
"Sai da yayi Mata likis ya turata waje Cikin Jin haushi..."Yace na soki Jalila!nayi Hakuri da ke da mugwayen halayenki!Amma a karshe kazafi Kika yi min....Kin cutarda yarinyar mutane saboda me!?"Hakurina yaqare kije gidan KU na sakeki saki daya Babu Ni Babu ke!"ki fita yanzu tun bansa ayi waje da ke ba..."
ni Jalila ka wulaqanta hakan Saddiq!!? Ni zaka saka!?Wallahi sai na dauki fansa bazan barku ba!"!Zan dauki mataki mafi Muni agareku!" mugu KAWAI...."