← Book details Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 65

Sashe 51

Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A cikin Yan kwanaki Duk nayi Baki na rame na lalace kamar bani ba!"Tsabar damuwa da bakin Cikin zaman agidan na neman salwantar da bugun zuciya ta!"Kuka da Addu'oin da karatun kur'ani su ne kadai ke min maganin zafin hawayena!"

"Ba karamin Dadi da nishadi yakeji ba!"Ganin Yana azabtar da Ni gashi ba Wanda ya sani,saboda Yana Dan Jin tsoron momy da kunyar su Baba,"Yanzu ko da na taimake SA,na tufawa kaina Asiri Yana cin karensa ba babbaka,sai wani Dadi Yake ji, Restaurant Yake zuwa ya ci ya koshi,yayi fari ya Kara kiba ga Kamala da kwarjini sun karou ajikinsa kamar ba shi ba,"kowa sai sa Albarka ake.

***************************
"MANSURA amaryar jibi an Sha gyara tayi wani irin kyau,sai baza sheki take!"Qawayenta na nesa Dana kusa Duk sun karasou bukin auren,"Yauma akwai event din friends Day da za'ayi a gesse phase ii da ke Birnin Kebbi."

"Fadar irin Shirin da Amarya da kawayenta sukayi fatar baki zata iya bae,saboda sunyi kyau acikin red and Arsh dress DINSU,Amarya Kam white wedding gown tasa,An cashe ba'a ko magana,Anyi hotuna mansura sai Jin Dadi take, mussamman yadda ta bada kala,A taron bukin ta haska sosai,"Abinka da 'yar son karya da bud'awa,"Kawayen nata Suma ba baya ba!sai wani karairaya ake Ana yanga!"kamar a karye dan kuri,"Haka aka Gama program din aka dawo,Sai Kuma na gobe dinner da akayiwa shiri fiye da kowanne Domin Abokan Ango zasu zo da uban gayya na mansura,"( _Nikam nace nasan gobe za'a sha kallo)_

*****************
"Tun lokacin da Nadiya tayi Masa magana Mai zarar bunu,Jikinsa Yayi Sanyi,yaji Bai KYAUTA Mata ba!"Da har ya amince da zuwan Mata amatsayin mijinta Jawad, Daga Ranar shi da Saudat suke tsare-tsaren yadda zasu gyara zaman Jawad da Nadiya su tafiyar da rayuwar su kamar kowanne Mata da miji Nagari,"Saboda Sam zaman doya da manja da ake agidan Amininsa Yana Bata Masa Rai!"Domin ya gane gaskiya Basu KYAUTA ba!rashin tunani Mai kyau ya haddasa hakan,"

"Tsoron SA Daya Kar ya rasa Rabin ransa Saudat adalilin abinda su ka Aikata, Shakka ba yayi idan asirin su ya tonu iyayen Nadiya suka ji abinda sukayi sai mama Lantana taji,hakan Idan tasan Waye shi bazata bar Saudat ta aure shi ba!"Wasu zafafan Hawaye Saif ya share tare da sauke Numfashi Daga nisan kiwon da ya fitou a duniyar tunani!"

"Allah na tuba!"Allah ka yafe Mana!"Allah Karka Bari na rasa Saudat ya Allah,shi kadai Yake Addu'oin tare da Daga hannayensa sama yana Kuka!"

****************
"Bakin ciki marar misaltuwa Baba laraba ta samu kanta aciki!"tun Ranar da D'anta Almu ke gaya Mata wani saurayi Mai Mota babba ke zuwa inda Saudat,"

"Har Kuka sai da tayi Domin kaf mazajen diyanta Babu Mai Keke bare Mota,"

"Daga RANAR bakin habaici ya mutu awurinta,Sai dai Babu kalar kazafin da batayiwa lantana da Saudat,Akan zancen saifullahi."

"Hajiya Lantana Kam ko a habar zanenta,Domin Idan da sabo sun Saba da tujarar laraba,Kasuwancinta ta Sanya agaba!"Da dadewa tagane Hassada ga Mai rabo Taki CE,saboda har Yanzu laraba da yaranta Basu Zan komai ba!"

"Amma ita Alhmdllh ga Saudat na aikin asibiti yaranta na karatunsu maza da Mata, Itama dai sana'arta takeyi,"saboda hakan NE taja kunnen su Saudat Akan su Kara kawarda Kan su Akan al'amurran laraba da yaranta,kowa ya rike Addu'a Kar Wanda ya kula su da Duk abinda zasuyi, Kar Wanda ya Koma ko yabi ta kansu."

"An saka RANAR auren Tahir da Rasheeda Rana daya,"Hajiya Atika sai shirye-shiryen buki ake,Tahir ya Kamala Gidansa Mai kyau,A unguwar Arqilla."Itama Rasheeda a tudun wada sokoto za'a ajiye a Babban Family house din gidan chairman na Yan kasuwa wato Alh.salisu Wanda akafi sani da sunan (Kai da kudi),"

Daren

"Ranar dai Jalila Bata runtsa ba!"Addu'oi da salloli take jerawa har asuba,"Tasha Kukan nadama har ta godewa Allah,Babu abinda take tunani sai sabon gidan su da ta Sanya arai,mijinta da yaranta!"( _Duniyar kenan daman abinda ka raina sai ka dawo nemansa_)

"Shima dai Saddiq, tun da yabar gidan Ali yaji Jikinsa ya sauya!"Ranar kwana yayi nafilfili da rokon Allah mafita!"Abinda ya Dade baiyi ba!"Saboda tun da Nadiya tabar gidan ya daina tashin dare,"ko yaso ya Tashi sai ya k'asa!"Sai dai yau yasamu kanshi da Tashi,"Yayi ibada sosai da tilawar Alkur'ani Mai GIRMA,Domin YUNIN yau Duka ya k'asa fahimtar meke faruwa da shi!"

*'YAR MUTAN DIKKAWA CE😍*
*SHARE,VOTE,& COMMENTS👍🏼*
[2/18, 7:28 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲

*NA*

*NABEELA DIKKO*

_________________________________

® _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
_________________________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~

https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/

*SHAFA NA 35-40*

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_

*TALAKA BA SHI NE, WANDA BAIDA KUD'I BA,TALAKA SHI NE MARAR LADABI DA TARBIYYA, ITA KUMA TARBIYYA BA'A SAYENTA, KUMA BA'A SAIDA TA, KOYONTA AKEYI*
______________________________________

"A hankali Numfashi na ya dawo gangar jikina,Sai dai ko ya tsana bana iya d'agawa saboda na lakadou sosai!"

"Ko da na Bud'e idona arba nayi da Hajiya Maryam,tana faman sha'fa fuskata!" Alhamdulillah ta CE"Tare da goge hawayenta,tana Dan murmushi Jin Dadi tare da"Kokarin tayar dani zaune,"

"A hankali na bisu da kallo!"Nan komai ya dinga dawo min,kokarin tuna komai da ya faru nake!"Sai dai kaina da ke min zafi na D'an dafe! Ina lumshe idona,"

"Momy rike min hannu tayi tana ta faman jera min sannu tare da goge min Jinin hancina da Baki da milk din gyalenta!"Batare da kyama ba!"

"Ko kallon inda Jawad Yake momy batayi,A hankali ta tayar da Ni tsaye,Tace "Hajiya Maryam mu Kaita Mota,Muje asibiti,"

"Da kyar nake tafiya Ina dingishi saboda har kofafuna Jawad ya Shure ya take Yana kwallo da Ni,A lokacin da yake mazgata!"Shiyasa naji ciwo sosai,"

"Parking place muka nufa,muna Tafiya Jawad na bin Bayan mu Yana zubda Hawaye!cike da kunya!nadama!da Tausayi,"

"Mota su momy suka sani sannan Hajiya Maryam ta shiga tana kokarin ta da Motar,Jawad ya koma gefenta,"Da sanyin murya yace"Dan Allah momy Maryam kuyi Hakuri Kada Baba malami yaji,Wallahi na tuba!"Raina NE ya baci!Domin Yarinyar Nan bansan Haka take ba!" Batada kirki!nagaji da Hakuri! shi ne ta tunzura!" Ni bansan Lokacin da nayi Mata wad'annan raunukan ba!"ya karashe zancen SA Yana sosar keya na rashin gaskiya..."

"Tsaki momy tayi,"Cikin bacin Rai!"tace haba Hajiya Maryam ko na dawo na amshi driving din!?"Dan Allah Muje aduba min lafiyar 'Yar Mutane!"

"Wani shock!jawad yaji ajikinsa! yanda momy ta turmuke fuska tana magana afusace!"kallon su Yake,Har Hajiya Maryam ta saka glass din Motar tana kokarin fita batare da sunce da shi uffan ba!"

"Nikam duk na k'osa muje inda zamu,su sallame Ni nakoma ga iyayenah,"A hanya ma Sai tattaunawa momy da Hajiya Maryam keyi Akan sanadin Wannan ta'asar,Rai ba Dadi mukaje asibitin,"Likitan ya dubani sosai tare da bani magani har na ciwon zuciya!"Saboda ya Gaya masu Ina fama da hawan jini da ciwon zuciya!"Kuma ayi Hattara! saboda zuciyata zata iya bugawa sau biyu!A lokaci daya!"Ya ce, da zarar taqara irin Wannan muguwar bugawa tofa Zan iya rasa Raina!"

"Ba Ni kadai ba!"dukkan su hankalin su ya Tashi!"mussamman momy da ke zargin d'anta NE sila,"Jiki ba kwari muka fitou asibitin,Gidan momy muka wuce,Nan Wasu Hawaye suka dinga min zuba!saboda nikam gidan mu Naso mu tafi!"Amma momy tayo gidanta da Ni,ina Jin nauyinta da kunyarta Shiyasa ba Zan iya musu da ita ba!"Naso na shaida Mata ta mayarda Ni gidanmu, Kuma ta SA danta ya sakeni Domin ko lahira bana fatan Allah ya sake sadani da macuci irin shi!"

"Kulawa nake samu sosai awurin momy da ma aikatan gidan,Har abinci ta dinga bani abaki,d'aki daya tasa Mai aiki ta gyara min tsaf,A hankali ta rakani Dakin tare da umurtar Inno ta had'a min ruwan wanka!"Ina fitowa na samu Kaya sabbi momy ta fito min da su!"Na saka,magani ta bani Nasha sannan Tace na kwanta!"Inno ce Tace" ta tsaya ta lura Dani ko da na farka Ina buqatar wani Abu!"

"Hajiya Maryam tana ganin na samu sauki sukayi Sallama da Momy Rai Babu dadi!"Saboda Duk da Basu San meye mafari ba!"Amma sun San Jawad ne Bai kyauta ba!"Da hakan dai suka rabou suna alhini abin,"

"Bayan an kammala sallar la'asar limamin masallacin Sheik Musa masani da sauran jama'ar unguwa da Yan uwa da Abokan arziki suka shaida da an sake daura auren Saddiq da Jalila akan sadaki naira dubu asirin,"

"Aliyu da waliyin Jalila Malam Habu Sunji Dadi matuka,"Haka Tahir da Mahmud godiya suka yiwa Allah."

"BARKAH jama'ar Wurin suka dinga yiwa Saddiq da bakinsa yaki rufuwa saboda Jin Dad'i,"Tare da fatan alheri."

"Suna barin Wurin direct shi da Mallam Habu,da Tahir da Mahmud,da Kuma Amininsa Aliyu,Gidan Hajiya Atika suka nufa,Nan ta dinga murna da godiya tare da masu fatan Alheri cike da kunya,"Saddiq yaqara ganin canji sosai awurin surukar Tashi da Yan uwanta,"Shima godiya yayi Mata cike da girmamawa,sannan suka bar gidan shi da Aliyu,"

"A hanya Saddiq ya Kira Lambar mahaifinsa Mallam Musa,Hankali kwance, ya bayyanawa babansa Dukkan abinda ya faru,"Har zuwa mayarda auren sa da Jalila!"Aliyu ma amsar wayar yayi ya qara yiwa Baba Musa bayanin komai tare da bashi Hakuri Akan an mayarda auren ba tareda sanin su ba!"

"Baba Musa yace"Bakomai Allah yasa hakan ne ALHERI,ya Kuma tsare gaba,"

"Ameen,Ali ya amsa Cikin murna,"tare da ba Saddiq waya"

"Baba Musa yace"Saddiq Ina son magana da Kai idan ka samu ka nutsu!"ko da zuwa da dare!NE ZANYIWA gwaggo bayanin komai!"Idan na koma gida,"

"Saddiq yace to Baba Babu damuwa nagode sai munyi waya,"

"Wani Sanyi yaji aransa,da mahaifin SA ya fahimce shi,"sabon Gidansa suka nufa Kai tsaye!"

"Ko da suka Isa su Umaima,Anty Talatu,da Rasheeda an dage,sai aikin gyaran gidan sukeyi!"Amarya Jalila ko tana jinsu ta boye!"Wai acewarta ango bazai ganta ba sai shirts,Anja Masa wankan k'wallabou,"

"Masu aikin jeren kayan furnitures din sai faman hada Wurin suke,Inda two bedrooms dinta green da orange ne,tun Kan gadajen har zuwa komai na Dakin Wannan green ne, Wannan Kuma orange ne,falonta ko dark purple NE,"tun Kan kujeru har daning da labulai kala Daya NE,A gaskiya Jalila Kam sai San BARKAH Domin ko Amarya bazata nuna Mata komai ba,"Ga Dakin Mufeed da Mufeeda Tuni Saddiq ya gyare masu an zuba masu komai na decorations da bed din Yara,"

"Babban falon gidan ma Saddiq ya zuba komai aciki da bedrum daya nashi,"
Chapter 51 · 0% Book details