← Book details Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 65

Sashe 24

Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Saif yace haba Jawad ba fa inda muka Saba zuwa da Kaftan NE zamu tafi ba!"Pls!Alhaji ka koma ka canja zubin wanka karka Bata Mana lokaci!"

"Murmushi yayi na gefen lebe ya dubi abokansa tare da kallon Jikinsa sarai...shafar gashin zajensa yayi tare da d'an rike gemunsa irin na matasa..."Kana yace kunga Guys Ni yau ahakan zanje birthday idan yaso Ilhaam din ta korouni.."Sai me!?"Kunga muje ko nace nafasa ahakan nake ra'ayin Tafiya!"

"Kallon JUNA sukeyi!"cike da Jin haushin canjin rayuwar Jawad din."

"Tashi Saif yayi Daga zaunen yace"Al-amin muje ko!"

"Jiki ba karfi Shima ya Mike suka bi hanya cikin rikitattar shigar su tamkar ta diyan kabilu...Bayansa Jawad yabi cikin hadaddiyar motar sa Prado suka shiga direct Miema Celebrity Hall suka nufa domin hallarta birthday din Ilham maina."Duk da ba hakan Saif da Al-amin suka so ba!"Iya kwafsawa ya kwafsa masu to meke faruwa!?"

"Tunda aka game sallar Isha Nike baza kunne akan sauraren Kiran Mallam Yunus..."Amma shiru kamar an aiki bawa garin su."

"Zaune Nayi Ina tunani na zabga uban tagumi cike da damuwa!"Ko dai malam Bilya Bai sanarwa Mallam Yunus din na dawo ba!?"

"Banyi aune ba sai Jin sanyi tafin hannun mamana Nayi tana dafani.."Zumbur na kalleta!"

"Nadiyatu!"Ta kirani."

"Na'am,Mama na Amsa

"Tunanin me kike Mallam nata kiranki Ni nama dauka ko bacci ne ya saceki saboda gajiya..."

"Daburcewa Nayi Nan dabara ta fadou min...nace bakomai mama Daman tunanin jarrabar mu nake..."

"To ke banda abinki ay Addu'a ce kan gaba adai-dai Wannan gabar,Allah ya Baku nasara in shaa Allah zakiyi nasara...muje muna son magana da ke."

"Raaaasssa!!!!gabana ya fad'i!cike da fargaba!"nace Amin..."A sanyaye na bi Bayan mamana izuwa waje Inda Baba yake zaune Yana sauraren rediyo."

"A sanyaye cike da rud'u na zauna gefen iyayena nace Baba gani."

"Yawwa,Nadiya...Daman magana nakeson muyi da ke."

"Gyaran murya yayi Sannan yace, Nadiya Ina son kibani hankalinki...Bayan tafiyarki makaranta akwai wani bawan Allah da yazo wurina amatsayin Mai neman aurenki!"

"Difffffh ....naji na dauke wuta arazane na dagou Kaina Duk da duhun dare NE sai da iyayena suka ga yanayin nawa."

"Baba ya Cigaba da cewa"To agaskia na yaba da hankalinsa da Kuma *TARBIYYAR SA* tunda har yafara neman mu amatsayin mutane na farko...kAfin ya ganki Kuma yazou maki da zancen...Kinga kuwa Wannan yaroun ya cancanci ayaba masa."

"Bugu da kari yace"Mana bazai shiga rayuwarki ba!"Har sai kin kammala karatunki duka!"Saboda baya son ya kawo maki cikas arayuwarki...Wannan uzuri nashi Kuma yayi min Dadi sai dai yace"A Gaya Miki zaku dinga waya..."

"Innerie,ki Bata wayarda ya saya mata..."

"Mamana wayar ta mikou min kamar yadda Baba ya Bata umurni..."

"Amsa,Nayi jikina Yana rawa saboda tsoro da fargaba...."murtar mama na jiyo tana cewa"Nadiya kinsan bazamu cutar da ke ba!"A gaskiya Muhammad Jawad yaron kirki ne,Kuma Yana sonki bakiga yadda yake hidima da mu ba!"Mu dai mun yaba da halayensa Duk da Kasancewar sa Dan masu kudi...baisa yaji wani abu ba!"Har mahaifiyarsa ya kawo Nan gidan Duk fa saboda ke."

"Saboda Haka Daga ke har mu Addu'a zamuyi Allah yasa Jawad ne Alheri gareki,ki bude wayar yace zai kiraki..."

"Sannan kashedina akAn wayar nan....Baba katse maganar Innerie, yace shine...Ka da Naga kinyi abubuwan Nan da ake da waya,daga ki Kira sai akiraki bana son shirmen banza!"Idan nasami kina ba dai-dai bazan karbeta Daman Ni ba so nake ba ko yanzu Alfarma CE jawad ya nema agurina..."Kinji ko!"
"kada Kaina Nayi Eh,."

"Yayi kyau ki kula sosai Allah yayi Miki Albarka..."

"Ameen,nace cike da kidima."

"Ya ce kina iya Tafiya,yau dai untuwa tayi Zane..."

"Mama ta amshe da cewa biyar gari ya tashi..."Dariya sukayi dukkan su cike da farinciki...."Mama takara da cewa"wayar Nan da aketa maita to ansamu Amma adai kiyaye Kinji saboda Kashi 70% na lalacewar *TARBIYYA* sanadin waya ne...Domin ta zamou tamkar wata uwa Mai kawo gyara asada zumunta da Kuma hanyar tabarbarewar addini da Kuma al'ada."

"Shiri Nayi Ina nazarin zantukan mama Tabbas na yarda da hakan domin nagani amakaranta...ko style akagani awaya ace shi akeso da sauran su."

"Nan dai na tashi...na shige daki Ina mamakin waye *Jawad*!?Me yake nufi da Ni!?"Shin Ni yakeso ko kuwa Iyayena!?

" *MUHAMMAD JAWAD* na Cigaba da nanatawa,A cikin Zuciyata...Wayar na bude ba laifi tayi min kyau, kuma Daga gani irin wacce ake yayi CE,Naji dadin Samun Kaina da waya..."Saboda Dan faso gari..in fita acikin duhun Kai!"Sai dai kashedi da gargadi Baba na tuna...Nan naji jikina yayi sanyi lakwas...Layin nasa acikin wayar saboda Ina ganin yadda Anty Jalila keyi shigen wayarta CE,"Bayan nasa zaune Nayi Ina shafa wayar saboda ba komai na iya ba na waya..."

"Da nagaji da Danna wayar kwanciyar Nayi Ina tunani barkatai!a Raina game da *JAWAD* Daga Nan malam yunus ne ya fadou min arai!"Bakomai gobe zan shiga Islamiyya da yamma..."Sai kuma kewar Naseer da su Esha ce ta darsu azuciyata!!!"In shaa Allah gobe zan Kira su musha fira........."

*'YAR MUTAN DIKKAWA CE😍*
[2/18, 7:25 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲

*NA*
*NABEELA DIKKO*

*PEN WRITERS ASSOCIATION*

_1st Jan 2020_😍

_Alhamdulillah Alaa kulli Halin....Da farko Ina taya Yan UWANA da Masoyana Munna shigowa shekarar bature....Sannan Ina Kara baiwa MASOYAN *TARBIYYA* Hakuri abisa korafe2nku, masu turoun min text,Kira,da comments duk Ina gani Kuma Ina GODIYA...kamar yadda kuka sani Na tsayarda rubutun ne akan wani uzuri...Amma gashi Allah ya nufa nadawo kuma Ina muku fatan Alheri..Masu Addu'ah wa kanwata muna GODIYA sosai Allah yabar zumunchi Ameen._

*Alhamdulillah,Anyi Auren Princess Yaseerah Dikko da Angonta Prince Uzairu LAFIYA, Ina maku fatan ALKHAIRI MY KANNAI Allah ya baku zaman lafia da zuriya Dayyaba Mai Albarka Ameen.*

*GODIYA TA MUSAMMAN A gareku 'Yan uwana, Dangina,Kawayenah da Kuma masoyana Na nesa da na kusa wad'anda suka zo tayamu murnar aure,Allah ya sakawa kowa da mafifichin alkharie ya mayarda kowa gidan sa lafiya ya huce gajiya Ameen,Mun gode kwarai da gaske irin sosain Nan, Allah yabar zumunchi Amin.😍

_Appee Bufday❤ My Dear Rahma m sanie, U re d first born,nd U born in first Jan,1st+1st=Special oneof the world so u r special,it's ur special day of the year,Wsh u Allah's khaira's nd Noor in ur lype,More many money in ur bnk.act...Allah ya qarou shekarou masu Albarka Amaryar 29 Feb 2020,In shaa Allah,Kuma Allah ya kawo Yara nagari masu Albarka ,Ina maki fatan Alheri MRS.ABDUL MALEEK GADO, Allah ya qara danqoun kauna ke da yayanmu Ameen.WLLP BESTIEHNAH🎂_

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_

*SHAFI NA 17*

"Tunda safe na shirya tsaf acikin shiga Mai kyau da tsari nayi kyau ba karya,Hijab Dina na Islamiyya na saka...Fitowa nayi na samu Mamana tana kokarin daura dumamen tuwo a madafa....Nace Mama zan wuce Islamiyya..."

"Kallona tayi cike da mamaki tace Nadiyatou...Tun yanzu baki ko karya ba!?"

"Mama na makara ne!"

"To...Shi kenan Allah ya tsare hanya adawo lafiya ki gaida min da yunus."

"Yawwa mama nace cike da Jin kunya saboda na lura kamar ta ganou rawar jikin da nakeyi saboda Naga malamina ne."

"Murmushi tayi tare da cigaba da aikinta Ni Kuma na wuce abina."

"A hanya ma na k'osa na ganni a kofar makarantar Nurul Huda...Sanda na shiga makarantar Sai Naga tamkar ta canja min....Farin ciki NE fal araina alokacin da na hango malam yunus a ajin mu Yana bayar da karatu...."Da Sallama na shiga ko kallona Mallam baiyi ba...Yan aji suka amsa min fuskar su asake sai ya makaranta suke min."

"Zama nayi Nima na Cigaba da daukar karatu agefena na hango wata kyakkyawa matashiya baka ga alama sabuwa CE saboda ban wayeta ba....sai faman hararata takeyi tana ya tsina fuska..."Nikam da mamaki na ke kallonta akarshe karatuna na Cigaba da yi...."

"Da lokacin tashi yayi akayi addu'ah muka tashi...Nan na Cigaba da gaisawa da Yan ajinmu da Yake Ana hutu kowa ya dawo gida yammatan makarantar har da kawata Saudat Yar gidan hajia lantana."

"Tare da ita muka fito muna firar mu....Gabas da ajin mu na samu Mallam da Wannan yarinyar atsaye Yana rike da hannun Yara biyu namiji da mace WADANDA ke matukar Kama da Wannan budurwar Mai hararena...Ras naji kohon zuciyata ya koka!"Nan take Kaina ya Sara!Ganin yadda Mallam yunus da ita ke magana cike da fara'ah...A hankali nake Tafiya idona ya rufe zuciyata tayi duhu bana ji bana gani har sai na tabbatar da abinda nake zargi!"FATANA kar ya zamou gaske!"Saudat magana take Amma bana Jin me take batu a Kai!"

"Da sanyi na Isa garesu na CE Mallam Ina kwana!"

"Mur...yasha kunu kamar Mai cin magani ko Wanda yaga wani sharri!"Ya nufoshi....Da kyar yace lafiya qlaw... Nadiyatu ya makaranta!?"Fuska ba walwalah

"A wahalce muryata na rawa nace Lafiya qlaw Mallam,saboda fargaba da tsoron da ya darsu azuciyata...."

"Ya Dan kalleni ya watsar!"Sannan ya ce Saudat duk Kuna lafiya!?"

"Saudat tace Lafiya qlaw,Mallam..."

"To....Madallah Allah ya taimaka..."Nagode ko!"yace tare da cigaba da magana yaran."

"Nikam Tuni na sandare...Saudat Amin Tace"Kana taja hannu nah saboda na kasa Motsin kirki!...muka wuce...A nan nale hango farinciki shimfide a fuskar yarinyar da muka barsu tare da Mallam yunus, WACCE bansan ko Wacece ita ba!"

"Tafiya muke Amma kukan zuci nakeyi!!na kasa jurewa sai da na tambayi Saudat shin wai Wacece wannan yarinyar da ke tare da Mallam yunus!?..."

"Hmnnnnn Nadiya kenan Nima ban santa ba!"Ko da na dawo daga Health (makaranta)na gansu tare Amma naji Ana gulma Wai ita CE zai aura har anyi masu baikoh...Sunanta BADI'ATU Lawal Wai ance takarin makka NE akwaita da ilimi ga hazaqa Tuni ta hadda CE Alqur ani Mai GIRMA ke idan tana larabci zakice balarabiya CE...Bugu da qari ta Tara sanin littafan musulunci Ina ganin akanta NE TAURARUWARKI ke neman disashewa can makarantar nan saboda malam yunus naji da ita kinsan shi da son Dalibai masu Hazaqa...."

"Innalillahi wa Inna ilaihir raju'un!!!!!"Nace a firgice!!Wani jiri ya kwasheni sai da na jini a jikin Saudat tareni saboda firgichi....A zaune ta ajiyeni na mintoci hankalina yadawo kwakwalwar Sannan tace in tashi mu wuce..."Bance komai ba sai Hawaye da ke min ratata!!!! Sauda dai da kanta ta fahimci na kamu da ciwon son Mallam alokacin da Shima ya fad'a tarkon son Badi'atu...Tabbas ta tausaya min domin son maso wani mu ke yiwa juna akace koshin wahala..."
Chapter 24 · 0% Book details